Tuesday 20 August 2019

KARANTA KA JI: MASU IMANI SUNA SAMUN KANKARAR ZUNUBAI TA HANYOYI GUDA GOMA 10

Tura Wannan Zuwa Ga
1-Tuba Ingantace, sai Allah ya amshi Tubansa ya kankare masa zunubansa, domin wanda ya Tuba daga Zunubai kamar wanda bai yi laifi bane.

Wasu daga cikin Mahajjatan Kasar Kuwait Kenan

2-Ko ya nemi gafarar Allah ta hanyar yawaita
Istighfari,sai Allah ya gafarta masa.

3-Ko ya aikata wani aiki mai kyau sai Allah ya kankare masa zunubansa sanadiyyar
wannan kyakkyawan aikin.

4-Ko yan uwansa Masu Imani su nema masa Gafara,lokacin rayuwarsa ko bayan ya
rasu,Sai Allah ya gafarta masa
laifukansa,Sanadiyyar addu'ar su.

5-Ko Allah ya bashi Ladar aiyukansa
wadanda,wanda Allah zai taimakesa su
rinjayi zunubansa, sai Allah ya gafarta masa.

6-Ko Yadace da cetan Annbi Muhammad (SAW) .

7-Ko Allah ya jarabce shi da wata masifa ko
jarabawa, anan duniya sai ta zama
sanadiyyar gafarta masa zunubansa.

8-Ko Allah ya sanya masa shan wahala acikin kabarinsa, sai wahalar ta zaman sanadin kankare masa laifukan sa.

9-Ko Allah ya kankare masa zunubansa ta
hanyar,shan wahalhalu daga cikin
wahalhalun ranar alƙiyama.

10-Ko kuma Allah yayi masa Rahama daga
cikin rahamarsa guda 99 da zai cikasawa
bayinsa a ranar alƙiyama.

Dukkan wanda ya ketare wannan hanyoyin guda goma bai sami kubuta daga laifukansa
ba, kada ya zargi kowa sai kansa idan ya fada cikin azabar Allah.

@ ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ﺷﻴﺦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺭﺣﻤﻪ
ﺍﻟﻠﻪ
‏( ﺝ 10/ ﺹ 45 )

DUBA WADANNAN:

KARANTA LABARI MAI SOSA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI

KARANTA HANYOYI GUDA 10 DOMIN MAGANCE MATSALAR YAWAN FISHI

KARANTA DALILAI 6 DAKE SA MATA KASHE MAZAJEN SU

Allah kayi mana rahama daga cikin
rahamarka ka kuma gafarta mana zunuban mu baki daya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user