Tuesday 31 January 2023

Sana'o'i 16 Da Za Su Sauya Rayuwar Mata

Tura Wannan Zuwa Ga

Babu shakka mata dake zaman aure na fuskantar ƙalubale masu matuƙar yawa, waɗanda ba kowa ne yake fahimta ba. Banda zaman aure da kula da iyali, akwai rashin tabbas na rashin kuɗaɗen shiga waɗanda za ta iya amfani da su wajen taimako, da kyautatawa, da kuma zaman ko-ta-kwana. Babu shakka akwai matan dake hali, ko suke da maza masu hali. Sai dai fahimtar yadda ake juya naira da kwabo na da matuƙar muhimmanci wajen fahimtar ƙalubalen rayuwa, darajar kuɗi da kuma nuna irin baiwa da zuciyar da Allah Ya baiwa mata. Saboda haka wannan rubutu zai mayar da hankali ne akan sana’o’in da mata masu ƙaramin ƙarfi dake zaman aure za su iya yi domin samun arziki da rayuwa mai amfani. 


JERIN SANA’O’IN DA MATA ZA SU IYA FARAWA
Hoto: Telegraph


MarubuciBello Galadanchi


Kafin mu fara lissafo sana’o’i, to ya kamata mu fahimci cewa idan za ki fara sana’a, to ki tabbatar kin amsa waɗannan tambayoyin:


1. Wacce matsala za ki warware wa jama’a?


2. Ta yaya sana’arki za ta rage wa jama’a ɓata lokaci?


3. Ta yaya harkar ki za ta kawo wa jama’a rahusa?


4. Ta yaya za ki banbanta sana’arki da sauran masu yin irinta?


Waɗannan tambayoyin su ne gimshiƙin duk wata sabuwar sana’a da ake son yin nasara. Idan sana’a ba za ta warware wata matsala da ta addabi jama’a ba, to kar ki kuskura ki fara. Ruyuwar nan a cike take da matsaloli da ƙalubale iri-iri. Duk inda kika duba za ki gani, akwai abubuwa iri-iri dake ciwa jama’a tuwo a ƙwarya. Mafi akasarin lokaci, mutane suna kashe kuɗi ne domin warware musu matsala. Idan har za ki warware wa jama’a matsala, to da gudu za su ɗauki kuɗi su miƙa miki. 


Sai dai kuma mafi yawancin lokuta, akwai hanyoyin da ake amfani da su wajen warware waɗannan matsaloli.


Kasancewar mun san waɗannan hanyoyi, sai ƙwaƙwalwar mu ta toshe, ta yi tunanin cewa ba za a iya samo wata sabuwar hanya ba. Wannan ba dai-dai ba ne. Anan nake so ki ɗan yi tunani, ki ƙirƙiri hanyoyin warware matsala cikin hanzari kuma cikin farashi mai rahusa. Idan kika yi haka, to jama’a za su yi watsi da ɗaya hanyar da suka saba da ita, domin yin amfani da naki. Wato a duniya babu abin da yake da daraja kamar lokaci. Lokaci ya fi kuɗi daraja, kuma sai da lokaci ake samun kuɗi. Idan har za ki rage wa jama’a ɓata lokaci, to babu shakka za ki samu nasara.


Ba dole sai kin ƙirƙiro sabuwar sana’a ba, a’a, za ki iya duba sana’ar da ake yi kullum, akwai akasi a yadda ake yinta, ko akwai matsala da kusan kuwa yake fama da shi bisa yadda ake wannan sana’a. Ke kuma idan kika tashi, to sai ki ƙirƙiri hanyar warware wannan matsala tare da rage wa kwastomomi ɓata lokaci da kashe kuɗi. 


Ga misali. Hajiyata tana da tela da take kai wa ɗinki. Telan ya ƙware, amma kwanaki bakwai yake ɗauka kafin ya kammala. Sai dai kuma bayan kwanakin bakwan, telan yakan yi jinkirin kwanaki biyu zuwa uku, sannan ga tsada. Ɗinkin riga ɗaya na kamawa dubu shida zuwa goma. To idan ke mace ce mai sha’awar ɗinki, to ga dama ta samu. Matsalolin anan su ne ɗaukan dogon lokaci, rashin cika alƙawari, tsada, da kuma zirga-zirgan zuwa wajen tela. Sai ki ƙirƙiri tsarin da zai ta warware duk waɗannan matsaloli. 


RAGE WA’ADI: Za ki iya tantance kwanaki nawa yake ɗaukar ki gama riga mai wahala, sai ki tsara yadda za ki rage wannan lokaci. Za ki iya ɗauko matasa ‘yan mata ki rarraba musu ɓangarori masu sauƙi na ɗinkin, ke kuma ki mayar da hankali akan masu wahala. 


KWANTAR DA HANKALI: Za ki iya rubuta takardar alƙawari ki saka hannu akai, sannan ki bai wa kwostomarki ita ma ta saka hannu don ki kwantar mata da hankali. Akan takardar, za ki iya saka sharruɗa kamar “Idan ba ki kammala ɗinkin a cikin wa’adin da kika yi alkawari ba, to kar ta biya rabin kuɗin ɗinkin”.


RAHUSA: Idan kuma za ki iya rage kuɗin ɗinkin, shi ma hakan zai kawo miki kwastomomi, sannan za ki iya ƙara abubuwa da yawa waɗanda wasu telolin ba sa yi. Ba sai kwastoma ta zo wajenki ba, ki ringa zuwa wajenta talla, ki nuna mata sababbin ɗinkuna. Ya zamanto kina da “LOKUTAN GARAƁASA”, inda za ki bada rahusa ta yin amfani da hikima iri-iri kamar “idan kika kawo ɗinkin atamfofi guda huɗu, to na biyar ɗin kyauta ne”, ko kuma a kowane wata, akwai irin ɗinkin da kike rage kuɗinsa da kaso hamsin cikin dari.


Za ki iya amfani da garaɓasa wajen tallata sana’arki. Kamar “idan kika saka hotunan kayana da shagona akan shafinki na facebook da WhatsApp, to zan rage nera dubu a ɗinkinki na gaba. 


TALLA: Idan kina da hali, ki nemi ‘yan wasan Hausa ku tsadance, su saka ɗinkinki a ɗauke su a hoto a gidan hoto. Idan ma za ki iya, ku tsadance a ɗauke su akan bidiyo suna yabon ki, da irin daɗin da suka ji wajen aiki dake. Ke kuma ki watsa ta Facebook, da WhatsApp da Instagram. 


Da gudu za ki ga mata suna rububin zuwa wajenki. 


KAFOFIN ZAMANI: Har yanzu jama’a ba su ankara ba da yadda ake amfani da waɗannan shafukan sada zumunta wajen bunƙasa sana’a. A wannan zamani, mutane sun gaji da talla. Kowa talla yake, kuma a ko ina. Yanzu mutane sun fi mayar da hankali akan mai tallar, ba kayan da yake sayarwa ba. Idan kina da kirki, ban dariya, murmushi mai kwantar da hankali, nutsuwa da riƙon amana, to jama’a za su bada labarinki. Yi tunani mana, sau nawa kika taɓa ganin wani yace “wai-wai, ashe wannan tsiren yana da daɗi haka?”, amma za ki ga jama’a suna rubuta kalamai kamar haka “yanzun nan na rabu da Aminu Maishayi Taraba. Mutumin arziki ne”. Duk wanda ya karanta wannan, zai ji yana begen haɗuwa da Aminu, sannan yasa a fasa masa ƙwai da indomie. Kina gani dai Aminu aka tallata ba shayinsa ba, amma harkarsa ce ta samu ci-gaba. Saboda haka za ki iya amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen tallata sana’arki, ta samun mutane su faɗi abubuwan alhairi dangane da yadda kike riƙe sana’arki. 


Bugu da ƙari, ya zamanto kina da shafi inda kika tattara duk masu hulɗa dake. Amma shi wannan shafi ya zama waje ne na gaisawa da tattauna batutuwa na rayuwa, ba talla ko zancen kasuwancin ki ba. Hakan zai sa kwastomomin ki su shaƙu dake, su ƙara fahimtar ki, sannan su zama suna gaya wa jama’a labarinki. Wannan shi ne zai jawo hankulan mutane. Idan ɗaya daga cikin kwastomominki ta samu ƙaruwa, ki bayyana a shafinki, kuma ki yi kira ga jama’a su taya ta murna da Allah Ya raya. Idan har kina da hali, ki sayo ‘yan riguna ki aika, ki ce mata wasu daga cikin kwastomomin ne suka bayar a baki. Kar ki so ki ga yadda za ta ji daɗi, ta ƙara darajanta ki. Game da kafofin zamani, zamu yi rubutu na musamman akai. 


KYAUTATAWA: Ɗaya daga cikin abubuwan da masu sana’a ba su fahimta ba a Najeriya shi ne kyautatawa. Hankalinsu yana kan samun riba. Albishirinki, mance da batun riba na shekara ɗaya. Duk ribar da kika samu, yi amfani da ita ki bunƙasa sana’arki ta yadda za ki ci-gaba da warware wa kwastomominki matsaloli. Idan da kina kammala ɗinkin riga a cikin kwanaki uku, kuma suna biyan dubu biyar, to idan kika tara riba, a maimakon ki fara tunanin siyan mota ko wayar hannu, a’a, sai ki fara tunanin yadda za ki yi amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen kammala ɗinkin a cikin kwanaki biyu, ko ma kwana ɗaya, da kuma yadda za ki rage farashin ɗinkin zuwa dubu uku, ko dubu biyu da ɗari biyar. Hakan zai iya yiwuwa ki ɗauko yara mata ko amare kina koya musu ɗinki, ƙarawa shagon ki girma, mallaki wani ɗan karamin shagon ɗinki da ma’aikatansa dake cikin matsala. Wani abu da za ki iya yi wanda ba a cika ganin shaguna suna yi ba shi ne kyauta. Idan kika sayi takalma, da mayafai, to duk lokacin da wata kwastoma ta yi miki cinikin misali dubu biyar, ko goma, to sai ki ba ta takalma ko mayafai ta zaɓa. Wannan ya zama al-adar sana’arki. Kar ki damu da samun riba, ki bai wa kwastoma komai ta yin amfani da hikima. Abin da kike yi shi ne tallata kanki da kasuwancinki ta hanya mai jan hankali, kuma ba kowa ne yake hakan ba. 


To jama’a, idan kuka dubi waɗannan bayanai, za’a iya ɗaukar hikimomin dake cikinsu a saka a kowace sana’a. Babban abin shi ne ki warware matsala, ki rage wa kwastoma kuɗin da take kashewa da ɓata lokaci, sannan ki jawo hankalin wasu kwastomomin ta hanyoyin da ba kowa ne yake bi ba. 


To yanzu ga lissafin sana’o’in da matar aure mai zaman gida za ta iya farawa ba tare da jari ba. 


1. HAJIYA GOOGLE: Wannan sana’a ce ta taimakawa mutane samun abin da suke nema. Misali shi ne akwai wanda yake so ya sayi mota Honda Accord 2002, kuma yana so ya kashe dubu ɗari shida, ke kuma sai ki aika saƙonni a shafukan Facebook da WhatsApp da Instagram, ki nemi wanda yake da wannan mota kuma yake sha’awar sayarwa. Idan kuka tsadance, to shi kuma sai a nuna mi shi mota. Idan ta yi, to sai ya biya kuɗin ta, ke kuma a yanka miki kwamashonki. Idan kina sha’awar wannan, to ya zamo kina cikin shafuka iri-iri akan Facebook da WeChat. Sai ki rubuta sanarwa kamar haka “Assalamu alaikum. Idan akwai wanda yake son sayar da Honda Accord 2002, ya iya aiko mun da hotunan ta.”


2. KOYAWA MATA DABARUN ZAMAN AURE: Babu shakka akwai matsala a wannan zamani, inda ‘yan mata da yawa da samari ba su fahimci zaman aure ba. Akwai abubuwa da yawa kamar rashin tsafta, iya kwalliya, iya girki, iya magana, ladabi da biyayya, da fahimtar yadda namiji ko mace ke tunani. Bisa la’akari da yadda aure yake saurin tarwatsewa a wannan zamani, koyar da zaman aure zai iya zama sana’a mai kyau idan malamar ta tsara shi sosai yadda zai ja hankalin jama’a, kuma ya ƙayatar da su. Ban da darrusa, za’a iya tsara wasannin kwaikwayo, kallon fina-finai, gasar girki, gasar kwalliya da kuma Certificate a ƙarshe. Wannan zai harzuƙa amare kuma jama’a za su yi marmarin shiga wannan makaranta. 


3. RUBUTA ƘASIDU DA WAƘE-WAƘEN SIYASA: Ba ke ce za ki rera waƙoƙin ba, amma za ki iya rubuta su, sannan ki sayarwa mawaƙa, ko wasu ‘yan siyasan dake ƙaunar wanda kika rubuta waƙar akan shi. Misali shi ne Malam Bello babban ɗan siyasa ne. Malam Aminu yana ƙaunar Mallam Bello. Idan kika rubuta waƙa akan Malam Bello, to ko za ki iya tallatawa Malam Aminu, ko wani mawaƙi ya rera ta don ki sayar wa Malam Aminu ko Malam Bello. Idan za ki rubuta waƙoƙin da kalmominsu sun yi fice, ba kamar waɗanda muke ji kullum ba, to kuwa za ki samu kasuwa. Idan za ki iya bai wa mutane dariya da farin ciki da waƙoƙinki, to ‘yan siyasa za su yi ta aiko saƙonni. 


4. FRUIT SALAD: Wannan sana’a ce mai sauƙi, kuma ba kowa ne yake yin ta ba. Ki fara da maƙota, da ‘yan uwa. Kina aika musu, suna sha. Ki share makonni kina yi, idan har akwai daɗi, to za ki ga jama’a sun fara ƙwanƙwasa ƙofa. Sirrin shi ne ki zuba lemo irinsu 5 Alive da Tang a ciki. Ɗan Adam yana son zaƙi.


5. HAƊA DARASI: Idan kin kammala karatu, to za ki iya zama mai haɗawa malamai darasi. Idan kina da na’ura mai ƙwaƙwalwa, to sai ki yi amfani da ita wajen kasafta lokacin darasi da abubuwan da za’a koya. Idan kin iya wannan aiki, to za ki iya ɗaukar malamai suna koyarwa a ƙofar gidanki, ke kuma kina neman ɗalibai a WhatsApp da Facebook. Ki biya malamin albashi, ki yanki naki rabon. Idan ki tara kuɗi, to sai ki yi hayar waje, ki nemi rijista, ki yi hayar manaja ya zama principal. 


6. MAI NEMAN ASALI: Akwai jama’a da ke so su san asalin iyayensu da kakanninsu. Idan kina da wannan baiwa, to ki mayar da ita sana’a. 


7. RUBUTA TATSUNIYOYIN YARA: Me zai hana ki rubuta tatsuniyoyin yara? Ai babu wahala, ki tantance yara ‘yan shekaru nawa za ki rubutawa, me iyaye suke ƙoƙarin koya musu a waɗannan shekaru, sannan ta yaya za ki yi amfani da hikima wajen rubuta labari mai ɗauke da wannan batu?


8. MALAMAR QUR’ANI: Za ki iya zama malamar mata. Ba dole sai yarinya mace taje wajen malami namiji ya koya mata karatun Qur’ani ba. Ki buɗe makaranta a cikin gidanki, kuma ɗalibai su ringa biya awa-awa. Zai iya kasancewa su ɗauki karatun da za’a share sa’o’i 30 domin kammala izifi biyar. Za’a ringa zuwa makarantarki sau biyu a mako, kuma karatun sa’o’i biyu za’a ringa yi. Za ki iya karɓar ɗari 2 duk sa’a ɗaya, saboda haka ɗari 4 kenan kowace ranar karatu. N800 a mako, N6,000 na sa’o’i 30. Idan kina da ɗalibai biyar, kin ga za ki tashi da N30,000 kenan. Shin akwai abin da yafi samun kuɗi da lada a lokaci guda?


9. KULA DA ‘YA’YAN MUTANE: Idan kina da gida mai tsafta, to za ki iya kafa sana’ar kula da yara idan iyayensu ba sa nan, ko suna buƙatar hutu. Mata masu aure sau da dama suna fuskantar ƙalubale daga ƙananan yara, wani lokacin har bacci ma gagararsu yake. Idan kin iya mu'amala da yara, to wannan sana’arki ce. Ita ma awa awa za’a ringa biyan ki. 


10. MARUBUCIYAR JAWABAN SIYASA


11. GWANJO


12. KULA DA TSOFAFFI


13. ƊINKIN HULA


14. HAƊA TAKALMI


15. RUBUTA LABARAN SOYAYYA


16. KWALLIYAR MATA


GARGAƊI: BABU BASHI! BABU BAYAR DA BASHI!!! BABU BASHI!!!!!!!! MASOYINKA BA YA KARƁAR BASHI A HANNUNKA!!!! MASOYINKA NA SO KA CI-GABA, SABODA HAKA SHI NE MUTUM NA FARKO DA ZAI BIYA KA DON KA BUNƘASA SANA’ARKA. SABODA HAKA BABU BABU BABU BABU BASHI!!!! GWAMMA AN BARKI DA KAYANKI, DA KI BADA BASHI.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user