Sunday 31 January 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (30) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa

KANA SO?


Da yawammu inda muke samun matsala kenan, mutum ransa bai kwanta da abuba sabo saboda matsalar da yake hangowa amma saboda rashin samun wani, ko shawarar da wasu suke ba shi ko tilastawar uwaye sai ka ga ya ɗauka, a ƙarshe da wahala ka ga mutum ya ci nasarar abinda yake nema, ko shawara mutum zai ba ka ya dace a ce ya san abin sosai, in ba haka ba da matsala, ba yadda za a yi mutum ɗan boko futuk ba abinda ya sani game da addini a ce shi ne zai riƙa faɗa muku halas da haram, da wahala ku ci nasara.


Matsalar Mu

MarubuciBaban Manar Alkasim


A addinance ma na ga wani hadisi na Musa bn Talha da ya jiwo daga babansa cewa shi da Annabi (S.A.W) sun wuce wasu mutane a kan dabinai ya tambaya cewa "Me waɗannan suke yi?" Suka ce "Aure suke musu, suna haɗa maza da mata" ya ce "Bana jin wannan zai amfanar" sai suka gaya wa manoman, su kuwa suka dena, da aka gaya wa Annabi (S.A.W) abinda suka yi sai ya ce "In dai hakan zai amfanar su yi mana, ni fa kintatowa na yi, kar ku ce za ku kama ni da abinda na kintata, in dai na gaya muku wani abu na ce daga Allah ne to ku yi kawai, don ba zan taɓa yi wa Allah ƙarya ba, Muslim (2361).


Akwai abubuwan karatu a wannan hadisin, in mutum ya gaya maka abu kuma ka san bai da masaniya a kai in ka ɗauka ka ga dama ne, a addinance ga dai abinda Annabi (S.A.W) ya faɗa nan, a zamanance kuma bai dace ba ka ba da damar da za a cilla ka wani wurin, ko matsalolin da kake gani ana samu a aure ana ba wa wanda bai san abinda ke faruwa tsakanin ma'aurata ne ba damar ya tofa albarkacin bakinsa sai ka ga ya wargaza komai, ƙila mutumin nan yana yi mata alkhairai masu yawa, waɗanda sun fi matsalolin nasa, amma saboda rigimar da ta rincaɓe tsakanin matar da shi in ta zo ba za ta faɗi alkhairansa ba, masu ji kuma sai su zata ba wani aikhairi ne sai su ba da munanan shawarwari a ƙarshe a kasa cin nasarar abinda ake so a auren.


Na ga wata mata da aka dinga kai-komo a kotu kan alaƙarta da mijin, uwayenta suka tsaya kai-da-fata sai an raba auren, saboda abinda 'yarsu ta gaya musu, alƙali ya ba da biko ba a daidaita ba, a ƙarshe mijin ya ce ya bi, ya bi, amma ya kasa cin nasara don haka a yi mata yadda take so, ta yi wub ta ce wallahi tana son mijinta za ta koma, daga kotun ta bi mijin, ba ta koma gida ba bare su ce sai dai ta koma ɗakinta ita kaɗai, na ga wani mutum da wasu bayin Allah suka jawo shi don ya ci arziƙi, da yake yana da masifaffen wayau sai ya yi ƙoƙari ya maida kamfanin nasa, masu shi kuma suka koma yi masa aiki, sai da aka kwashe shekara takwas a cikin wannan halin, a ƙarshe ya ƙirƙiro matsala ya kore su.


Wallahi da idona na gani ba labari aka ba ni ba bare na yi zaton gaskiya ne ko karya, ya kwashe labari, gaskiya da ƙarya, ya kai wa waɗanda ba su sani ba, su kuma suka ba shi shawara gwargwadon yadda suka ji ba tare da sun san haƙiƙanin abinda yake faruwa ba, gogan naka ya kai su ƙara kotu, sai ga reshe yana neman ya juya da mujiya, ba arziƙi ya janye ƙarar nan take ya fara neman sulhu, a taƙaice dai kamfanin ya balbalce, duk lokacin da za ka nemi shawara yi ƙoƙari ka yi da wanda ya san abinda kake ciki ɗari bisa ɗari, in ba haka ba kuwa to za a yi ba uwa ba riba, in ka ɗauki shawararsa ka zo ba ka yi nasara ba cikin sauƙi zai ce maka "Ai ban san haka ne ba, don Allah ka yi haƙuri" shi kam a wurinsa an gama kenan.


Akwai wani da ya gama sakandare ta boko sai ya yi shawarar sake wata ta Islamiyya, haka abokansa suka riƙa cewa "Wannan ai demotion ne, ya za a yi mutum ya shekara goma sha biyu a sakandare?" Mutumin nan ya ce ya ji ya gani, ya nemi taimakon Allah ya duƙufa, sai ga shi ya kammala, ya yi Diploma ya fara digiri, ya yi masters, masu maganar ba su kai inda ya kai ba, sai cewa suke "Ai wallahi ba mu san hakan ne ya fi ba, ai mu ma da mun bi ka mun yi tare" da ya biye tasu da shikenan ba-wan-ba-wan karatun ɗan kama, na yarda da shawara amma ga wanda ya san abu ciki da bai, sannan in ka san karatu bai dace da kai ba, ko sana'a ko wani aiki kar ka bi surutun jama'a bar shi kawai.


Ko aure ne ka ga ba ka so, ko ba a son ka haƙura kawai, ba wani zancen kunya da ƙarairayi marasa amfani, kai ne za ka zauna da ita, samun zaman lafiya da fahimtar juna shi ne cin nasarar aure, in karatu kake so, ka ga wanda ranka ya natsu da shi riƙe shi, kuma shi ɗin ne za ka iya kar ka bi shawarwarin wani, zai faɗa maka ne kawai ya barka da shi ka yi ta taɓurzawa, in har ba ka sha'awar zama lauya ko alƙali to tun farko kar ka karanta lauyanci ko alƙalanci, in ba haka ba karatun ba zai yi amfani ba, sai mutum ya ce bai sha'awar koyarwa a ransa ko kaɗan, amma ka ga ya karanta Education.


MAKALOLI MASU ALAKA:


Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (28) Cikin Sauki


Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (29) Cikin Sauki


Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (31) Cikin Sauki


Na ga mutum biyu waɗanda suka koyi gyaran wuta da wuyarin don su sami na cin abinci, da suka so ƙaro karatu sai suka faɗa Electrical Engineering, abin ya ba ni sha'awa, ko yaranka ne za su yi karatu lura da inda suka fi mai da hankali ka ba su shawara, sai ka ga an yi nasara a karatun, na ga wani uba da yake son ɗiyarsa ta karanta likitanci, amma ta ce ita sam ba za ta iya ba, ya damu matuƙa, na ce idan ya matsa mata ba za ta yi abin kirki ba tunda tun asali ba ta so, na ga wani uba wanda kullum sai ya jibgi ɗansa a kan sana'arsa amma ɗan ya ƙi yi masa biyayya, shi bai son sana'ar uban, da zan iya ba da shawara da na ce uban ya bar shi ya zaɓi sana'ar da yake so.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user