Saturday 14 March 2020

Karanta Cikakken Tarihin Oumou Sangare

Tura Wannan Zuwa
An haifi Oumou Sangare a 25 ga watan Fabrairu, 1968 a Bamako babban birnin ƙasar Mali.

Mawaƙiya Oumou Sangare

MarubuciMuhammad Lawal Barista

Sangare ‘yar na-gada ce a harkar waka, domin kuwa mahaifiyarta Aminata Daikhite, mawakiya ce, wadda ke waƙoƙi a yayin bukukuwa da kuma waƙoƙi a lokutan bukukuwan al’adu, da akan yi a ƙauyuka.

Rayuwar mahaifiyar Sangare ta fara shiga tsanani ne, lokacin da mahaifin na Sangare ya ƙaro mace ta biyu, ya kuma banzatar da mahaifiyar tata, a wannan lokacin Sangare tana ‘yar ƙarama.

Tarihi ya nuna cewa, Sangare da mahaifiyarta sun shiga tsananin rayuwa, babu mai taimaka musu.

Wannan ya tilasta mata shiga harkar waƙa don tallafar rayuwar mahaifiyarta da girma ya soma kama ta. Sangare ta fara da shiga wata gasa ne da aka sanya ta waƙa, don gano masu hikima. A lokacin tana da shekaru 16.

Allah mai iko. A cikin wannan gasa ne, baiwar Sangare ta bayyana. Kuma tun daga lokacin aka sanya ta cikin wata kwarya-kwaryar Kungiyar Mawaka da kan yi tafiye-tafiye don yin waƙoƙi, a lokutan da ake yin wasu manyan bukukuwa.

Shiga cikin wannan tawaga ta sanya baiwar Sangare ci-gaba da fitowa, har ma ta kai, wasu tafiye-tafiyen ba sa yiwuwa sai da ita. Ta fara samun ɗimbin masoyan da idan ba za ta je wajen wasa ba, to su ma ba za su je kallo ba. Bugu da ƙari, ta zama gangaran, da idan ta zo taron mawaƙa a lokacin, idan ta gama nata wasan, sai taro ya soma watsewa.

A shekarar 1989 ne, Oumou Sangare ta tattara wasu waƙoƙinta waje guda, ta fitar da album ɗinta na farko, mai suna Moussoulou. Wannan album ya sami karɓuwa, ba a Mali kaɗai ba, a faɗin Africa gaba ɗaya.

Wannan nasara, ta karɓuwa da album ɗin Sangare ya yi, ya janyo mata ƙarin farin jini, wanda hakan ya ba ta damar ƙulla kwantiragi (wato ta sanya hannu kan takardun yarjejeniya) da wasu kamfafoni don ta rika yi musu waƙe-waƙe; waɗannan kamfanoni kuwa su ne: International Record Label da World Circuit Records. Wannan kuwa ya ƙara mata girma da daraja.

Bayan fitar album ɗin ta na farko, Sangare ta ƙara fitar da wasu album ɗin har guda 4, sai dai likafa ta ci gaba, don kuwa, waɗannan album sai da suka zama sun sami karɓuwa, a faɗin duniya, ba wai Africa kawai ba. Wannan nasara kuwa, ita ta ba ta damar zama shugaba mara gafaka, wato dai ‘Unofficial Ambassador for Wassoulou Music (Wata Kungiya ce da ke da girma, tana da rassa a Southern Mali, Western Guinea da kuma Northern Cote d’Ivoire). Haka kuma tana da muƙami a wata ƙungiya mai rajin kare haƙƙoƙin mata, ‘Major Force in Africa Feminism.’

An lura kwarai da cewa, waƙoƙin Sangare sun fi mayar da hankali kan abin da ya shafi mata, da batu kan haƙƙoƙinsu.

Wasu na ganin cewa, ta samu wannan tasirin ne ta dalilin banzatarwar da mahaifinta ya yi musu (ita da mahaifiyarta). Wasu kuma na kallon abin da cewa, kawai ɗabi’a ce ta ɗiya mace, wadda ta fi son jinsinta.

Ko ma dai wane dalilin ne ya sa Sangare fifita jinsin mata a waƙarta, ya tabbata cewa, waƙoƙinta suna da ƙarfi kan ‘Matanci’ abin da Bature ke kira da ‘Feminism.’ Don takan yi waƙa a kan ‘yancin mace na zaɓar abokin rayuwa, a maimakon auren dole; da waƙoƙi don nuna rashin goyon bayan zaman mace fiye da ɗaya, a ƙarƙashin namiji ɗaya; da waƙoƙi don nuna damar da mata ke da shi na a dama da su a harkokin rayuwa, musamman riƙe muƙamai da sauransu.

Oumou Sangare yayin gabatar da wani Wasa

Oumou Sangare ta samu kyaututtuka da lambobin yabo da dama daga ƙasashen duniya. Wasu daga cikinsu su ne: Lambar ‘Jagorantar Harkokin Fasaha da Ƙirƙira’ daga Gwamnatin Faransa a shekarar 1998; sai gasar waƙa da ta cinye a shekarar 2001 wadda UNESCO ta sanya, mai suna ‘UNESCO Music Prize’ Sunanta ya shiga cikin wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya, masu aikin kula da aikin samar da abinci da amfanin gona a 2003, wato ‘Official Ambassador of the Food and Agriculture Organization of the United Nations’
Bugu da ƙari a shekarar 1993, album ɗinta mai suna ‘Ko Sira’ shi ya cinye gasar Ƙasar Turai, ‘European Award’ wanda album ɗin ya zama album mafi karɓuwa a Duniya ‘World Music Album of the Year.’

Himma ba ta ga rago. Bayan waƙa, Sangare ta shiga cikin harkokin kasuwanci da saka hannun jari a duniya. Ta mallaki wani ƙaton Hotel a Birnin Bamako. Kuma tana a wata katafariyar gona a birnin.

Da yake likkafar Sangare ta yi gaba, sun kulla yarjejeniya da wani kamfani a China da za su samar da wata mota mai suna ‘Oum Sang’.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: