Saturday 10 February 2018

KARANTA KAJI: Na gaji da wannan bala’in gara in mutu in tafi Aljanna-Ibrahim Shekau

Tura Wannan Zuwa

Shugaban qungiyar Boko Haram, Abubakar
Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar
Shekau ya bayyana cewa ya gaji da bala’in da
yake gani a halin yanzu, don haka yana son ya
mutu, ya tafi Aljanna.

Haka kuma ya ce duk da cewa sojoji sun kore su
daga dajin Sambisa, har yanzu suna rike da wasu
wurare, duk da cewa bai ambata maboyar tasu
ba.

Shekau ya fadi haka ne a ranar Larabar da ta
gabata, cikin wani bidiyo na minti goma, wanda
Aminiya ta samu gani.

“Idan da kun kashe mu, me ya sa har yanzu
muke raye?”

Abin da ya fada ke nan, yana kalubalantar
hukumomin tsaron Najeriya.

Ya bayyana cewa yana nan a boye, babu wanda
zai iya gano shi, kamar kuma yadda ya yi
alkawarin ci gaba da yakinsa na kafa “Daular
Musulunci.”

“Na gaji da wannan bala’in, gara in mutu, in tafi
Aljanna,” inji Shekau a cikin bidiyon, wanda ba a
samu bayanin inda aka dauke shi ba.

A wani labari mai kamar wannan, Sojan Najeriya
sun bayyana cewa sun kara samun gagarumar
nasara a yakinsu da ’yan Boko Haram, inda a
Talatar da ta gabata suka darkaki wasu
burbushin ’yan Boko Haram da ke boye a yankin
tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa, tare da
lalata da kwato muhimman makamai da na’urorin
sadarwa.

A nasarar da suka samu, kamar yadda Kanar
Onyema Nwachukwu, Mataimakin Daraktan Hulda
da Jama’a na Shirin Yakin Lafiya Dole ya
bayyana, rundunar ta yi nasarar gano boyayyun
wuraren da ’yan Boko Haram din ke hada bama-
bamai, inda suka yi nasarar kwato makamai da
alburusai da motoci da sauran na’urori daban-
daban da suke amfani da su.

A yayin wannan aikin, rundunar ta yi nasarar
kwato manyan tukwanen gas guda 88 da
kwamfutar tafi-da-gidanka guda 1 da Rediyon
Sadarwa mai cin zangon mita 100 da sauransu.

Haka kuma an lalata masu babura 22 da kekuna
18, kamar kuma yadda aka tarwatsa rumbun
ajiyar kayan masarufi guda daya

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source by ©Bashir Suleiman

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: