Thursday 25 July 2019

Ra'ayi Riga: Tabbas Isa Ali Pantami Shi ya dace da kujerar Minista daga jihar Gombe - Haji Shehu

Tura Wannan Zuwa Ga
Duk yan siyasar da ake tsammantawa mukamin minista a jihar Gombe babu wanda ya taka rawar ganin da Sheikh Isa Ali Pantami, ya taka a sake zaben shugaban kasa Buhari na shekarar 2019.

Dr Isa Ali Pantami

Baya ga jihar Gombe, Dr. Isa Ali Pantami na daga cikin wadanda suka kula da wasu jihohin Arewa maso gabar a lokacin da ake rububin siyasa, na kasance daya daga cikin mutanen da suke karbar koke da korafe-korafen jama'a yayin zaben shugaban kasa, nasan rawar da Sheikh Isa Ali Pantami ya taka a wannan lokacin, akwai wadansu abubuwa da dama wadanda in baka cikin system din ba zaka taba sani ba, amma mu da akayi abun damu mun salkamawa Sheikh Isa Ali Pantami.

Ba iya Arewa maso gabar ba, Sheikh Isa Ali Pantami ya kashe wuta wa tafiyar shugaba Buhari a jihohi da dama, nasan lokacin da Sheikh yake zurga-zurga daga jiha zuwa jiha duk a kokarin ganin Buhari ya sake dawowa karo na biyu.

Gaskiya ne Sheikh Isa Ali Pantami bai hau mimbarin kamfe ya tallata shugaba Buhari ba, amma aikin da nasan Isa Ali Pantami ya yiwa Shugaba Buhari yayin zabe, yafi hawa mimbarin siyasa amfani. Akwai shirye-shirye  da dama na shugaba Buhari wanda Isa Ali Pantami ya dauki nauyin su a jihohin Arewa, amma ya hana a sanya sunan shi, kuma wadanda suke korafin sun halarci irin wadannan shirye-shiryen ba tare da sunsan shi yayi ba

Da yawa daga cikin yan siyasar da ake tsammantawa mukamin minista a jihar Gombe, babu wanda ya tallafawa tafiyar shugaba Buhari ta sisin kobo, kuma babu wanda ya sadaukar wa tafiyar shugaba Buhari da takai wacce Isa Ali Pantami yayi, kawai suna tare da Shugaba Buhari ne a matsayin yan jam'iyar APC.

Na jagoranci tafiyar BNMC wacce ta zakulo ayyukan shugaba Buhari domin yi masa kamfe a yanar gizo karkashin jagorancin mai taimakawa shugaba Buhari akan sababbin kafafen sadarwar zamani wato Alhaji Bashir Ahmad, duk cikin mutanen dake neman kujerar Minista babu wanda ya tallafawa reshen jihar Gombe domin ganin ta gudanar da ayyukan ta, duk aiyukan da BNMC reshen jihar Gombe tayi ta samu tallafi ne daga tsohon Ministan Muhalli Suleiman Jara, da kuma Gambo Manzo.

Banyi wannan rubutu domin fallasa ko kuma batawa wasu ba, kawai nayi wannan rubutu ne domin haska kadan daga cikin abunda ke duhu yayinda naga wasu na kwaroroton cewar Sheikh Isa Ali Pantami bai taimakawa tafiyar shugaba Buhari ba.

MU KALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ZAFAFAN SHAWARWARI 10 ZUWA GA SHUGABAN KASAR NIGERIA MUHAMMADU BUHARI

KARANTA LAIFIN DA SHUGABAN KASAR MISRAH MUHAMMAD MURSI YA AIKATA A IDON DUNIYA

KALLI YADDA SA'IN SA YA JAWO WATA TA CAKA MA WANTA WUKA YA MUTU HAR LAHIRA


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






Source: Haji Shehu

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user