Showing posts sorted by date for query Abubakar Abba. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query Abubakar Abba. Sort by relevance Show all posts

Tuesday, 26 August 2025

Hanyoyi 9 Na Rabuwa Da Talauci

Hanyoyi 9 Na Rabuwa Da Talauci

Wato shi fa talauci babban maƙiyi ne, babu wata soyayya tsakaninku. Idan tsautsayi ya sa har yanzu ba ku gama raba hanya da shi ba, ga wasu dabaru da za ka iya amfani da su domin ku yi hannun riga da shi.


Hanyoyi 9 Na Rabuwa Da Talauci
Hoto: Mental health hope

Marubuci:- Abubakar Abba


Allah yake bayar da arziki, amma sai an yi aiki.


1. KAMA SANA’A MAI KAWO ARZIKI


Kowacce sana’a za ta iya bayar da arziki a wani zamanin, kuma ba lallai ba ne ta bayar a wani zamanin daban.


Yana da kyau ka tsaya ka duba wacce ce take bayar da arziki a zamanin da kake, ko kuma yaya za ka ingantata ta kawo arziki.


Arziki yana zuwa ne bayan an neme shi, ba’a yin arziki daga kwance.


2. KAMA ILIMI KAM-KAM


Duk yadda za’a zuga ka, kada ka yarda ka zauna ba ka da ilimin abin da kake yi.


Idan Leburanci kake, ka nemi ilimin inganta ta, idan kasuwanci kake, ka nemi ilimin gudanarwa, da bunƙasawa.


Babu wanda ya yi nasara tabbatacciya da jahilci.


3. KA YI NESA-NESA DA JAHILAI


Ko ka yarda ko kar ka yarda, mutanen da kake mu’amala da su yau da kullum suna da tasiri sosai wajen nasararka a rayuwa.


Jahilai har kullum lissafinsu ba na ci gaba ba ne, don ba su da masaniya akan me rayuwa take tafiya akai ba.


4. IDAN KA SAMU DAMA KA BAR UNGUWAR TALAKAWA


Masana halayyar Ɗan Adam, sun daɗe da fahimtar cewa zama cikin wajen da babu damarmaki yana taimakawa sosai wajen dawwamar da mutum cikin talauci.


Sauya muhalli yana tasiri sosai wajen sauya tunani, sannan yana taimakawa wajen samun damammaki, wanda idan aka yi amfani da su sai a samu dacewa.


A cikin littafin rayuwarsa, hamshaƙin mai kuɗi Femi Otedola, ya yi ƙarin haske akan wannan, a je a karanta za’a sha labari.


5. KA NEMI ILIMI AKAN KUƊI


Akwai wani babban ganganci da mutane da yawa suke yi shi ne, suna zama ba tare da sun nemi ilimin yaya ake tara dukiya, yaya ake alkintata, yaya ake bunƙasa ta ba.


A tunanin mafi yawan mutane, arziki zuwa kawai yake yi, ba tare da mutum ya yi wani hobɓasa daga ɓangarensa ba.


A tunanin mutane masu rauni, laifi ne ka nemi ilimin yadda za ka samu kuɗi ko yadda za ka yi arziki.


Don haka da yawansu suke fama da baƙin talauci.


Bayan ka nemi ilimin karatu da rubutu, to lallai ka nemi ilimin yadda harkokin kuɗi suke, zai taimaka sosai.


6. KA YI ƘOƘARI MASU ARZIKI SU SAN DARAJARKA


Kar ka yarda ka kulle kanka a waje ɗaya, idan Allah ya ba ka ilimi, ka yi ƙoƙari ka fito da shi duniya ta sani.


Ka yi ƙoƙari duk inda ake harkar arziki kai ma a gan ka a wajen, bayan ka je wajen, ka tabbatar ka nuna baiwar da Allah ya yi maka.


Daga haka ake samu silar arziki.


Kar ka yarda da shirmen jiran 'yan siyasa, ko Auren Hajiya, ko 'yar masu kuɗi, wannan duk baragada ce.


Ka gina daraja, ka yi tsari mai kyau, ka yi addu’ar dacewa.


7. KA TABBATA KA KOYI HALAYE MASU KYAU


Kyawun hali da mu’amala mai kyau tana ba wa mutum arzikin da bai taɓa zato ba.


Kar ka zama mai kaushin hali, ko mai wahalar mu’amala da mutane, ko mara haƙuri da juriya, ko mai yawan aibanta mutane, ko mai yawan gulma da neman laifin mutane, duk wanda ka ga yana wannan munanan ɗabi’un, to ka tabbata ba inda zai je a rayuwa.


8. KA CIRE TSORO DA SON JIKI


Ka daina tsoron shiga harkar da za ta ba ka alheri in dai halal ce.


Ka daina tsoron abin da mutane za su ce, ko abin da 'yan uwanka za su ce, ko abin da matarka, budurwarka ko abokanka za su ce.


Wannan shi ne abu na farko da zai ba ka damar shiga rayuwa mai cikakken 'yanci.


Arziki ba ya zuwa da tunani ƙarami ko lissafin mai tsoro.


9. KA KULA DA LAFIYARKA


Lafiyarka ita ce babban jarinka, babu wani abu da zai tafi daidai idan lafiyarka ba ta kan saiti.


Lafiyarka tana da tsada, don haka kada ka yi wasa da abincinka, hutunka, baccinka da motsa jiki.


Kada ka yarda wani aiki, ko wani mutum ya hana ka samun waɗannan ababen.


Ni ne jagoran masu yaƙi da talauci da tunani irin na talauci.


Idan kana son samun haske da samun dabaru masu inganci  akan yadda za’a samu hanyar da za ta ɓulle, to nan ce babbar tasha.


Ka ci-gaba da bi na, tare da yaɗa wannan saboda wasu ma su amfana, da haka ne za mu fatattaki talauci da 'yan koren sa.

Saturday, 3 May 2025

Yadda Za Ku Fara Sana'a Ba Jari

Yadda Za Ku Fara Sana'a Ba Jari

 1. AIKIN ƘARFI 


Muna da misalai da yawa na mutanen da suka yi arziki, kuma sun fara neman kuɗi ba tare da wani ya ba su jari ba.


Za ka iya fara aikin ƙarfi, tun da ba ya buƙatar wani jari sai lafiyarka, idan ka adana wani adadin kuɗi, sai ka tsunduma cikin kasuwa.


Yadda Za Ku Fara Sana'a Ba Jari
Hoto: Deposit photos

Marubuci:- Abubakar Abba


Amma idan ka zauna ka ce kana jiran wani ya ba ka ko kana jiran gwamnati ta ba ka jari, to alama ce da take nuna ba ka shirya rufawa kanka asiri ba.


2. NEMI UBANGIDA


Kowace sana'a tana buƙatar a koye ta a wajen wanda suka ƙware a cikinta, hakan yana ba wa mutum sani mai yawa, wanda idan ya zo ya samu jarin farawa da kansa, ba zai sha wahala ba.


Don haka, ka nemi wani mutumin ko abokinka wanda yake wata harkar kasuwar, ka zama yaronsa, koda aiken ka za'a yi  ko dakon kayan kwastoma a kasuwa, ko sayo kayan aiki ko wani abu makamancin haka, babu laifi.


Idan ka yi haƙuri mutane suka san ka a kasuwar, ko wajen aikin, lokaci zai zo da za ka iya samun 'yanci.


Zama yaron wani ba ya buƙatar sai kana da jari, hasali ma ita ce hanya mafi sauƙi ma wajen fara sana'a.


Sai dai ba kowa ne yake da wannan alfarmar ba.


3. SIYAR DA KANKA


Koda ba ka san kowa ba, ko ba ka da 'yan uwa a kasuwa, wannan ba zai zama uzurin da za ka ce ka rasa abin yi ba.


Yi amfani da Shafukan Sada Zumunta, ka zama mai ƙirƙirar maƙala wanda zai ja hankalin mutane, ka tara mabiya.


Yi amfani da wannan mabiyan ka je ka samu wasu 'yan kasuwar ka nuna musu cewa kana da mutane, su dinga ba ka talla, ko tsarin affliate ne, kai kuma kana samun wani abu.


Da yawan 'yan kasuwa za su ba ka wannan damar, domin zai kawo musu kwastomomi.


Ka je ka ɗauki hotuna da kanka, ka zo Shafukan Sada Zumunta ka fara tallatawa.


Wannan ma ba ya buƙatar sai kana da jari za ka fara.


4. KA YI AMFANI DA BASIRA


Wanda Allah ya sa yana da wata ƙwarewa ko wata baiwa, shi wannan nasa mai sauƙi ne.


Abin da ya rage maka shi ne, ilimin da kake da shi, da basirar da kake da ita, da wata ƙwarewa da kake da ita, ka fito da ita duniya ta sani, ka sanya farashin kuɗi mutane su biya ka koya musu.


Da haka za ka iya samun jarin fara duk sana'ar da kake buri.


Kuma sakamakon ilimin da kake bayarwa, wasu damarmakin za su zo maka, wasu Network ɗin za su ƙullu, da haka sai ka ga ka wuce wajen.


5. KA YI KARATU


Sau da yawa rashin bincike yake hana mutane da yawa samun wasu damarmakin. Don haka ka yi ƙoƙari ka inganta iliminka, da kuma mu'amalarka.


Ka yi ƙoƙari ka dinga halartar guraren ƙara ilimi, kamar tarukan kasuwanci, da taron ƙarawa juna sani, ka dinga halartar Online Classes, daga nan za ka iya samun wata fikira da za ka iya amfani da ita wajen rufawa kanka asiri.

Thursday, 13 March 2025

Rabe-raben Teloli Da Ba Ku Sani Ba

Rabe-raben Teloli Da Ba Ku Sani Ba

 1. TELA


Wanda ya dogara da abin da yake samu daga ƙwarewarsa ta ɗinki a matsayin hanyar kuɗin shiga.


Wannan shi babbar ribar sa shi ne mutane su kawo masa kayansu da yawa ya yi ɗinki da yawa.


Rabe-raben Teloli Da Ba Ku Sani Ba
Hoto: India Mart

Marubuci:- Abubakar Abba


Saboda haka shi kwastomomin sa su ne wanda suka san shi ko suka ji labarin ya iya ɗinki.


Idan ya yi sa'a ya shahara, zai samu kwastomomi da yawa, idan kuma ba haka ba, to fa sai a hankali, tunda idan ba'a kawo ɗinki ba; shi ba labari.



2. FASHION DESIGNER 


Wannan ba ya jiran sai ka ba shi kalar ɗinkin da kake so, a'a shi yana amfani da ƙwarewarsa wajen fitar da sababbin salo (styles) wanda mutane za su so kuma ya sakawa wannan salon farashi, da haka yake samun nasa kuɗin shigar.


Shi wannan salo yake dogara da shi, domin shi ne babban aikinsa, zai iya fitar da tsari (Design) amma ba lallai ya zauna ya ɗinka ba, don haka shi kwastomomin sa suna da yawa, ba wai iya ɗaiɗaikun mutane ba ne, a'a har da telolin da suke jira ya fito da sabon salo su kuma su kwaikwaya.


Fashion Designer ya fi Tela samun kuɗi, kuma ya fi shi samun kwangila a duniyar kasuwanci.


3. FASHIONPRENEUR


Wannan su ne wanda suka tara duka abin da aka ambata a baya, sannan kuma sun fi mayar da hankali wajen siyarwa da mutane suturar da za su saka nan take.


Za su fitar da tsari (Design), za su ɗinka, za su tallata, za su siyar a matsayin kayan kasuwanci.


Yana da kyau ka san a wanne mataki kake.


Matakin ƙarshen nan shi ne aka fi samun alheri a cikin sa.


Na san kuma da yawan Teloli masu wayo shi ne abin da suke hanƙoron samu.

Friday, 24 January 2025

Hanyoyi 4 Na Tattalin Riba A Kasuwanci

Hanyoyi 4 Na Tattalin Riba A Kasuwanci

Yanayin sukurkucewar tattalin arziki da ake ciki, dole ne Ɗan Kasuwa ya nemi wasu sababbin dabaru domin ganin ya tsaya da ƙafarsa.


Hanyoyi 4 Na Tattalin Riba A Kasuwanci
Hoto: Uwcped

Marubuci:- Abubakar Abba


Ita riba (profit) a kasuwanci ita ce ginshiƙin ci gaba, duk kasuwancin da ba'a samun riba to yana kan hanyar zuwa maƙabarta ne.


Kasuwa kacokan ana yin ta ne domin riba, idan ba ka gane inda ribar ka take zuwa ba, to alama ce da ke nuna wahala kake yi ba kasuwanci ba, kuma irin haka ne yake sa wa mutane su ce ana yi musu asiri, alhali kuwa ba wanda yake musu asiri rashin sani ne matsalar su.


1. DA FARKO YANA DA KYAU KA SAN ME AKE NUFI DA RIBA (profit)


Riba (Profit) shi ne kuɗin da ya rage bayan ka cire Kuɗin Product, da hidimar da aka yi masa.


Misali:


Idan ka je kasuwa ka saro Shadda a kan farashin ₦10,000.


Sai ka dawo shagonka ka siyar da ita akan farashin ₦12,000.


Ƙarin da ka samu na dubu biyu sunansa (Gross Profit) wato riba a dunƙule.


Idan ka cire kuɗin mota da kuɗin leda da na Data da ka saka wajen talla, abin da ya yi ragowa shi ne (Net Profit) wato tsantsar riba.


Sanin wannan zai taimaka maka ka gane inda kasuwa take dosa.


2. KA KULA DA KASHE KUƊINKA 


Idan kana samun ciniki mai yawa, to tabbas kashe kuɗinka zai ƙaru, sai dai idan ba ka bi a hankali ba, za ka ga kana cinikin mai yawa amma kuma ka rasa gane inda ribar take tafiya.


Wannan ta sa dole ka tsaya ka bi diddigin abin da kake kashewa a kasuwancinka, kada ka je ledar da kake zubawa kwastoma kaya ita ce take cinye ribar ba ka sani ba, kai kana ganin ka yi fashion domin samun ciniki alhali kuma fashion yana neman kashe maka kasuwa.


Sanin abin da kake kashewa kasuwarka zai ba ka cikakken haske, domin ka gane inda kuɗi yake zurarewa kuma ka ɗauki mataki.


Sau da yawa muna kashe kuɗi da sunan ɗaga darajar kasuwancinmu amma ba mu sani ba hakan yana cinye mana ribar da muke samu ne.


3. KA DUBA FARASHIN KA


Farashin kayanka yana taimakawa wajen ci gaba ko akasinsa, sanin yadda za ka sanya farashin da zai maye gurbin abin da ka kashe kuma a samu ragowa abu ne mai matuƙar muhimmanci.


Kafin ka saka farashi yana da kyau ka yi duba zuwa ga:


SU WANE NE KWASTOMOMIN KA?


Sanin ainahi da ajin kwastomomin ka zai ba ka dama ka sanya farashi daidai su kuma ka samu riba.


FARASHIN MAƘOTA


Wanda suke siyar da kaya irin naka da tsari irin naka, yana da kyau ka yi duba zuwa ga yadda suke fitar da farashi, hakan zai taimaka sosai kar ka je ka samu matsala.


ƘARIN DARAJA


Koda a ce maƙocinka yana siyar da irin abin da kake siyarwa, indai ka ƙarawa naka daraja, kamar sanya shi waje mai kyau, ba wa kwastoma kulawa ta musamman, hanyar biyan kuɗi mai sauƙi da sauransu, to farashinka ya kamata ya fi nasa domin ka yi ƙarin ɗawainiya sama da shi.


Hakan zai sa ribar ka ta maye gurbin hidimar da ka yi, har ma a samu ragowa.


4. TSIFA DA WARWARA


Ka tsaya ka dinga lissafin yadda kuɗi yake shigowa da kuma yadda suke fita, ka bi diddigin hanyar da kuɗi suke fita, inda za ka iya rage fitarsu, a rage, inda za'a daina, a daina.


Ku taimaka ku tura wannan saƙon ga  sauran jama'a saboda ya je ko'ina.


Na gode.

Thursday, 2 January 2025

Abubuwa 6 Da Za Su Sa Ka Yi Arziki A Sabuwar Shekara

Abubuwa 6 Da Za Su Sa Ka Yi Arziki A Sabuwar Shekara

KAR KA YARDA DA TALAUCI!


Shekarar 2024 ta wuce, amma har yanzu tarin matsalolinka suna nan ba su tafi ba, kuma girma yana ƙaruwa a kanka, burika da nauye-nauye  suna ƙaruwa.


Abubuwa 6 Da Za Su Sa Ka Yi Arziki A Sabuwar Shekara
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abubakar Abba


Kasancewarka a Nigeria musamman ta Arewa, ya gadar maka da wasu tarin ƙalubale wanda ba a yi shawara da kai ba, da wasu matsaloli wanda ba ka shirya musu ba, da ƙarin wasu nauye-nauyen da al'umma da iyalai suka ɗaura maka wanda ya zama dole idan kana son zaman lafiya ko kana son ka tsira da mutumcinka, to ka yi ƙoƙarin ɗauka koda kuwa ba ka da ƙarfi.


Duk wata hanyar nasara da fita daga ƙangin talauci an saka mata shinge tun kafin ka zo duniya, hakan ta sa ya zama dole ka yi aiki tuƙuru ko kuma kai ma ka zama tamkar ragowar mutanenka.


Yawancin mutanen yankinka sun fito ne daga iyalan da ba a tanadar musu da wata dukiya wanda ake jira su yi amfani da ita ba lokacin da ƙarfinsu ya kawo, a'a, ana jiran su ne ma idan sun yi ƙarfi su nemo hanyar da za su fitar da gajiyayyu a dangin su daga ramin talauci, su ɗauki nauyinsu da na yaransu, idan sun gaza; a aibata su.


Idan an ga alama sun sami wata dama komai ƙanƙantarta, kuma ba su ɗauki wancan nauyin ba, nan ma zaginsu ya zama aikin lada. 


Dangi suna tilastawa mutum ya ɗauki nauyin da ba nasa ba koda kuwa za'a taru a faɗi ƙasa wanwar.


A lokacin da ka fito neman arziki, al'umma ita ma ba za ta ba ka dama cikin sauƙi ba, tun a makaranta da unguwa za'a fara cusa maka tunanin ka zama talaka kawai ka huta, ai talaka ya fi mai kuɗi kwanciyar hankali, talakawa su ne mutanen kirki, da sauran zantuttuka da adabi wanda za su hana ka motsi a lokacin da ya dace.


Idan ka tsallake wannan kuma, ka ce kai lallai sai ka yi abin da zai fitar da kai daga talauci, nan ma ba za ka samu gwamnatin da za ta ba ka hanya mai sauƙin bi ba, ba ka da jari, gwamnati ba ta tanadar maka da shi ba, komai kuwa kyawun ra'ayinka ko fiƙirar ka.


Bankuna ba za su ba ka jari ba yawanci, sai sun haɗa maka da kuɗin ruwa (Interest), wanda kuma addininka ya haramta maka.


TO YAYA ZA KA YI?


1. KA YI FAƊA DA TALAUCI


Kar ka yarda ka zama talaka, kar ka yarda talauci ya birgeka, kar ka yarda da duk wani abu wanda zai hanaka arziki.


2. KA NEMI HANYAR FITA DAGA TALAUCI TABBATACCIYA


Wannan hanya ita ce, ka samu wata matsala wadda al'umma suke fama da ita, kuma suke a shirye su bayar da kuɗi a kanta, ka warware musu ita, su biyaka kuɗi masu kauri. (Entrepreneurship).


Wannan ita ce hanya sahihiya wadda aka gwadata kuma ake gwadawa kuma take fitar da mutane daga layin talauci take kai su layin arziki da wadata.


Amma fa ka sani, wannan hanya ba sauƙi ne da ita ba, sai dai tabbas hanya ce mai ɓullewa.


3. KA GYARA TUNANINKA


Wannan shi ne babban abin da zai taimakawa rayuwarka, ka cire duk wani tarkacen tunani wanda yake hanaka arziki, ko wanda yake hana ka bin hanyar tsira da mutunci, ko wani tunanin da yake nuna maka cewa ba za ka iya fita daga talauci ba.


Wannan kuma ba zai faru ba sai kana neman ilimi kana karatu.


Dole ka yi karatu, dole ka nemi ilimin addini ingantacce da kuma ilimin rayuwar duniya, ka kula, ilimi na ce ba Certificates ba, yawwa.


4. KA GINA KANKA, KAFIN KA GINA GIDA


Idan ka taso a cikin irin wancan yanayi da na ambata da farko, to lallai ba ka da wani abu da zai taimakawa rayuwarka kamar ka yi ilimi.


Gina kai anan yana nufin, ka yi ilimi, ka gina tunani mai inganci na rayuwa, ka ƙulla alaƙa da masu ilimi da masu arziki, da masu tunani irin wannan.


Ba ruwanka da sharholiya, ko fantamawa ko son birge mutane, wannan duk hanyar zama a cikin talauci ce.


5. KA YI TSANTSENI


Tsantseni anan yana nufin, duk abin da ka samu na kuɗi ka tabbata ka kashe shi ne a kan abin da zai inganta rayuwarka, kamar sayen littafin da zai taimakawa tunaninka, biyan kuɗin makaranta, ko zuwa halartar wani horo, ko wani taron kasuwanci ko wani abu makamancin haka.


Sannan kuma, ka yi ajiya (savings) domin amfanin kanka, ba domin ankon biki ba, ko shaddar sa wa a walima ko bidiri, ko kayan sallah ba, a'a, sai dai domin gina kasuwanci, gina jarin fara wata sana'a ko domin neman ilimin ci gaba.


6. KA KARANTA TARIHI


Wannan shawara ce da zan ba wa duk wani mai tasowa, kar ka yarda ka zauna ba ka da tarihin mutanen ƙwarai, wanda za ka koyi abin arzikin da suka yi a rayuwarsu, sannan za ka samu ƙwarewa ta musamman kan yadda za ka ɓullowa al'amuran rayuwa.


Tarihi zai taimaka maka sosai wajen ba ka ƙwarin gwiwa ka tunkari duk abin da ka sanya a gaba, koda kuwa wasu suna maka ganin cewa za ka gaza.


Tarihi zai ba ka fitila mai haske a wurin da mafi yawan mutane suke ganin duhu.


Tarihi zai ba ka taswira a inda mutane da yawa suke ɓacewa.


Tarihi zai ƙwace ka a wurin da mutane da yawa suke halaka.


Wannan shawara ce da zan ba wa duk wani masoyina da Allah Ya raya shi har ya ga wannan sabuwar shekarar ta 2025.


Kar ku manta, kullum da safe ana yin addu'ar neman tsari da talauci, sannan kuma a yi aikin korar talauci.


Da yammaci ana addu'ar neman tsari da talauci, sannan a yi shirin yadda za'a a yaƙe shi da safe.


A dage, kar a yi sanya, Allah Ya ba mu nasara akan talauci, amin.


Muna addu'ar Allah ya haɗa mu da duk wani alheri da wannan shekarar take tare da shi, Ya kare mu daga duk wani sharri a cikin wannan shekarar da ma wasu shekarun masu zuwa, Amin.

Wednesday, 25 December 2024

Yadda Za Ku Yaki Tsoron Fara Sana'a

Yadda Za Ku Yaki Tsoron Fara Sana'a

FARGABAR FARA SANA'A


Tabbas mutane da dama tsoro da fargabar wani abu mara kyau yana hana su fara wani abu muhimmi a rayuwarsu. Wanda suke so za su fara sana'a sau da yawa suna fuskantar tsoro kala-kala.


Yadda Za Ku Yaƙi Tsoron Fara Sana'a
Hoto: Kantver/Deposit photos

Marubuci:- Abubakar Abba


Wasu na tsoron wataƙila mutane ba za su so sana'ar da za su fara ba?


Wasu na tsoron ta yaya ma za su samu kwastomomi?


Wasu na tsoron abin da mutane za su ce a kansu saboda sun fara wata sana'a. 


Wasu kuma tsoronsu shi ne; idan sun fara sana'a ƙarshe jarinsu zai karye.


Wasu fargabar su shi ne, ta ina ma za su fara?


Wasu ma ba su san takamaimai abin da suke tsoro ba, su dai kawai suna fargaba kuma sun kasa shawo kanta.


Waɗannan tsorace-tsorace dama wasu wanda ba mu ambata ba, suna nan suna damun mutane da dama, kuma hakan ya hana su fara abubuwan da za su amfane su a rayuwarsu.


Idan kana fama da irin wannan matsalar, akwai hanyoyin da za ka bi domin shawo kanta, kuma da taimakon Allah za ka samu damar fara sana'ar da kake so cikin nasara.


1. KA RUBUTA NAU'IN SANA'AR DA ZA KA FARA


Duk lokacin da kake so ka fara wata sana'a ka yi ƙoƙari ka rubuta duk abin da ya zo ƙwaƙwalwarka a lokacin.


Rubuta nau'in sana'ar da za ka fara zai taimaka maka wajen fahimtar inda za ka dosa a gaba.


2. INA ZA KA DINGA SAMUN KAYAN AKAN SARI


Idan wani kayan za ka dinga sayarwa, ka nemi ina ne ake zuwa a sayo kayan akan sari, hakan zai taimaka maka wajen lissafin farashi da riba.


3. A INA ZA KA SIYAR DA KAYANKA?


Ka rubuta gurin da kake tunanin cewa ya dace ka yi sana'ar a wajen, a shagon kasuwa ne, ko a gida ne, ko a Online ne? Duka waɗannan abubuwan da ya kamata ka rubuta ne domin za su rage maka wahalhalu da fargabar abin da zai zo a gaba.


4. SU WANE NE KAKE SO SU SAYI KAYANKA? (TARGET CUSTOMERS)


Duk abin da za ka sayar ko za ka sarrafa, yana da kyau ka yi lissafin su wane ne za su saya idan ka fito da shi?


Hakan zai taimaka maka wajen farashi da kuma talla.


Za ka fita daga rigimar masu cewa kayanka ya yi tsada, ko masu cewa ba lallai ne kayanka suna da kyau ba saboda sun yi arha.


5. TA YAYA ZA KA TALLATAWA MASU SAYA?


Ka zauna ka yi iya tunaninka, wasu hanyoyi za ka bi domin tallata sana'ar taka idan ka fara, yin wannan tunanin zai taimaka maka wajen cire duk wani tsoro da fargabar abin da zai zo a gaba.


Rubuta irin wannan tsare-tsaren akan takarda zai taimaka ka daina tsoron fara wata sana'a kuma zai ƙara haskaka maka hanya domin za ka hango inda nasararka take da inda damarmakinka suke.


" Ba'a fafe gora ranar tafiya ".

Friday, 20 December 2024

Yadda Za Ku Biya Bashi Ba Tashin Hankali

Yadda Za Ku Biya Bashi Ba Tashin Hankali

1. ADDU'A


Duk wata dabara ba ta fitar da mutum daga rikicin bashi ba tare da taimakon Allah ba. 


Bashi wata iriyar matsala ce wadda bayan ƙarfinka na zahiri har ƙarfin tunanin ka tana karyawa, sai mutum ya ji duk ba shi da kuzari, ko ya ji ya kasa aikata wani abu da zai kawo masa ci gaba a rayuwarsa saboda tunanin bashin da ake bin sa.


Yadda Za Ku Biya Bashi Ba Tashin Hankali
Hoto: Sergei Chuyko

Marubuci:- Abubakar Abba


Shi ya sa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koya mana wasu addu'oi domin fita daga matsalar bashi.


Daga cikin su akwai:


"اللهم أكفني بحلالك عن حرامك وأغننى بفضلك عنمن سواك" 


Akwai wasu addu'o'in masu yawa, wanda idan ka bincika su za ka same su kuma da taimakon Allah za ka ga komai ya zo da sauƙi.


Sannan a yawaita Istigfari, da Salatin Annabi, wannan kuwa babban makami ne na yaƙar damuwa da tashin hankali.


2.  LISSAFA NAWA NE AKE BIN KA BASHI, DA WANDA SUKE BIN KA BASHI


Anan za ka gane muhimmancin lissafi da rubutaccen lissafi, domin idan ba ka rubuta wanda suke bin ka bashi ba, da kuma adadin abin da suke bin ka ba, za ka shiga ruɗani sosai, domin ƙwaƙwalwarka za ta iya ba ka kunya wata rana.


Rubuta sunaye na wanda suke bin ka bashi zai sauƙaƙa maka wajen sanin hanyar da za ka ɓullowa kowa wajen biyansa.


Sanin yawan bashin da ake bin ka zai taimaka maka wajen sanin hanyoyin da za ka bi wajen biya da kuma sanin irin aikin da za ka yi ka biya su.


3. KA TSARA KASAFI NA KOWANE WATA


Fitar da tsarin abin da za ka kashe a wata, da daidaita shi yadda zai taimaka maka ka biya wani kaso na bashin da ake bin ka, zai taimaka maka sosai wajen samun sauƙin biyan bashin.


Idan ka zauna haka babu tsari, zai wahala gare ka ka iya biyan bashi.


Amma ka tsara kasafi na abin da kake buƙata a wata, da abin da kake tsammanin samu, da yadda za ka ƙara hanyar shigowar kuɗinka, da abin da ya kamata ka biya bashi duk wata, abin da ya kamata ka kashe a wata, da taimakon Allah hakan zai sauƙaƙa maka wajen samun mafita.


4. FARA BIYAN BASHIN DA YA FI MATSALA


Idan ana bin ka basussuka da yawa, zai zama ka shiga ɗimuwa, wataƙila ka rikice ka ce za ka biya kowa lokaci guda, wanda yin haka kuskure ne.


Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka tsaya ka duba bashin da ya fi ba ka matsala, ko wanda zai iya jefa ka matsala a kusa, ko wanda ya fi ɗaga maka hankali ya hana ka sukuni ko wanda ya fi yawa kuma lokacin biyansa yake a kusa, kodai wani abu makamancin wannan, ka fara da shi ragowar za su zo maka da sauƙi, domin za ka samu nutsuwa da ƙwarin gwiwa bayan ka sallami bashin da yake ci maka tuwo a ƙwarya.


5. KA BIYA DAIDAI ƘARFINKA


Wasu da zarar an zo an matsa musu kan sai sun biya bashin da ake bin su, sai su ga gwara su biya nan take su huta, e hakan yana da kyau wani lokacin, amma a wajen ɗan kasuwa hakan zai iya zamar masa matsala gagaruma wadda za ta iya kai shi ga faɗawa wani bashin kuma.


A duk lokacin da ake bin ka bashi, yi ƙoƙarin biyan abin da za ka iya, a hankali har ka kammala biya, kar ka yi wa jarinka illa, kar ka yi wa kanka illa, wadda daga ƙarshe za ka faɗa wata rigimar da ta fi ta farkon.


6. RAGE KASHE KUƊI BABU DALILI


Idan ƙaddara ta sanya ana bin ka bashi, to ka yi ƙoƙari iya ƙarfinka ka ga ka sallami mutane.


Daga cikin hanyoyin da za ka bi shi ne ka rage kashe kuɗi babu dalili, da zarar ka ga mai kaza ko mai lemo ka ce za ka siya, ko da zarar maƙocinka ya sauya abin hawa kai ma ka ce sai ka sauya naka, ko da zarar shagon kusa da kai ya yi fenti kai ma ka ce sai ka yi, ko da zarar ƙawarki ta sayi kayan kitchen ki ce ke ma sai kin siya, duk irin wannan kashe-kashen kuɗin ba naka ba ne.


Dole ka tabbatar duk abin da za ka siya yana da wani amfanin da zai ba ka damar biyan bashi ko ya taimakawa kasuwancinka ya tsaya da ƙafarsa, ko abin da ya zamar maka dole sai ka siya domin rayuwa ta tafi yadda ya kamata.


7. KA CI BASHI ƊAYA MAI ƘWARI


Wato wani lokacin, masu ƙananun basussuka sun fi masu manyan bashi uzzurawa da matsawa mutum, idan tsautsayi ya sa ka ci bashin mutane daban-daban kuma suka uzzura maka, ka rasa yadda za ka yi ka biya su akan lokaci, to hanya mafi sauki shi ne ka ciyo wani bashin mai ƙwari wanda za ka biya su duka, kai kuma ka zo ka mayar da hankali wajen biyan wannan bashin da kaɗan-kaɗan.


Wani lokacin wannan ita ce hanya mafi sauƙi, domin za ta ba ka damar nutsuwa da kuma samun tartibiyar hanya ba tare da ka shiga uku ba.


8. NEMI WATA HANYAR ƘARIN KUƊIN SHIGA


Yawanci buƙatu ƙaruwa suke a yanzu, ware wani kuɗi domin biyan bashi yana da wahala sosai idan hanyar shigar kuɗinka ba ta sauya ba.


Kana samun dubu 30 a wata, ana bin ka bashin da kake biyan dubu 15 a wata, buƙatunka suna ƙaruwa duk wata, hakan zai jefa mutum cikin damuwa sosai.


Amma idan ka yi ƙoƙari ka samu wata hanyar da kuɗi zai ƙara shigo maka, za ka samu sauƙi.


Misali, kana sayar da Atampa a kasuwa, zai wahala ka ce za ka ƙara wata sana'ar ba tare da ta farko ta samu tasgaro ba. To amma yanzu zamani ya zo da abubuwa masu yawa da za ka iya ba tare da sun hana ka sana'arka ta farko ba.


Za ka iya Video Content wanda kake nuna inda kake sana'arka, kuma mutane za su kalla, kai kuma za ka samu 'yan kuɗaɗenka a Monetization.


Za ka iya shiga Crypto, amma fa ka tabbata ka koya, kar ka shiga da ka a zo a samu matsala, ba ruwana.


9. BA WA KANKA KYAUTA


Masana sun gano cewa duk lokacin da kake wani abu idan ka san cewa za ka samu wata kyauta ko karramawa ko wani lada a ƙarshensa, to ka fi bayar da himma.


Haka ma za ka yi idan kana biyan bashi, sakawa kanka wata kyauta da za ka ji daɗinta bayan ka biya wani kaso ko wani adadi na bashin da ake bin ka.


Misali, ka sanyawa kanka cin wani abu da kake matuƙar sha'awa amma saboda ana bin ka bashi ba ka iya saya ka ci, kamar a ce ka daina cin Naman Kazar da kake so saboda kana ƙoƙarin biyan bashi, to da zarar ka biya wani adadi, sai ka sayawa kanka Kaza ka more.


Yin hakan zai ƙara zaburar da kai wajen kula da kuma kiyaye lokacin biyan bashin.


Akwai wasu tarin hanyoyin da za ka bi wajen biyan bashin da ake bin ka, zamu tattaunasu da faɗi a nan gaba in sha Allah.


Ku yaɗa wannan don Allah, mutane da yawa suna cikin bashi amma ba su san yadda za su biya ba, za ka samu lada idan ka taimakawa wani ya fita daga matsalar bashi.

Monday, 9 December 2024

Kafin Ka Fara Kasuwanci Ka Karanta Wannan Sirrin

Kafin Ka Fara Kasuwanci Ka Karanta Wannan Sirrin

Mutane da yawa suna so su fara kasuwanci, amma shawarwari sun yi musu yawa, wasu kuma sun rikice sun ma rasa ta inda za su fara, wasu kuma sun fara amma ba wadda ta dace ba, wasu kuma kansu ya kulle, kawai sun haƙura sun bi yayi.


Kafin Ka Fara Kasuwanci Ka Karanta Wannan Sirrin
Hoto: LinkedIn

Marubuci:- Abubakar Abba


A gefe guda kuma, masana kasuwanci suna ba da shawara cewa kafin ka fara kasuwanci ka yi market research, ma'ana ka yi nazarin kasuwar ka san ma mene mutane suke da buƙata ko kuma mene zai ba ka ribar da kake buƙata.


Da yawa muna so mu yi nazarin kasuwa amma wasunmu ba su san ta ina za su fara ba.


Shi ne ya sa za ka ga mutane da yawa sun kashe kuɗi sun buɗe shago ko sun fara wani kasuwanci amma ba tare da an je ko'ina ba sai ka ga sun rufe saboda ba ciniki, ko kuma ana cinikin amma ba zai iya bayar da ribar da ake buƙata ba, saboda haka, ƙarshe sai dai a kwashe kaya a rufe kasuwanci.


Sau da yawa kai ma kana ganin wasu sun fara kasuwanci a wani wajen za ka ce lallai waɗannan ba su san abin da ya kamata su fara ba, da yawanmu muna ganin irin wannan kusa da mu, kuma muna fahimtar cewa akwai kuskure.


Wani lokacin mutane suna duba abin da yake birge su ne kawai, sai su narka kuɗi su fara kasuwancin wannan abin, ƙarshe kuma su ga mutane sun ƙi ba su haɗin kai.


Wasu kuma, da zarar sun ji an ce abu kaza yana tafiya a kasuwa, sai su yi maza su fara kasuwancinsa, daga ƙarshe kasuwancin ya durƙushe.


Wasu kuma da zarar sun ga wani yana samun kuɗi da wata sana'a, ba tare da sun yi nazarin da ya kamata ba, su ma sai su fara ƙarshe a zo a durƙusar da sana'ar ko kuma bayan sun fara sana'ar su ga ba sa ciniki ko ba sa samun kuɗin da suka yi tsammani za su samu.


Wannan duk yana biyo bayan rashin nazarin kasuwa ne wanda ya kamata.


Ita kasuwa kafin a fara ta akwai buƙatar a yi nazarinta kuma a auna ta.


1. MATSUWA


Abu na farko da ya kamata ka duba kafin ka fara wani kasuwanci a wani waje shi ne, yaya mutanen wajen suke da bukatar wannan abin?


Bayan ka zaɓi irin kasuwancin da kake so ka fara, to ka auna shi a wannan sikelin, idan ka ga mutane suna tsananin buƙatar abin, to lallai kasuwanci ne da za ka iya shiga amma fa bai tsaya iya buƙata ba, akwai wasu ƙarin ma'aunai da za ka duba.


2. GIRMAN KASUWA


Bayan ka duba buƙatar mutane, to abu na gaba shi ne, mutum nawa ne za su iya sayan wannan abin?


Wani lokaci za ka ga tabbas mutane suna buƙatar abin da za ka sayar amma yawan mutanen bai kai ka narka kuɗinka ba.


Idan za ka fara kasuwa to ka tabbata ka yi wannan lissafin.


Misali:


Za ka buɗe shagon cajin waya, sai ka ga duk yankin babu mai caji, kuma ka ga wasu mutanen suna tafiya mai nisa domin su kai cajin wayar su, to ka ga wannan alama ce da ke nuna maka akwai buƙatar shagon caji, to amma sai ka ga ai masu kai cajin su ne kaɗan a mutanen unguwar saboda yawanci suna da solar kuma suna da halin kunna generator, to ka ga anan ba za ka zo ka narka kuɗinka ba, saboda kwastomomin ba za su mayar da abin da za ka kashe ba.


3. FARASHIN DA ZA'A IYA BIYA


Bayan ka yi lissafi, ka ga cewa akwai buƙatar abin da za ka fara, sannan kuma masu buƙatar suna da yawan da za ka samu riba sosai, to abu na gaba shi ne, za su iya biyan farashin da za ka saka?


Wannan yana da matuƙar muhimmanci, duk Ɗan Kasuwar da bai lissafa wannan ba za ku ga ya zo yana ta kumfar baki yana ganin laifin mutane wai sun ƙi daraja sana'ar sa, kuma ba laifinsu ba ne, shi ne bai yi lissafi daidai ba.


Misali:


Idan za ki buɗe wajen gyaran gashi mai daraja, bayan kin gama nazarin kasuwa kin ga buƙatar mutanen wajen, sannan kin ga yawan kwastomomin ki, to sai ki duba; idan kin buɗe irin tsayayyen da kike buri, za su iya biyan kuɗin gyaran gashin da za ki musu?


Kar ki buɗe wajen gyaran gashin 'yan gayu a yankin 'yan koko ba za su zo ba, idan sun zo ma kin faɗa musu farashi, tafiya za su yi su je inda za'ayi musu da arha, domin su ba kwalliya ko adon shagonki ne zai ɗauki hankalin su ba. 


4. SAURIN SAMUN KWASTOMA


Yana da kyau sosai, bayan ka gama wancan nazarin, sai ka duba yaya saurin samun kwastoma yake, kuma nawa za ka kashe kafin samun kwastoma guda ɗaya?


Idan ba ka yi wannan lissafin ba, to zai iya yiwuwa ka zo kana ciniki amma ba ka ganin riba, saboda kuɗin da kake kashewa kafin samun kwastoma yana kusa ko kuma daidai da abin da kwastoma zai ba ka.


Misali:


Wadda ta buɗe shagon gyaran gashi, wajen da ta buɗe mutane ba za su gane ta ba sai ta saka allon talla, sai ta yi ƙatuwar abar talla, sai ta tayar da generator ta kashe kuɗin manfetur sannan za'a san da ita, sannan sai ta yi talla sosai kafin mutane su zo wajen, bayan sun zo kuma, ma'aikata 2 ko 3 ne za su yi musu hidima, kun ga dole su ma a biya su, kuma idan sun zo da farko ba lallai wasu su sake zuwa ba sai an kuma waccar wahalar, to kun ga samun kwastoma 1 ya ci mata kuɗi sosai, to idan ba za ta iya mayar da wancan kuɗin da take kashewa ba akan yawan kwastomomin da za su zo kullum ba, to ba lallai ta gane cewa tana samun riba a cinikin da ake yi a shagon ba.


5. DA ME KA FI SAURA


Idan kana so ka fara wata sana'a ko wani kasuwanci, bayan ka gama nazarinka, yana da kyau ka duba mene ne za ka yi wanda zai bambanta ka da ragowar masu irin wannan sana'ar?


Mafi yawan lokuta mutane ba su cika kallon mene ya kamata su inganta a wani kasuwanci da suke son farawa ba, wanda rashin yin hakan ya sa za ku ga an cunkushe waje ɗaya babu ci gaba, ƙarshe a zo a durƙusar da sana'ar baki ɗayanta.


Akwai ragowar abubuwa 5 wanda ba mu tattauna su anan ba, kuma suna da muhimmanci mutum ya duba su kafin fara wani sabon kasuwanci, ku ci-gaba da bibiyar mu za mu tattauna sosai akan wannan batun da ma ragowar ababen da ba mu tattauna anan ba.

Monday, 13 April 2020

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 8

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 8

Wannan wani sabon shirin rayuwar soyayya ne mai ƙayatarwa.

Rayuwar Masoya Fita ta Takwas

Idan har kana soyayya , lallai wannan shirin zai faranta maka rai, haka kema idan kina soyayya , karku sake a baku labari.

Wannan shine fita ta takwas, idan baku manta ba a baya mun kawo muku Rayuwar Masoya Fita Ta Bakwai, kamar yadda mukayi muku alƙawarin zamu kawo muku Ci gaban shirin , cikin nufin ubangiji mun samu damar kawo muku fita ta takwas.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Wannan sabon shirin (Fita Ta Takwas) ya bambanta da sauran, domin a wannan anyi wani sabon salo wanda bakasafai ake ganin irin haka a fina-finan Kannywood ba.

Jerin sunayen jaruman da suka taka muhimmiyar rawa a cikin shirin rayuwar masoya.

Ga kaɗan daga cikin sunayen su:

Fatima Tahir Saraki
Hajiya Bakyafishi
Muhammad Sani (Abba)
Sani Musa Abubakar

Da sauran su

Rayuwar Masoya shiri ne da ya samu kyakkyawan aiki daga hannun Mujahid M. Soja.

Ku Ci gaba da kasancewa da mu , domin samun Ci gaban shirin Rayuwa Masoya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 5

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 6

Rayuwar Masoya Full Episode 7

Dafatan shirin Rayuwar Masoya zai Ilimantar ya kuma faɗakar da al'umma, musamman matasan mu.

MURYAR HAUSA24 muna kuma fatan za'ayi kallo gami da sauraro lafiya cikin Nishaɗi da Walwala.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Monday, 30 March 2020

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 7

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 7

Wannan wani sabon shirin rayuwar soyayya ne mai ƙayatarwa.


Rayuwar Masoya Fita ta Bakwai

Idan har kana soyayya , lallai wannan shirin zai faranta maka rai, haka kema idan kina soyayya , karku sake a baku labari.

Wannan shine fita ta bakwai, idan baku manta ba a baya mun kawo muku Rayuwar Masoya Fita Ta Biyar, kamar yadda mukayi muku alƙawarin zamu kawo muku Ci gaban shirin , cikin nufin ubangiji mun samu damar kawo muku fita ta bakwai.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye..

Jerin sunayen jaruman da suka taka muhimmiyar rawa a cikin shirin rayuwar masoya.

Ga kaɗan daga cikin sunayen su:

Fatima Tahir Saraki
Hajiya Bakyafishi
Muhammad Sani (Abba)
Sani Musa Abubakar

Da sauran su

Rayuwar Masoya shiri ne da ya samu kyakkyawan aiki daga hannun Mujahid M. Soja.

Ku Ci gaba da kasancewa da mu , domin samun Ci gaban shirin Rayuwa Masoya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Rayuwar Masoya Full Episode 4

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 5

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 6

Dafatan shirin Rayuwar Masoya zai Ilimantar ya kuma faɗakar da al'umma, musamman matasan mu.

MURYAR HAUSA24 muna kuma fatan za'ayi kallo gami da sauraro lafiya cikin nishadi da Walwala.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tuesday, 17 March 2020

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 6

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 6

Wannan wani sabon shirin rayuwar soyayya ne mai ƙayatarwa.


Rayuwar Masoya Fita ta Shida

Idan har kana soyayya , lallai wannan shirin zai faranta maka rai, haka kema idan kina soyayya , karku sake a baku labari.

Wannan shine fita ta shida, idan baku manta ba a baya mun kawo muku rayuwar masoya fita ta biyar, kamar yadda mukai muku alƙawarin zamu kawo muku Ci gaban shirin , cikin nufin ubangiji mun samu damar kawo muku fita ta biyar.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Jerin sunayen jaruman da suka taka muhimmiyar rawa a cikin shirin rayuwar masoya.

Ga kaɗan daga cikin sunayen su:

Fatima Tahir Saraki
Hajiya Bakyafishi
Muhammad Sani (Abba)
Sani Musa Abubakar

Da sauran su

Rayuwar Masoya shiri ne da ya samu kyakkyawan aiki daga hannun Mujahid M. Soja.

Ku Ci gaba da kasancewa da mu , domin samun Ci gaban shirin Rayuwa Masoya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 3

Rayuwar Masoya Full Episode 4

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 5

Dafatan shirin Rayuwar Masoya zai Ilimantar ya kuma faɗakar da al'umma, musamman matasan mu.

MURYAR HAUSA24 muna kuma fatan za'ayi kallo gami da sauraro lafiya cikin nishadi da Walwala.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Monday, 13 January 2020

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 5

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 5

Wannan wani sabon shirin rayuwar soyayya ne mai ƙayatarwa.



Rayuwar Masoya Fita ta Biyar

Idan har kana soyayya , lallai wannan shirin zai faranta maka rai, haka kema idan kina soyayya , karku sake a baku labari.

Wannan shine fita ta biyar, idan baku manta ba a baya mun kawo muku rayuwar masoya fita ta hudu, kamar yadda mukai muku alƙawarin zamu kawo muku Ci gaban shirin , cikin nufin ubangiji mun samu damar kawo muku fita ta huɗu.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye..

Jerin sunayen jaruman da suka taka muhimmiyar rawa a cikin shirin rayuwar masoya.

Ga kaɗan daga cikin sunayen su:

Fatima Tahir Saraki
Hajiya Bakyafishi
Muhammad Sani (Abba)
Sani Musa Abubakar

Da sauran su

Rayuwar Masoya shiri ne da ya samu kyakkyawan aiki daga hannun Mujahid M. Soja.

Ku Ci gaba da kasancewa da mu , domin samun Ci gaban shirin Rayuwa Masoya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 2

RAYUWAR MASOYA FULL EPISODE 3

Rayuwar Masoya Full Episode 4

Dafatan shirin Rayuwar Masoya zai Ilimantar ya kuma faɗakar da al'umma, musamman matasan mu.

MURYAR HAUSA24 muna kuma fatan za'ayi kallo gami da sauraro lafiya cikin nishadi da Walwala.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Monday, 30 December 2019

Fitattun Wakoki Guda 10 Mafi Shahara a 2019

Fitattun Wakoki Guda 10 Mafi Shahara a 2019

Kamar yadda ya faru a shekara ɗaya zuwa biyu da suka gabata, a bana ma mawaƙan Hausa na zamani su ne kan gaba wajen fito da sababbin waƙoƙi tare da mamaye zukata da kuma kafafen yaɗa labarai, musamman gidajen rediyo da soshiyal midiya.

Mawaƙi Hamisu Breaker

DAGA IBRAHIM SHEME DA ABBA MUHAMMAD

Hakan ya sa su ne aka fi yayi fiye da waƙoƙin makaɗan gargajiya irin su Shata, Ɗanƙwairo, Uji, Uwaliya, Barmani ko Ɗan'anace.
Su mawaƙan gargajiya, babu wata sabuwar waƙa da ta fito daga gare su a bana har ta yi suna tare da mamaye zukata.
Hasali ma dai yawancin mawaƙan gargajiya sun mutu, 'yan ƙalilan ɗin da suka rage - irin su Atta Dabai, Musa Ɗanbade, Shehu Ajilo Ɗanguziri da Babangida Kakadawa - ba su yi wata sabuwar waƙa da za a ce ana zancenta ba a cikin wannan shekara.
Yawanci a kan saka su a rediyo ne saboda sabo, kuma ana jin su a kafafen soshiyal midiya irin su Facebook, WhatsApp, YouTube da Telegram inda aka buɗe dandali daban-daban domin su.
Yawancin masu sauraren su ɗin ma manya ne ko matasan da ke gab da shiga da'irar dattijai.
Hasali ma dai, in ban da Musa Ɗanbade da ya yi wa Sarkin Jiwa waƙa, da kuma Gwaggo Marka daga Jihar Nassarawa, babu wani mawaƙin gargajiya da za a ce ya yi wata sabuwar waƙa da aka saurare ta sosai a bana.
Wani abin lura kuma shi ne, mawaƙan zamani (kusan dukkan su masu amfani ne da fiyano wajen kiɗa), waɗanda su ka ciri tuta a shekara ɗaya ko biyu baya, yawanci su ɗin ne dai suka riƙe kambunsu na jagaban mawaƙa a 2019.
Sun yi waƙoƙi masu yawan gaske waɗanda suka yi fice, ta yadda aikin zaƙulo guda goma kacal mafi shahara a cikinsu ya kasance babban tasku.
Duk da haka, mun yi bincike mai zurfi a masana'antar fina-finai ta Kannywood tare da bibiyar wasu gidajen rediyo na FM da na talabijin da masu sayar da waƙoƙi, inda bayan mun tace sai muka zaƙulo goma da aka fi so ko aka fi saurare a wannan shekara ta 2019.
Wannan layi ne

Ga su kamar haka:

1. 'Hafeez' - UMAR M. SHAREEF (tare da Khairat Abdulllahi):

















Waka ta farko ta 'Hafiz ga ni na zo'

Waƙar 'Hafeez' ta fito ne a fim ɗin 'Hafeez' na furodusa Abubakar Bashir Maishadda, wanda Ali Nuhu ya ba da umarni.
Fitaccen mawaƙi kuma jarumi, wanda yana kan gaba a cikin jerin matasan jaruman da tauraronsu ke haskawa a wannan zamani, wato Umar M. Shareef, shi ne ya rubuta waƙar tare da rera ta tare da Khairat Abdullahi, kuma shi ne ya hau waƙar a fim ɗin tare da jaruma Hassana Muhammad.

Umar M ShareefHakkin mallakar hotoUMAR M SHAREEF
Image captionWakokin Umar M Shareef uku na daga cikin 10 da suka fi shahara a 2019
Waƙa ce tsakanin masoya biyu. A cikinta, Umar da Khairat sun nuna ƙwarewa wajen zuba kalaman soyayya da kuma raushin murya. Waƙar ta yi fice matuƙa, musamman a wurin bukukuwa.
Waƙar ta ƙara shiga zuciyar masoyan mawaƙin bayan an nuna fim ɗin a gidan sinima na Film House da ke Ado Bayero Mall, Kano. Ita ce waƙar da ta fi kowace waƙar fim yin fice a shekarar 2019.
Short presentational grey line

2. 'Hafeez' - NURA M. INUWA (tare da Zuwaira Abdulsalam):










Waka ta biyu 'Hafiz Ka zo'

Fitaccen mawaƙi Nura M. Inuwa shi ma ya yi waƙa da aka saka a fim ɗin 'Hafeez' na furodusa Abubakar Bashir Maishadda.
Kamar yadda aka sani, kusan dukkan fina-finan Maishadda daga Umar M. Shareef, Nazifi Asnanic, sai Abdul D. One ne suke yi masa waƙoƙin su, to amma a wannan karon, kwatsam, sai aka ji Nura M. Inuwa ya yi masa waƙoƙi a wasu fina-finan sa, waɗanda suka haɗa da 'Hafeez'.
Waƙar ta soyayya ce, inda mawaƙin ya yi amfani da kalamai masu ratsa zuciya kamar yadda aka san shi da yi.
Fitaccen mawaƙi kuma jarumi Umar M. Shareef ne ya hau waƙar a fim ɗin tare da Maryam A.B. Yola, A'isha Humaira, Maryam Yahya, Bilkisu Shema, Firdausi Muhammad, Hassana Muhammad da Amal Umar, inda dukkan su kowacce ta na neman soyayyar Hafeez.
Mawaƙin ya canza salo a ƙarshen waƙar, kamar yadda ya kan yi a wasu waƙoƙinsa. Waƙar sai ta zama kamar kishiya ga wadda Umar M. Shareef ya rera, wadda sunansu ma ɗaya.
Hakan ya sa masoyan mawaƙan suka dinga musu kan wacce ce ta fi daɗi.
Short presentational grey line

3. 'Kar Ki Manta Da Ni' - ABDUL D. ONE (tare da Murja Baba):










Waka ta uku a 2019 'Kar ki manta da ni'

Wannan waƙa ta fito ne a fim mai sunanta, wato 'Kar Ki Manta Da Ni'.
Fitaccen matashin mawaƙi Abdul D. One, wanda tauraruwarsa ke haskawa a wannan zamani, shi ne ya rubuta ta kuma ya rera ta, inda nan da nan ta yi farin jini musamman a fim ɗin 'Kar Ki Manta Da Ni' na darakta Ali Nuhu.
Duk da cewa shi ma ubangidan Abdul ɗin, wato Umar M. Shareef, ya yi waƙoƙi a fim ɗin, amma sai mutane su ka fi son ta Abdul ɗin.
Waƙar ta soyayya ce wadda a cikin ta mawaƙin ya ba soyayya haƙƙin ta yadda ya kamata.
Ya baje basira da hazaƙa ta yadda idan masoya su na sauraren ta za su ji kamar babu wani abu da ya kai soyayya daɗi a duniya, musamman masoyan da su ka yi wa juna alƙawarin ba za su taɓa mantawa da juna ba.
Mata, musamman sababbin shiga zarafin soyayya, suna son waƙar matuƙa.
Short presentational grey line

4. 'So Na Amana' - GARZALI MIKO - (tare da Zuwaira Isma'il)










Waka ta hudu a 2019 'So na amana'

Jarumi Garzali Miko, wanda a bana ya rikiɗe zuwa mawaƙi, ya shigo dandalin waƙa da ƙafar dama.
Ana kiran Garzali sabon mawaƙi ne domin bai daɗe da fara waƙa ba.
Duk da haka cikin ƙanƙanin lokaci ya yi fice.
Sai dai kuma masu saurare da dama ba su san cewa shi da kansa ne ya rera waƙoƙin ba, saboda murya da salon waƙoƙinsa sun yi kama da na mawaƙi Hamisu Breaker Ɗorayi ko Adam A. Zango.
Wani abu da ya ƙara yayata waƙar shi ne bayan an sake ta a YouTube, shi ne kama daraktan waƙar, Sunusi Oscar 442, da hukuma ta yi har ya yi zaman gidan yari na 'yan kwanaki.
Daga nan sai ta kasance kowa yana so ya ga abin da aka yi a cikin waƙar da har ya yi sanadin sakaya daraktan.
Dalilin kamun da aka yi wa Sunusi Oscar ya sa duk inda ka bi a arewacin Nijeriya ko ka saurari kafafen sadarwa na zamani, za ka ji kawai ana ta yaɗa waƙar.

5. 'Na Yi Sa'a' - HAMISU BREAKER ƊORAYI:










Waka ta biyar a 2019 'Na yi sa'a'

Hamisu Sa'id Yusuf, wanda aka fi sani da Hamisu Breaker Ɗorayi, fitaccen mawaƙi ne wanda ke kan ganiyarsa. Tauraronsa yana haskawa yadda ya kamata, domin da wuya ka ga ya fitar da sabuwar waƙa ba ta yi tashe ba.
A wannan shekara ta 2019, waƙarsa ta 'Na Yi Sa'a' ita ce waƙarsa da ta zagaya ko'ina, ta kasance waƙar da mata suka yi ta ɗaukar bidiyon kansu da wayarsu, suna bin ta suna ɗorawa a shafukansu na Instagram.
Har ta kai ga wasu yara ƙanana, mace da namiji, suka kwaikwayi rawar da Hamisun da jaruma Rakiya Moussa Poussi suka yi.
Waƙar ta ɗau hankalin matasa sosai.
Short presentational grey line

6. 'Abba Gida-Gida Abba' - TIJJANI GANDU:










Waka ta shida 'Abba gida-gida'

Tijjani Gandu ya fara yin tashe ne da waƙar 'Yar Maye' a 'yan shekarun baya, amma kuma daga bisani sai aka ji shi tsit, kamar ba a taɓa yayinsa ba a masana'antar Kannywood.
A baya ya yi waƙoƙi masu zafi da aka yi fina-finai da su.
Kwatsam, a bana sai ga mawaƙin ya faso fage da waƙa mai taken 'Abba Gida-Gida Abba' gab da zaɓukan shekarar 2019.
Waƙa ce ta yaƙin neman zaɓen Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda aka tsayar a matsayin ɗan takarar zama gwamnan Jihar Kano a jam'iyyar PDP.
Lokaci guda waƙar ta bazu a jihohin Arewa kamar wutar daji. Duk lungu da saƙon da ka shiga za ka ji ana jin waƙar. Maza da mata, yara da manya suna rera ta.
'Yan mata daga jihohi daban-daban sun yi ta ɗaukar bidiyon kansu, suna bin waƙar, suna sakawa a shafukan su na Instagram don nuna ƙaunarsu ga waƙar da kuma ɗan takarar.
A Gombe, wani mawaƙi ya ɗau samfur ɗin waƙar ya yi 'Inuwa Gida-Gida'.
Dalilin waƙar ta Tijjani Gandu ne aka daina kiran ɗan takarar na PDP da cikakken sunansa, sai Abba Gida-Gida.
Mawaƙin ya kambama gwanayen sa a cikin waƙar.
An tabbatar da cewa waƙar ta taimaka wa ɗan takarar wajen samun ƙarin magoya baya a zaɓen.

7. 'Baban Abba Ganduje' - DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA):










Waka ta bakwai a 2019 'Baban Abba Ganduje'
Mawaƙin siyasa Dauda Adamu Kahutu, wanda ake yi wa laƙabi da Rarara, ya mayar da martani ga mawaƙin 'Abba Gida-Gida', wato Tijjani Gandu.
Rarara ya yi waƙar ne bayan Tijjani Gandu ya fitar da waƙar 'Abba Gida-Gida Abba', inda shi kuma ya kira tasa waƙar da 'Baban Abba Ganduje'.
Waƙar kusan daga farkonta har ƙarshen ta habaici ce.
Wannan ya sa masoyan 'yan takarar suka samu abin da suke so; masoyan Gwamna Ganduje suka riƙa yaɗa waƙar don ɓata wa masoyan Abba rai.
Waƙar ta yi fice, ta inda ko'ina ka shiga za ka ji ta.
Har a gidajen biki ana saka ta don a nishaɗantar da mahalarta bikin.
Waƙar ta ƙara tashe ne bayan zaɓe da aka sanar da cewa Ganduje ne ya sake lashe zaɓe.

8. 'Sabada' - UMAR M. SHAREEF da KOREDE BELLO:









Waka ta takwas a 2019 'Sabada'

Waƙar 'Sabada' ta zo da wani sabon salo da ba a saba ji daga mawaƙan Hausa na wannan zamani ba.
Umar ya yi tattaki tun daga Kaduna zuwa Legas ya yi waƙar tare da fitaccen matashin mawaƙi Korede Bello na kamfanin waƙoƙi mai suna Mavin Records, mallakin fitaccen mawaƙi Don Jazzy.
Korede Bello ya yi waƙar ne cikin harshen Turanci, inda shi kuma Umar M. Shareef ya gwamutsa Turanci da Hausa.
Umar ya nuna waƙa burinsa ce, kuma ya kama da wuta.
Shi kuma Korede ya kama sunan Khadija ne yana cewa yana son yadda take rawa shi ma.
Waƙar ta yi daɗi matuƙa, ta inda masoyan Umar suka yi ta tururuwar neman ta.
Haka kuma Umar ya ƙara samun masoya daga Kudu saboda saka Korede da ya yi a waƙar.
Waƙar dai salon hip-hop ce, ba ta nanaye da su Umar suka saba yi ba.
To amma fa ba wannan ba ce waƙar da fara yi da mawaƙan Kudu ba, don kuwa a 2017 ya yi waƙa da fitaccen makaɗi kuma mawaƙi Selebobo.
Sai dai wannan da ya yi da Korede ta fi yin fice fiye da waccan, domin ita 'Sabada' har bidiyo an yi mata

Short presentational grey line

9. 'Yaran North Side Cypher 2019' - DJ AB, TEESWAGG, LIL PRINCE, JIGSAW







Waka ta 9 a 2019 'Yaran North Side Cypher 2019'

DJ AB, TEESWAGG, LIL PRINCE, da JIGSAW mawaƙan salon hip-hop ne da ke zaune a garin Kaduna.
Sun yi waƙoƙi da dama, sai dai wannan waƙar ta haɗaka ce, inda aka nuna su a wani wurin cin abinci suna hira, daga nan ɗaya bayan ɗaya kowannen su ya fara ba junansu labarin sabuwar budurwar da ya yi, har ya ke nuna masu hotonta a wayarsa a bidiyon waƙar.
Nan take duk suka gane cewa ai yarinya ɗaya su ke nema.
Waƙar ta yi fice wurin samari da 'yan mata, musamman masu sauraren waƙoƙin hip-hop.
Hatta wasu manyan da ƙananan yara suna sonta.
Waɗannan mawaƙa dai tauraruwarsu na hasakawa a ɓangaren waƙoƙin hip-hop.
Sai dai shi DJ Abba ya ɗauki shekaru yana jan zarensa, domin ya yi waƙoƙi da suka yi suna a baya irin su 'Su Baaba Ne', 'Kumatu', 'Kowa Ya Ɓace Don Babar Sa', 'Totally', 'Babban Yaya' da sauran su.

10. 'Tsaya' - LILIN BABA da UMAR M. SHAREEF:










Waka ta 10 a 2019 'Tsaya'

'Tsaya' waƙar haɗaka ce da fitattun mawaƙa su ka rera.
Ta bambanta da wasu waƙoƙin da Lilin Baba ke yi, duk da cewa ita ma samfurin ta hip-hop ce, sai dai saka Umar M. Shareef cikinta ya ƙara mata karsashi domin sun yi amfani da kalamai na soyayya.
Duk yarinyar da ta saurari kalaman mawaƙan za ta ji kamar da ita ake yi, domin kalamai ne masu ratsa zuciya.
Mawaƙan sun yi bidiyon waƙar ne da fitacciyar jaruma Rahama Sadau, inda aka nuno su a cikin kantin sayar da kayayyaki, sun yi ƙoƙarin yi mata magana a dalilin karin waƙar kenan 'Tsaya'.
Bidiyon waƙar ya yi kyau sosai.
Har sai da ta kai waƙar ta zama abar maimaitawa a shirin "Top 10" wanda mawaƙi Nomiis Gee ke gabatarwa a tashar talabijin ta Arewa 24.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





Source: BBC HAUSA