Tuesday 28 January 2020

Karanta Abinda Yakamata Ku sani Dangane da Rayuwar Duniya

Tura Wannan Zuwa Ga
Duk wanda ka gani a duniya yana rayuwa haka Allah Ya ga dama, kar ka wulaƙantashi, kar ka zalunceshi, kuma kada ka rena matsayinsa, baka san baiwar da Allah Ya masa ba, saboda a kwai gaba, sannan ita rayuwa na duniya ba ka san waye zai taimake ba.


KUKAN KURCIYA JAWABI NE...

Marubuci: Datti Assalafiy

Akwai mutanen da kuke rayuwa tare, idan Allah Ya ba su wata dama sai su rena kowa, suna ganin kowa a matsayin wulaƙantacce, irin waɗannan mutane sun jahilci menene ma'anar rayuwa ta duniya da bata da tabbas.

Tsarin mulkin Demokaradiyyah da akeyi a Nigeria ba kayan gado bane da za'a tabbata a kan karagar mulki, akwai ranar da wa'adin mulkin zai ƙare dole a sauka, mutanen da ka rena matsayinsu dole ka dawo cikinsu ka ƙarasa rayuwa, duk wanda Allah Ya bashi wata dama to yayi ƙoƙarin aikata abin alheri, a guji cin amana da wulakanta bayin Allah.

Masu kuɗi 'yan kasuwa da waɗanda suka taɓa rike manyan muƙamai nawa ne Allah Ya jarrabesu a rayuwa suka dawo matsayin da sai dai a taimaka musu?, sun zama abin tausayi.

Kuskure ne a rayuwa ka sakankance akan kowanne irin matsayi ko aikin gwamnati ba tare da ka iya sana'a ba, har ya zamto kana rena mutane saboda giyar mulki ko gwamnati, ka kasance mai nutsuwa kana tunanin gaba ba baya ba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Shin Ko Abokina Zai Iya Canza Min Halayena Bansani Ba?

KARANTA HANYOYIN SAMUN RAYUWA MAI DADI CIKIN SAUKI

KARANTA NASIHOHI GUDA 10 GA 'YAN UWANA MATASA

Haƙiƙa naga aya a kan rayuwar wani babban mutum da na sanshi a baya, yau ya dawo abin tausayi, har ɓuya yake saboda masu neman haƙƙinsu a gurinshi, wato ya ciyo bashi, ga hawan jini ya kamashi, wanda a da ya kasance mai yawan ɗagawa da raina matsayin bayin Allah saboda wata dama da Allah Ya bashi a gwamnati.

Kukan kurciya jawabi ne, masu karin magana sukace mai hankali ke ganewa.

Allah Ya taimakemu a har kullum Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user