Friday 1 December 2017

HOTUNA DA CIKAKKEN TARIHIN NURA M. INUWA: BABBAN DALILIN DA YASA NA FARA HARKAR FILMS DA WAKA INJI- NURA M. INUWA

Tura Wannan Zuwa
HOTUNA DA CIKAKKEN TARIHIN NURA M. INUWA BABBAN DALILIN DA YASA NA FARA HARKAR FILMS DA WAKA INJI- NURA M. INUWA.


Tarihin Nura M. Inuwa

Nura M. Inuwa daya ne daga cikin fitattun mawaka a masana'antar shirya fina-finan Hausa (KANNYWOOD).

Mawakin yana da wakoki masu yawan gaske kuma yana daya daga cikin mawakan da suke fitar da kundin wakokin su (Album) duk shekara.

Takai Taccen Tarihin
Mawaki Nura M Inuwa
Tattaunawa Kai Tsaye
Tare da Jarumi Abas
Sadiq Cikin Shirin Gani
Da Idonka.

ABBAS SADIQ : Da farko
dai masu Sauraro zasuso
suji takai taccen
tarihinka?

Nura M Inuwa : Da farko
dai sunana Nura Musa
Inuwa wanda a yanzu
akafi sani da Nura M
Inuwa, Ni Haifaffen Garin
Kano ne Gommaja
Karamar Hukumar Dala.
Nayi Makaranta na na
primary school a masaka
special primary school
daganan na wuce
Gommaja two inda inda
acan nayi secondry school
dina daga nan kuma cikin
ikon ubangiji banci gaba
ba, Daganan sai na fara
harkar waka.

ABBAS SADIQ : Nura M
Inuwa me yaja hankalin
kane har ka fara harkar
waka.

Nura M Inuwa : Aah!
Alhamdulillahi Nidai tun
farko bani da wani dalili
da yaja hankalina na fara
harkar waka, sabo da ya
samo asaline tun ina yaro
ni kaina haka kawai
inayin waka haka kuma
idan akan batamun raj
nakanyi waka domin in
huce bacin ran nan da
akamun hakama idan an
faranta mun nakanyi
waka.

Ta yadda tun bansan
kalar ko launin wakaba da
yadda take nidai kawai
inayi, daga baya kuma
saina sawa raina cewa
inason in fara waka, ina
girma ina girma sai nazo
na fara Makaranta, Sabo
da haka Allah cikin ikon
sa sai na fara waka a
Makaranta inda nakanyi
waka ta Yabo musamman
in ana Maulidi inzo in
rera a haka a haka abu
yanaci gaba.

Tarihin Nura M. Inuwa

Kancewar ba wakar Yabon
na fara yiba, Sai akazo
idan na kalli Film "Misali"
Ace wannan Film din na
daya ne lokacin ana yin
film part 1 and 2 to a
lokacin sai ya zamana ina
iya kirkirar waka ta kaina
idan na kalli film na daya
kuma ya burgeni to sai in
kirkiri waka tawa ta kaina
wacce nake ganin itace
zata zama ci gaban
wannan shirin film din.

Da haka da haka inayi
Allah cikin ikonsa har
nazo na fara Waka dana
farane kuma sai na
fahimci cewa zan iya
daukar waka a mastayin
haryace ta tura sakon ni
na fadakarwa sannan
kuma zan iya rikanta a
matsayin sana'a kamar
yadda take yanzu a
wurina.

Wannan Shine Kadan
Daga Cikin Abunda Muka
Dan Tsakuro Muku
Dangane Da Tarihin
Mawaki Nura M Inuwa,
Akwai Yiwuwar Ci Gaba
Da Kawo Muku Wannan
Tattaunawa Nan Bada
Jimawa Ba.

HOTUNA DA CIKAKKEN TARIHIN UMAR M. SHARIF: BABBAN DALILIN DA YASA NA FARA HARKAR FILM DA WAKA INJI- UMAR M. SHARIF

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: Hausa Media

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user