Tuesday 29 October 2019

KARANTA SANARWA GAME DA BATUN YUNUSA YELLOW

Tura Wannan Zuwa Ga
1. Da farko, jiya na yi waya mai tsayi da Barrister Huwaila wacce tun farko ita take kula da case ɗin Yunusa Yellow har ta nema masa beli. Ta min bayanin yadda ta cigaba da kulawa da shi kafin a sake samun matsala. Daga ƙarshe dai na bata haquri kan wasu matsaloli da misinformation da aka samu. Kuma tunda dukanmu don Allah muke yi, bai kamata mu dakata ba saboda ajizancin dan Adam. Duka aikin alkhairi yana zuwa da jarabawa iri iri. Kuma idan kana taimakon mutum ba halinsa ake dubawa ba.

Yunusa Yellow


MarubuciDr Auwal Mustapha Imam

Zamu cigaba da kokari domin Allah har ya samu 'yanci domin dalilan da suka sa aka kama shi tun farko basu chanza ba. An samu wata yarinya 'yar shekara 14 'yar jahar Delta a kwanannan ta gudu Lagos wurin saurayinta har aka ce Fulani sunyi kidnapping ɗinta, amma daga baya da ta bayyana ba a kamashi ba. Kun ga kenan dalilan ƙarar Yunusa da cigaba da tsare shi a bayyane suke.

2. Na biyu, a firar mu da ita Barrister, na mata tambaya kan wani da ya nemeni cewa ɗan majalisar tarayyya mai wakiltar Kura/GarunMalam ya gana da ita a Abuja bayan ya ji abin ya ƙara kururuwa musamman a media da kuma batun neman taimako, ta tabbatar min da cewa lallai ya neme ta kuma sun sadu sun tattauna.

3. Na uku, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya nemi sanin bayanin haƙiƙanin abinda ke faruwa dangane da wannan matsalar domin suna so su zauna a kai bayan sun ga ƙoƙon barar mu na yawo a media. To amma na masu bayanin cewa duk duniya babu wanda zai iya basu cikakken bayani kamar Barrister Huwaila, domin itace ta fi kowa aiki a kan case ɗin. Mu daga baya muka shigo saboda mu taimaka masa ya samu yanci bayan mun ji labarin halin da yake ciki a gidan yari. Na faɗa wa Barrister Huwaila sannan na basu numbarta domin su neme ta su ji bayani yadda zasu shigo ciki su taimaka.

4. Na huɗu, a jiya na samu ɗaya daga cikin waɗanda suka ce Senator Kabiru Gaya ya shiga cikin lamarin mai suna Ausman Maiduniya wanda shi ne mataimakin Sanata na musamman kan yaɗa labarai, inda na masa tambayoyi kuma ya haƙiƙance min cewa lallai sun ga abinda muke yi a media, hakan ya sa suka isar masa, shi kuma ya bada umurnin a shiga lamarin.

5. Na biyar, dangane da maganar tallafi da muke amsa saboda case ɗin, zuwa yanzu muna da jimillar kuɗi Naira dubu ɗari biyar da biyar da ɗari shida da biyar (N505,605.00). Waɗannan kuɗaɗe suna account ɗina a yanzu haka. Kuma ina sa record na duk hanyoyin sa suka shigo.

6. Na shida, dangane da abinda na rubuta a 1, 2, 3, 4 da 5: mun yanke shawarar sanar da jama'a da su dakata da turo taimakon su kan wannan matsalar saboda an samu tabbacin shigar hannayen da sun fi namu ƙwari. Ba burinmu bane a ce mune muka yi sanadiyyar fitar Yunusa, babban burinmu shine ya samu 'yanci a yafe masa laifukansa da ake zarginsa, kuma haka ya zama izna garesa. Saboda haka ne ma muke maraba da duk wanda ta dalilinsa wannan buri zai cika. Za mu saurara kuma mu cigaba da bibiya da fatan alkhairi har haka ya tabbata.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA RA'AYIN 'YAN NIGERIA AKAN GIDAN ABINCI WANDA ZAKA CI FILATE DAYA A ₦30 KACAL

'YAN AREWA BA MU DA HANKALI BA MU DA TUNANI

Karanta Illolin da Kabilar IGBO ta yiwa Sauran Kabilun Nigeria Wanda Hakan Zai Iya Haifar da Matsala anan Gaba

7. Waɗannan kuɗaɗe da gaba ɗayanmu muka tara kamar yadda na ambata a 5 suna account ɗina, kuma ko sisi ba zai fita ba sai munyi shawara da ku kan yadda za a yi da su in an sa mu nasarar fito da Yunusa domin ita Barrister Huwaila ba da su ta dogara ba kamar yadda na ambata a baya, tana da nata hanyoyin. Idan ta kama in dawowa da kowa kuɗinsa ma duka zamuyi shawara da ku, abinda kuka aminta shi za a yi. Saboda haka a dakatar da tura kuɗi don in sa mu sauƙin mayarwa idan hakan ta kama. Kuma zan cigaba da sanar da ku duka halin da ake ciki InshaAllah.

Da fatan Allah Ya bamu da cewa da nasara, kuma ya dubi niyyarmu ya biya mana buƙatunmu na alkhairi, ya kawar mana da fitintinu. Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user