Sunday 22 September 2019

KARANTA GUSHEWAR TSOFFIN AL'ADUN MU NA HAUSA A WANNAN ZAMANIN DA MUKE CIKI

Tura Wannan Zuwa Ga
"ƙaƙa-tsara-ƙaƙa"

Marigayi Mallam Aminu Kano ya rubuta a littafin sa 'Hikayoyin Kaifafa Zukata' wanda aka soma wallafawa a cikin shekarar 1982, cewar tabbas kyawawan al'adun Hausawa sun soma dusashewa tun a wancan lokacin, tare da maye gurabensu da ruɓaɓɓun al'adun da ake koyowa daga Turawa.


Gushewar Tsofaffun Al'adun Hausawa


Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo

Malamin yace "Babu shakka, duk mai hankali zai bar wuri a ransa inda zai karɓi juyin zamani. Amma kuma ya yi hankali kada ya karɓi kowanne irin juyi, in ya yi haka yanzun nan sai a neme shi a rasa.

Domin kuwa asali zai rasa. Shikuma duk wanda ya rasa asali ya zama banza a duniya.

Misali, a da akwai abin da ake kira "tsarunce". Wato abota tsakanin tsara saurayi da budurwa.

Yadda ake yin sa shine, budurwa za ta je gidan saurayinta ta kwana; ta dawo gida da safe a idon kowa saboda kowa ya amince babu maganar baɗaka a game da su ko ƙyas.

Domin a wurin kwanciya ma juya baya ake yi.

Idan ya kuskura ya juya gabansa sai ta yi wuf ta tsallake ta tafi gida komai nisan dare.

Daga nan shi kam ya samu matsala, kafin ya samu wadda zai aura sai an kai ruwa rana domin ya ɓata sunansa, ya baiwa kowa kunya.

Yanzu ma wa ke jin labarin wannan al'ada balle ya jarraba?

Al'ada ta biyu mai ban sha'awa itace ta wankan amarya, wanda akeyi idan mace ta yi haila ta fara yin durwa. Shi ya sa ake kiran ta da "Mai durwa" ko "Budurwa".

A ranar da za a kai ta ɗakin miji sai an yi mata wanka a gaban danginta da na mijinta, don a tabbatar yarinyar su ƙalau take..

Ranar biki kuwa asha kiɗan ƙwarya wanda ake kira 'tirƙeƙe-tirƙeƙe'. Koda yake yanzu an fara mancewa da shi, har an soma shan coca-cola da sauran abubuwan zaƙi. Fatan mu dai kada wannan ya janyo shan giya a tsakanin matan aure.

Wannan al'ada ma tuni an fancakalar da ita.

Al'ada ta uku itace gaɗar samari, wadda tuni aka daina ta.

Amma kowa ya san farin jinin rawar 'tamalmala-tamalaye' da 'ruwan jiran bawaita'.

Haka ma rawar ƴan mata a dandali ta fara sanewa, sai rawar disko da ta iskanci daga America.

"ƙaƙa-tsara-ƙaƙa".

Don haka yawan al'adun mu na kirki an sauya su da na iskanci da rashin hankali.

DUBA WADANNAN:

Kalli Yadda Aka Kashe Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto A Kan Idona-Inji Direban Sardauna

Karanta Takaitaccen Tarihin Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN BIAFRA

Saboda haka yaa kamata ga duk abubuwan da zasu zo sababbi lallai ne matasa su tsaya su auna tasirin su a ƙasa don su yarda ko su ƙi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user