Saturday 9 November 2019

Mafi Yawancin Mazajen da Suke Son 'Yam Matan Kannywood Mayaudara Ne - Jaruma Maimuna Muhammad

Tura Wannan Zuwa
Jarumar fina finan Hausa Maimuna Muhammad wacce akafi sani da Maimuna Wata Yarinya, ta yi korafin cewa mafi yawan mazajen da suke zuwa wajen su da sunan aure mayaudara ne amma sai su fake da soyayya domin biyan bukatar su.


Jaruma Maimuna Muhammad

Maimuna ta bayyana hakan ne a lokacin da suke wata tattaunawa da wakilin mu a game da irin kallon da ake yi wa mata yan fim na mayar da hankalin su kan rayuwar duniya fiye da lamarin aure, duk da dumbun masoyan da ake ganin suna da su.

Inda ta kada baki ta ce, "To gaskiya ba haka bane saboda mu yan fim mata muna fama da wani abu guda daya wanda ba kowa ya ke lura da hakan ba kuma mutane basa mana uzuri.

A gaskiya mafi yawancin maganar da mazaje suke zuwar mana da ita cewa suna son mu, wallahi kaso casa`in da tara cikin dari karya suke, Sai mace ta tara samari sun Kai dari, da wuya ta fitar da guda biyu da suke son ta tsakani da Allah, sauran duk na banza ne”.

Jarumar ta kara da cewa “Zuwa suke da abinda bai dace ba idan kin basu hadin kai kuma sai su yi tafiyar su. Wannan ba sai lallai matan fim ba matsalace da mata suke fuskanta a wannan zamanin da muke ciki.

Domin haka duk masu fadar cewar mun ki yin aure ko mun dade ba mu yi ba to wanan itace matsalar da muke fuskata, musamman ma mu yan fim ba wai bama son auren bane muna son mu yi sabo da shine zaman lafiyar ya mace ta gari.

Mazan da za su so mu tsakani da Allah ne ba su da yawa, amma ko yau mijin aure yazo a shirye mu ke in har masu son mu ne tsakani da Allah ba mayaudara ba." Inji Jarumar

Tun da dai Maimuna ta gano wannan matsalar wanni Kira za ta yi ga matan musamman yan fim da suke fuskantar Wannan matsalar?

"To ya kamata dai mu zauna mu yi wa kan mu fada tun da mun san mafi yawan maza a yau ga yadda su ke, don haka mu rike mutuncin mu da darajar da Allah ya ba mu ta 'ya'ya mata, ta haka ne kawai za mu nemawa kan mu 'yanci a wajen mazaje masu mummunar manufa a kan mu.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Babban Dalilin da Yasa Kullum Kannywood Take Ci baya akan Sauran Takwarorin ta - Yakubu Mohammed

SHIN SHIGOWAR JARUMA MARYAM YAHAYA KANNYWOOD CE SILAR KWARAROWAR KANANAN JARUMAI A KANNYWOOD?

Kalli Yadda a Karrama Jaruman Kannywood a London

Ina kuma kira ga dukkan masoyan mu da su rika yi mana uzuri, mu ba yan iska bane, muna kuma kare mutuncin kanmu a matsayin mu na Yaya mata”.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: NORTHFLIX
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user