Friday 7 February 2020

Shin ko Kasan Abinda Ya Faru da Kai a Farko Rayuwar Ka Kuma Zai Sake Faruwa a Karshen Rayuwar Ka?

Tura Wannan Zuwa Ga
1. Ka zo Duniya kana kuka, ƙarshen ka za'ayi maka kuka.

Komai Mai Gushewa ne Hatta ita kanta Duniyar..

2. Ka zo Duniya tsirara sai a kayi maka tufafi. ƙarshen ka zaka koma tsirara a kuma yi maka Tufafi.

3. A lokacin da kazo Duniya an yi maka wanka, a lokacin da zaka koma za a ƙara yi maka wanka.

4. A lokacin da kazo Duniya baka Iya tafiya ba sai dai a ɗauke ka, lokacin da zaka koma kuma sai dai a ɗauke ka.

5. Ranar da kazo Duniya an yi maka Kiran Sallah ba tare da an yi Sallah ba, a ranar komawar ka za a yi maka Sallah ba tare da an kira Sallah ba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Abinda Yakamata Ku sani Dangane da Rayuwar Duniya

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa Cikin Sauki

ALLAHU AKBAR DAGA KARSHE SUNYI KWANCIYAR DA BABU RANAR TASHI

Komai mai Gushewa ne Hatta ita kanta Duniyar,  Ɗan Uwa kada ka bari zuciyar Ka takai ka ta baro, hanzarta yin guzurin tafiya tun kafin ranar tafiyar tazo (Mutuwa).

Yakamata mu farka daga mafarkin da muke yi domin samun lahira, mu haƙura mu koma ga Allah.

Allah yayi mana gafara Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user