Showing posts sorted by date for query Fati Niger. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query Fati Niger. Sort by relevance Show all posts

Monday, 7 October 2024

Zan Bar Muku Najeriyarku Na Koma Kasata - Fati Niger

Zan Bar Muku Najeriyarku Na Koma Kasata - Fati Niger

Fati Niger ɗaya ce daga cikin fitattun mawaƙan Kannywood, a ɗaya daga cikin sababbin waƙoƙin ta da ta saki na baya, bayan nan, tana mai nuni da yadda take fama da ƙalubale a zaman ta a Najeriya.


Zan Bar Najeriya Na Koma Ƙasata - Fati Niger

A saboda haka ne take tunatar da masoyan ta da maƙiyanta a fakaice cewa tana da ƙasa, za kuma ta je can amma za ta dawo.


Waƙar mai taken "Fati Fatima Fatiti.".


Ga kaɗan daga cikin wasu baitocin da ke bayyana irin halin da take ciki;


Ba ku zamtowa daidai da ni.


Maƙiyana dole ku bar mini.


Lokacin Allah ke yi da ni.


Ciwuka ba sa rasa magani.


Na riga ni nai nisa tuni, don ko sunana ya kai gurin da ni ma ban je ba.


Sanannen mawaƙin nan na Kannywood Ado Gwanja shi ne ya yi mata amshin waƙar, amshin da ke nuni da yadda yake lallashin ta kan yanayin da ta kasance a ciki.

Saturday, 7 September 2024

Waƙar Mai Kishina A Rubuce Ta Sadiq Saleh

Waƙar Mai Kishina A Rubuce Ta Sadiq Saleh

Hayye kun ga ina jin daɗi.


Ina jin daɗi.


Na samu muradin raina.


Tana kishina ni dai.


Kun ga ina jin daɗi.


Ina jin daɗi.


Na samu muradin raina yana kishina ni ma.


Mai Kishina A Rubuce
Hoto: Sadiq Saleh Official

Son ki ya fatattake ni har na durƙusa.


Shi ya addabe ni har ya sa ni fallasa.


Ni da ke mu raini so ta kai mu ƙyanƙyasa.


Na yi binciken kamar ki babu na rasa.


Zaɓina.


Mai kishina.


Mai kishina! Kai ne!!


Wayyo zaɓina.


Me kishina.


Me kishina! Ke ce !!


Ɗan rakiya nasaba duk ka haɗa.


Kan ka zo mini nai maka shimfiɗa.


Kwalliya zan maka har nai rangwaɗa.


A kanka ne jama'a ke gane ina faɗa.


Ke ce sila.


Samun canjin kala.


Sai hamdala gun Allah maƙaƙina.


Yau nai bara.


So kuma nai nasara.


Ba na jira gun yaba mai so da ƙaunana.


Oo idan na yaba ki.


Suka ce nai zaƙin baki.


'Yar gata ce ke fitar ki ana kakaki.


Zan hidimta ƙaunar ki.


Ko za a kiran bawan ki.


Wayyo zo ki ceci bawan nan wanda ya zautu kanki ni ne nan.


Ƙauna ta shige ni kar ka ce mini za ka bar ni.


Nai nisa ba a ganina ko an haura tsani.


Yadda na so ka so ni ko gida ma nai bayani.


Ba ni da wani buri in gida har sun ka bar ni.


Kai ku taho ku gan ta ita ce zaɓina.


Ga zaɓina.


Mai kishina.


Ga zaɓina.


Mai kishina!! Kai ne!!


Sadiq Saleh ne ya rera wannan waƙar tare da Fati Niger, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi  ku. Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce.

Saturday, 26 September 2020

Sauke Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Ft Umar M Sharif - Arewa Mu Farka

Sauke Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Ft Umar M Sharif - Arewa Mu Farka

Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.


Arewa Mu Farka

Gamayyar mawaƙan fina-finan Hausa ne su fito su rera wannan waƙar domin ƙara tunatar da al'umma halin da ƙasar Nijeriya take ciki a halin yanzu, kana kuma a ƙara tunatar da al'ummar Nijeriya musamman yankin arewacin hanyoyin da za abi domin daƙile yaɗuwar fyaɗe da sauran ayyukan ta'addanci wanda su addabi yankunan ƙasar baki ɗaya musamman arewacin Najeriya.

Taken waƙar "INA ZAMU JE! INA ZAMU KWANA! MU TASHI MU FARKA 'YAN AREWA".

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Kaɗan daga cikin mawaƙan da suka bayar da muryoyinsu domin isar da wannan saƙon ga dubban al'ummar Hausawa dake cikin ƙasar Nijeriya dama Duniya baki ɗaya:

Ali Jita
Adam A. Zango
Adamu Nagudu
Ado Gwanja
El-Mu'az Birniwa
Fati Niger
Fresh Emir
Dan Musa Gombe
Hamisu Breaker
Hussaini Danko
Ibrahim Ibrahim
Nazifi Asnanic
Naziru M. Ahmad
Sadik Zazzabi
Umar M. Sharif

Waƙar ta hau kan  tsari bisa tsarin mawaƙan waɗanda su baje kolin basira da hikimar su a cikin waƙar.

Mawaƙan sun yi kira sosai ga shugabanni, kana sun taɓa fanni daban-daban wanda 'yan arewa suke ciki a gwamnatin ƙasar amma babu abinda muƙaman nasu suke tsinanawa al'ummar ƙasar musamman matasa waɗanda sune mafiya yawan al'ummar ƙasar Nijeriya.

Wato tsayawa bayyana abinda wannan sabuwar waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Thursday, 11 June 2020

Zazzafan Sabon Video Wakar Mawakan Sakamakon Chanji Ft Fati Niger | Full HD VIDEO

Zazzafan Sabon Video Wakar Mawakan Sakamakon Chanji Ft Fati Niger | Full HD VIDEO

Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Faɗakarwa.


Fati Niger Ft Tijjani Gandu

An rera wannan waƙar ne domin tunatar da al'umma cewa "Covid-19 Gaskiya Ce". Abinda ya rage mana mu bi matakan kare kai.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi kallo lafiya cikin Nishaɗi da Walwala.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng

Wednesday, 8 April 2020

Sauke Wakar Alan Waka - Buri Uku A Duniya

Sauke Wakar Alan Waka - Buri Uku A Duniya

Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Soyayya.

Buri Uku A Duniya

Aminuddeen Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan Waka, ɗaya ne daga cikin fitattun mawaƙan masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood) ya daɗe yana nishaɗantar da al'ummar Hausawa dake arewacin ƙasar Nijeriya (Nigeria) dama sauran sassan duniya baki ɗaya.

Taken waƙar "SARKAKIYA GUDA UKU TAI SANSANI A ZUCIYA BURI UKU A DUNIYA".

Alan Waka ya saki zazzafar waƙar soyayya , wanda acikin waƙar yake bayyana wasu mafarkansa (Buri) na rayuwa. Fitacciyar mawaƙiya Fati Niger ce ta taimaka masa wajen isar da wannan saƙo ga dubban al'ummomi.

Idan baku manta ba a baya an shirya wani fim mai suna BURI UKU A DUNIYA kamar dai yadda sunan waƙar yake haka ma sunan shirin yake.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

Zaku iya sauke sababbin wakokin Alan Waka harma da tsofaffin wakokin Alan Waka  a kyauta idan ku shiga link ɗin dake ƙasa.

SABABBIN WAKOKIN ALAN WAKA

Idan kana ko kina buƙatar sanin irin gwagwarmayar da mawaƙin ya fuskanta a rayuwar sa kafin ya kai wannan matsayin da yake Kai a yau.

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN AMINU ALAN WAKA

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za'ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Saturday, 3 February 2018

KARANTA KAJI: Lallai Ummi Zee-zee Tanayin Abinda taga dama ko Kasan babban Abinda ta Aikata???

KARANTA KAJI: Lallai Ummi Zee-zee Tanayin Abinda taga dama ko Kasan babban Abinda ta Aikata???

Ummi Ibrahim, wadda aka fi sani da Zee-Zee, wadda a yanzu idan aka kira ta da biloniya babu wata matsala, idan aka yi la’akari da irin manyan motoci da yanayin yadda take rayuwa mai dan karen tsada a yanzu.


Babu shakka za a iya cewa ta kere wa sa’anninta da dama da suka shiga harkar fim tare a ba
Bayan tsohuwar jarumar wadda ‘yar kabilar Shuwa ce daga jihar Borno, ta dan fito a finanan Hausa da kuma matsalar da ta samu da saurayin da ya yi niyyar aurenta, wato Dan Chana, sai ta yi bulaguro zuwa jihar Lagos, inda ta koma can da zama.
Bayan ta koma jihar Lagos da zama ne, Ummi Zee-zee ta soma soyayya da fitaccen mawakin Turancin nan, wato Timaya, inda har ta bayyana cewa tana da burin aurensa idan har ya amince zai Musulunta, amma daga baya sun rabu. Soyayyar Timaya da tsohuwar jarumar finafinan Hausan, ya yi matukar daukar hankalin jama’a musamman na yankin Arewa kasancewar a matsayinta na Musulma tana soyayya da wanda ba addininsu daya ba, amma daga baya sai ta fito ta wanke kanta da zimmar cewa za ta aure shi ne idan har ya amince zai musulunta.
Sai dai daga bisani bayan an rasa ina soyayyar Zee-zee da Timaya ta kwana, kwatsam sai labari ya soma yaduwa na cewa tuni jarumar suka raba gari da mawakin. Wanda kuma bincike ya nuna cewa tun daga wannan lokacin ta yi bulaguro daga jihar Lagos ta dawo yankin Arewa, inda ta koma jihar Kaduna, inda take zama a kawataccen gida, sannan duk inda za ta tare da masu tsaron lafiyarta take zuwa.
A yayin da al’umma suka soma mancewa da batun Zee-zee, kwatsam sai fitacciyar Mujallar nan ta Fim da jaridar Turanci ta Blueprint suka yi hira da ita, inda a hirar ta ce akwai soyayya mai karfi tsakaninta da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, kuma tana sa ran za su yi aure nan ba da jimawa ba.
Idan ba a manta ba, a farkon shekarar da ta gabata, wani na kusa da jarumar, ya fadawa majiyarmu cewa Ummi Zee-zee ta sha fiya-fiya don ta kashe kanta, sakamakon matsalar da ta samu da janar Babangidan, wanda har ta kai ga janar din ya kashe duk wasu lambobin wayoyinsa da ya sa jarumar za ta same shi, kuma ya hana ta mu’amala da duk wasu kadarorinsa da ke jihohin Kano, Kaduna, Niger har ma da na kasashen waje.
Kasancewar Zee-zee tana bukatar janar Babangidan ya san irin halin da ta shiga sakamakon matsalar da suka samu, sai ta bayyana a jaridar Blueprint kan yadda ta yi kokarin halaka kanta ta hanyar shan fiya-fiya, inda bayan an buga labarin wani na kusa da ita, ya kira majiyarmu yake cewa Janar din ya kira ta, kuma har ya tura tawaga zuwa Kano domin duba lafiyarta, ko da bukatar a haura da ita kasar waje domin duba lafiyarta.
Majiyarmu ta ci gaba da cewa tun daga wannan lokaci, a duk sanda aka nemi Zee-zee aka rasa, idan aka tambayi makusantan jarumar, sukan bayyana cewa walau ta wakilci Janar din a wurin taro a fadin kasar nan, ko kuma ta wakilce shi a harkokin kasuwancin da yake gudanarwa a kasashen waje.
Majiyarmu ta kuma kara da cewa, akasarin kwafen jaridun da ake hira da jarumar janar Babangidan yana da su, kamar yadda wani na kusa da tsohon shugaban kasan ya bayyana, inda ya kara da cewa ya sha ganin kwafen jaridar Blueprint mai dauke da hirar Ummi Zee-zee a gidan Janar din.
Sannan kuma duk inda tsohuwar jarumar finafinan Hausa za ta, za ka ganta ta ne a kawatattun motoci tare da masu kare lafiyarta, wanda hakan na nuna cewa akwai alaka tsakaninta da tsohon shugaban kasa.
Wani abun dubawa game da lamarin alakar da ke tsakanin jarumar da Janar din, shine babu wasu daga cikin iyalan Janar din da suka kalubalanci lamarin. Sannan kuma soyayyar dake tsakanin Zee-zee da Janar din ya samo asalin ne tun lokacin da take karama, inda take nuna farin cikinta a duk lokacin da aka nuno sa a talabijin. Haka kuma ta samu ganawa da Janar din ne ta hanyar mahaifinta, tun mai dakinsa marigayiya Maryam Babangida tana raye.
Wanda tun daga wannan lokacin ne ta shaku da IBB din. Kuma ta ce tun kafin su yi ido hudu da Janar din ya soma yi mata goma ta arziki.
Jarumar wadda yanzu haka ta koma kasar Dubai da zama bayan ta sayi gida a can a makon da ya gabata, (sai dai ta shigo Nijeriya na dan wani lokaci ta koma), tana gudanar da kasuwanci, inda take amfani da lakabin Zee-zee a wuraren kasuwancin nata.
A kwannan ma wani kamfanin shirya finafinan Hausa, ya yi amfani da motocinta masu dauke da sunan Zee-zee, inda aka yi amfani da su a fim din mai makamncin wannan suna, wanda Fati Washa ta fito a matsayin jarumar fim din.
Game da ko me ya sa ba a ganin fuskarta a matsayin jakadiyar kamfanonin sadarwa irin su Glo, MTN, ZAIN da Etisalat? Ummi ta ce IBB ya fada mata cewa za ta iya samun sama da naira milyan dari idan har tana bukatar yi wa kamfanin Glo talla, amma a ganinta wannan kudin bai taka kara ya karya ba da har za ta yi tallar ba. Sannan kuma a bangaren shirin fim kuma, ta fadi cewa tana da tabbacin cewa ta wuce matsayin ta yi fim don kudi a yanzu, domin babu furodusan da yake da kudin da zai dauke ta domin sanya ta a fim, sai dai ta taimakawa harkar domin a samu ci gaba.
Sannan ta kuma baiwa masoyanta hakurin daina fuskarta a fim da suka yi, amma kuma za ta dinga amfani da kafafen yada labarai domin su san halin da take ciki. Haka kuma jarumar ta yi ikrarin cewa wasu daga cikin gwamnoni a kasar nan suna ba ta kwangiloli.
Game da batun aurenta da Janar din kuma, ta ce har yanzu maganar na nan, kuma a duk lokacin da labarin ya auren ya bayyana zai dau hankalin al’umma.
Ta kuma ce masu ganin cewa Janar din ba zai aure ta ba, su jira su gani. Sannan kuma a jwabinta na karshe, Ummi ta nuna jimaminta game da rashin lafiyar da tsohon shugaba kasan ya dan yi fama da shi, wanda har ta kai ga an garzaya da shi kasar waje domin duba lafiyarsa, inda ta ce kamar ta mutu.
Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba
Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
ALLAH yabar Zumunci Amin
Source By ©Rariya and Sadikblog