Tuesday 5 November 2019

Kalli Yadda a Karrama Jaruman Kannywood a London

Tura Wannan Zuwa Ga
Fitattun jaruman fina finan Hausa, Fatima Abdullahi da aka fi sani da Fati Washa da Ali Nuhu wadanda su ka lashe kyautar gwarazan jaruman finafinan Hausa na shekarar 2019 da kuma Raham Sadau wacce ta Karbi kyautar fitacciyar Jaruma na wannan shekarar a wani gagarimin bikin finafinan Afirka da aka gudanar a Birtaniya.

Bikin Karrama Jarumai


Washa ta samu nasarar lashe kyautar ne a matsayin gwarzuwar jaruma daga fim din Sadauki wanda kamfanin Giggs Entertainments ya shirya. Karramawar ta hada da Jaruma Rahama Sadau da kuma Ali Nuhu, wanda Jamilu Yakasai ya wakilta.

Bikin wanda ake kira da Afro Hollywood Awards ya shafi karrama jaruman finafinan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka. Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din 'Sadauki, inda ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a Fim din da ta fito "Jamila" da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a "Uwar Gulma"

MAKALOLI MASU ALAKA:

Hotuna da Cikakken Tarihin Fati Washa

Babban Dalilin da Yasa Kullum Kannywood Take Ci baya akan Sauran Takwarorin ta - Yakubu Mohammed

Hotuna da Cikakken Tarihin Rahama Sadau 

A tawagar tafiyar da suka yi zuwa Birtaniya dai ta hada da Rahama Sadau, Hadiza Gabon da Kuma Jamilu Yakasai.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeSource: NORTHFLIX
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user