Friday 29 November 2019

KARANTA LABARIN SOYAYYAR WANI MATASHI DA MUTUWA TA RISKE SHI YANA TSAKA DAYIN SOYAYYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Kwanakin baya, Sheikh Tijjani Ahmad Gurumtum ya gabatar da lakcoci guda goma (WASIYYOYI GOMA DAGA CIKIN SURATU AN'AM) lokacin da Malam yazo kan wasiyyar da take magana akan KISAN KAI ya bada wani labari mai ban tausayi da tsoratarwa.

Rayuwar Soyayya

Marubuci: Datti Assalafiy

Wadanda suke bina a group WhatsApp na saka Lakcocin.

Malam yace; akwai wani mutumi da ya sani yazo ya sameshi da wani labari, labarin shine kamar haka:

Wani saurayi ne bai da sana'a yana neman wata budurwa suna son juna, sai mahaifin budurwan ya gargadi saurayin da kada ya sake zuwa gurin 'yarsa saboda bai da sana'a
Saurayi bai hakura da zuwa ba.

Uban yarinyarya sake kama saurayin a kofar gidansa, sai ya masa gargadi na karshe, sannan ya bada sanarwa a unguwar cewa idan anga yaron ya sake zuwa gurin 'yarsa a dauki mataki.

Duk da haka saurayin bai hakura da zuwa ba, watarana da yazo gidansu yarinyar, sai matasa suka tasammasa zasu kamashi, shine sai ya rantama a guje zai gudu, sai makwabcin Uban yarinyar ya yiwa saurayin ihun barawo, nan da nan jama'a suka kawo dauki aka buge saurayin ya mutu har lahira.

Iyayen yaron da sukaji labarin abinda ya faru cewa 'dansu ya je zai aikata sata ne aka bugeji ya mutu, sai hankalinsu yayi mummunan tashi, suka shiga cikin wani yanayi na tashin hankali da damuwa da bakin cikin 'dan su ya bar musu mummunan tabo da bakin tarihi, amma dai sun hakikance cewa 'dansu ba barawo bane, domin ba su taba kamashi da laifin sata ba, daga karshe suka barwa Allah, bayan wani lokaci bakin ciki ya kashe uban saurayin.

Ana nan shi kuma wancan makwabcin Uban yarinya da yayi uhun barawo wa saurayin da aka kashe, sai Allah Ya cire masa nutsuwa a zuciyarsa, sai ya tsinci kansa cikin damuwa da firgici da rashin nutsuwa, hankalinsa yayi mummunan tashi, sai ya je ya samu Malam Ahmad Tijjani ya bashi labarin abinda ya faru, sai Malam ya bashi shawara cewa ya tafi yaje ya binciko labarin iyayen yaron don ya nemi yafiyarsu, idan ya tashi tafiya neman iyayen yaron ya tafi da mutane masu mutunci Dattawa.

Akayi dace suka je suka samu gidan su yaron, aka kaisu gaban mahaifiyar yaron, aka bata labarin duk abinda ya faru da 'danta har aka masa ihun barawo, sai Uwar yaron tace a nuna mata wanda yayi ihun barawo aka kashe 'danta, sai aka nuna mata, da ta kalleshi sai ta fashe da kuka.

Bayan ta nutsu sai ta bada jawabin cewa;

Uban yarona bakin cikin abinda ya faru da yaronmu shine yayi ajalinsa, don girman Allah a bar wannan maganar sai ranar tashin Al-Qiyamah Allah Ya mana Hisabi da kansa, haka suka dawo, magana sai an tsaya a gaban Allah.

Malamai sun karantar da wani Hadisi daga Manzon Allah (SAW) da ke cewa:

Ranar tashin Al-Qiyamah kafin a fara yin hisabi wa mutane, wani tsun-tsu zai jawo wuyan wani mutum yazo dashi gaban Allah yace; "Yaa Allah wannan mutumin ya harbe ni a duniya, ya kashe ni, kuma ba nama na zai ci ba, haka kawai ya kashe ni, Ya Allah Ka yi hisabi tsakanina dashi, sai ayi hisabi a tsakanin su".
Inji manzon Allah (SAW)

Abunda ake so a nuna maka a cikin wannan Hadisin shine, duk wanda ya kashe mutum ko yayi sanadin kashe wani mutum a babin zalunci ya shiga uku ya lalace, ina kuwa ga mutanen da suka zubar da jinin bayin Allah musamman Malamai magada Annabawan Allah? a ranar da zasu shako wuyan wanda ya kashe su, da jini a jikinsu yana kamshin turaren Almiski su kawo gaban Allah su ce Allah Ka tambayeshi laifin me na masa ya kashe ni?

Ina mutanen da suna ji ana ihun barawo ko an kama barawon mashin sai su bugeshi su kunna masa wuta ya kone kurmus? wa ya fada muku hukuncin barawo kisa ne a Musulunci?

MAKALOLI MASU ALAKA:




Wallahi duk wanda ya taimaka aka kashe rayuwar da hukuncinta ba kisa bane to ya shiga uku ya lalace, kada ka yarda a hada kai da kai ko ka tallafa ta kowace hanya a kashe wani, akwai tashin hankali da zai biyo ka a nan duniya ko a ranar gobe ƙiyamah.

Allah Ka tsaremu Amin!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user