Sunday 7 July 2019

HOTUNA DA CIKAKKEN TARIHIN FADAR BEGE

Tura Wannan Zuwa
Fadar Bege ya fara Nursery
(boko) dinsa kenan da
makarantar allo(Islamiyya)
mahaifiyar shi ta kuma
saka shi primary a cikin
wudil din, ya gama kuma
yayi secondary, da ya kare sai
bai samu ci gaba da
karatun zamani ba.

Fadar Bege

Domin haka ne sai ya
shagala da neman yanda
zai dauki nauyin
mahaifiyar tashi, to akan
wannan gwagwarmaya
har sukan tafi "Kudu" dashi
da Mahaifiyar tashi zuwa
irinsu "Onitsha, Enugu da
ire iren wa'annan
garuruwa suyi sayayya su
dawo, wanda da wannan
ne suke samu su dan rike
kansu tare (mahaifiyar shi )

To daga baya sai(fadar
bege) yaga ita mahaifiyar
shi girma ya fara kamata,
sai shi kadai ya dinga zuwa
yana dawowa, sai ya hutar
da Mahaifiyarsa daga wannan
abubuwa (zuwa kudu
sayayya), daga baya sai
yayi Aure inda Allah ya
azurtasu da ya mace, sai
yayi wa uwar tashi
takwara ya samata suna
"Khadija" sai ake kiranta
"Mama", to Allah baisa
Auren yayi tsawo ba sai
suka rabu da matar tasa.

A wannan shekarun
yarantar dai dai, ya koma
yana yabo Annabi(s.a.w)
kuma yana "Video
coverage".

Watarana sai fadar bege
yaci karo da wani cassete
dina (wato sharu Sani
kenan) cassete din da nayi
akan Sayyidina Rasoolullah
s.a.w, jin wannan cassete
din ya hana fadar bege
zaune da tsaye a cikin
Wudil, ya zabura yace:-
"In Allah ya yarda Sai na
nemo inda wannan
Malamin da ke maganar
Annabi s.a.w yake!!!"

Fadar Bege a Majalisi


sai Fadar bege ya zo Kano
nemana, bamu hadu ba sai
suka hadu da Sheikh
Dahiru, sai "Fadar Bege"

yake tambayar shi cewa
yazo ne neman Maulana
Sharu Sani r.t.a, sai aka ce
kwarai nan yake.

to lokacin kuma saura
kwana Uku da Maulidin
maulana sheikh Barhama
Nyass Al-kaolakhi R.T. A
(wa abqa....) sai yace wa
fadar bege to ka bari tunda
kazo baku hadu ba, to
za'ayi maolidin Maulana
Barhama Nyass RTA sai
kazo can.

sai ko fadar bege" yazo
wurin Maulidin a watan
Rajab, yazo a lokacin kayan
dake jikinsa poplin ne mai
dinkin 'yar shara da wando,
gashi dai matashi siriri
babu hula a kansa.

Daman ni (sharu Sani) a
qa'ida kowane batu indai
nine zanyi to da Manzon
Allah s.a.w nake budewa,
saboda:
"BIHEE KHUTAMUL ZHIKRUL
JAMEELU WA YUBDA'U.......


Fadar Bege


ma'ana:: Duk kyakyawar
ambato dashi ake cikawa
kuma dashi ake budewa
(Alfatih lima ughliqa wal
Khatimu limaa Sabaqa).

To tun a nan ne fa!

Da Fadar Bege yaji yanda
ake maganar Annabi s.a.w,
WALLAHI TUN DAGA NAN
YA FADI YA SUMA! (Jazb).

akayi sallar asuba, dan
wannan kamin gari ya
waye sai ya karba sai yayi
Qasidar sa na "Dan Asali" ni
kuma(sharu Sani) daga jin
Qasidar sai na dimautu
naga wannan bai kamata
in kyaleshi ba, bayan ya
gama sai na rike shi, na
tambayeshi daga ina yake???

yace min shi mutumin
wudil ne, sai ce masa dan
Allah kada ya tafi ya tsaya
mu tashi, da muka kare sai
na jashi gidan da nake yanzu
lokacin ana gini, yayi barci
ya tashi sannan sai muka
zauna, shiko sai yana ta
tambayata game da
lamarin manzon Allah
s.a.w, ni kuma sai ina ce
masa ya daga Dan Asalin
mu gyagyara, gata da
ma'ana dayawa amma
akwai abubuwan da ya
kamata zare wannan a
saka wannan.

Tun daga wannan lokaci
muke tare da shi har izuwa
yanzu, nina karfafeshi
cewar ba'a yabon Manzon
Allah s.a.w da tunani sai da
Ilimi, dan haka nace masa
kafuwa ya kamata kayida
kyau kayi Ilimi na Addini,
sai ka kasan me zaka gaya
Wa Rasoolillah s.a.w "bi
hujjatin"

To Domin haka ne sai
muka fara karatun littafai
dashi (fadar bege) da
abokansa.

Fadar Bege


Muka fara karatu tun daga
kan "Qawa'idi" mukayi
Ahdari" da "Ishmaawi"
muka gama sai muka dora
"Izziyyah" mukayi "Risaala"
Sai mukayi Hadithai"
mukayi bangare na Tarikh
"Seeratul Nabiyyi s.a.w da "
khasa'isul Nabawiy" da
"Mu'ujizaatu Rasool(s.a.w)"
muka kuma karanta
"Luggah" wadda ta shafi su
"Al-Burda(Imam Busairi)"
su "Sallu alaihi wa Sallimoo
Taslimaa" su Badamasi,
Qantarami, Ishriniyyah" da
Diwanin Maulana Sheikh
Barhama Alkaolakhi RTA da
dai sauran litattafai da
dama, domin litattafai da
mukayi dashi marigayi
(wato Fadar bege) sun kai
littafi 33(Talatin da Ukku).

Daga baya bayannan
kamar wata Hudu da
kwana goma sha ukku da
ne sai tarasu duka nace
kowa ya tsaya da karatun
littafai da yakeyi, Muna son
kowa ya kawo Qur'ani Izzu
sittin aka(hifz).

kuma ikon Allah muna
tsakiyar Qaratun ne sai
wanda ya fimu qaunar sa
ya dake kayanshi.

RASUWAR FADAR BEGE

Aminin marigayin Malam Hafizu kuma daya daga cikin wadanda suka yi jinyar marigayin  da shi , ya ce: “Ba kamar yadda mutane suke rade-radi ba, Umar ya rasu ne a sakamakon rashin lafiya wanda ya yi ta fama da ita, amma ba jifa ba ne ko hadari ko kuma wani dalili da mutane suke ta cece-kuce ba. Matsalar daukewar numfashi ne a sakamakon wani abu kamar majina da take damunsa a kirji.”

“Umar ya soma wannan rashin lafiya ne a tsai-tsaye tun ashirin da uku ga watan azumi, a inda ya same ni a gida ya ce min in kai shi asibiti, na kai shi asibiti, an duba shi an ba shi magani, amma tsawon wannan lokaci bai rabu da wannan larurar b a, sai  dai ya kwanta ya tashi; yau da lafiya gobe babu lafiya. Amma duk da haka mun yi majalisi da shi a Gombe da Nasarawa da sauransu wasu garuruwa.

Cutar dai ba ta ci karfinsa ba sai gabannin Babbar Sallah a inda ya kira aminin nasa a waya amma ya kasa magana da shi, sai matarsa Ramla ta ce asibiti za a kai shi jikin ya yi tsanani. Daga nan ya kai shi asibitin kudi  a Sharada a inda ganin yadda numfashinsa yake daukewa, suka sanya masa na’urar yin numfashi ta Odygen. Bayan wani lokaci sai asibitin suka ce musu odygen din su za ta kare cikin minti talatin sai dai su je asibitin gwammanti. Suka rubuta musu takarda, daga nan sai  asibitin Aminu Kano. A nan ana yajin aiki. Sai suka tafi Asibitin Nasarawa, a nan babu gado, A asibitin Murtala kuma nasu ya kare. Sai suka tafi Asibitin Zana watau IDH. 

Nan kuma ba su da Odygen. A takaice ce sai da suka je asibitoci biyar sai daga karshe a wani asibiti mai zaman kansa ya karbe su, aka kuma sa masa abin numfashi na Odygen. Cikin wannan hali Umar ya galabaita domin tun misalin Azahar suke yawo har sai da suka kai bayan isha.

Ya ce: “A wannan  asibiti aka yi shawarar  yi masa aiki ta makoshinsa domin fidda numfashi watau ‘bypass’. Sai dai matsalar a nan ita ce zai rasa muryarsa kuma idan aka huda zai yi kamar shekara biyar kafin ya warke. Ba a yi aikin ba amma an sa masa odygen kuma numfashinsa ya dawo. A nan ma yake ce mini shi fa mutuwa zai yi, na ce masa, a’a. Kuma Allah Ya sa har ya samu sauki, domin a wannan hali na ba shi takarda ya soma rubuta kasida wacce na ba shi amshinta. Da hannunsa ya rubuta Bismilla. Ya kuma cire abin numfashinsa.

“Bayan mun koma gida sai jikin ya rikice, ma’ana numfashinsa ya rika daukewa sai ya rika salati yana hailala a tsakani. kafafuwansa su ka yi sanyi, sai muka garzaya da shi asibitin Nasarawa ashe shirun da muka ji ashe ya cika. Muna isa wani likita wanda ya san shi, ya tabbatar mana da hakan.” Inji shi.

Umar Abdul Azeez wanda aka fi sani da Fadar Bege, mutumin Wudil ne ta Jihar Kano, kuma almajirin Sidi Shariff Sani na Jan Bulo ne.

Malam Umar  ya wallafa wakokin yabon Manzon Allah (SAW) masu yawa. Cikin wakokin da suka yi fice akwai ‘Labbaika Rasulullah’ da ‘Ahlan Wasahalan ya shugabana’ da sauransu

Kusan shekara goma sha bakwai kenan da rasuwar Fasihin mawaƙin Manzo (S.A.W), wato Umar Abdulaziz (Fadar Bege).

ALLAH YA JADDADA RAHAMA
A GARESHI AMIN.


MUKALOLI MASU ALAKA:

Download Zazzafar Kasidar Murjanatu Hafiz Abdullah Kasidar Ta dauki Hankulan Duniya Sosai

KARANTA YADDA RAYUWA TA KASANCE A AREWACHIN NAJERIYA KAFIN ZUWAN TURAWA

Karanta Takaitaccen Tarihin Sheikh Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u

Karanta Takaitaccen Tarihin Aminu Alan Waka

Domin samun sababbin waƙoƙin siyasa, waƙoƙin Soyayya, waƙoƙin bege, Hausa Comedy, waƙoƙin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
Source: Garkuwar Sufanci Da Sufaye and Aminiya


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user