Thursday 18 February 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (31) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa

DUK ABU NAKA NAKA NE


Sakaci da rashin kulawa ko rashin sani su ne manyan abubuwan dake sanyawa mu rasa damar dake hannunmu ko mu bar ta wani ya ƙwace mana, da farko fara gina kanka tukun, yi ƙoƙari ka sami ginshiƙi mai ƙarfin gaske, kar ka yarda ka yi abu a kan jahilci, in kamfanin gyaran mashin za ka gina binciki kanka tukun, shin kana da kuɗin da zai ba ka damar aiwatar da wannan aikin? In ba ka da shi to ya za a yi ka samu? Ilimin aikin dai yana kanka kuɗin aiwatarwan ne ba bu.


Nasara A Rayuwa

MarubuciBaban Manar Alkasim


Da farko tsaya ka karanci sana'ar da za ka fara, shiga ciki a matsayinka na mai koyo, yi ƙoƙari ka san komai nata, kayan aiki, abubuwan da ake buƙata, masu kyau da jabu, kuɗaɗen su, daɗewarsu, bambance-bambancen dake tsakanin kamfanoni, lokutan da suka fi dacewa da inda ya kamata a yi saboda yawan mabuƙata, ya zamanto dai a matsayinka na mai koyon aiki ba abinda ba ka sani ba, albashi in ka zo ɗaukar ma'aikata da za su yi maka bayani kan kayan aiki da sauransu ba abinda ba ka sani ba, kuma ba wanda zai yi ƙoƙarin cutarka ko ɓata maka aiki.


Na koyar a wata makaranta ta Misho, inda na ga hedimastan ko yaushe yana zagawa azuzuwa yana ganin darussan da ake koyarwa, da lokutan da ake koyarwan, wata rana ya amshi wani aji ya koyar ko ya yi musu tambayoyi don ganin shin abin da suke buƙata malaman suke ba su ko kuwa? Na yi mamakin ƙwaƙwalwar mutumin yadda ya san komai kai har da sunan ɗaliban, ba abinda malami zai faɗa wanda bai sani ba, sai na tambaya, ya aka yi ya san duk waɗannan abubuwan? Sai aka ce ya koyar na tsawon shekaru da dama kafin ya kai ga riƙe makarantar a hannunsa, ashe asali ma ba ɗan ƙasa ba ne, amma yana tsari mai ƙarfin gaske, koyarwar ta taimake shi sanin komai.


Idan ka gama sanin komai ya za a yi wani mutum ya zo maka daga waje ya mallake ka? Ba zai yuwu ba, na ga wata makaranta da wani ya so gudanar da ita, ya tanaji komai amma bai da kuɗi, sai suka haɗa hannu da wani mai abin hannunsa, a ƙarshe aka fara rigimar shin wa ma yake da makarantar tukun? Wanda ya fi ƙarfinka sai ya ɗauki hannunka ya mare ka da shi, kusan abinda aka yi kenan, mutumin farko da a ce yana da kuɗinsa sai ya ci gaba da gudanar da lamuransa shi kaɗai ba zai jawo kowa ba.


Duk abinda za ka yi in dai kai da ƙarfinka za ka yi aiki wani da dukiyarsa kar ka yarda a ce komai shi zai yi, wani zai ce kar ka damu, ko nawa kake so ni zan ɗauki nauyi, in ka yarda da wannan to ko shakka babu ka sayi wuƙar yanka kanka, sanya taka dukiyar kuma ka yi aiki da ƙarfinka, ba yadda zai dawo wata rana ya yi farfagandar cewa komai nasa ne don shi ya yi, kai ma ka sanya kuɗinka, ka yi aiki da ƙwaƙwalwarka sannan ka ba da lokacinka dai-dai gwargwado, abubuwan dake faruwa a duniya yanzu yadda ka san ba lahira a gaban mutane.


Akwai wata makaranta da wani ya so gudanarwa, shi ya ke da wuri a hannunsa, sai ya jawo wani babban malami wanda ya yarda da shi sosai, ya danƙa komai a hannunsa, sai mutumin ya yi aiki da wannan damar ya maida mai wurin yaronsa ya yi ta yi masa bauta na tsawon shekaru, sai dai ya ɗan gutsuro a wata ya miƙa masa, ba wanda ya san abinda ake ciki, a ƙarshe da yake mai wurin shi ma ba nasa ne na kansa ba sai mutumin ya kori shi wai bai gamsu da irin gudummuwar da yake badawa ba, idan kana da rai ba abinda ba za ka ji ba, waɗannan su ne abubuwan da ni na gani da idona Allah ne kaɗai ya san abubuwan dake faruwa a wasu wuraren.


Da a ce mutumin nan ya koyo aikin, ya fara da kansa bai janyo kowa ba, shi yake gudanar da komai ba wanda zai zo rana tsaka ya mamaye masa wuri, balle ya tuhume shi da rashin gaskiya har a ƙarshe ya ce zai kore shi, duk sana'ar da za ka shiga yi ƙoƙari ka san gabanta da bayanta yadda ba wani abinda zai ɓoyu maka, kana da cikakken 'yanci, kana da duk wata dama da za ka ɗauki matakin da kake so, ba tare da wani ya yi aiki da ƙwaƙwalwarka ya cuce ka ba, in kana gaya wa kanka cewa ba za ka iya kaza ba ina tabbatar maka daga lokacin da wani ya karɓe maka wannan damar sai yadda ya yi da kai.


DUBA WANNAN: Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (32) Cikin Sauki


Za a kai yadda ba za ka iya zartar da komai ba sai abinda ya so, shi kuma abinda ya ce ka yi ba ka da makawa, ko kafin ka farga ya yi maka babbar illa, don duk abinda zai amfane ka ba zai yarda da shi ba, duk kuma wata hanya da za ka bi wace za ta nuna maka hanyar dai-dai ba zai yarda ka san ta ba, taka ta ƙare kenan, ka buɗe idanunka, ma'ana duk lokacin da ka gano cewa nasararka tana kan ɗakinka ne to ka gina matakalanka da kanka, ka hau da kanka ka ciro, ka sani in ka tura wani ya ciro maka to shi ma fa yana so.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user