Sunday 8 September 2019

KARANTA MANYAN MUSTAHABBAN SALLAH GUDA ASHIRIN 20

Tura Wannan Zuwa
Mustahabban sallah na da yawa gasu kamar haka:-

1-Karatun mamu tare da karatun liman a lokacin da ake karatu a asirce.

2- Daukaka hannuwa yayin haduwa cikin kabbarar harama kawai yana daga su daura da kafadunsa.

Yayin Sujjada

3-Tsawaita karatu a sallar asuba da azzahar sai dai a sallar asuba yafi tsawo.

4- Gajarta karatun a sallar la’asar da magriba.

5- Yin karatun tsaka-tsaki a sallar Isha’i.

6-Gajarta raka’a ta biyu akan ta farko.

7-Gajarta zaman tahiyar farko akan na biyu.

8- Fadar Rabbana walakal hamdu ga mamu yayin da liman ya ce sami’allahu liman hamidahu. Haka ma mai sallah shi kadai zai fada bayan ya ce sami’allahu liman hamidahu.

9-Yin tasbihi a cikin ruku’u da sujjada.

10-Fadin (Amin) a asirce bayan kammala karatun fatiha. Ma’anar ita Amin a nan shine (ka amsa addu’armu ya Aminu) saboda an ce shi (Aminu) suna ne daga cikin sunayen Allah. To duk da haka mamu ba ya yin (Amin) a bayan liman har sai idan ya ji karatun shi liman din.

11-Yin Alkunuti, shi ana yinsa ne a sallar asuba kawai kuma bayan an kammala karatun sura daga raka’a ta biyu kafin a yi ruku’u sannan kuma a asirce ake yinsa.

Lafazin Alkunutun kuwa shine:-

ALLAHUMMA INNA NASTA’INUKA WA NASTAGFIRUKA WA NU’UMINU BIKA WA NATAWAKKALU ALAIKA WA NUS-NI ALAIKAL KHAIRU KULLUHU NASHKURUKA WALA NAKFURUKA WA NAH’NA’U LAKA WA NAKHLA’U WA NATRUKU MAN YAKFURUKA.

ALLAHUMMA IYYAKA NA’ABUDU WA LAKA NUSALLI WA NASJUDU WA ILAIKA NAS’A WA NAHFIDU NARJU RAHAMATIKA WA NAKHAFU AZABAKAL JIDDA INNA AZABAKAL BIL KAFIRINA MULHIKUN.

12-Yin addu’a bayan tahiyar karshe.

13- Gabatar da hannuwa kafin guiwoyi yayin tafiya sujada.

14-Gabatar da guiwoyi a bisa hannuwa yayin mikewa tsaye.

15-Tankwashe ‘yan yatsu uku na hannun dama a tahiya yana mai shimfide manuniya da kuma babban dan ya tsa.

DUBA WADANNAN:

KARANTA MANYAN SUNNONIN SALLAH GUDA GOMA SHA HUDU 14

KARANTA KADAN DAGA CIKIN FALALAR RANAR JUMA'A

KARANTA MANYAN FARILLAN SALLAH GUDA 14

16-Motsa manuniyarsa yana mai kudurcewa ita mai korewa ce ga shaidani.

17-Shimfide hannunsa na hagu bisa cinyarsa.

18-Sanya hannayensa akan guiwoyinsa a cikin ruku’u.

19- Sanya hannuwansa daura da kunnuwansa ko kusa da su a cikin sujjada.

20-Namiji ya nesanta tsakanin guiwar hannunsa. Da hakarkarinsa, haka da tsakanin guiwoyin kafafuwansa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user