Tuesday 24 July 2018

HOTUNA DA BIDIYO: Kalli yadda 'Yan sanda suka kulle gidan Saraki suka hanashi fita ko ina, Ko Kunsan yadda yayi ya fita?

Tura Wannan Zuwa Ga
Rahoton da ke shigowa yanzu na nuna cewa jami'an hukumar SARS na ofishin yan sandan Abuja sun tare shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, da safen nan sun hanashi fita daga gidansa da ke unguwar Maitama dake Abuja.


Jami'an yan sandan sun dira gidansa ne misalin karfe 6 na safe kuma sun hana kowa fitowa daga gidan.

Kana sun hana mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, fitowa yayinda suka tsare gidansa dake Apo.

Kakakin Saraki, Yusuf Olaniyonu ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Saraki ya sa an fita da motoci waje domin ya halarci gayyatar da yan sanda suka yi masa a ofishin SARS da ke Guzape, Abuja.

“Amma ‘yan sanda tuni sun gitta motocin su kuma sun jibge jami’ai kan titin kofar gidan, sun hana kowa shiga ko fita.”

“Yanzu haka da na ke maka magana ban iya fita waje, ina ciki.”

Shi ma kakakin Ike Ekweremadu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda sun kewaye gidan, sun hana shi fita.

“Ba na jin zai iya fita a yau idan aka yi La’akari da yawan jami’an da aka jibge a kofar gidan sai.”

Dama dai jiya ne R-APC suka ce alkalami ya bushe, ba za su yarda a sasanta ba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito kakakin rundunar 'yan sandan kasar Jimoh Moshood yana cewa ba shi da masaniya kan batun killace gidan shugaban majalisar da mataimakinsa.

Shi Saraki ya fita daga gidan nashi na Maitama tun da sanyin safiyar, amma dai suna gidan Ekweremadu dake Apo Legislative, amma zuwa yanzu ba a san dalilin yin kawanyar ba.

KALLI VIDEO ANAN:

DOWNLOAD VIDEO NOW


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user