Showing posts sorted by relevance for query Imran Musa Jahun. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Imran Musa Jahun. Sort by date Show all posts

Sunday, 11 August 2024

Wasikar Yabo Ta Soyayya

Wasikar Yabo Ta Soyayya

Sallama a gare ki tare da tausasan kalamai masu tausasa zuciya.


Wasiƙar yabo
Hoto: City living


MarubuciImran Musa Jahun


Ki sani yake masoyiyata tun da Allah maɗaukakin sarki ya yi ni ban taɓa ganin ko jin zazzaƙar murya mai tausasa zuciyata cikin daƙiƙa ɗaya tamkar taki ba.


Kyawun fuskar ki tare da kyawun halayenki sun zarce a misalta su  ko a suffanta su.


Domin ko farin wata bai haska ba ba wanda bai shaida cewa ke kyakkyawa ce ba.


Ki huta lafiya. 


Daga masoyinki mai tsananin ƙaunarki, IMRAN MUSA JAHUN.

Wednesday, 19 June 2024

Hirar Masoya Mai Daɗi Kafin Aure

Hirar Masoya Mai Daɗi Kafin Aure

Imran: Barka da zuwa sarauniyar zuciyata, daman tun safe nake burin zuwa gare ki domin faɗa miki irin ƙaunarki da ta ƙara yawa a zuciyata. 


Hirar Masoya
Hoto: Top10


MarubuciImran Musa Jahun


Nafisa: Hmm mai sona gaskiya na jima ina jiranka don kai na yiwa kwalliya, sannan na tanadar maka kayan alatu, gaskiya turarenka yana burge ni, don tun isowarka zuciyata ta faɗa min kai ne ka zo gare ni, kuma za ka ban dukkan jin daɗin da masoya suke ba wa juna. 


Imran: Ina so ki sani da ke zan zauna har abada ba zan iya rabuwa da ke ba, ke ce kika zama farin cikin rayuwata da ke nake alfahari a duniyar soyayya.


Nafisa: Don haka zuciyata take ƙara aminta da kai kodayaushe, ina son ka fiye da kaina, kai ne na ba wa sarautar birnin zuciyata, komai rintsi da kai zan zauna. 


Imran: Haka nake tunanin zan ji daga bakinki, daman a kullum burina ki zama uwar 'ya'yana, ba ni da zaɓi wanda ya wuce naki mai kyau da kwalliya, na jima ina jin dadin haɗuwata da ke, domin kin zamar min akalar rayuwata, ina son ki ina ƙaunarki, ina muradin zama da ke na har abada. 


Nafisa: Gaskiya bakina ba shi da furucin da zai faɗa maka irin son da nake maka, a kullum ƙaunarka ƙaruwa take a raina, kai ne ka zamo min jagoran rayuwata, soyayyar ka ta zama gata a gare ni, da kai zan yi alfahari a birnin masoya, masoyina. 


Imran: Ban son rabuwa da ke, don muryarki ta fi min zuma, zaƙi, sannan fuskarki ta fi min komai kyau a duniya, amman na ga dare ya yi sweety na, zan tafi amman ki sani da zuciyarki zan koma gida, kuma mu yi bacci tare.


Nafisa: Hmm masoyi kenan, daman kullum ruhina tare suke da naka, sannan zuciyarmu a tare suke kuma gado ɗaya suke kwana, ina so ka ƙara haƙuri don gangar jikinmu ba sa jin ɗumin juna amman nan kusa zan zama taka ka yi komai da ni na ba ka amanar kaina ka yi bacci lafiya. 


Imran: Kai dadi kar ka kashe ni mana. Na gode sweet dream. 


Nafisa: Me too, my angel. 


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.

Tuesday, 6 August 2024

Sirrin Yadda Ake Bayyana Soyayya Ga Saurayi Ko Budurwa

Sirrin Yadda Ake Bayyana Soyayya Ga Saurayi Ko Budurwa

Ana isar da saƙon soyayya ta hanyoyi da dama, wasu hanyoyin sun haɗa da wasiƙa da zuwa da kai, su ne hanyoyi mafi dacewa ko mafi ƙarfi da aka fi isar da saƙon soyayya kuma aka fi saurin gasgata cewa lallai wanda ya isar da wannan saƙo na soyayya  ya kamu matuƙa.


Bayyana soyayyar ku
Hoto: Independent


MarubuciImran Musa Jahun


NA MAZA


Zuwa da kai ya fi saƙo, shi ne mutum ya shirya, musamman ya je gidan su wadda ya gani yake so ya tura a kirawo ta, cikin shigar kamala, da nuna halin kawaici.


Idan ta fito ka isar mata da saƙon da kake tafe da shi, cikin kyakkyawan lafazi da tausasa murya, kada ka sanya ƙarya a zancenka ko batun da hankali ba zai ɗauka ba, ƙwaƙwalwa ba za ta amince da shi ba.


Abin da ya kamata ka fara shi ne ka gabatar da kanka a gare ta.


MISALI


Sunana Imran,  ba don komai na zo gare ki ba face sai don na isar miki da saƙon da nake ɗauke da shi a cikin zuciyata.


Wanda wata ƙila ya yi miki daɗi ko akasin hakan.


Na san kin san cewa Allah ta'ala shi ne wanda ya halacci soyayya, sannan ya sanya ta a tsakanin halittunsa, musamman ga jinsin mace da namiji walau Namiji ya kamu da son Mace ko Mace ta kamu da son Namiji.


To ni dai ina daga cikin waɗanda Allah ya yi

halittar so a zuciyarsu.


A wannan lokaci, a sanadin ganin ki, jin sautinki, tarbiyarki, halayenki, musamman tarbiyarki da kuma iliminki.


Saboda waɗannan halaye naki na zo domin na isar miki da saƙon zuciyata zuwa gare ki, zuciyata ta kamu da soyayyar ki, a sakamakon gamsuwa da ta yi da tarbiyarki, kuma ta ga dacewar ƙulla alaƙar  soyayya da ke.


A taƙaice wannan shi ne saƙon da nake ɗauke da shi.


Zan so ki aminta da ni, ki ba ni damar zuwa

gare ki, wata ƙila zuciyar ki ta aminta da ni kamar yadda tawa ta aminta da ke.


Wannan ita ce kawai alfarmar da nake nema a gare ki.


NA MATA


Mace ma tana iya isar da saƙon soyayyar ta kwatankwacin hakan, ta hanyar zuwa wajen wanda ta kamu da soyayyar sa ta isar masa da saƙonta, wata ƙila kunya ta hana ta, don haka sai ta rubuta wasika.



MISALI


Assalamu alaikum, bayan shimfiɗaɗɗiyar sallama wadda addinina ya tanadar, ya harkokin yau da kullum ya lafiyarka?


Bayan haka, kada ka yi mamakin ganin wannan wasiƙa tawa, ko kuma Shaiɗan ya yaudare ka cewa kada ka amince da ni domin na yi tallan kaina a gare ka.


Sam-sam kada ka yarda da hakan, ya zo a

hadisin Manzon Allah ( S. A. W) cewa a zamaninsa mata suna zuwa ga maza suna neman amincewar su domin su yi aure, don haka neman soyayyar namiji a wajen mace ba rashin aji ba ne, ko zubar da kima.


Wannan shi ne cikakken aji da kyautatawa, domin mun yi koyi ga bayin Allah na gari.


Sunana Khadijah, wataƙila ka san ni, wata

ƙila kuma ba ka san ni ba.


A wata rana ina tafiya na haɗu da kai a hanya, cikin ikon Allah sai na ji na kamu da soyayyarka sakamakon ganin tsananin kamalarka, ilimi, hankalinka, ga tsafta.


Zuciyata ta aminta da kai, ta fara azabtar da

gangar jikina.


Lallai ina buƙatar agaji daga gare ka, don haka zan so ka ziyarce ni.


Zan ci gaba daga inda na tsaya a mako mai zuwa.

Sunday, 7 July 2024

Karanta Saƙon Soyayya Na Farko A Soyayya

Karanta Saƙon Soyayya Na Farko A Soyayya

Saƙon farko da za ka fara turawa budurwa idan ka gan ta ka ji kana son ta.


Saƙon Soyayya Na Farko A Soyayya
Hoto: Pinterest

MarubuciImran Musa Jahun


Ga saƙon nan a taƙaice..:


Assalamu Alaiki So da ƙauna su ne maƙasudin wannan saƙon nawa, matuƙar zan samu so na ya shiga cikin zuciyarki zan yi farin ciki, zan yi matuƙar farin ciki mara misaltuwa tare da bada jinina da ƙarfina kai har da rayuwa matuƙar kin yarda mu sha ruwan soyayya a ƙwarya guda.


Ba na shakka ko fargaba kamar yadda na fuskanci halayyar ki sun dace da rayuwata da rayuwar masoya a ko'ina take a faɗin duniya, domin ga duk namijin da ya same ki a matsayin mata ya tsira daga wulaƙanci irin na 'yan matan zamani.


Na san za ki yi matuƙar mamakin wannan saƙon nawa, sirrin da ke cikin zuciyata ne, domin zuciyata ta daɗe tana son ki.


Rayuwata ta daɗe  tana ƙaunarki, raina ya daɗe da yabawa da halinki.


Idona ya yaba da suffar ki, bakina kuma a kodayaushe zancen ki yake yi.


Na kamu da son ki kuma so ba na wasa ba, kuma ina buri da zumuɗi da shauƙi idan kika amince da ni a matsayin masoyinki.


Ina son ki. Ina ƙaunarki, kuma an ce dai garin masoyi ba ya nisa a duk inda abun son sa yake, kuma ni a tunanina duk wanda ya ce yana son ka a rayuwa ya gama maka komai na duniya, domin shi so sinadari ne kuma bai taɓa kafuwa ko ɗoruwa sai da jinsi guda biyu. Ina mutukar ƙaunarki a raina, tun daga lokacin da na fara tozali da kyakkyawar fuskarki a gare ni, da fatan za ki amshi batuna.


Sai na ji amsata daga gare ki nan bada jimawa ba, na gode ki huta lafiya.


Daga mai ƙaunarki a kowanne irin hali Imran.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.

Friday, 13 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Da Kwaila

Gajerun Kalaman Soyayya Da Kwaila

Bayan dubun gaisuwa mai fesar da tsantsar so da ƙauna, mara misaltuwa, jinjina da yabo da kirari su ƙara tabbata a gare ki yake burin zuciyata, fatana shi ne mallakarki a matsayin uwar 'ya'yana abar alfaharina, burina mu kasance tare ba na fatan rasa ki domin muhimmancin ki a gare ni.


Gajerun Kalaman Soyayya Da Kwaila
Hoto: Prostock Studio/ISTOCK PHOTO

MarubuciImran Musa Jahun


Zuciyata da ruhina suna azabtuwa ta dalilin son da nake miki, ƙishin ruwan son ki ya gallabi dukkan ilahirin sansanin zuciyata na rasa yadda zan yi, domin samun sassauci daga raɗaɗin da zuciyata ke faman yi shi ne nuna soyayyar ki a gare ni, rashin samun haka daga gare ki kan iya janyo barazana ga rayuwata.


Na ɗauki alƙawarin samar miki da farin cikin zuciyar ki, ba zan taɓa sa wa ki ji ba daɗi a cikin zuciyar ki ba. Ina son ki.


Ke na ba mulkin zuciyata ki mulke ta yadda kike so taki ce kuma mallakin ki ce.


Ina son ki, ina ƙaunar ki ba na fatan rabuwa da ke, saboda irin son da nake miki.


Rashin samun soyayyar ki a gare ni zai iya zama silar faruwar komai, burina shi ne ki ba ni dama domin nuna miki soyayya ta haƙiƙa.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

Wednesday, 18 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Na Dare

Gajerun Kalaman Soyayya Na Dare

Ba na tunanin samun kamar ki domin raina gabaɗaya ya kamu da son ki. Na sani cewa zan yi alfahari da ke idan kika furta kalmar ina son ka a matsayin amsar ki gare ni.


Gajerun Kalaman Soyayya Na Dare
Hoto: Pinny Pinny/Dreams time

MarubuciImran Musa Jahun


Lambar yabo a gare ki mai sona.


Zinariya masoyiyar raina.


Gimbiya alkhairin rayuwata.


Sarauniya cikon farin cikina.


Tauraruwa hasken ruhina.


Lokaci ɗaya rurutaccen son ki ya ruru a zuciyata, sai dai sanin cewa ke wata daban ce cikin 'yammata, ma'ana ke tamkar sarauniyar su ce, shi ya sanya na miƙo gaisuwar ban girma a gare ki sahibata.


Ina son ki da wani irin so mai ɗauke da sinadarin ratsa dukkan sassan jiki. Ke ɗaya ce mafi haske da dawwama a zuciyata. Ina son ki.

Friday, 6 December 2024

Zazzafan Sakon Karshe Ga Saurayi Mayaudari Daga Budurwa

Zazzafan Sakon Karshe Ga Saurayi Mayaudari Daga Budurwa

Ka cuce ni, ka yaudare ni, ka ha'ince ni, tsakanina da kai sai tsinuwa kodan da ma an ce ku maza haka halin ku yake na mugunta da cin zali ga duk wata mace, musamman waɗanda suka amice muku.


Zazzafan Sakon Karshe Ga Saurayi Mayaudari Daga Budurwa
Hoto: Pathdoc/Stock Adobe

MarubuciImran Musa Jahun


Allah ya isa ita ce kalmar da zan aika maka, mayaudari kawai, ba zan taɓa yin wani abu da sunan yafiya a gare ka ba.


Kaicon ku tir da halin ku, daga tsohuwar budurwar ka.

Monday, 30 September 2024

Gajeren Sakon Nuna Amincewar Soyayya Ga Masoyi

Gajeren Sakon Nuna Amincewar Soyayya Ga Masoyi

Ka buɗe mini zuciyarka tare da barka na shiga ciki ta zamo sirrina.


Saƙon Nuna Amincewar Soyayya Ga Masoyi
Hoto: Medium

MarubuciImran Musa Jahun


Tabbas ina son ka a cikin raina, kai kaɗai kake ɗebe mini kewa, idan na ji muryarka.


Ka kewaye dukkan zuciyata gami da ruhina.


Son ka shi ne komai a gare ni.


Muradina gare ka shi ne ka zamo uban yarana.

Monday, 17 June 2024

Kalaman Soyayya A Hirar Farko

Kalaman Soyayya A Hirar Farko

Lokacin da ka nemi izini  a wajen Budurwa domim kawo mata ziyara gidansu, idan ta amince. Yadda ake samun matsala shi ne kalaman da za ka yi amfani da su ta yadda za ka sace zuciyarta ka tafi da wayonta, ka ja hankalinta ta ji kamar ta bi ka gidanku.



Kalaman Soyayya A Hirar Farko
Hoto: Getty Images


MarubuciImran Musa Jahun


Shi ne wasu samarin ba su iya ba, dalilin da ya sa kenan 'yanmata ba su amincewa da soyayyar ku.


Wallahi ko ba ka da kuɗi idan ka iya zance me daɗi na kwantar da hankali, mace za ta so ka saboda suna da tausayi.


Ga yadda za ka yi;


Haƙiƙa na yi farin ciki da har kika ba ni damar ziyartar gidanku, tun lokacin da muka haɗu na ji son ki ya shiga cikin zuciyata.


Wannan shi ne dalilin da ya sa na buƙaci ki ba ni izini na same ki a gida domin mu tattauna.


Bayan rabuwar mu da ke na lura ke mace ce mai kyakkyawar halayya da kuma tarbiyya me kyau.


Kina da Ilimi da hankali da tunani. Sannan kin iya mutunta surar jikinki wajen kyautata sa sutura da kuma nutsuwa a wajen magana.


Wannan su ne abubuwan da suka ja hankalina.


Ina so na zama garkuwa a gareki don kare miki mutuncinki.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.

Monday, 2 December 2024

Sakonnin Soyayya Na Bayyana Damuwar Zuciya Ga Budurwa

Sakonnin Soyayya Na Bayyana Damuwar Zuciya Ga Budurwa

Ba ni da laifi domin ko shawara zuciyata ba ta nema ba a lokacin da sonki ya kawo ziyarar bazata, sai dai kawai na ji farin cikina,burina,walwala da annashuwata duk suna a cikin duban tsaleleiyar fuskarki ne.


Saƙonnin Soyayya Na Bayyana Damuwar Zuciya Ga Budurwa
Hoto: Mirror

MarubuciImran Musa Jahun


Yanzu na yi laifi idan na nemarwa raina abinda ya fi so? Koda ba za ki so ni ba, to ina alfahari da cewa ba za ki taɓa samun wanda ƙaunarki ta cuɗanya da farin cikinsa ba tamkar ni.


Ban da laifi, ki yi tunani za ki tabbatar da hakan domin burin zuciya samun abin da take so. Don haka ya zama dole na sanar da ke cewa ke ce zuciyata ke so.


Ni kaina ban san lokacin da zuciyata ta kamu da tsananin ƙaunarki ba.


Sau da yawa na kan rasa bacci saboda tsananin zafin son ki, na daɗe ina zama dirshan a hanyoyin wucewarki domin kawai na ga tafiyarki irin ta ƙasaita. Ke ce kaɗai ke wahaltar da tunanina, ki yi mini uzuri.


A ƙarshe ina fatan kalamaina za su zamo masu sauƙin fahimta a gare ki.

Friday, 29 November 2024

Alamomi 9 Na Gane Mace Ba Ta Son Ka

Alamomi 9 Na Gane Mace Ba Ta Son Ka

1. Idan budurwa ba ta sonka to ba za ta taɓa yi maka maganar aurenku da ita ba, ko maganar yadda tsarin aurenku take so ya kasance ba.


Alamomi 9 Na Gane Mace Ba Ta Son Ka
Hoto: Shutterstock

MarubuciImran Musa Jahun


2. Idan budurwa ba ta son ka, za ta yi ta maka ƙorafi akan ƙananun buƙatunta.


3. Idan budurwa ba ta son ka to za ta yi maka wasa da dariya da murmushi ne kawai a lokacin da za ka ba ta kuɗi (money), ko kuma a lokacin da take so ka ba ta kuɗi.


4. Idan budurwa ba ta sonka ba za ta iya kiranka a waya da kuɗinta ba sai dai ta yi maka filashin don haka iya mutuncin da za ta iya maka kenan ta yi maka filashin amma ba za ta taɓa iya kiranka a waya ba.


6. Idan budurwa ba ta son ka to ba za ta taɓa raka ka wani waje ba, kuɗin da ita za ta karɓa daga wajenka kawai ta fi so.


6. Idan budurwa ba ta sonka ba za ta ringa ba ka shawara akan rayuwarka ba, sannan ba za ta nemi ka ba ta shawara akan rayuwarta ba.


7. Idan budurwa ba ta son ka ba za ta taɓa kawo muku ziyara a gidanku ba.


8. Idan budurwa ba ta son ka to ba za ta taɓa gaya maka gasakiya akan labarin kanta ba, sai dai ta yi ta maka ƙarairayi.


9. Idan budurwa ba ta sonka to ba za ta taɓa yarda a ce ka karɓi wayarta ka gani ba, saboda akwai lambobin samarinta da yawa a ciki.

Wednesday, 25 December 2024

Zafafan Kalaman Soyayya Da Karamar Yarinya

Zafafan Kalaman Soyayya Da Karamar Yarinya

Zarah ki ke cikin taurari, Sarauniya cikin Sarakuna haka Gimbiya kike cikin kuyangi. Ke daban ce ga komai, ƙaunarki ita ce jarina, na kan manta da komai na tuna ki.


Zafafan Kalaman Soyayya Da Karamar Yarinya
Hoto: Adobe Stock

MarubuciImran Musa Jahun


Amincin Allah ya tabbata a gare ki motsin zuciyata. Raunanniyar zuciyata ba za ta iya juriyar rashin ki a gare ni ba, babu wani daɗi da zai kai matsayin daɗin da zan ji idan kika kasance tare da ni ma'ana ki aminta da ni ki ce kina sona. 


Ƙunci ko damuwa ba ya hana ni ambaton haruffan sunayenki domin ko su ne mafi daɗi a gare ni a jerin sunayen 'yammata.


Kyawunki ya kai matuƙa ta yadda ba zan iya jeranta shi da dukkan wani kyau ba.


Rurutacciyar ƙaunarki ta cinye dukkan komai nawa, da sonki zuciyata ke rayuwa.


Na kamu da son ki a sa'ilin da ban yi aune ba, ina son ki, zan ci gaba da son ki har abada. Ke ce kawai a zuciyata, ke ce alfaharina, da ke nake a kodayaushe. Ki so ni.


Tsiron son ki ya yalwatu a ruhina a lokaci ɗaya da na kalli kyakkyawar surar jikin ki, kina da kyawun da duk wani ɗa namiji sai ya jinjina miki, ko cikin kyawawa ke ce Sarauniyar su. 

Sunday, 24 November 2024

Zafafan Kalaman Karfafa Soyayya Ga Masoyiya

Zafafan Kalaman Karfafa Soyayya Ga Masoyiya

Duk da cewa da akwai kyawawan 'yammata a duniya da yawa amma sai na ga kin yi musu zarra, ma'ana kin kere su wajen kyau da haɗuwa.


Zafafan Kalaman Ƙarfafa Soyayya Ga Masoyiya
Hoto: Next luxury

MarubuciImran Musa Jahun


Ke mai kyau ce, dole a ce kina da kyau, haka surar ki kyakkyawa ce wadda ko maƙiyinki ya san da hakan.


Ina son ki kodayaushe.


Rurutacciyar wutar ƙaunarki tana ci-gaba da ruruwa a zuciyata wanda hakan ya sanya son ki yake sake kwaranyuwa a cikin zuciyata.


Na ji son ki ne a take a yayinda idanuwana suka yi arba da tsaleliyar kyakkyawar fuskarki. 


Sai na ji bugun zuciyata yana fita da ƙarfi, dukkan wani kuzari na rasa shi, kin dolantar da ni sosai hakan ya sa na zama mara wayo.


Tauraruwarki ba za ta taɓa disashewa a zuciyata ba, abadan da'iman son ki yana tare da ni.


Haƙiƙa kin ɓoye ni a cikin hazo na so ta yadda ba na kallon kowacce 'ya mace sai ke. 

Friday, 6 December 2024

Sakonnin Soyayya Ga Budurwar Da Za A Raba Ku Don Janyo Hankalin Ta

Sakonnin Soyayya Ga Budurwar Da Za A Raba Ku Don Janyo Hankalin Ta

Da yawan masoya na rabuwa saboda tilastawa daga wajen mahaifan ɗaya daga cikinsu, idan irin hakan ta faru gare ka, ga kaɗan daga irin saƙon da za ka tura mata domin jawo hankalin yarinyar gare ka.


Sakonnin Soyayya Ga Budurwar Da Za A Raba Ku Don Janyo Hankalin Ta
Hoto: Raw pixel

MarubuciImran Musa Jahun


Ga su kamar haka:


Me ya sa ake son na rasa rayuwata tunda sauran ƙuruciyata?


Ban taɓa ganin inda aka raba hanta da jini ba kuma aka rayu ba.


Babu sauran numfashi daga ranar da zuciya ta daina amsar jini.


Babu sauran farin ciki daga ranar da aka raba uwa da ɗan ta.


Rayuwa za ta zamo mai ƙunci gare ni daga ranar da aka raba ni da ke.


Me ya sa ake son rusa tanadin da na daɗe ina yi miki don kyautata rayuwarki?


Zan iya jurewa duk ƙaddara amma ban da ta rasa ki, har yanzu ina kallonki a matsayin matata. 


Har gobe zuciyata tana muradinki, kuma rayuwata ta ginu saman farin ciki saboda tarayyar soyayyar mu, yanzu aka raba mu mece ce makomar rayuwar mu?

Wednesday, 18 September 2024

Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi

Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi

Ya kai ɗan uwana ka sani ɗabi'ar 'ya mace kamar iska ce da take kaɗawa a hankali, idan ka furta wa 'ya mace kalma mai kyau to za ka tashi a tutocin soyayyarta. Idan kuma kai mata magana mara daɗi koda kalma ɗaya ce za su rusa soyayyarka.


Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi
Hoto: Shutterstock


MarubuciImran Musa Jahun


Lallai ne ana son namiji ka siffantu da waɗannan siffofi ashirin ɗin domin ka samu cikakkiyar soyayya da ƙauna a wurin

matarka.



1. KA MUTUNTA MATARKA: Ka nuna mata kai da ita duk abu ɗaya ne ba bambanci kana da buri ita ma tana da shi, kana da sha'awa ita ma haka, lallai ne ka mutunta ta, kamar yadda kai ma kake son ta girmamaka.


Manzon Allah (S.A.W) yana cewa "Duk wanda ya samu mace to ya girmamata.". Don haka kuskure ne da jahilci a hanawa mace 'yancin faɗar ra'ayinta ko neman shawararta, ko tattaunawa da ita a cikin wasu al'amura.


Kar a maida ita kamar kayan

wasan yara, ba a nemanta sai za a buƙaceta, duk wanda yake wa mace irin wannan ɗabi'ar tabbas zai rasa soyayyarsa a cikin zuciyar matarsa.


2. KA ZAMA ABOKIN MATARKA: Ma'ana ka yi mu'amala da ita ta kowanne ɓangare, kada ka bar wata kafa a buɗe ta yadda za ta fahimci ba ka damu da ita a wannan ɓangaren ba, lallai ne ka zama mai ɗebe mata kewa ta kowanne ɓangare, mai saka ta farin ciki da nutsuwa.


3. KAR KA ZAMO MAI CIN DUNDUNIYAR TA: Ma'ana kai a kullum burinka so kake ka ga ta yi laifi kai kuma ka buɗe mata wuta. A'a! Ka zama tamkar mai koya mata yadda

za ta yi rayuwa, inda ta kauce sai ka saitata domin a kullum ita mai raunin tunani ce idan har ta aikata mara kyau, to kada ka sakamata da mara kyau. A'a! Sai ka saitata da mafi kyau, tabbas za ka dace da soyayyarta.


4. LALLAI NE KA ZAMA MAI JURE WAUTAR 'YA MACE: Ka zama mai kyautata zamantakewarka gare ta, ka saki fuskarka

gare ta, ta yadda ba za ta rainaka ba, ma'ana kada ka yi sakacin da za ta iya raina ka.


5. KA ZAMA MAI TAIMAKONTA: Yayinda ta

shiga tsanani, kada ka yi banza da ita.


6. Ka zama mai ɗebe mata kewa yayinda

take ita kaɗai.


7. Ka zama shimfiɗar kwanciyarta yayinda

ta buƙaci bacci.


8. Kar ka nuna mata ƙosawa ko ka fara gajiya da ita.


9. Idan ta kamu da cuta kar ka share ta, ka yi iya ƙoƙarin ka wajen nema mata waraka.


10. Idan za ka shigo mata gida to ka shigo da murmushi, kuma idan za ka fita ka fita da murmushi. Hmmmmm.


11. Kar ka tozarta ta yayin da ta nemi wata

buƙata a gare ka, kuma idan har za ka yi mata alkhairi, to kada a yi mata mafi ƙaranci.


12.  Idan ta yi abu mai kyau, ka yabe ta ka gode mata.


13. Idan ta yi kuskure, ka yafe mata.


14. Kar ka yabi wata mata a gabanta.


15. Ka zama mai tsafta da kwalliya.


16. Kar ka zama mai yawan mita da dawo da kuskuren da ya wuce.


17. Ka zama mai kishin iyalinka, kar ka zama Dayyus.


18. Ka zama mai girmama 'yan uwanta,

musamman iyayenta.


19. Ka zamo mai kiyaye sirrinta, kada ka

zama mai yaɗa kuskurenta a cikin ɗaiɗaikun jama'a.


20. Kar ka zama mai son kai, wato ka girmama kanka, ita kuma ka wulaƙantata.


Da fatan za mu kiyaye.


Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

Sunday, 4 August 2024

Gajeriyar Wasikar Soyayya Zuwa Ga Masoyiya

Gajeriyar Wasikar Soyayya Zuwa Ga Masoyiya

Cikin zumuɗi da zaƙuwa irin ta masoya nake rubuta miki wannan gajeriyar wasiƙa da ta ɓulɓulo daga cikin ƙoramar zuciyata.


Gajeriyar Wasikar Soyayya
Hoto: Advice


MarubuciImran Musa Jahun


Soyayya kamar yabanya take, idan ana ba ta ruwa sai ta girma, idan kuwa aka manta da ita sai ta fara yamushewa, cikin kalamai masu daɗi da baitocin bege nake ba wa soyayyar mu ruwan ƙauna. 


Ki sani cewa kina cikin zuciyata a kowacce daƙika ta saukar numfashin jikina, da soyayyar ki ne nake morewa.


Ina matuƙar ƙaunar ki masoyiyata.

Wednesday, 27 November 2024

Zazzafan Kalaman Soyayya Na Rarrashin Budurwa

Zazzafan Kalaman Soyayya Na Rarrashin Budurwa

Kin san ina sonki!!! Me ya sa za ki guje ni a daidai wannan lokacin da na kamu da matsananciyar soyayyarki a zuciyata? 


Zazzafan Kalaman Soyayya Na Rarrashin Budurwa
Hoto: Lysenko Andrii/Shutterstock

MarubuciImran Musa Jahun


Wannan ba wani abu ba ne da ba ki sani ba, ni kaɗai ne saurayi na farko da ya fara ganin ki ya ce yana son ki a duniya, ba don ba ki da kyau ba, babu wani namijin da zai gan ki bai yi fatan ki zama masoyiyar shi ba. 


Wannan shi ne abin da nake ji a zuciyata tun lokacin farko da na ɗora idanuwana a kan hotan fuskarki.


Ina son ki kuma ina ƙaunarki, ki amince da ni, ki amshi batuna, ki riƙe shi bisa amana domin zan ba ki kulawa har ƙarshen rayuwar mu.


Ya kamata ki saurare ni, kuma ya kamata ki yi wa kalamaina fahimta mai kyau.


Amsar ki nake jira masoyiya.

Monday, 17 June 2024

Kyakyatawa Dole: Yaro Da Limamin Gari

Kyakyatawa Dole: Yaro Da Limamin Gari

A wani ƙauye kimanin shekaru dubu aka yi wani yaro Ɗan baiwa, wato duk lokacin da aka je maƙabarta jana'iza sai yaron ya ga wata jar hula ta taso daga kan mamacin ta hau kan wani mutum.


Mu ƙyaƙyata
Hoto: News18


MarubuciImran Musa Jahun


Duk kuwa wanda ta hau kansa to fa shi ne mai mutuwa na gaba a garin, da Yaro ya ga haka sai ya je yasanar da Liman, da farko Liman bai yarda ba amma yaron ya dinga

faɗa masa wanda hular ta hau kansu har mutum uku kuma suna mutuwa, sai Liman ya samu yaron ya ce masa "Don Allah duk sa'adda ka ga hulal ta taho wajena ka yi min

magana".


Wata rana an je maƙabarta an haƙa rami sai ƙasa ta hau kan Liman, yaron kuma ya ga ƙasar don haka sai yake so ya sanar da

Liman don ya goge ƙasar kansa, sai ya ce "Liman kanka...."


Ai bai ko ƙarasa ba, da Liman ya zabura a guje har yanzu ba a 

samu labarinsa ba.

Monday, 5 August 2024

Sirrin Yadda Ake Rubuta Wasikun Soyayya Masu Ratsa Zukatan Masoya

Sirrin Yadda Ake Rubuta Wasikun Soyayya Masu Ratsa Zukatan Masoya

Shin ko ka taɓa samun saƙon wasiƙar da ka karanta kuma kake maimata karantawa kullum, har ba ka iya ɗauke ganin ka saboda jin daɗi?


Rubuta wasiƙar soyayya
Hoto: Cafemom


MarubuciImran Musa Jahun

Shin ka taɓa karanta wasiƙar da ta juyar da  tunanin ka ta saka zubar hawaye?


Idan ka taɓa samun irin wannan wasiƙar to lallai ka san ƙarfin da ke cikin rantsattsiyar wasiƙa.


Rubuta wasiƙar soyayya a wannan zamani ya zama ruwan dare musamman shigowar wayar salula.


Sai dai da yawa kan kasa rubuta wasiƙa 

ingantacciya ga masoyi. 


A wannan shafin zan koya maka yadda ake tsara wasiƙar ban girma.


Zan kawo maka hanyoyi daki-daki, su za ka bi ka zama ƙwararren marubucin wasiƙar soyayya. 


TUNANIN KU


Zahiri masoyin ka shi ne a kullum abin tunanin ka, shi ne ko ita ce dalilin da ya sa

kake jin za ka rubuta wasiƙa.


Wasu mutane suna kunna waƙoƙin soyayya ko wata waƙa da suke ganin tana da tasiri da soyayyar su kafin su rubuta wasiƙa. 


Kallon hoton sahiba yana taimakawa ƙwarai a yayin da kake rubuta mata wasiƙa.


Ka tsaya ka nutsu ka san abin da sahibar ka ke so, shin mene ne ya fuzgi zuciyarka da har ka ba ta masauki a cikin ta? Mene ne yake burge ka game da sahibar taka?


Dukkanin waɗannan tambayoyi za ka amsa su a cikin wasiƙar ka. 


Ga misalin irin ta nan kamar haka:


Zuwa ga kamilallar mace mai kyau da tsarin siffa, Amina.


Bayan gaisuwa mai ɗauke da shauƙin jin

yadda kike da yanayin da fuskarki take, ina miki fatan alkhairi a cikin wannan wata mai albarka. 


A kowanne lokaci na zauna ba ni da wani tunani idan ba naki ba, na kan tuna irin murmushinki da dariyar da kike mini.


Na kan tuna irin kallon da dara-daran idanuwanki ke min da ke fizgar imanin zuciyata, haƙiƙa na yi dace da samun kyakkyawar mace abar kwatance. 


Zan kasance tare da ke a duk inda kike, cikin mafarkinki, cikin tunaninki, cikin farin ciki da baƙin ciki.


Zan kasance mai share miki hawayenki, ta ya ya ma za ai na bar idanuwanki su zubar da hawaye? Komai na jikin ki yana da muhimmanci a gare ni. 


Fatana ki kasance cikin farin ciki da annashuwa, fatana ki zamto tauraruwar da ke haske duniyar mutane.


Ke ce tawa har abada, ki huta lafiya.


Idan ku kai duba da wannan wasiƙar, an gina ta ne da irin tunanin da marubucin yake a kan sahibar shi, ya gaya mata dalilin da ya sa take ƙara shiga zuciyar shi. 


To, duka duka anan zan tsaya, sai mun sake

haɗuwa a tsarin rubuta wasiƙar soyayya kashi na biyu.