Showing posts sorted by relevance for query Anas Darazo. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Anas Darazo. Sort by date Show all posts

Sunday, 7 March 2021

Banbanci Tsakanin Mutane Masu Nasara A Rayuwa Da Mutane Marasa Nasara

Banbanci Tsakanin Mutane Masu Nasara A Rayuwa Da Mutane Marasa Nasara

Mutanen dake nasara a rayuwa suna murna idan sunga wasu sunci nasara. Mutanen da basa nasara a rayuwa suna murna idan sunga wasu sun faɗi.


Banbanci tsakanin masu nasara da marasa ita


Marubuci: Anas Darazo


Ma'abota nasara sukan tattauna hanyar da za a bi don cim ma nasara. Ma'abota rashin nasara sukan tattauna kan mutane masu nasara ne kawai ba damuwar su ce a tattauna yadda zasu samu ba.


Idan masu nasara suka samu faɗuwa ko wata tangarɗa sukan ɗora laifin akan su suyi ƙoƙarin kiyaye gaba. Marasa Nasara idan suka samu kowace irin matsala sukan ɗora alhakin hakan akan mutane ne.


Mutane masu nasara sukan ɗauki darasi a wurin kowa basa jin sun tara ilimi. Marasa nasara suna da ganin sun fi kowa sani su san komai.


Masu nasara sukanyi yabo kan daidai ɗin mutane su musu nasiha kan kuskuren su. Marasa nasara sukan rintse idon su kan daidai ɗin mutane sannan suyi ta ƙalubalantar kuskuren su.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Thursday, 16 January 2025

Uzuri 3 Masu Cutarwa Ga Matasa

Uzuri 3 Masu Cutarwa Ga Matasa

Uzuri guda uku da matasa kan ba wa kansu kariya da su, ba tare da sun san hakan ne ke katange su daga nasara ba.


Ga su kamar haka:


1. Ƙaryar busy da rashin lokaci


Matasa da yawa ba sa zuwa makaranta ko zumunci ko wani abu mai amfani ga rayuwarsu sakamakon uzurin su na wai ba su da lokaci, amma idan ka yi wa rayuwarsu duba na tsanaki za ka ga suna da lokacin aikata abubuwa marasa amfani ko wanda ba su kai wannan abun da su ƙi yin amfani ba, yaudarar kansu kawai su ke yi da su ke ganin rashin lokaci ne ya hana su yin abun da ya kamata.


Uzuri 3 Masu Cutarwa Ga Matasa
Hoto: Discover hub pages

MarubuciAnas Darazo


Zai ma ka wahala ci-gaba matuƙar ka ci-gaba da amfani da lokacin ka wajen shashanci amma kana cewa ba ka da lokaci idan an zo abu mai amfani.


2.  Isasshen lokaci


Tunanin gaba za su samu isasshen lokaci da za su yi abun da ya kamata. Eyyah! Ɗan uwa yanzu ne ka ke da dama, gobe da nisa.


Duk matashin da ya jinkirta taimakon iyaye, neman kuɗi da neman ilimi, inganta lafiya da ƙulla alaƙa mai kyau da mutane ya na ganin sai ya gama jami'a ko sai ya yi aure ko ya yi kuɗi ko sai ya shekara kaza ko ya mallaki abu kaza lallai ya sani shi makararre ne.


Ka yi amfani da damar da Allah Ya ba ka yanzu, ka yi duk abun da za ka iya koda kaɗan ne hakan ka iya zama silar ka ta zama mai nasara, jinkiri kuwa koda na daga safe zuwa dare ne zai iya zama sanadin tabbatar ka cikin ƙasƙanci.


3. Alhakin matsaloli 


Ɗorawa wasu mutane alhakin matsalolin da ka ke ciki, matasa da yawa su na ganin matsala ta same su ne sakamakon sakacin wasu mutane kamar iyaye, dangi, shugabanni, iyayen gida ko abokansu, lallai ka sani duk abun da ya same ka kai ya samu babu ruwan wani, idan har ka yi hankalin da ka gane mahaifanka ba su sauke ma ka wani haƙƙi ba wanda hakan ya jefa ka a matsala to ya kamata wannan hankalin naka ya gano ma ka mafita.


Ka sani ba ka da iko akan kowa amma kana da iko akan kanka, don haka manta da wanda sakaci ko muguntarsu ya jefa ka a matsala ba za ka iya tilasta su gyara ba, amma kana da iko da kanka don haka tilasta ma kanka ka yi abun da ya kamata.

Sunday, 16 June 2024

Karanta Hikimomin Yau Da Kullum

Karanta Hikimomin Yau Da Kullum

Aboki

Ba aboki ka rasa ba, mugun iri ne suka ragu. Shi Aboki ai ba a rasa shi, saboda nasiha yake maka akan gangancin ka, ya maka uziri akan kuskuren ka, ya yafe maka idan ka ɓata masa, ya yi ƙoƙari abotar ku ta ɗore.

Hikimomin Yau Da Kullum
Hoto: 2018 Flora expo


Marubuci: Anas Darazo


Faɗa

Idan ka tabbatar da abin da kake aikatawa ko kake faɗa mai kyau ne, yana da kyau ka zama mai ɗabi'ar ko in kula ga abinda mutane za su faɗa kan abun. Duk tsiyar su kada ka ɗaga kafa.


Mu'amala

Ka kula da irin mu'amalar da kake da mutane, ka zama mai gaskiya kada ka kuskura mutane su ɗauke ka maƙaryaci. Ka ga idan ka duba kasuwanci ko sana'a ko aure da sauran harkoki masu muhimmanci mutane sun fi son su yi da wanda suka yarda da shi ne. Idan kana da burin ɗaya cikin waɗannan abubuwa lalle ne ka gujewa ƙarya, ka zama mai gaskiya ka tabbatar ka samu yardar mutane.


Magana


Baƙar magana ba tada 'expire date' mutane sukan daɗe suna kallon ta a goshin wanda ya faɗa musu.  Ka guji faɗawa mutane baƙar magana.

Lokaci

Ya kai Matashi ka ɓata lokaci tare da Dattijai, duk lokacin da ka samu dama ta kasancewa tare da wani mai yawan shekaru wanda kuma ya taɓuka abun arziki cikin shekarun nasa, kada ka yi wasa da damar, idan ka zauna da shi za ka koyi abubuwa da yawa musamman idan kana masa tambaya.

Tuesday, 12 May 2020

Hanyar Da Kowa Yake Bi Yayi Arziki

Hanyar Da Kowa Yake Bi Yayi Arziki

Arziki nufin Allah ne, babu wani Mahaluki da yake azurtawa ko talautawa, babu wata nau'in sana'a ko kasuwa bayyananniya da aka ce a iya ita ake arziki, ba kasuwar da wani baiyi arziki ta silar ta ba, ba kuma kasuwar da wasu basu karye a cikin ta ba. Kai dai ka roƙi Allah ka kuma yi riƙo da sila ɗin.

Arziki Nufin Allah Ne

Marubuci:- Anas Darazo

Na tuna lokacin da Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba dabbobi (Akuya) ga mata suyi kiwo mutane sukai ta dariyar abun suna ganin hakan a matsayin renawa talaka hankali ko rashin sanin makamar aiki.

Yanzu sai naga wani bidiyo da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa tayi hira da wata mata da ta ci moriyar waɗancan dabbobi da gwamnatin jihar ta raba, matar tayi iƙirarin tafi ƙananan ma'aikatan gwamnati abun hannu, tunda har bashi suke zuwa karɓa a wurin ta su ce "sai ƙarshen wata" tace yanzu ma kenan nan gaba kam (idan suka ƙara haihuwa sukai yawa) tace manyan ma'aikatan ma zasu buga da su, ta bada labarin yadda Awakin guda uku da aka bata suka yaɗu daga haihuwar ɗaya zuwa uku har sukai yawan da take sayarwa take samun alheri tana ci tana sha ƴaƴan ta suna karatu.

Wannan shima misali ne ta yanda Allah Ya ke azurta bayin shi a wasu harkokin da mutane ke musu kallon ƙaskanci ko abun dariya, kada ka damu da wane irin kallo mutane suke yiwa kasuwancin ka, kai dai kayi kasuwancin da gaske ka nemi dacewa a wurin Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 27 December 2024

Makiyi Da Abokin Bogi Da Abokin Gaskiya

Makiyi Da Abokin Bogi Da Abokin Gaskiya

1. Maƙiya su ne abokan bogin da ka sani, abokan bogi su ne maƙiyan da ba ka sani ba.

2. Maƙiya za su maka fatan mutuwa, abokan bogi za su haƙa ramin binne ka.

3. Maƙiya su ne sheɗanun da ka ke gudu, abokan bogi su ne sheɗanun da za ku mutu tare.

Maƙiyi da Abokin Bogi da Abokin Gaskiya
Hoto: We are brothers

MarubuciAnas Darazo

4. Maƙiya su ne ka ke yi wa fatan kada su yi nasara, abokan bogi ke fatan kada kai nasara.

5. Maƙiya su ne su ke fatan kai ka ƙasa, abokan bogi su ne masu kai ka ƙasa.

6. Ko ka san za ka iya sanin maƙiyi zai kawo maka hari, amma abokin bogi shi ke ma ka yankan baya.

7. Zagin maƙiyi ya fi alheri akan shawarar abokin bogi.

8. Shugaban su gabaɗaya, shi ne aboki na gaskiya; maƙiyi zai iya harbin ka, abogin bogi zai maka yankan baya, abokin gaske zai mutu a kanka.

9. Abokin bogi zai yayata laifukan ka, abokin gaskiya zai gyara maka su.

10. Abokin bogi zai rungume ka ya ce jikinka yana wari, abokin gaskiya zai saya maka turare bayan ya rungume ka.

11. Abokin bogi zai taya ka ku cinye kuɗin ka ya ci zarafin ka bayan ka talauce, abokin gaskiya zai saka ka juya kuɗaɗen ka ya ba ka goyon baya idan ka talauce.

12. Abokan bogi za su yayata sirrinka, abokan gaske za su ɓoye sirrinka.


Mcedopikin ne ya faɗa a bidiyon sa, ni kuma na rubuta na fassara.

Sunday, 23 February 2020

Shin ko Kana Yin Irin Wannan Tunanin Kafin Kayi Komai a Rayuwar Ka?

Shin ko Kana Yin Irin Wannan Tunanin Kafin Kayi Komai a Rayuwar Ka?

Shin ko kana yin tunani irin wannan kafin ka yi komai a rayuwar ka.

Rayuwa Tana Buƙatar Yin Nazari..

Marubuci: Anas Darazo

Ka lura da waɗannan abubuwan:

1. Idan ka shiryawa ɗaukaka, ka shiryawa ƙasƙantar da kai.

2. Idan ka shiryawa nasara, ka shiryawa aiki tuƙuru.

3.Idan ka shiryawa zama da mutane lafiya, ka shirya yi musu uzuri.

4. Idan ka shiryawa samun masoya, ka shiryawa kyauta da sakin fuska.

5. Idan ka shiryawa faɗan gaskiya, ka shiryawa baƙin jini.

6. Idan ka shiryawa ƙwarewa, ka shiryawa koyo da koyarwa.

7. Idan ka shiryawa zama tauraro, ka shiryawa shiga duhu.

8. Idan ka shiryawa samun mutunci, ka shiryawa ƙin abun hanun mutane.

9. Idan ka shiryawa samun mace ta gari, ka shiryawa zama miji nagari.

10.Idan ka shiryawa gagarar matsafa, ka shiryawa addu'a.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa

Shin ko Kana Yin Irin Wannan Tunanin Kafin Kaci Abinci?

Karanta Yadda Ake Neman Izinin Shiga Gidan Mutane

11.Idan ka shiryawa gagarar munafukai, ka shiryawa zama mai gaskiya.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.



Saturday, 15 March 2025

Mai Kasuwancin Yanar Gizo-gizo Lura Da Wannan

Mai Kasuwancin Yanar Gizo-gizo Lura Da Wannan

1. Idan ka na kasuwancin yanar gizo-gizo, ka kiyayi ajiye kaya ga wanda bai ba ka ko sisi ba, ƙarshe za su iya zama maka asara.


Mai kasuwancin yanar gizo-gizo lura da wannan
Hoto: Patrick George/Getty Images

MarubuciAnas Darazo


2. Ba kowane kwastoma ke bambamce taya kaya da sayan kaya ba, wani tayawa ce ta kawo shi amma zai ce ya saya, kai ɗan kasuwa kai ne za ka bambamce su.


3. Lallai za a ɓata maka rai a kasuwa, ka yi haƙuri gwargwadon yadda za ka iya amma ka ƙwaci kanka iya wuya, ta tsaya a bacin rai ban da asarar kuɗi.


4. Kwastomomi su gane 'yan kasuwa su ma mutane ne, tsoka ce a zuciyarsu, yadda ranku ke ɓaci idan an ɓata muku haka nan su ma nasu ke ɓaci, ku nuna tarbiyya kada ku ɓata mana, haka idan mun kasa jurewa mun ɓata muku ku yi haƙuri mu ma mutane irin ku ba daga wata duniya mu ke ba.