Showing posts sorted by date for query Abdallah Aliyu Saint. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query Abdallah Aliyu Saint. Sort by relevance Show all posts

Monday, 26 May 2025

Halayen Mace A Soyayya Da Aure

Halayen Mace A Soyayya Da Aure

Idan mace tana halayen yara da ƙuruciya a wajen namijin da take so, hakan na faruwa ne idan ta samu tsayayyen namiji, tana jin aminci da kwanciyar hankali a soyayyar.


Halayen Mace A Soyayya Da Aure
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Idan mace tana jajircewa kamar namiji tana ɗaukar ɗawainiyar da namiji ya kamata ya ɗauka , to saboda tana tare da namiji mai rauni ne wanda bai jajirce ba akan al'amuran ta, hakan ya tilasta mata zama jagora.


Idan mace ta fara ƙoƙarin barin soyayya to ta fara hango cewa wanda take tare da shi ba zai cika mata wasu manufofinta ba ne.


Idan mace kullum tana wahalar aiki fiye da kima, to tana tare da namiji mai sakaci. Tana jin babu kariya a ɓangaren kuɗi, tana ƙoƙarin cike giɓin da ya gaza samu.


Muhimmin abin lura shi ne, halayen mace sau da yawa amsa ne ga irin ƙarfi ko rauni da take samu daga namiji.


Halaye mace sukan canja ne kuma su ta'allaƙa ga irin namijin da take tare da shi.

Saturday, 10 May 2025

Yadda Mata Suke Rusa Arzikin Mazajen Su

Yadda Mata Suke Rusa Arzikin Mazajen Su

Da yawa daga cikin matasa masu aure, matansu ne silar lalacewar tattalin arzikinsu, kuma su ne ummul-aba’isin daƙile ci gaban mazansu a rayuwa.


Yadda Mata Duke Rusa Arzikin Mazajen Su
Hoto: LinkedIn

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ba na cewa duka ba, amma kusan kaso casa’in cikin ɗari (90%) na mata su ne ke jawowa mazansu jarrabawa da karya musu tattalin arziki a aikace, da kuma karya musu gwiwa wajen jajircewa akan neman halal a kowanne aiki.


Na san za ka yarda da ni idan ka duba a unguwarku, ka ga yadda wasu matasa suka taso da ƙwazon nema da tattali da iya sarrafa kuɗi don rufin asiri. Amma da zarar sun yi aure, komai sai ya lalace.


Hatta ɗan gidansa wani sai ya siyar, balle kuma ɗan lifan da ya tara da wahala.


Ana ɗaura aure, sai ka ga wata tana fara fitowa da hanyoyi masu kai namiji ga lalacewa.


Wata tun daga suturarsa take fara ingizawa, tana cewa:


 "Gaskiya kamata ya yi yanzu ka dinga ɗinka shadda. Haka za mu shiga dangina ana nuna mijina, ana cewa kamar ɗan dako ba shi da suturar arziki."


Musamman idan ta ga yana ɗan sarrafa kuɗi, sai ka ji tana cewa:


 "Gaskiya ya kamata mu dinga cin miya da kaji kullum. 'Yan uwana za su tarar da ni kullum ina fama da shinkafa fara da miyar jajjage da ɗan kifi."


Haka za ta ci gaba da ingiza shi. Shi kuma yana cikin jin daɗin amarci, har ta rinka raɗa masa a kunne:


 "Wallahi, mijin maƙwabciyarmu bai kai ka samun kuɗi ba, amma har solar ya haɗa a gidansa. Dan Allah ni ma a saka min, na daina sintirin kai caji maƙwabta."


Shi kuma namiji, saboda ƙarfin hali da rashin son a ce ya gaza, sai ya ci gaba da yi wa jarinsa rubdugu, kamar wanda ya samu kuɗin gado.


Kafin ya farga, sai ka ga shagon nasa yana ramewa kamar wanda cutar ƙanjamau ta kama. A hankali, sai a cinye komai.


Daga nan kuma ta fara zuga shi da cewa:


 "Tun da babu jari, sai ka siyar da gidan, ka sayi ƙaramin gida, ragowar kuɗin ka ja jari. Tun da jama'a sun gano komai ya ƙare, kada abinci ya fara gagarar mu a ji kunya."


Ƙarshe idan bai yi hankali ba, har ƙaramin gidan zai siyar, ya koma haya. Ita kuma sai ta kai shi kotun ƴan alluna ta ƙofar Wambai, ta ce ya kasa ciyar da ita, dole a raba auren.


Ƙarshe ya shiga uku, babu:


Babu gida,


Babu jari,


Babu aure.


Ita kuwa ba ta yi asara ba. Tana fitowa, wani ya aure ta, musamman idan tana da haske.


Don haka, idan amaryarka ta fara kawo maka waɗannan jahilan shawarwarin, kai shiru ka ce:


 "Ba zan iya ba."


Idan ta matsa, ka ce:


 "A aika a kawo daga gidanku.".


Ya kai ango!! Dole ka lura kada santin amarci ya sa ka bindige jarinka kamar yadda sojojin Najeriya ke bindige ɗan ta'adda har lahira a daji.

Friday, 9 May 2025

Zabar Abokai A Tsakanin Maza Da Mata

Zabar Abokai A Tsakanin Maza Da Mata

A yau kowa kana haɗuwa da shi sai ka ce abokinka ne. Kowa yana dariya da kai sai ka ce kun yi shekara goma da sanayya. Wasu ma idan sun haɗu da mace, ba su fi sau biyu ba sai ka ji yana cewa "ai wannan matata ce nan gaba." Ashe rayuwa haka take da sauƙi kenan?


Zaɓar Abokai A Tsakanin Maza Da Mata
Hoto: Photosvit/Dreams time


Bari na faɗa maka gaskiya, domin ko ka ji daɗi ko ka ɓata rai: ba kowa ba ne abokinka, kuma ba kowacce mace ba ce ta zama taka. Kaso casa'in cikin ɗari (90%) na nasarar rayuwarka ya dogara ne da irin mutanen da ka zauna da su, wato abokai da matar aure. Sauran goma cikin ɗari kuwa addu'ar iyaye da ƙoƙarin kanka ne ke ɗauke da su.


Iyaye fa Allah ne ya zaɓa mana su. Ba mu da zabin su. Idan sun ba da shawara, to da soyayya suke, amma ba duka shawarar tasu ce ta dace da zamani ba. To amma abokai da mace kuwa, kai kanka za ka zaɓa. Kuma idan ka yi zaɓi da hangen ido kawai, ba da hangen zuciya ba, to ka shirya zaman nadama.


Mutane da yawa suna ɗaukar abokai kamar ana tara busasshen totuwar rake da daddare bayan an tashi daga dandalin wasa. Kowanne ya zo, a jefa a ɗaki. Ba duba hali, ba duba buri, ba duba irin gudunmawar da zai bayar. Idan ka tambayi wasu, me yasa suke tare da abokansu, sai su ce "ai mun saba," kalmar sabo ba za ta amfanar da kai komai ba cikin alaƙar da ke jawo ka baya kamar mai haƙan rijiya.


Aboki ya zama abokinka idan kuna ƙarfafa juna, ba idan kuna janyo juna ƙasa ba. Misali, kana da buri na kafa kamfani ko kasuwanci, abokinka kuma kullum yana zaune yana sharhi kan fim da wasan kwallon ƙafa. Kana tsammani irin wannan aboki zai taimaka maka ka cimma burinka? Sam sai dai ƙarshe ku ƙare da siyan ƙatuwar "Plasma" Ku yi ta kallon tashoshin Arewa24 kuna sharhin fina-finai.


Idan abokinka ba ya faɗa maka gaskiya, ba ya ƙarfafa ka ka fita neman ilimi ko aiki, sai fa ya zama kamar dutse ne a wuyan riga, yana hana ka motsi, amma ba ka gane ba. Aboki nagari yana tura ka gaba kamar iska ke tura kwale-kwale a cikin ruwa.


Amma ba abokai kaɗai ba, mace ma tana da rawar takawa a ginin rayuwa. Duk da cewa ana cewa kyau na da daɗi, amma ba kyau ka aura kyau kawai ba tare da hankali ba. Kallon mace kawai da kyau, ka mata tambayar: "Ta na da buri kuwa? Ta na da hangen nesa kuwa? Ta san me ake nufi da gida kuwa?" ai kai da kanka ka ɗaura kanka igiya a wuya kana ƙoƙarin rataye kanka.


Misali, ka haɗu da mace kyakkyawa tamkar hasken wata, amma kullum ba ta da wani buri sai selfie da TikTok.


Ba ta da buri sai kwaikwayon matan film da kwatanta irin rayuwarsu, burinta ta yi kwalliya kawai kowa ya dinga yaba mata.


Kana burin ya za ka gina gida ? Tana kawo maka labarin abaya 'yar 400k ta shigo kasuwa.


Kana gaya mata kana son sake buɗe shago tana sa ka rigima akan dole sai ka siya mata iPhone. Lallai kuwa a matsayinka na matashi kuma mai ƙoƙarin gina kasuwanci za ta daɗe tana jawo ka baya da wannan baƙar al'ada.


Zaman aure fa kamar haɗa tawagar ƙwallon ƙafa ne, sai kowacce lamba da kusurwa ta yi motsi kuma ta yi aikinta sosai sannan za'a yi nasara.


Rayuwa dai kamar jirgin ruwa ce, kuma abokanka da matarka su ne fasinjojin ka. Idan fasinjoji marasa amfani suka cika jirgin, jirgin zai nutse kafin ya kai bakin gaɓa. Amma idan ka tara masu ƙwazo, masu buri, masu kyau da hankali, kai tsaye za ka ratsa gaɓar arziki lafiya.


A duniyar nan, wanda bai iya zaɓar abokansa da matarsa ba, to kamar mai shuka rogo a sahara ne, ruwa babu, ƙasa busasshiya. Shuka sai a banza.


Ka buɗe idanu ka zaɓi abokai da mata masu hankali da buri. Kada ka karɓi kowa kamar ana raba ruwan sanyi a rana. Ka ɗora su a sikeli: me za su kawo maka, me za ka koya daga gare su?


Ka tuna, aboki mara amfani kamar mugun tunani yake, da ƙyar ake  iya nasarar kuɓucewa daga gare shi. Mace marar hangen nesa kuma kamar bokiti marar tsafta take, duk ruwan da ka zuba, haka zai ɓaci.


Don haka, ka yi amfani da hankalinka kafin zuciyarka ta ɓatar da kai. Rayuwa ba ta ƙyale masu saurin yarda, su ne suka fi saurin nadama.

Monday, 5 May 2025

Ka Tashi Matashi

Ka Tashi Matashi

Kai Matashi! Ka tashi!


Kai matashi! Me ya sa kake zaune da jajayen idanuwa, da hawaye akan kumatunka? Zuciyarka cike da tunanin cewa wai ka haƙura ba za ka yi nasara ba.


Shin don ka kasa yau, sai ka daina mafarkin gobe?


Ka tashi matashi
Hoto: Dreams time

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Kai dai ka sani, rashin nasara ba ƙarshe ba ne, kuma nasara ba ta zuwa idan ka tsaya kana jajen gobe da jin tausayin kanka.


Ka kalli rana, kullum tana faɗuwa, amma sai gobe ta dawo da haske.


Ka kalli tsuntsaye, kullum suna fita neman abinci, kuma ba duk rana suke samu ba.


Amma har yau, ba su daina shawagi ba.


Wannan ya nuna cewa tsayawa ba mafita ba ce. Ci gaba shi ne mafita.


Idan ka faɗi yau, ka tashi gobe da ƙarin ƙarfin zuciya.


Ka ƙara tunani, ka gyara kuskure, ka rungumi sabuwar dama.


Rayuwa tana wa mai juriya albarka.


Ba sai ka yi sauri ba, sai dai kada ka tsaya.


Ka riƙe burinka da gaskiya kamar amana.


Ka dinga cewa: “Na faɗi yau, amma gobe zan tashi.”


Domin wanda ba ya tsayawa, shi ne ya kan isa inda sauran suka gajiya.


Ka tashi matashi! Ka tashi! Ka ci  gaba da gina burinka a zuciya.


Ka san cewa: gobe taka ce, idan ka daina tsoron kuskuren jiya.


A hankali wahalhalun da kake tsoro za su dawo suna ba ka dariya.

Friday, 25 April 2025

Gina Goben Ka

Gina Goben Ka

Nasara ana ginata ne a hankali ba da garaje ba. Nasara ba ta zuwa da gaggawa, kuma ba ta samuwa a dare ɗaya kamar yadda rana ke fitowa.

Gina Goben Ka
Hoto: Jeweller Magazine


Ita nasara gini ce da ake kafawa a hankali, tana buƙatar juriya, dagewa da kuma bin hanya mai ma’ana. Kamar yadda ake shuka iri a gona, sai an jira ya girma, a kula da shi, sannan a girbe amfanin.

Wani fitaccen malamin falsafa, Aristotle, ya ce:


“Mu abin da muke yawan aikatawa ne. Don haka nasara ba aiki guda ba ce, ɗabi’a ce.”.


Wannan yana nufin cewa idan mutum yana fatan kai wa wani matsayi ko cimma wata manufa, dole ne ya maida abin da zai kai shi can zama ɗabi’a. wato abu da zai dinga aikatawa kullum.

Misali

Kana son ka zama ɗalibi nagari? To, kada ka jira lokacin jarrabawa ka fara nazari. Ka maida karatu na yau da kullum, koda shafi ɗaya ne. Da haka za ka samu ƙwarewa fiye da wanda ke karatu kwatsam.

Haka ma lafiyar jiki, ba sai mutum yana da damar shiga manyan wuraren motsa jiki ba. Ka iya fara yawo da safe na minti goma, kullum. Wannan abu ne ƙarami, amma da zaran ya zamo ɗabi’a, zai haifar da babban canji a rayuwar mutum.

James Clear, marubuci da masani kan ɗabi’un Ɗan Adam, ya ce:

“Duk wani aiki da kake yi yau, kamar ƙuri’a kake kaɗawa ne don irin mutumin da kake so ka zama gobe.”

Wannan yana ƙarfafa cewa mu lura da abin da muke maimaitawa, domin a cikin hakan ne akwai asalin ginin rayuwarmu.

Confucius kuwa ya ce:

“Koda tafiyarka tana tafiya a hankali, babu laifi muddin ba ka tsaya ba.”

Abin da wannan ke nufi shi ne: komai da ka sa gaba, muddin kana ci gaba, ko da a hankali ne, za ka kai inda kake so.

Misali mai sauƙi shi ne: ɗalibi mai halartar makaranta kullum, yana sauraro, yana tambaya da karatu, ya fi wanda yake zuwa lokaci-lokaci. Sakamakon su a ƙarshe ba zai daidaita ba, saboda mai maimaitawa yana gina fasaha, yana samun ƙwarewa da fahimta.

Don haka, idan kana da buri ko a karatu, ko a sana’a, ko a neman dukiya, sai ka maida hanyar da za ta kai ka ga hakan ɗabi’a.

Ba sai ka fara da abu mai girma ba. Farawa da ƙanƙani, amma a kullum, shi ne hanya mafi kyau. A haka ne za ka gina nasara wacce za ta ɗore.

A taƙaice: Maimaita abu na gari kullum, zai zama ita ce hanyar da kake gina gobenka.

Ɗabi’a mai kyau ita ce ginshiƙin nasara mai ɗorewa.

Sunday, 20 April 2025

Zafafan Tambayoyin Da Za Ka Yi Wa Budurwar Ka

Zafafan Tambayoyin Da Za Ka Yi Wa Budurwar Ka

Ka tambayi budurwarka waɗannan tambayoyi guda uku. Daga amsasoshin da za ta ba ka za ka gane mai buri ce a rayuwa ko kallon fina-finai kawai ta sa a gaba.


Zafafan Tambayoyin Da Za Ka Yi Wa Budurwar Ka
Hoto: India

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Mace mai aji kake soyayya da ita ko 'yar hajijiyace da rawar zubar gado a gidan biki.


Ga su kamar haka:


"Me ne ne shirin ki a rayuwa?".


"Wanne tsari kike kai nan da shekaru 5 masu zuwa"?


"Idan na mutu na bar ki da 'ya'ya, yaya za ki yi da su?

Wednesday, 16 April 2025

Ka Kalli Kanka A Madubi Yanzun Nan

Ka Kalli Kanka A Madubi Yanzun Nan

Kana fama da zafin talauci? Da rashin ci gaba a rayuwa? Shiga ɗaki. Ka rufe ƙofa. Ka kalli madubi, wane ne ka gani cikin madubin?


Kalli Kanka A Madubi Yanzun Nan
Hoto: Stock Adobe

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Wannan da kake kallo, shi ne wanda ke da alhakin mafarkin da bai cika ba. Shi ne mai laifin faɗuwar burin ka, ɗan lalaci, ɗan fargaba, wanda yake gaza tsayawa ya fuskanci rayuwa.


Dole ka zage ka gaya masa maganganu kamar haka:


"Na gaji da zama a haka. Idan ba za ka tashi ba, to zan bar ka a baya."


Dole ka bar gida, ka bar danginka kuma ka yi watsi da abokanka.


Ka nemi inda babu wanda ya san ka. Ka hau titin da babu fuskokin da suka saba da kai, saboda gaskiyar magana ita ce:


"Ɗan Adam ba ya samun cikakken kuzari sai idan ya yi nesa da harshen da ya saba yi masa dariya".


Sai a lokacin za ka gane dalilin da ya sa mai kuɗin Afirka Aliko Ɗangote ya bar garinsa Kano kuma ya bar mahaifiyarsa Mariya Sunusi Ɗantata, kuma ya bar danginsa Alasawa masu tarin dukiya ya tafi Lagos don gina kansa.


Kamar yadda Ibn Khaldun ya ce:


“Rayuwa tana canjawa daga wuri zuwa wuri; wanda ya tsaya a wuri ɗaya, zai tsaya da cigaba.”


Ka je ka yi faɗa da rayuwarka a wajen da ba kowa ya san ka ba.


Ka yi aikin da ba ka taɓa tunanin za ka iya yi ba. Ka wanke mota, ka share titi, ka ɗauki kaya, ka zauna kasuwa, duk saboda makomar da kake so.


 “Man is condemned to be free.” – Jean-Paul Sartre


Fassara


Mutum an haife shi da alhakin zaɓar makomarsa.


Babu laifi a ƙasa, amma laifi ne ka zauna a ƙasa har ka ji daɗin zama.


Kana jin daɗin zama amma aljihunka yana ƙonewa kamar kara a cikin gobara.


Ka yi ta tattakawa akan wahalhalun da na jikin  madubin nan bai so.


Ka kakkarya shakkunsa. Idan ya ce "Ka gaji", ka ce masa "Gajiya ba tamu ba ce".


Idan ya ce "Za su yi min dariya", ka ce masa "To su yi ta yi har su gaji."


Saboda:


 “The cave you fear to enter holds the treasure you seek.” – Joseph Campbell


Fassara


Ramin da kake tsoron shiga, shi ne ke ɗauke da dukiyar da kake nema.


Mun fi aiki idan muka fita waje, saboda babu wanda ya san mu.


Babu ido, babu tsoron abin da za a faɗa.


Muna zama kamar Ronaldo a cikin gasar Champions League.


Muna aikin da zai saka mu haskaka.


To me zai hana mu daina fargabar ido?


Ka tambayi zuciyarka: Shin kana rayuwa ne don jin daɗin mutane, ko don gina kanka?


Kafin ka fita daga madubin, ka ɗauki alƙawari:


"Zan dawo nan na sake kallonka, amma da kyau da girma. Kai da nake gani a yau, zan sa ka zama abin da kowa zai so ya gani a gobe."

Friday, 11 April 2025

Gaskiya 7 Da Babu Mai Sanar Da Ku Su

Gaskiya 7 Da Babu Mai Sanar Da Ku Su

1. Sauƙin kai ga kowa yana rage maka daraja


Idan kana da sauƙin kai ga mutane, suna kallonka a matsayin wanda bai da wata daraja ta musamman.


Gaskiya 7 Da Babu mai Sanar Da Ku Su
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Misali, kullum da an neme ka za a same ka kullum kana liƙe da mutane to lallai waɗannan mutane za su rage ganin darajar ka .


2. Mutane ba sa son gaskiya, sai abin da ya dace da ra’ayinsu


Yawancin mutane ba sa son gaskiyar da za ta motsa su ko ta canza tunaninsu, sai dai su ji abin da ya dace da abin da suka riga su gaskata.


Misali, idan wani ya yi imani da cewa duniya tana da siffar leda, ba zai so jin hujjojin da ke nuna akasin hakan ba.


3. Za ka iya ruɗar da kanka idan ka maimaita ƙarya sau da yawa


Idan mutum yana maimaita wani abu, koda ƙarya ce, a hankali zai iya fara gasgata hakan. Misali, idan ka ci gaba da cewa kai ba ka da kyau ko basira, lokaci zai zo da hankalinka zai gasgata hakan, cewa kai mummuna ne ko daƙiƙi ne kai.


4. Shiru a yayin ciniki yana ba da nasara


A duk lokacin da ake ciniki ko tattaunawa mai muhimmanci, wanda ke magana kaɗan shi ke da iko. Wanda yake magana marasa yawa a irin wannan tattaunwa ta ciniki ko yanke shawara maganarsa ita ta fi muhimmanci kuma ta fi cike gurbin da ake buƙata wajen tsayar da matsaya.


5. Mutanen da ke tilasta ka yawan bayanin a kanka suna sarrafa ka ne


Idan wani yana yawan jefa ka cikin halin da za ka riƙa kare kanka da bayanai, yana iya zama yana ƙoƙarin sarrafa tunaninka.


Misali, idan wani yana son ya ja hankalinka zuwa ga laifinka, zai sa ka yawan bayani har sai ka ji kamar kai ne ke da matsala.


6. Jinkiri kafin amsa tambaya na iya nuna ƙarya ce maganar


Idan mutum ya tsaya yana tunani kafin ya ba da amsa ga tambaya mai sauƙi, yana iya nuna yana ƙoƙarin ƙirƙirar amsa maimakon ya faɗi gaskiya. 


Misali, idan ka tambayi wani: "Kana ina jiya da dare?" Sai ya yi jinkiri kafin amsawa, hakan zai iya nuna yana ƙoƙarin tunanin wata ƙarya mai ma’ana da zai ƙirƙira ya gaya maka.


7. Shiru


Idan mutum yana shiru bayan wata magana ko rikici, hakan na sa ɗayan ɓangaren jin damuwa da ƙoƙarin yin sulhu.


Misali: Idan mutum ya ƙi yin magana da kai, za ka iya jin kamar kai ne da laifi, duk da ba haka ba ne.


Me ya kamata a yi da wannan Ilimi?


Waɗannan dabaru na dark psychology ana amfani da su a zamantakewa, kasuwanci, da siyasa.


Fahimtarsu na iya taimaka wa mutum wajen kare kansa daga sarrafawar wasu ko kuma amfani da su a hanyoyin da suka dace.

Thursday, 27 March 2025

Alamomin Gaskiya Kan Macen Da Ke Son Ka Dagaske

Alamomin Gaskiya Kan Macen Da Ke Son Ka Dagaske

 1. Macen da ke lura da ƙananan abubuwa game da kai tana ƙaunarka. 


Kamar sabon aski idan ka yi ko idan ka rage gemunka ko sajen ka.


Alamomin Gaskiya Kan Macen Da Ke Son Ka Dagaske
Hoto: Jovanmandic/iStock photo

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


2. Macen da koyaushe ke ƙoƙarin taimaka maka da ƙananun abubuwa kamar turare ko ba ka kyautar abinci tana da wani motsin soyayya mai ƙarfi a gare ka.


3. Macen da ke tunawa da ƙananan bayanai game da kai tana daraja ka sosai.


Kamar sunan 'yan gidanku, wacce makaranta ka yi?  sunan abokanka da sunan iyayenka, wanne abinci ka fi so? Wanne gurin ƙwallo kake so da sauransu dai.


4. Idan mace tana keɓe lokaci domin kai duk da kasancewar tana cikin aiki, tana kula da kai sosai.


Misali duk hayaniyar gidan bikin da take ciki sai ta ware lokaci ta kira ka duk uzurin da take ciki ba ya hana ta mantawa da kiranka.


5. Idan tana kare ka a gaban jama’a amma tana gyara maka kuskure a sirrance.


6. Macen da ke sauraron surutunka ba tare da gundura ba tana ƙaunarka da gaske.


7. Idan tana lura da shirunka kuma ta tambayi abin da ke damunka, tana son ka da gaske.


8. Macen da ke gardama da kai amma ba ta taɓa barin ka ba. Duk yadda za ku yi faɗa ba ta iya share ka na tsawon kwanaki.


Idan ba ka samun wannan daga matarka ko budurwarka lallai ba ta son ka.

Wednesday, 26 March 2025

Alamomi 10 Na Zama Mahaukaci

Alamomi 10 Na Zama Mahaukaci

Wadannan su  ne abubuwa 10 da ke nuni da saura kaɗan ka zama cikakken mahaukaci. Idan mutum yana da waɗannan alamomi, yana da kyau a nemi taimakon likitan ƙwaƙwalwa da wuri kafin lamarin ya yi tsanani.


Alamomi 10 Na Zama Mahaukaci
Hoto: skynesher/Getty Images

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ga su kamar haka:


1. Rikicewar tunani


Tunanin mutum ya rikice ya kasa tantance me zai yi a rayuwa? Ina ya kamata ya dosa ? Me ne ne zai amfane shi?


2. Ganin abubuwa da ba su wanzu ba


Ko yana ɗaki ya dinga ganin giftawar wani abu mai rai ko mara rai, ko ya dinga jin maganganu ko ana kiransa wanda a zahiri gizo ne.


3. Rikicewar hankali


Ya dinga imani da abubuwan da ba su da tushe, kamar cewa ana bibiyar rayuwarsa za'a cutar da shi, ko ya dinga tunanin yana da wata baiwa ta musamman kamar  kusanci da aljanu ko wata halitta ɓoyayyiya.


4. Rashin kulawa da kansa


Ya daina wanka, wanke kaya, ko gyara kansa.


5. Matsananciyar ƙiyayya da mutane


Yana guje wa jama’a ko jin cewa kowa maƙiyinsa ne.


6. Rashin barci ko barci mai yawa


Kodai ba ya samun barci kwata-kwata ko yana yin barci sama da kima.


7. Rashin jin daɗi da rayuwa


Zai iya rasa sha’awar rayuwa ko jin cewa babu amfani a rayuwarsa.


8. Aikata abubuwan da ba su dace ba


Yana son yawo tsirara cikin ɗaki ba ya son saka wando, yana magana da kansa, ko aikata abubuwa masu hatsari ba tare da tunanin hatsarin ba.


9. Rashin gane gaskiya da wuri sai ya aikata abu ya dawo yana da-na-sani


Yana kasa banbance abin da ya kamata wanda zai dace daidai da shekarunsa, ya dinga yin abubuwa da ya kamata a ce wanda suke ƙasan shekarunsa ke aikatawa.


10. Saka sutura wadda ta sha bamban da yanayin da ake ciki


Ya dinga saka ƙatuwar rigar sanyi lokacin zafi, ko kuma ya dinga yawo da singileti lokacin da ake sanyi.


Idan ka ga waɗannan alamomin ina mai yi maka bushara da cewa ka kusa haukacewa.

Monday, 17 March 2025

Sana'o'in Da Ba A So Ka Yi Wa Mata Dariya Idan Kana Yin Su

Sana'o'in Da Ba A So Ka Yi Wa Mata Dariya Idan Kana Yin Su

Idan kana wannan sana'o'i guda biyar kada ka sake ka dinga yi wa mata dariya.


Ga su kamar haka:


Chajin Waya


Aradu idan ka yi wasa ko kuɗin fetur ɗin da ka siyo ba zai haɗu ba.


Sana'o'in Da Ba A So Ka Yi Wa Mata Dariya Idan Kana Yin Su
Hoto: New York Post

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Provision store


Aradu kafin ka ankare shagonka sai ya zama saura kwalaye sai sun bindige maka jari kamar yadda soja ke bindige ɗan ta'adda a daji.


Kayan kwalliya


Faka-faka za su kwashe maka ƴan mayukan shagon da kwalli da barbaɗa kumatu da jan baki, su bar ka ƙuda yana bin bakinka yunwa ta kassara ka.


KeKe Napep


Adai-daita shi ma kada ka dinga yi wa mata dariya musamman zawarawa, yanzu za su yi ta hawa suna sauka na fetur ma sai ka yi ciko su bar ka ku yi ta wasan ɓuya da mai mashin. Ka ci balas ƙarshe ya ƙwace mashin ɗinsa ka lashe kenan.


Mai Siyar da wayoyin hannu


Taɓ wannan idan ba ka yi wasa ba lokaci guda mace za ta mayar da kai ƙauye ta cinye jarin ta bar ka da ƙaton akwakun glass a gaba kana ta gogewa ƴan wayoyin ba su fi biyu a ciki ba.


Sai a lura masu irin waɗannan sana'o'in kada ku dinga yi wa mata dariya.


Ku ci magani kamar kakarku ta mutu kullum ko matanku sau biyu za ku dinga musu dariya a rana, sau ɗaya ƙarfe 10 na dare da kuma ƙarfe 2 na dare.

Saturday, 15 March 2025

Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba

Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba

1. Kada ka raina iyayenka. Ba za su dawwama ba, ka kula da su matuƙa.


2. Idan ka gyara kanka, kamar ka  gyara iyalinka. Idan ka gyara iyalinka, kamar ka gyara al’umma ne, idan ka gyara iyalinsa kai ma ka gyara ni ma na gyara sai al'umma ta gyaru.


Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba
Hoto: Getty Images

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


3. Namijin da ya iya fin ƙarfin  sha’awarsa yana da cikakken iko kan rayuwarsa.


4. Kunya ta ɗan lokaci ce, amma nadama tana dawwama. Ka fi son fuskantar kunya da wuri a kan ka yi nadama daga baya. Ka yi aiki tuƙuru kada ka ji junyar wulaƙancin jama'a kan sana'arka.


5. Namiji mara manufa yana rayuwa ne kawai don shagaltuwa da abubuwan banza. Kamar zuwa fati, shaye-shaye da neman mata.


6. Ka guji mutanen da ke ƙin jinsin da suka saɓa da nasu; suna da matsala a zukatansu.


7. Ka saurari tsofaffin da suke farin ciki, sun san abin da suka gani a rayuwa.


8. Ɗa’a (hazaƙa) ta fi ƙwazo (motsi zuciya). Ka dinga yin abin da ya dace, koda ba ka jin daɗin aikata shi a ranka.


9. Idan kana jin buƙatar burge kowa, to kai bawa ne gare su.


Duk lokacin da kake son burge mutane za ka zama kamar bawansu . Duk abin da suke so shi za ka aikata ko ba daidai ba ne. Hakan ya sa malamai suka zama karnukan 'yan siyasa.


10. Mafi yawancin baƙin ciki a cikin maza na faruwa ne sakamakon rashin manufa a rayuwa.


Kaso 90 na maza suna faɗawa wahala ne da ƙunci da talauci saboda rashin manufa da gina kasuwanci ko aiki tun suna ƙananu.


11. Idan namiji yana rashin kunya ga uwarsa, kada ki amince da sh, ba zai girmama ki ba.


12. Namijin da ya saba da jin daɗi mara amfani yana lalacewa. Dole ka saba da wahala don ka bunƙasa.


13. Halayen mace suna ƙarfafa namiji, haka nan kuma halayen namiji suna ƙarfafa mace.


Idan namiji ya samu mace mara manufa sai ta rage tasa manufar da kaso 70 haka idan ya samu mai manufa sai ta cike shi ya zama mai  ɗari bisa ɗari.


14. Rayuwa ba za ta sauƙaƙa ba, kai ne kawai za ka ƙara ƙarfi don fuskantar ta.


15. Babu wanda ya taɓa zama babban mutum ta hanyar zama kan kujera yana kallon fina-finai da tsalle tsakanin facebook da tiktok tsawon wuni/yini.


16. Namiji yana samun mafi yawan farin ciki ne lokacin da yake gina abin da zai bari bayan ya tafi.


17. Kada ka saurari marasa fata da ke cewa rayuwa tana muni idan shekaru suka kai 40. Idan ka dage, kana inganta ta fiye da matashin ɗan shekara 20.


18. Kasance namijin da ke da nutsuwa lokacin da kowa ke firgice aka rasa mene ne mafita. Yi ƙoƙari ka nemo mafita.


19. Gwamma ka yi kuskure a kokarinka fiye da ka zauna ba ka yi komai ba.


20. Yin dariya da mai kiba a dakin motsa jiki kamar yin dariya da marasa gida ne don yana neman aiki. Wannan rashin tunani ne.


21. Zama cikin yanayin wajen da yake shiru da shan iska yana rage damuwa fiye da shan magungunan maye da giya.


22. Koyi yadda za ka karɓi suka ba tare da ka fusata ko ka mayar da martani da zafi ba.


23. Daina kallon batsa, za ka ji daɗin rayuwa kuma ka fi zama namiji nagari.


24. Ka nemi abin da kake so ta hanyar aiki da ƙoƙari, kada ka yarda da son cin banza da neman alfarma.


25. Ka tuna cewa wasu maza suna da kirki ba don suna da hali mai kyau ba, sai don sun kasa tsayawa tsayin daka wajen kyautatawa mata har matan ke juya su kuma suke ganin mazajen nasu masu kirki ne.

Thursday, 13 March 2025

Muhimman Abubuwa Kan Maza Da Mata

Muhimman Abubuwa Kan Maza Da Mata

Mata suna zina ne da wanda suka yi ra'ayi. Yayin da maza kuma ke yi da duk wadda ta ba su dama. Don haka idan aka aikata zina mace ita ce mai kaso 90 wajen ba da gudummuwa.


Muhimman Abubuwa Kan Maza Da Mata
Hoto: God design path

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Maza na auren macen da suka ga alamun za su iya juyawa ne kuma take nuna musu tausayi tun daga waje shiyasa za ka ga namiji ya shekara biyar yana soyayya da mace amma ya ƙi aurenta rana ɗaya kuma ya haɗu da wata daban cikin wata shida ya aure ta ya ƙyale waccan.


Kaso 90 na matan zamani suna auren wanda ya shirya ne zai yi auren ba ɗan soyayya gwanin iya kalamai da nuna musu soyayya ba amma ba shi da manufa.


Kaso 99 na maza ba su damu da kwalliyar zamani da mata ke yi ba wadda suke mulka kwalliya a fuska, sannan maza ba sa bambance tsadar tufafin da mata suka saka sun fi ganewa idan kayan ya yi musu kyau.


Macen da ta sa jan mayafi ta fi ɗaukar hankali akan wadda ta saka wata kala ba ja ba.


Matan da suka haura shekara 30 babu aure sukan yi fama da lalurar baƙin ciki (Depression). Shekararsu ta farko bayan aure ya kan warke.


Kaso 90 na maza 'yan shekara 25 zuwa sama wanda ba su da aure suna aikata istimna'i (Mastubartion).


Auren mummuna da mai tsakatsakin kyau ya fi na kyakkyawar mace ƙarko.

Monday, 10 March 2025

Abubuwa 10 Masu Amfanarwa

Abubuwa 10 Masu Amfanarwa

1. Sanin cewa duk mutum na da matsalolinsa


"Illusion of Transparency" yana nuna cewa kowa yana jin kamar matsalolinsa sun fi yawa, amma a gaskiya kowa yana da matsala kuma kowa tasa ya sani (Gilovich et al., 1998).


Gaskiya 10 Masu Amfanarwa
Hoto: Your Tango

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


2. Kamanta rayuwarka da ta shafukan sada zumunta


Nazarin Self-Discrepancy Theory ya nuna cewa yawan kallon rayuwar wasu a shafukan sada zumunta da ƙoƙarin kwatanta abin da suke yana karya lagon mutum da mayar da shi baya (Higgins, 1987).


Bincike ya nuna cewa wanda suka fi amfani da shafukan sada zumunta kaso 70 cikinsu suna fama da cutar "Depressions "wato  cutar damuwa. 


Kawai suna ta ƙoƙarin neman abin da zai ɗebe musu kewa ne.


3. Ƙwarewa akan neman kuɗi fiye da tara su waje ɗaya


Bincike ya nuna cewa mutanen da ke saka kuɗinsu a ƙwarewa (kamar tafiya ko koyon sabuwar sana’a) sukan fi jin daɗi fiye da masu ajiye kuɗin kawai ba sa ƙoƙarin zuba kuɗin inda za su haɓaka.(Van Boven & Gilovich, 2003).


4. Sanin cewa ba kowa zai so ka ba


"Negativity Bias " yana nuna cewa mutane kan fi mayar da hankali ga rashin so fiye da soyayya, mutane sukan fi damuwa da maƙiyansu akan masoyansu.


Misali , Ɗan Siyasa zai fi damuwa da ya jawo maƙiyansa su dawo masoyansa, haka budurwa ba ta cika damuwa da namijin da yake nuna mata tsantsar soyayya ba, tana ta ƙoƙarin cusa kai wajen namijin da bai damu da ita ba. 


Dalilin haka kuma kaso 90 suke rasa masoyan nasu wajen neman soyayyar wasu da ba su damu da su ba. Ɗan siyasa ya kan rasa masoyansa wajen ƙoƙarin kyautatawa abokan adawarsa ya manta da hidima wa masoyansa. 


Haka ita ma macen ke rasa masoyi na gaske wajen ƙoƙarin shawo kan wanda bai damu da ita ba (Baumeister et al., 2001).


5. Sanin lokacin da ya dace ka yi magana da wanda za ka yi shiru


Emotional Intelligence yana nuna cewa sanin lokacin yin shiru da lokacin magana yana ƙarfafa dangantaka da mutanen da ke kewaye da kai (Goleman, 1995).


Ba komai ne sai ka sa baki akai ba koda kuwa kana da iko ko akan 'ya'yan cikinka ne.


6. Guje wa rashin haƙuri da son komai a gaggauce


Delayed Gratification yana nuna cewa mutane masu iya jira don samun sakamako mai kyau sukan fi samun nasara (Mischel et al., 1972).


7. Yin godiya da abin da kake da shi


Nazarin Positive Psychology ya tabbatar da cewa mutanen da ke yin godiya akai-akai sukan fi samun kwanciyar hankali (Emmons & McCullough, 2003).


8. Sanin cewa lokaci shi ne abu mafi daraja


Mutanen da suka fahimci cewa lokaci ba ya dawowa sukan fi amfani da shi cikin hikima (Carstensen et al., 1999).


9. Guje wa yin buri ba tare da aiki ba


Fantasy Realization Theory ta nuna cewa mutane da ke yin tunanin nasara ba tare da aiki ba, suna fuskantar gazawa (Oettingen, 2014).


Ka yi aiki da hankali da basira kada ka zama mai son cin banza da neman alfarma akan komai.


10. Sanin cewa rayuwa na buƙatar Daidaituwa


Work-Life Balance Theory ta tabbatar da cewa mutane da ke daidaita aikin su da rayuwarsu sukan fi farin ciki (Greenhaus & Allen, 2011).

Thursday, 6 March 2025

Abin Da Ke Nuna Mace Na Kaunar Ka

Abin Da Ke Nuna Mace Na Kaunar Ka

Idan ta na gaya maka kwanakin hailar ta, yana nuna ta amince da kai, kuma tana jin kusanci da kai, kuma tana son ka fiye da kowanne namiji a duniya.

Abin Da Ke Nuna Mace Na Kaunar ka
Hoto: Deposit photos



Shin budurwarka tana gaya maka idan baƙon wata ya zo mata?

Tuesday, 4 March 2025

Abubuwan Da Sanin Su Ya Fi A Ba Ku Kyautar Kudi

Abubuwan Da Sanin Su Ya Fi A Ba Ku Kyautar Kudi

Kana canja tunaninka komai zai canja na jikinka tun daga suturar da kake sakawa, yanayin tafiyarka, abokanka da cin abincinka wani lokacin har matarka sai ta sauya ita ma.


Abubuwan Da Sanin Su Ya Fi A Ba Ku Kyautar Kudi
Hoto: Vecteezy

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Mata suna son jima'i kwatankwacin yadda suke son kuɗi, don haka tafiya ka bar matarka har wata shida ba ka da hurumin tsananta bincike akan yadda ta riƙe sha'awarta.


Idan ka ba wa abokinka hoto a waya ya gani kuma sai ya ci gaba da dudduba wasu hotunan ka rage yarda da shi da ka yi.


Maza na son mace mai biyayya fiye da yadda suke son jima'i, shiyasa wasu mazan suke ajiye kyakkyawar mace mai sura a waje su ƙi aurenta amma kuma suke auren mace mummuna mara ƙira indai tana kwantar musu da hankali.


Mace na son namiji mai ƙarfin hali da naci akan burikansu kuma wanda zai iya saurin rabuwa da ita cikin sauƙi.


Kaso 70 na maza suna soyayya ne da mace daidai ajinsu, haka kuma suna auren mace ne daidai ajinsu.


Mata ba kamar maza ba suna soyayya ne da ƙasa da su ko wanda ya fi su aji zai wahala ka ga mace na soyayya da daidai ita.


Idan kana son ka gane halin mutum lokaci guda ka ba shi rabon abincin taron mutane, wanda ya ɓoye abincin da zai ci kafin ya fara rabo azzalumi ne kada ka ba shi amana, wanda ya fara rabawa sai da abincin ya je tsakiya ya ware wanda zai ci wannan komai zai iya faruwa, zai iya cin amana zai kuma iya riƙe amana.


Wanda ya rabawa mutane sannan ya fara neman wanda zai ci wannan zai riƙe amana da kaso 70 cikin ɗari.


Mazan jigawa suna ƙaunar mace mai ƙaton bille a kumatu.


Kada ka tambayi mace shekarunta sai idan ita ce ta gaya maka.

Gaskiya Kan Rayuwar Yau Da Kullum

Gaskiya Kan Rayuwar Yau Da Kullum

Ba a yin arziki a sana'oin da ake yi cikin unguwanni sai dai a samu na abinci, don kuwa makusantanka da maƙwabtanka suna ganin ka fara tashi za su yi duk mai yiwuwa wajen durƙusar da kai.


Gaskiya Kan Rayuwar Yau Da Kullum
Hoto: Unsplash

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Babban wanda zai iya ceto ka daga talauci ya saka a harkar arziki sam ba shi da alaƙa da kai ta jini ma'ana baƙo ne.


Idan ka sa haka a ranka ka huta da zafin aƙida ko tsatstsaran ra'ayi.


Gajeriyar mace baƙa mai ƙarancin kyawu ta fi kowacce mace biyayyar aure da kaifin hankali wajen zamantakewa da bayar da shawarwari masu amfani da tallafar miji.


Babban maƙiyinka shi ne na kusa da kai.


Kyakkyawar mace doguwa fara ta fi daɗin zaman aure idan kana da dukiya ko kuma kana yawan zuwa taron manyan masu kuɗi da matarka.


Ko ba ka so baban matarka ya fi wasu daga cikin ƙannenka da yayyenka son ganin ka ci gaba a rayuwa.


Bayan mutuwarka matarka sai ta fi wahala da 'ya'yanka akan mahaifiyarka.


Ƙanwarka mace ta fi ƙaunarka akan yayarka mace, kuma ta fi ƙaunarka akan 'yan uwanka maza.


Ƙanwar matarka ta fi rainaka akan ƙannen matarka maza da yayyenta maza.


Jarin farko da aka buɗe kasuwanci da shi indai ba ka koyi kasuwancin tun daga tushe ba ko ka yi zaman yarinta a shagon wani ba, ka ɗauka kawai gidan marayu ka buɗe ba shago ba don jarin sai ya zurare kamar fashashshen kwano.


Ka girmama ra'ayin kowa hatta baƙo ba mamaki mafitarka a rayuwa tana tattare da shi.

Tuesday, 18 February 2025

Abubuwa 10 Masu Gurbata Rayuwar Saurayi

Abubuwa 10 Masu Gurbata Rayuwar Saurayi

Akwai abubuwa 10 da ke rushe rayuwar saurayi, kuma su hana shi ci gaba har abada.


1. Rashin ingantaccen tsarin rayuwa


Hujja


Mutumin da bai da tsari a rayuwarsa yana yawan shiga damuwa da rashin tabbas (uncertainty), wanda ke iya hana shi samun nasara.


Abubuwa 10 Masu Gurbata Rayuwar Saurayi
Hoto: Petar Chernaev/iStock photo

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Bincike


Masana sun nuna cewa tsari da tsayayyen manufa na ƙara wa mutum ƙaimi da mayar da hankali wajen nasara a rayuwa.


2. Yawan jinkirta aiki


Hujja


Jinkirta aiki yana haddasa damuwa da yawan nadama, wanda ke hana mutum cimma burinsa.


Bincike


Psychology Today ta bayyana cewa jinkirta aiki na hana mutum samun nasara da gamsuwa a rayuwa.


3. Rashin ƙwarewa wajen sarrafa lokaci


Hujja


Rashin iya sarrafa lokaci yana hana mutum yin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwa. Ya ɓuge da shiririta da abubuwan da ba za su amfane shi ba.


Bincike


Masana sun nuna cewa sarrafa lokaci da kyau na ƙarawa mutum ƙwarin gwiwa da yawan nasara.


4. Shaƙuwa da mutanen da ba su da kyakkyawan tasiri


Hujja


Mutanen da ke da mugun hali na iya raunana zuciyar mutum da hana shi ci-gaba.


Wannan ya haɗa har matarka ko budurwarka, abokanka da 'yan uwanka.


Bincike


Nazarin Harvard Study of Adult Development ya nuna cewa mutumin da ke zagaye da mutane masu kyakkyawar manufa da ƙwazo ya fi yin nasara da cimma burinsu fiye da mutumin da ke zagaye da malalatan mutane.


5. Damuwa da ra'ayin wasu fiye da kima 


Hujja


Wanda yake yawan ƙoƙarin faranta ran mutane yana yawan fuskantar gajiya da damuwa.


Bincike


Nazarin Self-Determination Theory ya nuna cewa mutum yana buƙatar samun ‘yancin yanke shawara a rayuwarsa.


6. Dogaro da wasu


Hujja


Wanda ba ya iya dogaro da kansa yana shan wahala idan babu wanda zai taimake shi.


Bincike


Masana sun nuna cewa samun ‘yancin kai na ƙara wa mutum jin cewa yana da iko a kan rayuwarsa.


7. Rashin lura sosai wajen sarrafa kuɗi


Hujja


Rashin iya sarrafa kuɗi yana jefa mutum cikin wahala da damuwa.


Bincike


Journal of Economic Psychology ta bayyana cewa matsalolin kuɗi suna da alaƙa da ciwon damuwa da rashin jin daɗin rayuwa.


8. Rashin kulawa da lafiya


Hujja


Rashin kula da lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa yana hana mutum samun kuzari da farin ciki.


Bincike


Masana sun tabbatar da cewa motsa jiki da bacci mai kyau suna da matuƙar tasiri wajen inganta tunani da jin daɗin rayuwa.


9. Zaman banza da rashin yin aiki


Hujja


Rashin yin aiki yana haifar da gundura da jin cewa rayuwa ba ta da ma’ana.


Bincike


Nazarin Flow Theory ya nuna cewa samun aiki mai amfani yana ƙara jin daɗin rayuwa.


10. Rashin karatu da ilimantarwa


Hujja


Wanda ba ya ƙara neman ilimi kan wanda yake da shi yana da sauƙin fuskantar matsaloli a rayuwa.


Bincike


Nazarin Cognitive Flexibility Theory ya nuna cewa ƙara ilimi na taimakawa mutum wajen daidaita kansa da sabbin yanayi.


Duk waɗannan abubuwa suna iya rushe rayuwar saurayi.


Don kauce wa hakan, yana da kyau mutum ya tsara rayuwarsa, ya guji jinkirta aiki, ya zaɓi abokai nagari, kuma ya kula da lafiyarsa da kuɗaɗen sa.

Monday, 17 February 2025

Abubuwa 10 Masu Janyowa Mutum Raini

Abubuwa 10 Masu Janyowa Mutum Raini

Waɗannan su ne abubuwa 10 da suke tarwatsa girma da darajar mutum kowa ya raina shi.


Abubuwa 10 Masu Janyowa Mutum Raini
Hoto: Manari TV/YouTube

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ga su kamar haka:


1. Yawan kule-kulen 'yammata ga namiji


Yawan nuna soyayya ga kowacce mace idan ka gani shikenan ta zama budurwarka, hakan yana sa wa mutuncin mutum ya zube kamar an zuba ruwa a kwando.


2. Yawan yin gulma


Mutanen da ke yawan gulma da yayata magana ba tare da tabbaci ba ana raina su. Nazarin Journal of Social Psychology ya nuna cewa yawan gulma yana rage daraja da amincewa.


3. Rashin iya sarrafa fushi ko matsala


Mutane suna raina wanda ba zai iya sarrafa fushinsa ba ko wanda ke yawan tsawwala magana a lokacin da yake cikin matsala ko yawan mita da ƙorafi.


Nazarin Journal of Emotional Intelligence ya nuna cewa iya sarrafa fushi yana ƙarfafa mutum.


4. Rashin alƙibla da rashin faɗin gaskiya a rayuwa


Idan mutum ba shi da tsayayyen shiri ko burin rayuwa, mutane kan raina shi. 


Nazarin Journal of Career Development ya nuna cewa mutanen da ke da alƙibla sun fi samun mutuntawa a cikin al’umma.


5. Rashin tsaftar jiki da muhalli


Idan mutum ba ya kula da kamanninsa ko tsaftarsa, wasu kan raina shi.


Nazarin Psychology Today ya nuna cewa tsafta tana taka rawa wajen yadda mutane ke kallon darajar mutum.


6. Yawan faɗar sirrin iyalinka ga na waje


Tun da ga kan mahaifi, mahaifiya, matarka, ƙanneka da yayyenka dukkansu fallasa wani asirinsu a waje ga wani kamar kanka ka daɓawa wuƙa ƙarshe idan an tashi har kai za a gorantawa.


7. Rashin dogaro da kai da rashin ƙwarin gwiwa


Idan ya zama ko me za ka yi sai ka nemi shawara ko izinin mutane ko yardar su hakan yana bazar maka da kimarka kamar an watsa gari a iska, don kuwa koyaushe zai zama juya ka ake yi sai abin da aka tsara maka za ka yi ka zama bawan mutane a taƙaice.


8. Yawan tambayar kuɗi ko roƙon taimako


Mutanen da ke yawan roƙon taimako ba tare da ƙoƙarin dogaro da kansu ba, suna zama abin raini.


Nazarin Journal of Economic Behavior & Organization ya nuna cewa mutane suna mutunta waɗanda ke ƙoƙarin magance matsalolinsa.


9. Yawan cewa "Ni ne na fara" ko "Ni na fi kowa"


Mutanen da ke yawan jaddada kansu a kowane yanayi suna sa wasu su raina su. 


Nazarin Personality and Individual Differences Journal ya nuna cewa waɗanda ke da hali na son ɗaukaka kansu ba sa samun mutuntawa.


10. Yawan yi wa wasu kishi da fatan mugun abu


Mutanen da suke yawan jin kishin wasu ko fatan sharrinsu, sukan zama abin raini. 


Nazarin Psychology Today ya nuna cewa kishi da mugun nufi suna rage mutunci a idon jama'a.


Ya ku taron matasa ina horonku da ku guji waɗannan abubuwan.

Sunday, 16 February 2025

Gaskiya 21 Game Da Mata Da Maza Da Ba Ku Sani Ba

Gaskiya 21 Game Da Mata Da Maza Da Ba Ku Sani Ba

1. Mata suna son namiji mai yawan murmushi, domin hakan na nuna musu cewa wai zai tausasa musu ko bayan aure.


2. Maza suna son mace mai saurarensu fiye da yawan yi musu magana. Mace mai amfani da kunnuwa fiye da baki. Mace mai tsayawa tana saurare fiye da yawan magana.


Gaskiya 21 Game Da Mata Da Maza Da Ba Ku Sani Ba
Hoto: Ammentorp/Dreams time

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


3. Idan mutum yana son ka da gaske, zai kula da ƙananan abubuwa game da kai da wasu ba su lura da su ba.


4. Mata sukan fi sha’awar namiji mai ƙwarewa da wani abu, kamar kiɗa, rubutu,zane ko wasan motsa jiki.


5. Saurayi da budurwa da suka fi yawan dariya tare, da abubuwan da a zahiri ake ganin kamar shiriritane ko yarinta sun fi samun dangantaka mai ɗorewa, da kuma samun kwanciyar hankali bayan aure.


6. Muryar mutum tana canzawa idan yana magana da wanda yake so, yawanci tana yin taushi ko zurfi.


7. Idan mutum yana yawan tunaninka, zai fara yin mafarki da kai, koda kuwa bai bayyana hakan ba.


8. Idan mace ko namiji yana zaune kusa da wanda yake so, jikinsa na iya yin zafi ko tafasa kaɗan saboda yawan ƙwayoyin halittar jininsa sun fara haɗuwa da na wanda yake so ɗin suna son rungumar juna.


9. Mutane sukan fi sha’awar waɗanda ke nuna yarda da su fiye da waɗanda ke da kyau kawai.


10. Idan mutum yana son ka/ki, zai koyi abubuwan da kake/kike so ba tare da an tilasta shi/ita ba.


11. Idan matarka na son ka sosai za ta fara kwaso wasu ƙananun ɗabi'unka wanda ita kanta ba ta san tana yi ba kamar yadda kake magana, yadda kake cin abinci, tsayuwarka, har sai ta fara kamanni da kai ta fuska.


12. 'Yar farko da aka fara haifa a gida tana kwaso kamanni da halayyar mahaifinta ne.


13. Mata sukan fi sha’awar maza masu iya yanke shawara da sauri.


14. Idan mutum yana jin daɗin zama da kai, zai riƙa kallon fuskarka sau da yawa.


15. Mata suna jin daɗin zama da maza masu iya sanya su dariya akai-akai.


16. Mata sun fi maza son yin zancen batsa amma a zahiri sai su nuna kamar ba sa so.


17. Mata sukan tuna saurayin da suke so ne kawai yayin da suka ji waƙa da kiɗan da ya burge su.


18. Kaso 20 na mazan duniya su na Gidan Yari (Prison) a ɗaure yayin da mata kaso 5 ne kacal ke ɗaure.


20. Ƙanwar mace mai bin ta (Sakuwarta) tana kishi da ita sosai , shiyasa take kwaikwayonta a komai kuma take fatan samun duk abin da yayarta ta mallaka.


21. Namiji mara jin magana da taurin kai ya fi shiga zuciyar mata fiye da mai sanyin rai, saboda suna ganinsa a matsayin mai ƙarfin hali da ƙarfin da zai iya kare su daga rikici ko tashin hankali.