Monday 27 January 2020

SHIN KO KASAN ME NE NE ASALIN SO?

Tura Wannan Zuwa Ga
Sau da dama mutane basu san me ake nufi da So domin ALLAH da ƙi domin ALLAH ba, su dai kawai sun sani a baki amma sam basu san shi a aika ce ba.

Kaso Mutum Don Allah Ka kuma ƙi Shi Domin Allah...

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

WANNE IRIN SO NE DOMIN ALLAH ?

SO DOMIN ALLAH: Shine kaso mutum domin yana son ALLAH kuma yana son Addinin Musulunci kuma yana tsaye wajen bin dokokin addinin tare da sauke haƙƙoƙin addini a Taƙaice mutum ne mai kwaikoyon Annabi (ﷺ) ta kowace fuska.

Wannan shine mutumin da ya cancanci a soshi saboda tsayuwa ga ALLAH da bin umurnin ALLAH.

Duk wata soyayya da zaka so mutum saboda wasu abubuwa kamar kaso shi saboda dukiyarsa, ko kuma saboda kyawunsa, ko kuma saboda yaɗuwar sunansa a Duniya ko don shi mutum ne mai yawan mutane kaima ka shiga sahun son shi saboda yawan jama'arsa ko wani abu mai kama da haka toh wannan duk shirme ne.

Sau da dama mutum sai yayi ta ikirarin wai yana son mutum amma kawai yana son shine don wasu abubuwa masu gushewa, baya tunanin shin wanda yake so ɗin nan yana son ALLAH, shi dai kawai ba ruwansa idan dai wanda yake so ya dace da abubuwan dake burge shi shikenan ba damuwarsa bace yaso ALLAH ko kada ya soshi. Idan ya mallaki abubuwan da yake so shine masoyin sa, idan kuma ya rasa Toh shine maƙiyinsa. Wannan shine halayyar mafi yawan mutane.

WANN IRIN ƙI NE DOMIN ALLAH ?

ƘI DOMIN ALLAH: Shine kaƙi mutum domin yana ƙin addinin ALLAH kuma baya sauke haƙƙoƙin Musulunci, irin wannan mutum shi yafi cancanta aƙi shi domin idan zaka so wanda yake ƙin ALLAH da addininka, zaka iya tauye addininka ta wani waje.

Duk da haka ba a hanaka yin mu'amala da wanda yake ƙin ALLAH da addininka ba kamar kyautata masa idan bai yaƙe ka ba, ko kasuwanci tsakaninka dashi da dai sauran mu'amala, amma dai kada ka ruɗi kanka cewa wai yana sonka don kawai kai kana son shi har ma hakan yakai ka ga sassutawa a inda shari'ah ta tsananta don shi.

Ka sani cewa duk wanda yaƙi Ubangijinka da addininka bazai taɓa sonka ba koda kuwa kai ka nuna masa soyayya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ALAMOMI 10 DAZAKA FAHIMCI MACE TANA SON KA

KARANTA LABARIN SOYAYYAR WANI MATASHI DA MUTUWA TA RISKE SHI YANA TSAKA DAYIN SOYAYYA

KARANTA ZAFAFAN SAKONNIN SOYAYYA GUDA 32 MASU RATSA ZUKATAN MASOYA

A lura cewa duk wani SO wanda badon ALLAH bane indai don wani abu mai gushewa ne na Duniya to ƙarya ce ba soyayya bace. Kuma duk wani ɗan adam wanda bazai ringa tunatar da kai da kusantar da kai zuwa ga ALLAH ba toh baya daga cikin masoyanka sai dai ka sanya shi cikin jerin maƙiyanka.

ALLAH Ya haɗamu da masoyan mu masu son mu don ALLAH, Ya nisantar damu da duk wanda ke son mu badon ALLAH ba Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user