Wednesday 4 December 2019

KARANTA AMFANIN ZAKKA DA SADAKA A RAYUWAR BAWA MUSULMI

Tura Wannan Zuwa
Daga cikin amfani da fa'idojin Zakka, tana tsarkake mai bayar da ita, kuma tana kara masa imani, kuma tana tsarkake dukiyar ta sa, kuma tana ƙarata ta bunƙasata, kuma tana amfanar da wanda aka ba shi ita.

Amfanin Yin Zakka

Marubuci: Sheikh Aliyu Sani

1. Amma tsarkakewa da take yi wa shi mai bayar da ita, lallai tana tsarkake halayensa, tana tsarkake shi daga kwaɗayi da rowa, da munanan halaye da ɗabi'u.

Kuma tana bunƙasa halayensa, sai ya siffantu da siffofin masu karamci da kyauta da yin alheri wa mutane, kuma masu godiya ma Allah a kan abin da ya yi musu na arziki da ni'imomi, saboda ba da Zakka yana daga cikin manyan aiyukan godiya ma Allah, ita kuwa godiya ma Allah a kullum tana tare da samun ƙari daga wajensa.

Kuma Zakkar tana bunƙasa ladansa da sakamakonsa a wajen Allah, saboda Zakka da ciyar da dukiya ana ninka ladansu ninki masu yawa, gorgodon imanin wanda ya bayar da ita da Ikhlasinsa, da kuma amfaninta da ajiyeta a muhallinta (nau'in mutane (8) wadanda ake ba su Zakka).

Kuma Zakka tana fadada zuciya, ta faranta rai, kuma tana kare wa bawa bala'o'i da cutuka masu yawa.

Kuma Zakka da Sadaka suna kulla soyayya a tsakanin musulmai, suna gusar da gaba da kiyayya a tsakanin su, su mai da su su zama 'yan uwa abokan juna, saboda ɗabi'a ce ta zukata son wanda ya kyautata mata, wannan zai sa a samu haɗin kai a tsakanin musulmai su zama al'umma guda daya a kan Addinin Allah, masoya juna.

Kuma Zakka da kyauta suna sa wadanda aka ba su su yi addu'o'in da Allah yake amsawa ma waɗanda suka bayar da ita.

2. Sa'annan kuma Zakka tana bunƙasa dukiyar da aka fitar da ita daga gareta, tana kareta daga masifa da bala'i, kuma tana janyo mata albarka.

Kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya ce:

"Sadaka ba ta tauye dukiya, a'a, tana ƙarata ne".

Allah ya ce:

{ ﻭَﻣَﺎ ﺃَﻧْﻔَﻘْﺘُﻢْ ﻣِﻦْ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﻬُﻮَ ﻳُﺨْﻠِﻔُﻪُ ﻭَﻫُﻮَ ﺧَﻴْﺮُ ﺍﻟﺮَّﺍﺯِﻗِﻴﻦَ { ‏[ ﺳﺒﺄ : 39]

"Duk wani abu da kuka ciyar, to Allah zai maye muku gurbinsa, kuma shi ne fiyayyen masu arzurtawa".

3. Amma amfanin Zakka ga wanda aka ba shi ita, lallai Allah ya yi umurnin a bayar da ita ne ga mabuƙata, daga fakirai, da miskinai da waɗanda ake bi bashi, da kuma bayar da ita don 'yanta bayi, da kuma bayar da ita don gudanar da maslahohin da musulmai suke buƙatansu, don haka duk lokacin da aka ajiye Zakkar a muhallinta, aka bayar da ita ga wanda ya dace, to za a biya masu buƙatunsu da yaye musu laruran da suke ciki, fakirai za su wadata ko talaucinsu zai ragu, kuma za a samu daman gudanar da ayyuka na maslahar al'umma gaba daya.

Da ace; mawadata da masu arziki za su fitar da Zakkan dukiyoyinsu ta fiskar da aka shar'anta, a bayar da ita ga wanda Allah ya yi umurni, da an cimma maslahohin Addini da na duniya masu yawan gaske, da an kawar da talauci ko an rage shi, da an magance sharri masu yawa, na zaman banza da rashin aikin yi, da sace-sace da fashi da makami, da ha'inci da satar dukiyar al'umma, da an samu Ci gaban tattalin arziki a cikin al'ummar musulmi.


MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA MA'ANAR ZAKKA A TAKAICE CIKIN ADDININ MUSULINCI

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

Wannan ne fa ya sa Zakka ta zama daga cikin manyan abubuwan da suke nuna kyaun Shari'ar Muslunci, saboda abin da ta kunsa na janyo maslahohi da amfani wa mutane da kawar da barna da abin da zai cutar da su.

Daga littafin Sheikh Ibnu Sa'adiy (r): Al- Riyadhun Nadhirah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user