Monday 14 October 2019

'YAN AREWA BA MU DA HANKALI BA MU DA TUNANI

Tura Wannan Zuwa Ga
A ranar 12 ga watan Agustar 2015 wani matashin Bakano mai suna Yunusa Dahiru (Yellow) dake ci-rani a kauyen Yenagoa ta jihar Bayelsa ya samu soyayyar wata budurwa da aka yi kiyasin shekarunta 14 mai Eseoghene Rita Oruru.

Barayin Yara da suke mayar da su addinin Kirista

Marubuci: Maje El-Hajeej Hotoro

Ta kuma amince zata bar addinin Kiristanci domin komawa addinin Musulunci, wannan ya sa jirgin soyayya ya dauko su zuwa jihar Kano domin daura aure.

Yayin da wannan labari ya fito fili duk wata kafar yada labarai a Kano a Arewa a Kudu a Najeriya a Afirka a Duniya sai da ya ya dawo jihar Kano domin kare hakkin wannan budurwa.

Yunusa Yellow


Gwamnan Kano da 'yan majalisar dokoki da Sarki da Malamai da duk wani mai fada aji sai da ya kasa samun lafiyayyen barci saboda Bakano ya sato yar Kudu.

Buruwar da Yunusa Yellow ya Musulintar 

Aka kama shi aka naka masa ankwa aka rika yayata hotonsa a matsayin kasurgumin dan ta'addan Duniya.


Yarinyar da aka Canzawa suna daga Aisha zuwa Chioma a addinin Kirista


Amma yau a jihar Kano an kama kananan yara an mayar da su addinin Kiristanci daga addinin Musulunci. Ana safarar su zuwa Kudu don sayar da su, amma yau wannan ba labari ba ne a kafafen yada Labaran mu.

Kowa yayi shiru tun daga manyan mu har kananan, saboda tsabar munafurci da dakikanci gami da rashin ciwon Kanmu. Muna mayar da kanmu marasa tunani marasa daraja marasa hankali.

Yunusa Yellow

Idan batu ne Ba hauka da rashin tushe na cin zarafin manyan mu ko masu mulkinmu ko malamanmu a nan za a same mu.

KARANTA WANNANKARANTA DALILIN DA YASA GWAMNATIN NIGERIA TA HANA SHIGO DA SHINKAFA TA KAN IYAKOKIN KASAR

Wallahi Mu FARKA daga barcin da muke yi mu san mutuncin kanmu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user