Showing posts sorted by relevance for query Auta Waziri. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Auta Waziri. Sort by date Show all posts

Friday, 22 March 2024

Kalli Sababbin Kyawawan Hotunan Auta Waziri

Kalli Sababbin Kyawawan Hotunan Auta Waziri

Abdullahi Abubakar, wanda ya yi fice da sunan Auta Waziri, daɗadɗen mawaƙi ne a masana'antar Kannywood, wanda a halin yanzu tauraron sa yake ci gaba da haskawa a ko'ina.


Mawaƙi Auta Waziri
Hoto: Auta Waziri


Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.



Auta Waziri
Hoto: Auta Waziri


Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan sa.


Mawaƙi Auta Waziri
Hoto: Auta Waziri


Fatan hotunan nasa, sun burge masoyan sa.


Auta Waziri
Hoto: Auta Waziri


Ku ci gaba da kasancewa da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun sababbin hotunan mawaƙan ku.

Saturday, 8 August 2020

Sauke Sabuwar Wakar Ado Gwanja Ft Hussaini Danko - Kara Yunkuri Baba

Sauke Sabuwar Wakar Ado Gwanja Ft Hussaini Danko - Kara Yunkuri Baba

Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.


Kara Yunkuri Baba

Gamayyar mawaƙan fina-finan Hausa ne su fito su rera wannan waƙar domin ƙara tunatar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari halin da ƙasar Nijeriya take ciki a halin yanzu, kana kuma a ƙara tunatar da al'ummar Nijeriya musamman yankin arewacin ƙasar irin gudunmawar da shugaban ƙasa da gwamnonin arewa su bayar a fannin tsaro da kuma haɓaka tattalin arzikin ƙasar Nijeriya.

Taken waƙar "KAYI ƘOƘARI BABA A ƘARA YUNKURI, AKAN GYARAN ƘASA MUSAMMAN SHA'ANIN TSARO ƘYALE 'YANSAN A ƁATA BAZASU TAYAKA BA".

Idan baku manta ba, tun a shekarar dubu biyu da sha biyar (2015), mawaƙan fina-finan Hausa suke tare da Baba Buhari, idan muyi waiwaye a shekarun baya sun yi waƙoƙi da dama cikin waɗanda suka fi shahara sune: Lema Ta Yage, Sakamakon Chanji, Aikin Gama Ya Gama da sauran su.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Kaɗan daga cikin mawaƙan da suka bayar da muryoyinsu domin isar da wannan saƙon ga dubban al'ummar Hausawa dake cikin ƙasar Nijeriya dama Duniya baki ɗaya:

Adamu Nagudu
Auta Waziri
Audu Boda
Baban Chinedu
El-Mu'az Birniwa
Dan Musa Gombe
Ibrahim Ibrahim
Isyaku Forest
Jamilu Jadda Garko
Sani Sabo Kwarko

Waƙar ta hau kan  tsari bisa tsarin mawaƙan waɗanda su baje kolin basira da hikimar su a cikin waƙar.

Wannan dai sabuwar waƙa ce da Mawaƙan Sakamakon Chanji su rera cikin wannan sabuwar shekarar da muke ciki (2020), waƙar dai tazo da wani sabon salo mai tafiyar da zukatan Masoya Baba Buhari cikin farin ciki da walwala.

Wato tsayawa bayyana abinda wannan sabuwar waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 16 April 2021

Sauke Sabuwar Wakar Nazifi Asnanic Ft Hussaini Danko - Sabunta Katin Jam'iyya

Sauke Sabuwar Wakar Nazifi Asnanic Ft Hussaini Danko - Sabunta Katin Jam'iyya

 Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.


MU SABUNTA KATIN JAM'IYYA


Gamayyar mawaƙan fina-finan Hausa ne su fito, su rera wannan waƙar domin ƙara tunatar da al'ummar Nijeriya domin su hanzarta su sabunta katin su na jam'iyyar APC.

Taken waƙar "MU SABUNTA KATIN JAM'IYYA....".

Idan baku manta ba, tun a shekarar dubu biyu da sha biyar (2015), mawaƙan fina-finan Hausa suke tare da Baba Buhari. Idan mu yi waiwaye a shekarun baya sun yi waƙoƙi da dama cikin waɗanda suka fi shahara sune: Lema Ta Yage, Sakamakon Chanji, Aikin Gama Ya Gama da sauran su.

Kaɗan daga cikin mawaƙan da suka bayar da muryoyinsu domin isar da wannan saƙon ga dubban al'ummar Hausawa dake cikin ƙasar Nijeriya dama Duniya baki ɗaya:

Adamu Nagudu
Abubakar Sani (Ɗan Hausa)
Ahmad Shanawa
Alfazazi
Ado Gwanja
Abdul Smart
Auta Waziri
Dan Musa Gombe
El-Mu'az Birniwa
Hussaini Danko
Ibrahim Ibrahim
Ikram Kano
Musa Isah Gwanja
Nazifi Asnanic

Da sauransu

Waƙar ta hau kan  tsari bisa tsarin mawaƙan waɗanda suka baje kolin basira da hikimar su a cikin waƙar.

Wannan dai sabuwar waƙa ce da Mawaƙan Sakamakon Chanji su rera cikin wannan sabuwar shekarar da muke ciki (2021), waƙar dai tazo da wani sabon salo mai tafiyar da zukatan jam'iyyar APC cikin farin ciki da walwala.

Wato tsayawa bayyana abin da wannan sabuwar waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin dai sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tuesday, 23 October 2018

Yanzu - Yanzu: Sabuwar Wakar da Mawakan Hausa suka Yiwa Ganduje Mai Zafi - Ku Sauke Waƙar Yanzu a nan

Yanzu - Yanzu: Sabuwar Wakar da Mawakan Hausa suka Yiwa Ganduje Mai Zafi - Ku Sauke Waƙar Yanzu a nan

Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.



Muryar Hausa24 Yau ma gamu tafe da sabuwar waƙar siyasa wacce haɗakar mawaƙan hausa suka rerawa gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, waƙar nuna goyan bayan su a gare shi.

Waƙar ta tsaru bisa tsarikan mawaƙan waɗan da suka baje kolin basirar su a cikin waƙar.

Kaɗan daga cikin mawaƙan sune kamar haka:

Sadi Sadi Sharifai
Wazirin Rarara
Alfazazi
Abubakar Sani
Auta Waziri
Ali Jita

Da sauran su.

Ku sauke waƙar anan a kyauta.


Ku sauke waƙar yanzu domin sauraro.

Muryar Hausa24 Muna fatan za'ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Ku kasance damu a www.MuryarHausa24.com.ng domin samun bidiyon waƙar nan bada daɗewa ba, tare da cikakkiyar waƙar nan bada daɗewa ba Insha Allah. 

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode




Sunday, 18 August 2024

Karanta Hakikanin Asalin Sunayen Hausawa Tare Da Ma'anonin Su

Karanta Hakikanin Asalin Sunayen Hausawa Tare Da Ma'anonin Su

A zamanin da kafin zuwan musulunci ƙasar Hausa babbar hanyar samun sunaye ta dogara kacokam a kan faruwar wani muhimmin abu sai Bahaushe ya laɓe da guzuma ya harbi karsana, ma'ana ya laɓe da faruwar wannan abu ya sa wa yaro ko yarinya suna.


Asalin Sunayen Hausawa Tare Da Ma'anonin Su
Hoto: Hausa Naija News


Kasancewa ta mazaunin Kano sai na fara binciken nawa da ma'anar sunan.


Ga kaɗan daga cikin binciken da na gudanar zan gutsura muku ku lasa:-


1. SHEKARAU :- Yaron da ya shekara a ciki shi ake kira Shekarau mace kuwa ana kiranta SHEKARE ko SHEKAU.


2. TANKO :- Shi ne namijin da aka haifa bayan haihuwar mata da yawa.(ya ɗan bambanta da mati kaɗan).


3. DELU :- Yarinyar da aka haifa bayan maza da yawa.


4. GOSHI :- Yarinyar da lokacin haihuwar ta aka samu arziki mai yawa ba zato ba tsammani.


5. YALWA :- Yarinyar da aka haifa iyayenta na cikin wadata.


6. MAITAMA :- Yaron da aka dawo ɗibar TAMA aka tarar an haife shi.


7. ƊAN DARE :- Yaron da aka haifa da daddare.


8. TINAU :- Yaron da haihuwa ta ɗauke wa mahaifiyar shi sai bayan lokaci mai tsawo aka haife shi, shi ake kira TINAU.


9. SO-DANGI :- Yaro ko Yarinyar da iyayen  ke zaune nesa da dangi sai zama ya ƙare musu suka tashi suka dawo cikin dangi uwar na ɗauke da tsohon cikin shi ana zuwa aka haife shi, shi ake kira SO-DANGI.


10. GAMA :- A zamanin da ana aure bisa cancanta ne, to duk lokacin da wani da bai cancanta ba ya yi sa'a ya auri wata isassa/isasshiya to ɗan da ta haifa sai a sa mai suna GAMA.


11. SADAU :- Yaron da uban ya ɓata da uwarshi daga baya suka shirya to duk yaron da ta fara haihuwa sai a kira shi da SADAU.


12. AUTA :- Ƙarshen haihuwa.


13. KYAUTA :- Yaron da uwar sa ba ta taɓa haihuwa ba shekara da shekaru sannan aka haife shi.


14. DAWAI :- Saɓanin da ya kai ga saki sannan uwar ta yi kome to ɗan da ta haifa shi ake kira DAWAI.


15. BAKWAI :- Yaron da aka haifa cikin shi na da wata bakwai (Bakwaini).


16. SHAWAI :- Yaro/yarinyar da aka sha wurin haifuwar shi/ta.


17. GWAMMA :- Yarinyar da aka haifa lokacin da ake da burin haihuwar ɗa namiji.


18. MARKA :- Yarinyar da aka haifa lokacin ruwa na marka-marka.


19. AMARYA :- Yarinyar da aka haifa ranar da jinjirin wata ya tsaya, namiji kuma ana kiran shi MAGAWATA.


20. BUJI/HAZO :- Yaron da aka haifa lokacin da ake hazo.


21. CI-TUMU/SHA-GERO/SHAGE :-Yaron da aka haifa lokacin nunar gero.


Za mu kawo muku ƙari akan wannan kamar su Makwashi, Mati, Tsoho, Ɗan Dare, Talle, Magaji, Babangida, Mai Damma, Ayashe, Ajuji, Yaduwa, Bawa, Barau, Barmani, Dan Wabi, Ƙosau, Jimrau, Nomau, Wada, Gayya, Mayau, Na Hantsi, Gambo, Kadarko, da sauran su.


Tushe/Asali: Waziri Aku