Saturday 9 November 2019

KARANTA MANYAN LADUBBA AKAN MUSULMI GUDA 10 A RANAR JUMA'A

Tura Wannan Zuwa Ga
Hakika Annabi (S.A.W) ya kebe ranar juma'a da wadansu Ladubba masu yawa.

Yayin Zaman Tahiya

Marubuci: Abu Aysher

Ga kadan daga cikin su:

1-Karanta suratul Sadaja da suratul Insan Acikin Sallar Assuba ta ranar Juma'a.

Domin Annabi s.a.w ya kasance yana karantasu a Sallar assubar ranar Juma'a.

@Bukhari da Muslim.

2-Yawaita Yin Salati ga Annabi s.a.w

Annabi s.a.w yana cewa:

"Ranar juma itace mafificiyar rana daga cikin ranakunku acikinta ne aka halicci Annabi Adamu................. Kuma ka yawaita yimin Salati acikinta......"

@Ahmad Kuma Albany yace Hadisine HASAN

@Ana fara yawaitawa

Annabi s.a.w Salatine na ranar juma'a tun daga daran juma'ar wato yau alhamis da dare kamar yadda wani Hadisin ya bayyana.

3-Yin wanka ranar juma'a

Saboda Fadar Annabi s.a.w:

"Idan ranar juma'a ta riski dayanku to yayi wanka".

@Bukhari da Muslim

4-Sanya Turare Da Yin Aswaki.

Annabi s.a.w yana cewa:

"Wankan ranar juma'a wajibine akan duk wanda ya balaga,da yin Aswaki da Sahafa abinda ya saukaka na Turard".

@Muslim

5-Zuwa Masallacin Juma'a da wuri.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

"Idan Ranar juma'a tazo Mala'iku suna tsayawa abakin kofar Masallaci suna rubuwa wanda yazo dawuri sannnan wanda ya biyo bayansa................ idan kuma liman ya hau kan minbari yafara khudiba sai su nade takardun su saurari khudibar liman".

@Bukhari da Muslim

6-Karanta Suratul Kahfi.

An samu daga aikin wadansu Sahabbai R.A sunayin Hakan.

@Saheehul Jami'i

7-Yin Shiru da Sauraran Khudiba idan liman Yanayin Khudiba.

saboda fadar Annabi s.a.w:

"Idan kacewa dan uwanka yayi shiru alokacin da liman yake huduba, to kayi Lagawu".

@Bukhari da Muslim

8-Kada ka riƙa ketara mutune dan Kazauna asahun gaba, ka zauna idan sahu ya tsaya

Daga Jabir Dan abdillahi yana cewa wani mutum yashiga Masallaci ranar juma'a alokacin Annabi s.a.w yana yin khuduba sai ya riƙa ƙetara mutane, sai Annabi s.a.w yace dashi

"Zauna hakika ka cutar ka cutar".

@Ibn Majah ya ruwaitoshi kuma Albany ya Ingantasa.

9-Yin Nafila raka'a guda biyu, idan kashiga Masallacin koda liman yana Hudubane

Annabi s.a.w yana cewa:

"Idan dayanku yazo sallar juma'a sai ya tarar da Liman yana huduba,to kada ya zauna har sai yayi sallah raka'a biyu sannan ya zauna".

@Muslim

10-Yawaita rokon Allah aranar Juma'a

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

"Ku yawaita rokon Allah aranar juma'a domin akwai wani lokaci acikinta wanda babu wani bawa da zai dace da wannan lokaci ya tsaya yana rokon Allah acikinsa face Allah ya bashi abinda yaroka".

Sai yayi nuni da hannunsa akan lokacin dan kadanne.

@Bukhari da Muslim

Amma malamai sunfi rinjayar da lokuta guda biyu:

1. Daga Hawan Liman kan mimbari zuwa kare Sallah.

2. Daga Bayan Sallar La'asar zuwa Faduwar rana.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA KADAN DAGA CIKIN FALALAR RANAR JUMA'A

Karanta Amfanin Sada Zumunta Guda 20

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

Amma magana mafi inganci kuma mafi rinjaye awajan Malamai shine daga bayan Sallah La'asar zuwa faduwar Rana.

Allah ne mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user