Saturday 28 December 2019

Shin dagaske Ne Jaruma Halima Atete ta Kusa Amarcewa?

Tura Wannan Zuwa Ga
Batun auren fitacciyar jaruma Halima Yusif Atete daya daga cikin manyan jarumai a masana'antar finafinai ta Kannywood ya ja hankalin masu kallon, dama bibiyarsu shafukan sun a soshiyal midiya da ma yan masana’antar ta kannywood.

Jaruma Halima Atete

A yan kwanakin nan ne dai maganar auren Halima Atete ta kara yin karfi a cikin masana'antar fina-finai ta Kannywood, wanda hakan ya sa duk inda ka samu 'yan fim sai ka ji labarin su ke yi.

Baya ga haka ma labarin ya kara karfi ne ta yadda aka ga na kusa da ita su na dora labarin a shafukan su na soshiyal midiya.

A sakamakon hakan ne ya sa Sashin labarai na Northflix ya nemi jin ta bakin jarumar Halima Atete kan gaskiyar maganar auren na ta, sai dai duk kokarin da muka yi na samun ta abin ya gagara, kuma mun yi ta kiran ta a waya ba ta daga ba, baya ga sakon kar ta kwana da muka tura mata amma ba mu samu amsa daga gare ta ba.

Sai dai daya daga cikin makusantan ta Isa Bawa Doro ya tabbatar mana da gaskiyar maganar auren, in da ya shaida mana cewar, ai an ma daga auren ne shi ne ya sa ba a yi ba, domin an shirya za a yi auren ne a cikin wannan watan na Disamba, amma sai aka daga shi zuwa sabuwar shekara.

Mun tambaye shi ko wa Halima Atete za ta aura?

Ya amsa mana da cewa; Har yanzu babu Wanda zai iya fada maka mutumin da Halima za ta aura domin kowa hasashe ya ke yi, amma a hasashen da mutane ke yi shi ne ana zaton Isiyaku ferus mawakin siyasar nan da ya yi tashe wajen wakar Buhari da Jam'iyyar A P C za ta aura.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Mafi Yawancin Mazajen da Suke Son 'Yam Matan Kannywood Mayaudara Ne - Jaruma Maimuna Muhammad

Karanta Abinda Mutane Suke Cewa akan Shigar 'Yan Daudu da Jarumi Rabi'u Rikadawa Yayi a Wani Sabon Shirin Film

HUKUNCIN DA KANNYWOOD TA DAUKA AKAN HOTUNAN TSIRAICIN RAHAMA SADAU - AFAKALLAH

Jarumar ta dauki lokaci mai tsawo ta na soyayya da mawakin, kuma soyayyar ta su ba a boye take ba, domin a tsawon zaman Halima Atete a harkar fim, babu wani da aka taba gani ta bayyana soyayyar sa a fili kamar ta sa, saboda haka ne ma aka fi kyautata zaton shi ne angon na Atete.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





Source: Northflix
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user