Wednesday 19 February 2020

Karanta Ma'anar Soyayyar Gaskiya a Mahangar Masana

Tura Wannan Zuwa
Ina ganin wasu masu bincike da fashin baƙi dangane da ma'anar soyayya, ko ƙauna, koma bege za su iya yarda da ɗan bayanin da zan yi a taƙaice, wanda wata ƙila a sami matsaya guda ɗaya a ƙarshe.

Rayuwar Soyayya

Marubuci: Baban Manar Alkasim

Kalmar So ko Kauna ana iya fassara ta ne da irin madubin da kowa yake kallonta, amma waɗannan kalmomi guda biyu, kowacce daga cikinsu tana tsayawa ne a matsayin ɗayar, sukan zama aikatau ko suna, misali: "Ina ƙaunar ki" sai ta ba da amsa da cewa "Ni ma ina son ka" a ƙarshe dai duk suna son juna, har ma sun zama ƙawaye, duk da cewa ranar suka fara ganin juna.

Akan ce kuma "Wannan abin fa so ne" sai a ce "I, wallahi ƙauna ce ta gaskiya" dukkansu a nan sunaye ne, wasu suna ganin ƙauna ta fi so ƙarfi, amma a zahiri duk abu guda ne, don kana iya gaya wa mutum kana ƙaunarsa ko kana son sa a ranar farko da ka fara ganinsa, idan ka ce kana son sa ko kana ƙaunarsa abu guda kawai zai fahimta, wato yana zuciyarka.

Abubuwan da suke janyo so ko ƙaunar wani, ba a iya iyakance ƙimarsu ko gwargwadonsu ko yawansu, galibi akan iya faɗin kaɗan ne kawai.

Amma daga cikinsu akwai:

1. Dukiya
2. Kyau
3. Tausayi
4. Matsayi
5. Iya kyawawan lafuza
6. Zama wuri guda
7. Fahimtar juna
8. Faɗa
9. Sabo
10. Abuta
11. Furta kalmar so
12. Kunya da sauran kyawawan ɗabi'u
13. Kallo ɗaya
14. Iya kwalliya
15. Zaƙin murya
16. Jarumta
17. Gaskiya da riƙon amana
18. Yawan kyauta da jin kyawawan halaye

Wani zai ce maka wallahi ina son wane ko wance amma ba dalili.

A lokacin da ka haɗu da mutum, sai wasu ƙwayoyi su yi tashin gwauron zabi su dira a kanka, in suka kutsa idanunka, sai ka ji ganin wannan mutumin kawai kake so, in suka isa kunnenka, sai ka ji kana son jin muryarsa kowani lokaci, in kuwa suka gangaro bakinka, to ba ka da wata hira sai ta sa, a lokacin da suka haura ƙwaƙwalwa, nan fa tunaninsa zai dabaibaye ka, a haka za su shiga zuciya, in da za ta buga su har su watsu a cikin jikinka yadda kowace gaɓa ta ka za ta fara aiki dominsa, ƙafafu su so zuwa wurinsa, hannu su so taɓansa da sauransu.

A wannan gaɓar za ka kasa ɓoye abin da yake damun ka, har sai ya sani, yadda kalmar za ta canza suna zuwa soyayya, in kuwa ka kasa sanar da shi, sabo da nisa ko mantuwa da sauran su lamarin ya zama bege, musayar wannan kalma ake kira soyayya, kai a koda yaushe za ka iya aiki da kowace gaɓa don faranta wa masoyinka rai, kuma a cikin kowace iriyar sifa ka gan sa.

Irin wannan soyayya ta gaskiya in ba aure ba ta yuwuwa "Kamar dai yadda Dr Aminu Sagagi ya faɗi ( A wata hirata da shi)" domin kuwa wasu gaɓoɓi ba za ka iya motsa su ba dominsa, sabo da haramci, kusan duk gaɓoɓin ma a cikin haramci za a yi aiki da su in ba aure, kallo, ji, shaƙa ko taɓa jiki.

Kamar masoya mace da namiji kuwa, ba wanda yake iya fitowa a haƙiƙaninsa, domin ita ba za ta zauna kusa da kai ba sai ta sha ado da nau'o'in ƙanshi kala daban-daban, ta canza murya, komai kasawar abu sai ta yi masa murmushi, ba wata mummunar ɗabi'arta da za ta yarda ka sani, kai ma ɗin haka, ga ma kuɗi da za ka riƙa miƙawa kamar ba na ka ba.

To da an shiga ɗakin aure, ayyukan gida sun dabaibaye ta, wasu sirrori na zahiri sun bayyana, ɗabi'un da aka ɓoye sun fito sarari, kai ma neman halas ya sa ka dawo a gajiye, nauyin gida ya hana ka miƙawa, ku biyun dole ku canza, sai kowa ya fara tunanin ɗan uwansa ya canza masa, sai a ce soyayya ta ƙare sai zaman haƙuri, tsakani da Allah ba ta ma fara ba, kawai dai tun farko ne ba a gina ta a matsayinta ba,  tsabar sha'awa ce kawai ake mata kallon soyayya, da zarar kowa ya sami ɗan uwansa sai rigima.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA KADAN DAGA CIKIN ALAMOMIN GANE MASOYIYA TA GASKIYA

SHIN KO KASAN ME NE NE ASALIN SO?

KARANTA BABBAN KALUBALEN DAKE GABAN SAMARI

SHAWARA

Mu rage zaman hira sai bayan aure domin samun soyayya ta gaskiya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user