Wednesday 25 July 2018

Hotuna Da Cikakken Tarihin Nasir Ahmad El-Rufa'i: Abubuwan da Yakamata Ku Sani Dangane Da Rayuwar Dan Siyasar Arewacin Nigeria Nasir Ahmad El-Rufa'i

Tura Wannan Zuwa
El-Rufai ya kasance mamba a jam’iyya mai ci a Najeriya wato APC wanda a cikin ta ne aka zabe shi a matsayin gwamnan Kaduna a zaben shekara ta 2015. el-Rufa’i ya fara shiga gwamnati ne a lokacin tsohon shugaban Najeriya wato janar AbdulSalami Abubakar inda ya rike mukamin mai bayar da shawara na musamman a harkar mika mulki.

Tarihin Nasir Ahmad El-tufa'i

Shi dai El-Rufai ya rike mukamai da dama a Najeriya wadanda suka hada da babban daracta ta cibiyar kula da sayar da kayan gwamnati da kuma ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja a shekara ta 2003 zuwa 2007.

Nasir Ahmad El-Rufai wani shahararren dan siyasa ne wanda kuma a yanzu yake zababben gwamnan jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Tarihin Nasir Ahmad El-tufa'i

Kuruciya da Rayuwar Gida

An haifi Nasir El-Rufai a garin Daudawa na karamar hukumar Faskari a cikin jihar Katsina daga kabilar Hausa. Mahaifinsa ya rasu yana da shekara takwas a duniya inda dan uwan mahaifinsa ya dauki nauyin karatun sa tun daga kuruciyarsa inda kuma ya sami halartar makarantar Barewa mafi shahara a arewacin Najeriya inda ya sami babban yabo gami da samun babbar nasarar kammala karatun a matsayin babban dalibi.

Tarihin Nasir Ahmad El-tufa'i

Karatu

Nasir El-Rufai ya samu halartar jami’ar Ahmadu Ballo dake Zariya inda ya yi karatun digirin digirgir a fannin duba kasa wanda kuma ya samu lamba ta daya wanda a turance akan kira da First Class.

El-Rufa’i ya samu halarta kwalejin Harvard da kuma Georgetown. Sannan ya samu halartar jami’ar London a shekara ta 2008 gami da kwalejin John F. Kennedy dake Harvard a June 2009.

Siyasa

Tarihin Nasir Ahmad El-tufa'i


Mutane da yawa kan kalli Nasir El-Rufai a matsayin wanda baya karbar cin hanci.

Hakan ta samar masa samun nasara a fannoni daban daban na siyasa a Najeriya.

Ya kasance makusanci ga tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo , inda wasu da dama kan kalli Nasir El-Rufai a matsayin mataimaki ga Obasanjo ko kuma ma magaji ta bakin tsohon shubagan hukumar fasa kwauri Mallam Nuhu Ribadu.

Abubuwa da dama da wadansu kan ga cewar suna da wuyar yiwuwa a zamaninsa ya iya samun aiwatar da su. Ciki harda rusau a lokacin sa a matsayin ministan babban birni Abuja. Mutane da dama sun yaba yadda ya kasance yana tsara birnin na Abuja wajen ganin ya tabbatar da ainihin tsarin sa na asali.

A shekara ta 2014, Nasir El-Rufai ya samu lashe zaben share fagen shiga takara a jam’iyyar adawa ta APC inda ya zama dan takarar gwamna na Kaduna. Nasir El-Rufai ya samu lashe zaben gwamna wanda akayi a watan Aprilu na 2015 inda ya kayar da abokin karawar sa wato gwamna mai ci a wannan lokaci Mukhtar Ramalan Yaro na jam’iyyar PDP da kuri’u 1,117,637. Duk da dai an kalubalan ci zaben a kotun sauraron korafe korafen zabe, amma daga bisani kotun ta tabbatar masa da kujerar sa watan Oktoba na 2015.

Tarihin Nasir Ahmad El-tufa'i

Gwamnan Jihar Kaduna

Nasir El-Rufai ya kasance gwamna na 22 a jihar ta Kaduna bayan ya samu rantsarwa a ranar 29 ga watan Mayu na 2015. Bayan karbar rantsuwar fara aiki, Nasir El-Rufai ya sanar da cewar da shi da kuma mataimakin sa zasu raba albashin su gami da duk wani alawus gida biyu domin bayar wa a gidauniyar gwamnati kyauta domin samun tallafawa gwamnati ta mike.

A ranar 6 ga watan Agusta na 2015 Nasir El-Rufai ya sanar da cewar jihar Kaduna zata fara asusun bai daya daga ranar 1 ga watan Satumba na 2015 wanda a karshe aka rufe asusun ma’aikatun gwamnati dake bankuna daban daban har guda 470, hakan kuma daga karshe ta samar wa da gwamnatin jiha biliyan ashirin da hudu da dubu dari bakwai (24.7 billion) wanda aka dawo dasu a asusun bai daya dake babban bankin kasa mallakin gwamnatin jihar Kaduna.

Nasir El-Rufa’i ya samu rage ma’aikatu da dama a jihar Kaduna domin rage kashe kudi da gwamnati kanyi a ko wanne lokaci wajen tafiyar da mulki daga 19 zuwa 13 wanda hakan ya bashi damar nada kwamishinoni 13 gami da samun sauki na rarar kudi biliyan biyu da dubu dari biyu (1.2 billion) a cikin watannai biyu kacal.

A 2016, Nasir El-Rufai ya kaddamar da ciyarwa a makarantun firamare na fadin jihar Kaduna inda yake ciyar da dalibai akalla miliyan daya da rabi (1.5 million). Sannan ya sako karbar kudin makaranta daga daliban duk wata makarantar firamare ta gwamnatin Kaduna domin saukakawa iyayen yara da basu ilimin farko kyauta.

Tarihin Nasir Ahmad El-tufa'i

Mallam Nasiru el-Rufai: Dangajere Kusar Yaki! Cewar Yasir Ramadan Gwale

Kamar yadda tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya taba fada a wata hira da ya yi da Jaridar This Day, cewar tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya buka ce shi da ya zabo masa mutum mai jini a jika kuma wanda ba shi da tsoro, wanda idan ma ta kama zai iya yin akuya ga mahaifiyar obasanjon don ya bashi mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja saboda ya dai-daitawa mutane sahu daga karkacewar da ya yi. Atiku ya shaidawa Obsanjo cewar Nasan wasu mutane guda biyu abokai da Allah bai sanya sun taba hada hanya da tsoron wani mahaluki ba a fadin tarayyar kasar nan, daya daga cikinsu kuwa shi ne Nasiru el-Rufai, wanda a lokacin shine shugaban hukumar sayar da kadarorin gwamnati ta kasa ( Director General
Bureau of Public Enterprises (BPE) and the Secretary of the National Council of Privatisation) .

Tabbas Mallam Nasiru el-Rufai ya nuna cewar shi ba matsoraci bane, lokacin da majalisa ta zo tantance shi a matsayin mutumin da za’a nada minister. Domin idan zamu iya tunawa anyi dauki babu dadi da el-Rufai kafin a nada shi minister, inda aka nemi ya bayar da cin-hanci shi kuma ya yi kememe ya ki bayarwa, wanda wannan ta sanya wasu da yawa daga cikin shugabannin majalisa a wancan lokacin jin kunya ciki kuwa harda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Nasir Ibrahim Mantu, inda el-Rufai ya bayyana a majalisa dauke da al-qur’ani a hannunsa ya yi rantsuwa cewar an nemi hanci daga wajensa, kuma shi Mantu ya karyata, inda el-Rufai ya bukaci Mantu shima da ya rantse da Al-qur’ani amma hakan ta gagara inda ya ce shifa bashi da tsarki duk kuwa da cewar akwai makewayi a majalisar, kusan zamu iya cewa tun a wannan lokacin el-Rufai ya nuna jarumtaka da tabbatarwa da duniya cewar shifa ba mutumin banza bane.

Wannan namijin kokari da bajinta da el-Rufai ya nuna, shi ya sa jihar Georgia da ke kasar Amerika ta bashi izinin zama dan wannan jihar, wanda yanzu haka el-Rufai yana daga cikin ‘yan Najeriya da suke zuwa kasar Amerika ba tare da anyi musu binciken kwakwaf ba.

Lokacin da Mallam Nasiru el-Rufai ya zama babban ministan babban birnin tarayya ya nuna babu sani babu sabo. Domin ya kau-da duk wasu gine gine da akayi ba bisa ka’ida ba, ciki kuwa harda gidan matar shugaban kasa marigayiya Stella Obasanjo da gidan shugaban PDP na wannan lokacin Sanata Amadu Ali da wasu manya manyan kusoshin gwamnati a wancan lokacin. Haka dai el-Rufai ya ringa sanya gireda yana ma-ke duk wani gini da aka gina shi ba bisa kai’da ba a Habuja.

Mallam Nasiru el-Rufai kusan shine ministan Abuja mafi dadewa a tarihin wannan birni tun daga 1999 har zuwa 2007, kuma ya yi aiki dai-dai nasa.

Tun da Marigayi Mallam Umaru Yar’Adua ya zama shugaban kasa el-Rufai ya tsallake yabar kasar nan inda ya tafi kasar Amerika ya koma makaranta, ya halarci kwasa kwasai da dama a fannoni daban daban, ciki kuwa harda katafariyar Jami’arnan ta Harvard, kadan daga Makarantun da el-Rufai ya halarta sun hada da Jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria, Najeryia, Jami’ar London ko University of London a Burtaniya da Harvard Business School, Arthur D. Little School of Management a birnin Massachusetts da Georgetown University da School of Foreign Services a birnin Washington dukkaninisu a kasar Amerika da kuma D.C. da John F. Kennedy School of Government da Harvard University duk dai a can Amerika.

Sannan el-Rufai yana da babbar Lambar yabo ta kasa wadda ake kira OFR (Officer of the Order of the Federal Republic of Nigeria) wadda aka bashi tun yana BFE, kuma yana da digirin girmamawa wanda Jami'ar Abuja ta Bashi a 2005 wato Doctorate Degree.

Bayan da el-Rufai ya dawo gida Najeriya, ya fada Jam’iyyar adawa ta CPC inda ya mara baya ga takarar tsohon shugaban kasa Gen. Muhammadu Buhari duk kuwa da ana kallon zai goya baya ne ga takarar babban abokinsa wato Mallam Nuhu Ribadu.

A halin yanzu dai Mallam Nasiru el-Rufai shi ne babban bakaniken jam’iyyar ta CPC wadda Buharin ya dora masa wannan nauyi na dai-daita sahun jam’iyyar kamar yadda a yiwa birnin tarayya Abuja, saboda fama da matsaloli da jam’iyyar ta ke yi a kusan daukacin jihohin kasarnan.

Bayan haka kuma, el-Rufai shi ne kusan mutum daya tilo wanda tauraruwarsa ke haskawa wajen adawa da gwamnatin Goodluck Jonathan da kuma Jam’iyyar PDP.

Mallam Nasir el-Rufai ya dauki lokaci yana sharhi akan kasafin kudi na shekarar ta 2012 inda ya yi kaca-kaca da gwamnatin Jonathan ya nuna ma basu san me suke yi ba.

Hakan ta sanya el-Rufai ya dinga daukan hankalin jama’a a ciki da wajen kasarnan wajen yadda yake fashin baki a harkar tafiyar da wannan gwamnatin musamman a harkar da ta shafi tattalin arziki, wannan ta sanya jami’an SSS suka ringa sanya masa tarko suna kamashi a kusan duk lokacin da zai yi wata tafiya zuwa kasashen waje, haka nan yake tsallake irin wannan turaku da ake sanya masa.

Bahaushe ya ce al-kalami ya fi Takobi, lallai wannan magana haka ta ke, domin shakka babu wannan gwamnatin Jonathan babu alkalami da ta ke jin tsoro a kullum kamar na el-Rufai, domin sun san cewar mai ilimin gaske ne kuma masani ta fannoni da daman gaske.

Mallam Nasiru el-Rufai dai idan ka ganshi irin mutanan nan ne da zaka gansu ‘yan tsirit wato ba shi da wani cika ido, wannan ce ma ta sanya abokansa suke masa lakabi da sunan GIANT wato wani babban mutum kamar dai yadda Bahaushe yake ce wa
gajere malam dogo .

Lallai kam ya zuwa yanzu babu wani daga cikin ‘yan Adawa wanda tauraruwarsa take haskawa kamar el-Rufai ba, kuma duk wannan ya faru ne ta sanadiyar al-kalaminsa da yake caccakar wannan gwamnati da shi. Tabbas maganar Bahaushe gaskiya ce da ya ce Alkamai ya fi takobi, domin idan da fada za’a iya da takobi watakila da farat daya za’a gama da el-Rufai amma da yake fadan na alkalami ne, babu yadda aka iya da shi sai dai a kayar da shi da hujja idan ana da ita.

Lallai Najeriya tana bukatar mutane masu gaskiya wadan da zasu iya yakar cin-hanci da rashawa da gaskiya kuma hazikai irinsu Mallam Nasiru el-Rufai.

Takaitaccen Tarihin Rayuwar Dr Rabiu Musa Kwankwaso


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


Source: Muryar Arewa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user