Showing posts sorted by date for query Nura Nakowa. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query Nura Nakowa. Sort by relevance Show all posts

Saturday, 30 November 2024

Soyayya Mai Tashi Lokaci Zuwa Lokaci

Soyayya Mai Tashi Lokaci Zuwa Lokaci

Za ka samu wasu masoyan suna gudanar da soyayyar kamar tashin kumfar omo. Kumfa ba a ganinsa sai an haɗa shi, kuma da zarar an haɗa shi yake tashi ya yi sama yana sheƙi da ƙyalƙyali. Bayan wani ɗan lokaci kuma sai ka ga yana yin ƙasa-ƙasa da kansa ba tare da ana so ba sai dai idan wani lokacin amfanin ya taso sai a kuma haɗa wani.


Soyayya Mai Tashi Lokaci Zuwa Lokaci
Hoto: Vocal

MarubuciNura Nakowa


To haka rayuwar wasu masoyan take, haka za ka ga suna gudanar da soyayyar su lokaci zuwa lokaci. Allurar soyayyar su ba ta tashi sai sun ga juna. Idan kuma suka rabu sai a ɗauki tsawon lokaci ba a haɗu ba, kuma fa kar ka ce suna raya soyayyar ta wata hanyar ta daban ce a'a, kawai dai sun tafi kenan tamkar ɗaukewar wutar NEPA sai wani jiƙon idan an sake haɗuwa.


A duk lokacin da suka haɗu za su yi ta cin soyayyar su kamar babu kamar su a duniyar so.


Irin wannan soyayyar ba wai sai da akwai matsala a tsakanin masoyan ake samun haka ba. Wata ƙila wani dalili ne na ƙashin kai, ko sabgogi ko kuma zarafin rayuwa, su suke sanyawa ake samun hakan. Wani sa'ilin kuma rashin maida hankali ne ga wanda ake soyayyar da shi da kuma rashin shiri, wato an shiga soyayya ba tare da an shirya yin aure ba ko kuma ba a da lokacin da za a tsaya a gina soyayyar yadda ya kamata.


To babban abin da ke janyo irin haka shi ne:-


1. Rashin tsayayyan masoyi ko manemi.


2. Rashin tsayar da maganar aure a tsakanin masoyan.


3. Rashin kulawar iyaye na idan za a yi, a yi. Idan kuma ba za a yi ba a san matsayin da ake kai.


Wasu masoyan irin waɗannan kuma suna matuƙar son junansu kuma ba sa kula wasu amma kuma za ka ga ana samun irin wannan soyayyar ta tashin kumfar omo. 


Abin da ke faruwa shi ne, za ka ga wata ƙila da akwai wasu 'yan rigingimu ko wasu matsaloli na gida waɗanda ya kamata a ce an kawar da su (kamar son a haɗa auren dangi ko auren zumunta ko kwaɗayi ko buri) to amma matsalolin ba su kau ba sai ka ga masoya sun daɗe a cikin irin wannan halin.


Akwai waɗanda na sani shekaru biyar zuwa shida su ka yi a cikin irin wannan yanayin.


To abin da ya fi shi ne, idan an shiga so to a kula da shi domin so ba abin wasa ba ne.

Thursday, 8 August 2024

Alakar Soyayya Da Kyau Ko Muni

Alakar Soyayya Da Kyau Ko Muni

Shi dai so haka yake ba a iya masa, babu ruwansa da kyau domin kyau yana gushewa, haka kuma babu ruwansa da muni domin ba shi ne abin da wani yake dubawa ba.


Alaƙar So da Kyau
Hoto: 4kwallpapers


MarubuciNura Nakowa


Kowa da abin da yake kallo a matsayin so.


So ya kan yi abin da ya ga dama. Ya kan haɗa kyau da kyau ko muni da muni ko kuma ya haɗa kyau da muni ko muni da kyau.


Haka za ka ga wasu tamkar ba su dace da juna ba ta ɓangarori da dama, amma shi so babu ruwansa, kai kake ganin hakan.

Tuesday, 11 June 2024

Shin Da gaske Ne Babu Sauran Soyayya Ga 'Yan Kauye Ko 'Yan Karkara?

Shin Da gaske Ne Babu Sauran Soyayya Ga 'Yan Kauye Ko 'Yan Karkara?

Da yawa daga cikin mutane a yanzu gani suke kamar babu cikakkiyar kulawa da tarbiyya a ƙauye don haka suke gani kamar ma ba za su iya aurar 'yar karkara ba.


Soyayya a ƙauye
Hoto: Zaheer Shakeel


MarubuciNura Nakowa


Da na yi Hira da wasu sun bada misali da yaran nan 'yammata waɗanda suke shigowa cikin birane talla, Wai ba za ka taɓa ganinsu suna sallah ba, ba su da nutsuwa, ba  su da kunya, idan suna magana ma ba sa girmama mutane.


Waɗansu kuma suka ce min waɗanda kake ganin suna fitowa tallace-tallacen nan tun dama haka suke ba masu mutunci ba ne, masu mutuncin suna nan dabam, sannan kuma waɗannan talauci da jahilci ya yi musu katutu shi yasa koda sun shigo gari talla ba sa kulawa da addinin su.


Wasu kuma sun zarge su da cewa lalatattu ne su don babu abin da ba sa yi saboda kuɗi, yayin da wasu kuma suka ce ai 'yan birnin ne suke lalata su amma kuma ba za su iya auren su ba.


TO WAI YAYA ABIN YAKE NE?


Shin, a Ina gizo yake saƙar ne? Shin waɗannan hujjojin sun ishi mutum ya ce ba zai auri 'yar ƙauye ba, ko kuma da akwai wasu dalilan?


Me za ka ce akan wannan batun..?


Idan ka na jin daɗin kasancewa da ni, to ka ba wa wasu labarin wannan shafin.

Monday, 25 March 2024

Matsalar Naci Ko Izza Ko Ƙarfin Iko Ko Takurawa Ko Tilastawa A Soyayya

Matsalar Naci Ko Izza Ko Ƙarfin Iko Ko Takurawa Ko Tilastawa A Soyayya

Abin da ake nufi da naci dai shi ne nuna ƙwazo da jajircewar mutum a wajan nema da kuma son ya mallaki abin da yake so.


 MATSALAR NACI KO TILAS A YAYIN NEMAN SOYAYYA
Hoto: Etc


MarubuciNura Nakowa


Za ka iya yin naci akan abubuwa da dama kama a harkar kasuwanci ko aiki da wasu ɓangarorin na neman abin duniya. A irin wannan nacin kakan iya jure samu da rashi ba tare da yanayi ba, kuma koda ka shiga wani hali za ka iya samun tallafi ko sassauci daga wasu wuraren.


Shi kuma Naci A Soyayya ba kamar kowanne irin naci ba ne.


Naci a Soyayya tamkar tilastawa ne. Shi kuma so ba a tilas. Abu ne na yarda da aminci da nutsuwa.


Za ka iya neman soyayyar mutum idan ka yi sa'a a cikin ɗan kankanin lokaci a karɓi soyayyar ka. Wani lokacin kuma sai an ɗan ja lokaci kafin a amshi buƙatar ka. Jinkirin da aka samu kuma ba yana nufin ba a son ka daga farko ba ne sai daga baya aka so ka, a'a, yanayi ne yazo da hakan. Hakanan kuma idan aka yi saurin karɓar soyayyar ka, shi ma ba yana nufin an fi sonka ba ne, yanayin ne dai ya zo da haka.


Da akwai mutanen da idan suka ƙyallara idanu suka hango wanda suke so (musammam maza akan mata) sai sun nace akan sai sun yi soyayya da ita.


Kuskure na farko da suke yi shi ne, ba za su tsaya su yi tunanin, shin, za ta so su ko ba za ta so su ba, kawai su buƙatar su na sai sun yi soyayya da ita shi ne a gaba.


Za ka ga saurayi ya kula budurwa da zummar yana son ta domin ita ma ta so shi amma ta ce da shi a'a ko kuma ta nuna masa alamar cewa ba ta yi ko ba ta da ra'ayin yin soyayya da shi, amma kuma a maimakon ya haƙura ya godewa Allah da ya sauƙaƙa masa wahala, ba tare da an wahalar da shi ba aka nuna masa cewa fa wannan buƙatar da ya zo da ita ba za ta karɓu ba. Sai ka ga ya kasa fahimtar hakan.


A haka zai yi ta ƙoƙarin sai ya burgeta ta kowacce siga domin ya sace zuciyar ta, amma kuma ba zai yi nasara ba saboda ba ta son sa kuma tun da farko ta nuna masa haka.


Wasu sukan janye da wuri idan suka fahimci cewa hanyar ba mai ɓullewa ba ce ko kuma su janye don sun ga an fara musu gashin-ƙuma.


Wasu kuma ba za su haƙura ba, hasali ma, cewa za su yi ko ta halin-ƙaƙa sai an so su. Da haka sai ka ga an fake da bin malamai da bokaye domin a tilastawa zuciyar wadda suke so ba ta son su ta dawo tana son su.


Wasu kuma ba za su kai ga bin bokaye ko malamai ba, amma za su zafafa wajan iyaye da 'yan uwa ko dangin wadda suke so don a shawo kanta domin ta yarda a so ta ko a aureta. Ko kuma ma ka ga idan me dukiya ne, zai kashe ko miliyan nawa ne domin a ba shi aurenta.


To shi irin wannan soyayyar me za a kira shi kenan?


Ko da yake bai cancanci a kira shi da soyayya ba tunda an yi amfani da ƙarfin iko da isa wajan tilastawa zuciya karɓar abin da ba ta so.


Duk wanda ya jefa kansa cikin irin wannan chakwakiyar soyayyar, to, ya yi kuka da kansa.


A soyayya ana buƙatar amincewar zukata biyu, watau mutum biyu, waɗanda suka yarda cewar za su shiga cikin rayuwar junarsu. Idan aka samu akasin haka, to tabbas, za a zalunci ɗaya daga cikin su.


So ba a samun sa da ƙarfi ko izza, dole sai da lallama. Duk abin da ake so neman shi ake yi ba ƙwato shi ake yi ba. Shi kuma nema sai da hikima da dabara ake cin ribar sa.


Alhamdu lillah. Idan ka ji dadi to ka sanar da wasu.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun LitininLaraba, da Juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

Tuesday, 16 May 2023

Hanyoyin Faranta Wa Masoyiya Cikin Sauki

Hanyoyin Faranta Wa Masoyiya Cikin Sauki

So mai abubuwa daban-daban. Mutuncin da ke tsakaninka da shi kawai kulawa.


Farantawa Masoyiya
Hoto: Wallpaper Safari


MarubuciNura Nakowa


Idan aka rasa kuka a tsakanin masoya, to so da kansa yake yin abin da ya ga dama. 


Idan ya ga dama ya cutar da mutum ɗaya, idan kuma ya ga dama ya cutar da su duka.


Rashin kulawa yana rage shaƙuwar da ke tsakanin masoya biyu. Yana sa su fara yin nesa da juna ta sigogi daban-daban.


Idan aka fara yin nesa da juna sai tsana ta fara shigowa a tsakani.

Ba kuma sai tsanar ta haddasa gaba ko tashin hankali ba a'a, kawai dai soyayyar ce za ta fara yin sanyi sai ka ga an soma yin baya-baya da juna, ko a koma kamar abokai amma ba aminai ba ko kuma a zama kamar dai irin an san juna ne amma ba lallai sai an shaƙu da juna ba, sai a rinƙa gaisawa daga nesa wanda idan aka ci-gaba a haka wata rana sai ka ga an rabu.


Kulawa na daga cikin abin da ke ƙarfafa wa masoya ƙwarin gwiwa.


Kulawa na da bambanci da hidima. Kada don kana taƙamar kana bada wani abu ko kuma kakan yi sayayya ka kawo ko ka aiko ya zama shi ne dalilin da zai sa a yi maka irin son da kake da muradi.


Sakin fuska, yin murmusi da dariya suna daga cikin hanyoyin faranta ran masoyiya.


Hira da bada labari me daɗi yana ciki.


Ziyara da Kira a waya da tura saƙonni da kuma maida martanin saƙo idan an yi maka shi ma abu ne me kyau a soyayya.


Tsokana, barkwanci  suna ƙara sanyawa a samu sakewa a tsakanin masoya.


Kada ka bari ka ce wai sai an yi maka sannan za ka yi, soyayya takansa a yi 'yar rige.


Ya Allah ka ba mu ikon farantawa masoyan mu sannan kuma su ma ka ba su ikon faranta mana. Amin.

Wednesday, 25 January 2023

Dadin Da Ke Cikin Soyayya Tare Da Rahamar Da Ke Cikin Alakar Masoya

Dadin Da Ke Cikin Soyayya Tare Da Rahamar Da Ke Cikin Alakar Masoya

Duk da cewar lamarin so nada ban al'ajabi ba za a fasa cewa so da daɗi ba.


Shi kansa kalmar so daɗi gareshi don haka ne ma ba a furta shi wajan da babu shi.


Kafin a furta shi sai an tabbatar da an ji shi.


Ba a jin shi har sai an gan shi.


Daɗin Soyayya
Hoto: Wallpaper House


MarubuciNura Nakowa


Idan aka ganshi sai zuciya ta karɓe shi. Idan kuma zuciya ta karɓe shi sai rai ya yi daɗi. (Wato ba a furta so ga wanda ba a ji son shi ba kuma zuciya ba ta yi na'am da shi ba).


A duk lokacin da mutum ya ga wadda ya so ko wadda yake so koda ba su fara soyayya ba sai ya ji daɗi a ransa. Abin da ake ji rai na farin ciki shi ne daɗin so. 


Idan kuma aka fara soyayya ana ganin juna kuma ana samun musayar kalamai masu daɗi da sanyaya zuciya sai ka ga masoya suna shiga cikin walwala.


Idan rai ya san cewa ya samu wanda yake sonsa. To, wannan kaɗai ya ishi mutum jin daɗin rayuwar duniya.


Samun nutsuwa a tsakanin masoya yana sa su manta da damuwarsu.


A duk lokacin da za a yi maka magana za a yi maka me daɗi, ba za a yi maka magana da hararramu ba. Ba za a nuna maka izza da isa ba. Ba za ayi maka gatsali ko shaguɓe ba, a'a, magana za dinga yi maka a cikin hikima da nutsuwa domin kada ka ji wani abu a ranka.


Hakanan kuma duk lokacin da ake hira da kai a cikin hikima da dabara za a dinga furta maka abin da zai ƙarawa soyayyar ku armashi.


A ko da wani lokaci ana haba-haba da kai.


Ba a so ranka ya ɓaci.


Ba a so a daina jinka.


Ba aso a ji ka ce yau ba zan zo ba.


Komai ka buƙata ba za a so a ce maka babu ba, duk yadda za ayi sai an taɓuka wani abu. Burin zuciya shi ne kawai a faranta maka.


Za a yi maka hidima ba tare da ka nema ba. Za a yi maka tanadi kafin ka zo. Za a ba ka ba tare da an buƙaci naka ba. Kana da shi ko ba ka da shi ba a damu ba kawai dai soyayyar ka ake da buƙata.


Duk wani abu naka shi ake son a ji ko a gani. An damu da kai fiye da yadda ka damu da kanka.


Lafiyar ka da hulɗar ka da jama'a da mu'amalar ka ta yau da kullum, duk suna ran masoyinka. Kai, wani abin ma sai dai ayi shiru kurum.


Tabbas so da daɗi. Akasi ne yake sa a ji babu daɗi.


Masu soyayyar gaskiya suna jin daɗi.


Ya Allah ka farantawa masoya masu soyayya don Allah.


Alhamdu lillah.


Domin kyautata soyayyar ka da zamantakewar aure da kuma sanin haƙiƙanin mene ne ainihin so da abin da yake assasa so a cikin jikin Ɗan Adam, ka nemi littattafai na 'Sinadarin So' da 'Mene Ne Soyayya'.


Za ka same su a shagon 'Abin Yabo Book Shop' kasuwar kurmi, 'yan littafi, rijiyar 'yan goro.


Ko ka kira Abu Huraira akan wannan lambar 08036527328.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun LitininLaraba, da Juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

Friday, 13 January 2023

Matsalolin Soyayya 12 Ga Masoya

Matsalolin Soyayya 12 Ga Masoya

Shi dai so abu ne me daɗi wanda kowa yake so, to amma a cikinsa da akwai wahalhalu kala-kala waɗanda kowa da irin wanda ya taɓa fuskanta.

BABBAR WAHALAR DA KE CIKIN SOYAYYA
Hoto: Wallpaper House

MarubuciNura Nakowa

Wani bai taɓa shan wahalar soyayya ba, wani ya sha ɗan kaɗan, wani kuma gabaki ɗaya soyayyar sa a wahale take.

Idan aka ce wahalar da ke cikin soyayya wasu za su yi tunanin cewa rashin dace a soyayya ko ka nema ka rasa shi ne kaɗai wahalar soyayya. Ba haka ba ne. Daɗi da ɗacin da ke cikin soyayya kowannen su yana ɗauke da nasa irin nau'in wahalar.

Bari mu fara da ɓangaren daɗin:

Daɗin dake cikin soyayya shi ne Farantawa, Kyautatawa, da Kulawa.

To a yayin gabatar da waɗannan abubuwan guda uku dole sai da ujula. Kowanne daga cikin su (farantawar da kyautatawar da kulawar) a aikace ake yinsa.

Dukkanin su suna buƙatar lokaci da yanayi da kuma Ihisani. Sai ka samu lokacin da za ka dinga zuwa yin hirar da za ta farantawa masoyiyar. Haka ma ita macan. Hakanan kuma a soyayyar ku kakan yi alkhairi da yin kyauta, kamar sayawa masoyin ka abin da zai ci ko ya sha ko abin da zai saka a jikinsa domin ya yi kwalliya irin su sutura da kayan ƙyaleƙyale.

Waɗannan aikace-aikacan da zirga-zirga da baye-bayen da kakeyi, su ma wahalhalu ne a cikin soyayya amma ba a lissafa su a matsayin wahalar da ke cikin soyayya saboda su suna taimakawa ɗorewar soyayyar ne.

Da za ka tsaya ka yi lissafin lokacin da ka ɓata ba dare ba rana kana zuwa hira, da dukiyar da ka kashe a dalilin zuwa hirar, to za ka san cewa ba ƙaramin aiki ka yi ba. Kuma kai ka san cewa idan ba a dalilin so ba, babu wanda ya isa yasa ka yin wannan hidimar.

To wannan kenan;

Idan kuma za mu duba ɗayan ɓangaren na Ɗacin So a matsayin wahalar dake cikin soyayya, za ka ga cewa rashin dacewa da samun wanda zai so ka shi ne kan gaba a wannan matakin domin shi ne zai sa ka rinƙa shiga cikin ragowar matakan tsanani da ƙuncin da za ka iya tsintar kanka a ciki.

A sanadiyyar soyayya wani/wata ya shiga cikin ruɗanin da bai ma san ana sonsa ko ba a sonsa ba.

1. Wani ya san ba a sonsa amma yana sa rai da cewar wataran za a so shi. Kuma haka za a yi ta tafiya har a rabu ba tare da an so shin ba.

2. Wani ya kashe dukiya me tarin yawa amma ko sau ɗaya bai taɓa cin ribar abin da ya kashe ba saboda ba a karɓi soyayyar sa ba.

3. Wani kuma rayuwar soyayyar sa mujadala aka dinga yi saboda wadda yake so tanada manema dayawa. Ko da kuwa zai yi fintinkau a ƙarshe, shi kansa yasan babu sauƙi.

4. Wani yana ji yana gani za a bada wadda yake so ga wani amma babu yadda zai yi.

5. Wani yana so ana son shi amma kuma iyayensa ko iyayenta su ce ba za ayi auren ba. Haka zai yi ta fama amma ba za a yi auren ba. Kuma koda kuwa anyi auren, to fa babu kwanciyar hankali.

6. Wani kuma ƙarancin shekaru ko ƙarancin lokaci ko rashin ko rashin sana'a ko aikin yi ne yake jefa shi cikin shan wuya a soyayya, yayin da wani kuma an rena arzikinsa ne ko asalin sa shi yake haifar masa da wahalhalun soyayyar sa.

Da akwai kuma waɗanda wahalar tasu ta zarce na waɗannan.

7. Wani ya ci dukan tsiya akan Soyayya.

8. Wani an ɗaure shi.

9. Wani an yi masa sharri iri iri.

10. Wani an yi masa barazana da lafiyar sa da rayuwar sa.

11. Wani ma ya rasa rayuwar sa akan soyayya.

12. Kai, na ga wanda aka ɗaure shi tsawon watanni sai bayan an yi auren yarinyar da yake so sannan aka sako shi, amma a cikin ikon Allah sai da ta zama matarsa bayan ta yi auren ta fito da 'ya'ya biyu.

Alhamdu lillah.

Kaɗan kenan daga cikin abin da na za ƙulo na irin wahalhalun da ke cikin soyayya.

A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun LitininLaraba, da Juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

Friday, 9 December 2022

Shin Ko Kun San Muhimmancin Bayar da Kyautar Fure A Soyayya?

Shin Ko Kun San Muhimmancin Bayar da Kyautar Fure A Soyayya?

Barkanmu da Juma'a. Da fatan masoya suna tsinkar fure cikin ƙoshin lafiya. Shin ko ka san cewa 'fure' tambari ne daga cikin tamburan masoya?


Muhimmancin Furen Soyayya
Hoto: About Islam


MarubuciNura Nakowa


A zamanin da, ana bada kyautar fure ga masoyi domin nuna masa matsayin darajar sa a gurin masoyin sa.


A kan samu mazubi ko maɗauri domin alkinta furen da za a kai wa masoyi.


A kan tura ɗan aike ya kai ko kuma mutum ya kai da kansa. Ya danganta da manufar abin da masoyi yake so ya bayyana wa masoyinsa.


A yadda tsarin yake tun a baya, mata su aka fi ba wa furanni don a burgesu.


Abin ya samo asali ne daga nahiyar turai har ya yaɗu zuwa sauran nahiyoyi daban-daban wanda a yanzu kusan kowacce nahiya da dauloli wannan al'adar ta shiga. Kusan dukkanin fitattun ƙabilu na duniya suna kwatanta wannan al'adar ta miƙa furanni ga masoya.


Fure ganye ne da ke tsirowa da launi iri-iri masu ban sha'awa, kamar launin fari da ja da kore da rawaya ko ruwan ƙwai da launin shuɗi, wani sa'ilin ma da launin makuba da shanshanbale. Ba ya ga kyawawan launuka da furanni ke ɗauke da su, hakanan kuma wasu daga cikin su suna da ƙamshi me daɗin gaske wanda ke jan hankalin masoya. Sai dai kuma furannin da masoya suka fi amfani da su su ne ja da ja me haske (pink) da kore da ruwan ƙwai.


Dalilan bada furen soyayya suna da yawa;


1. Ana bayarwa domin neman soyayyar mace, wato, a ja hankalin ta don ta fahimci cewar ana son ta.


2. Ana bayarwa domin jaddada so da ƙauna a tsakanin masoya.


3. Ana bayarwa domin tambaya ko neman izinin aure.


Haka kuma ana bayarwa idan masoyi zai yi wani shagali ko biki domin taya shi murna. 


Kamar cin jarrabawa na kammala karatu da murnar zagayowar ranar haihuwa ko yayin da masoyi ya yi kyau a wani guri ko a gasar wasanni da makamantan su.


A wannan yanki namu na ƙasar Hausa abin baida tasiri sosai sai ɗan kaɗan da waɗansu waɗanda ake wa kallon wayayyu ko 'Yan Boko suke yi.


Kowacce ƙabila da irin abin da suke kallo a matsayin tambarin da masoya ke amfani da shi a matsayin alamar soyayyar su.


To tambayar da zan muku ita ce, tun da wannan lamari ya bunƙasa a duniya har zuwa wannan yanki namu.....,


Menene tambarin masoya a ƙasar Hausa?


Shin ka taɓa saya ko tsinkar fure ka kai wa masoyiyar ka ko matar ka?


Shin mijinki ko masoyin ki ya taɓa ba ki kyautar fure?


Sai na ji daga gare ku.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun Litinin, Laraba, da Juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

Friday, 25 November 2022

Hanyar Da So Ya Fi Kama Wasu Mutanen Cikin Sauki

Hanyar Da So Ya Fi Kama Wasu Mutanen Cikin Sauki

Tabbas shi SO tamkar tuntuɓe yake, a kan cikaro da shi wajan da ba a yi zato ba. Abin nufi anan shi ne, wani lokacin ba ka shirya yin Soyayya da kowa ba amma za ka ga ka ci karo da wadda ta zama tilas sai ka kulata.


Yadda So Yake Kama Wasu Mutane
Hoto: Wallpaper Cave


MarubuciNura Nakowa


Misali, za ka iya tsintar kanka a wani guri wanda ba da manufar ka kula wata ka je gurin ba amma hira ko kwatance ko tambaya ya zama sanadin ƙulla alaƙar soyayya tsakanin ka da wata (su ma matan haka ne).


A wani lokacin ma a dalilin wasa ko tsokana ko ɓacin rai yakan zama sanadin soyayya har ma ta kai ga an yi aure.


Ga wasu misalai kamar haka:-


Akwai wani bawan Allah wanda yana daga cikin abokan wani ango waɗanda suka haɗu a wajan walimar aure. Suna zaune a mazaunin su sai ya fuskanci cewa ɗaya daga cikin 'yammatan da suka zauna a kujerun da suke fuskantar nasu ta yi zaman ƙasaita (wato ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya akan guwairta). To sai shi wannan mutumin yake gani kamar ta yi rashin kunya saboda haka bari ya je ya ankarar da ita. To da ya je sai ya je a fusace, yana zuwa sai yasa hanu ya tunkuɗe ƙafar yarinyar kuma ya rufe ta da faɗa. Ita ma da ta ga haka sai ba ta raga masa ba, ta dinga gaggaya masa magana. 


Haka a ka zo aka shiga tsakani aka raba su da ƙyar. 


Amma na katse muku labarin, kasancewar sa abokin ango, ita ma ƙawar amarya sai da sanadi ya sa suka shirya har kuma ya aure ta.


To wannan kenan, karku tambaye ni ko wanene don na san shi ma zai ga wannan saƙon. Hahaha..


Shi kuma wannan ya zo unguwar su abokin karatun sa ne (Ɗan ajin su). Suna tsaye a ƙofar gida sai wata budurwa ta wuce ta gaban su ta shiga cikin gidan, da ta fito sai shi baƙon yake cewa abokinsa ka ga wata kyakkyawar yarinya. Shi ne abokin nasa ya ce masa ai ƙanwata ce idan kana so sai na ba ka ita. Tana waigowa sai ta ce da shi da ya ke haka bayarwar keda sauƙi ba? Shi ne shi baƙon ya ce mata "Ki yi haƙuri, ni da wasa ma nake ina da wacce zan aura.". Sai ta maida martani cewa idan ma da gaske kake kwaji dashi.


To wannan ma kar na kaiku da nisa ashe 'yar maƙotan su ce kuma alaƙar ce silar auren su.


Wannan abu ya faru a ɗaya daga cikin unguwannin ƙofofin Kano.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litininlaraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

Monday, 7 November 2022

Alamomin Gane Soyayyar Gaskiya Da Gaskiya

Alamomin Gane Soyayyar Gaskiya Da Gaskiya

A lokuta da dama wasu masoyan suna tare da masu son su da gaskiya amma ba su sani ba.


Gane Soyayyar Gaskiya
Hoto: HD Wallpapers

MarubuciNura Nakowa


Rashin fahimtar alamomin da za su bayyana soyayyar gaskiya shi yake sa masoya su yi ta bilayi suna taraddadi a soyayyar su.


Ba a ƙulla alakar so da nufin ɓatanci ko baƙanta wa juna sai dai idan ba da manufar alkhairi aka zo ba. To wannan shi ne dalilin da yasa wasu masoyan (maza da mata) suke kokwanton ko wanda suke tare da shi da gaskiya ya zo kokuma akasin haka.


Ba dukkanin soyayya ce ake farawa da manufar aure ba amma kuma daga baya sai a ƙudurci aure kuma a yi auren. Wata soyayyar haka za a soma ta har a gamata ba ayi aure ba. To amma wannan ba yana nufin ba a so juna da gaske bane, a'a, da akwai wasu dalilai masu tarin yawa da suke hana soyayya ta kai ga yin aure.


Da akwai wasu alamomi guda goma sha biyar da na kawo su a cikin littafi na mai suna "Mene Ne Soyayya" waɗanda za su taimaka ƙwarai wajan gane soyayyar gaskiya da kuma irin dacewar da ka yi a soyayyar ka.


Ga kaɗan daga cikin su kamar haka:-


1. Za ka ga kuna samun dama da lokacin kasancewa a tare domin farantawa juna da kuma bayyanawa junanku abin da ke a cikin ran ku.


2. Idan bakwa tare zai zama tamkar kuna a tare ne. Alal misali; idan ba a gida ɗaya kuke ba ko kuma ba kwa kusa da juna kokuma ɗayanku ya yi tafiya zuwa wani garin, to zukatanku suna tare da juna ba sa rabuwa. Kuna kulawa da haƙƙoƙin junan ku tamkar kuna tare. Ba kwa aikata abin da ɗayan ku ba ya so koda kuwa a bayan idanunsa ne. Haka kuma za ka ga kuna kulawa da juna ta hanyar kiran waya da turawa juna saƙonnin soyayya ko kuma na wani sha'anin dabam.


3. Za ka ga saɓanin da ke shigowa tsakaninku ba mai tsanani ba ne, kuma idan aka samu rashin jituwa a tsakaninku cikin hikima da dabara kuke sasantawa.


Ragowar alamomin guda goma sha biyu suna ƙunshe a cikin littafin Mene Ne Soyayya wanda na yi muku bayani a baya. 


Kai dai ka nemi naka a kasuwa domin kada ka tsinci kanka a cikin chakwakiyar soyayyar da ba za ka iya warwarewa ba.


Guraren da za a iya samun littattafai na guda biyu "Sinadarin So" da "Mene Ne Soyayya" sun haɗar da....,


1. Arewa Radio 93.1 da ke lamba 64 a unguwar farm centre kusa da gidan kallo na Marhaba.


2. KASUWAR KURMI:- Abin Yabo Book Shop wajan Abu Huraira - 08036527328.


3. ƘOFAR FAMFO:- Shagon TJ Zarewa mai kayan wuta - 07039582763.


4. ZOO ROAD:- Bayan Hikima Multi Media wajan Salisu Maizare - 08175935495.


5. DAKATA:- Sunusi mai cajin waya bakin kasuwar dakata - 07066016221.


6. RIJIYAR LEMO:- Naziru Messi me kanti rijiyar lemo yammata gabas - 08066546638.


7. NA'IBAWA:- Megga Solution Internet Cafe dake jikin masallacin juma'a na uhud a na'ibawa 'yan lemo.


8. ƊORAYI:- Sutudiyon Habeeb Director dake gidan dakali saman benen gidan buredi - 09036686868.


9. BRIGADE ƘAURA GOJE:- Ras Communication - 08163972880.


A wannan lokacin ana sayar da kowanne akan kuɗi naira ₦300, idan kuma duka biyun za ka haɗa za a ba ka akan ₦500.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litininlaraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

Wednesday, 2 November 2022

Kyawawan Hanyoyin Furta Kalaman Soyayya

Kyawawan Hanyoyin Furta Kalaman Soyayya

Ashe dama so yana da murya kuma yakan yi magana. Wani zai yi mamaki shin ta yaya so yake magana?


SAUTIN SO
Hoto: Today Tip


MarubuciNura Nakowa


Shi sautin so ba sai da kunne kaɗai ake jin shi ba. Akan iya jin sautin so a cikin zuciya da gangar jiki.


Shin, ka manta daga cikin alamomin so da akwai kallo, kunya da kuma ambato? To ashe kenan kallo da kunya duk da ba sa ɗauke da nau'in sauti amma suna tura saƙon da za a fahimci abin da ake nufi. 


Wannan saƙon da suke turawa kuma, wani lokacin ya fi wanda ba ki zai furta tasiri domin shi saƙo ne da ake jin shi a cikin ruhi da zuciya.


Wani lokacin ma ɗaga hannu tsakanin masoya ko motsa kai ko motsa idanuwa da sauran sassan jiki yakan sanar wanda ake tare da shi abin da ake so ko ake da buƙata.


To mu dawo batun mu na "SAUTIN SO".


Shi sauti dai a zahirance shi ne abin da muka saba ji da kunnuwanmu.


Da za a tambayeka me ka fahimta da sautin so, cikin ƙanƙanin lokaci wani zai ce kalamai masu daɗi da masoya kan gaya wa junansu. Hakane, duk wata kalma da za ta fito daga cikin baki dole sai da sauti.


Kalaman soyayya akan iya faɗarsu ta sigogi da yawa, kamar a rubuta a takarda ko saƙon waya ko hoto mai motsi da mara motsi, da dai sauran kafofin sadarwa. To amma wanda sautin murya ke fita, wannan shi ne wanda ya fi kowanne shiga cikin zuciya da kuma kama zuciya.


Idan kuma mutum bai iya ba ko kuma bai san ta wacce sigar ake iya furta kalmar da ke ratsa zuciya ba, to lallai da akwai aiki a gabansa, domin zai yi ta yi ne amma kuma ba ya ganin tasirin sa.


Kasancewar so abu ne me daɗi, to haka ake so kalmomin sa da amon sautin sa su zamto masu daɗi, masu laushi, masu sanyi, masu zaƙi, sannan kuma masu faranta rai.


A duk lokacin da ake son a furta kalmar da ake so a sace zuciya ko kama zuciya ko a ja ra'ayin wanda ake so, to sai an kula da abubuwa kamar haka:-


1.  Tausasa murya; Banda hargagi ko ɗaga murya ko kausasawa wajan furta kalamai masu kama da izza ko tilastawa.


2. Ƙanƙan dakai; misali, tunda nema kake yi to sai ka yi ƙoƙarin aikata abin da zai sa ka samu, ba kuskuren da zai sa ka rasa ba. 


A yayin nema za ka iya fuskantar abin da zai saɓawa tsarin ka ko kuma wanda zai ɓata maka rai. (Idan ka maida kanka bawa, wataran za ka zama sarki).


3. Tsarkin zuciya domin samun damar furta kalamai masu tsafta; idan zuciyarka ba ta da tsarki za ta dinga ingiza ka wajan yin komai a gaggauce. Ita kuma soyayya sannu a hankali ake bin ta. Ko magana idan ana yin ta da gaggawa harɗewa ta ke yi.


A hurumin soyayya ana buƙatar yin magana daki-daki kuma a-jere-a-jere.


Dalilin hakan kuma shi ne, zai ba ka damar yin amfani da hankalin ka da tunanin ka wajan sarrafa kalmomin da za su dinga fitowa daga bakin ka.


Haka kuma ana so ka yi ƙoƙari wajan sassaita muryarka ta yadda za ta yi daɗi a kunnen wanda yake jin ta.


Ka koyi yin magana da aji, sannan kuma ka zama me salo ta yadda salonka zai dinga ƙara samar maka da gurbin zama a cikin zuciyar wanda kake so. Don haka ne zai sa ka ji ana mararin a ji sautin muryarka, haka kuma za ka ga ana muradin a ganka a ko da yaushe.


Masha Allah, Alhamdu lillah. Idan ka ji daɗin kasancewa da ni, to ka sanar da 'yan uwa da abokan arziki wannan shafi domin su ma su ƙaru da rubuce-rubuce na.


Nagode da ka ba ni lokacin ka.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litinin, laraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

Wednesday, 26 October 2022

Matsalolin Masoya Da Maganin Su

Matsalolin Masoya Da Maganin Su

Wasu daga cikin masoya sukan yi murabus daga soyayya saboda wata matsala ko ɓacin rai da suka taɓa fuskanta daga abokin soyayyarsu, ko su ce sun daina ko su ce sun haƙura da soyayya.


NA HAƘURA DA SOYAYYA.
Hoto: Love Shayari Images


MarubuciNura Nakowa


Wai shin faɗin haka yana maganin baƙin ciki kuwa?


Hakan yana faruwa ne kasancewar dayawa daga cikin masoya sun kasa fahimtar cewa soyayya tamkar rayuwa take, wataran ka ji daɗi, wataran ka ji ɗaci. Ba ko da yaushe ake samun yadda ake so a rayuwa ba dole wata rana a samu akasin rayuwa.


Soyayya sa'a ce, hakanan kuma aure rabo ne. Wata takan haƙura da soyayya saboda ba ta yi sa'ar irin saurayin da take so ba. 


Wata kuma tana haƙura da soyayya ne saboda samarin da take samu ba mutanen kirki ba ne, wasu mayaudara ne wasu kuma 'yan iska ne. Wata kuma ba ta ma iya rarrabewa tsakanin mayaudara da 'yan iska kokuma waɗanda ba hakan ba, kawai dai duk waɗanda suke zuwa mata ba masu tsayar da magana ba ne, daga waɗanda ba su shirya yin aure ba sai waɗanda suka kasa tafiyar da soyayyarsu yadda za ta yi daɗi.


Haka abin yake a ɓangaren samari, su ma suna fuskantar kwatankwacin hakan daga wajan 'yammatansu.


To ruwa ba ya tsami banza. Wata ƙila da akwai wasu halaye ko ɗabi'u da kake da su waɗanda ya kamata a ce ka sauya su domin su zama gyara ga matsalolin da kake cin karo da su a soyayyar ka.


Ga su kamar haka:-


1. Sakankancewa mara ma'ana da wanda kake soyayya da shi.


2. Yarda wadda ta wuce misali. Kana gani kamar masoyin ka ba zai taɓa cutar da kai ba. Shi kuma cutarwa a soyayya ba sai an yi maka da gangan ba. Wani lokaci akasi da kuskure ne suke haifar da cutuwa a so.


3. Rashin cikakkiyar yarda da masoyin wanda zai iya haifar maka da zargi a cikin zuciyar ka har ma shi masoyin ya gane cewar ba ka yarda da shi ba.


4. Ba wa masoyi damar da bai kamata ka ba shi ba a fannin furuci  da mu'amala ba. Idan ka ba wa masoyi wata damar za ka ga yana furta maka magana yadda ya ga dama. A ɓangaren mata kuma idan kika ba wa saurayi damar furta miki kalamai na rashin ɗa'a wataran zai kai ga taɓa jikin ki, daga nan kuma sai akai ga abin da muke magana akai na ɓacin rai domin hakan ne yake sa idan an ci moriyar ganga sai ayi watsi da ita.


5. Ruwan ido da kuma rarraba zuciyarka gida-gida. Misali, yin soyayya da masoya daban-daban kuma kowanne zuciyarka tana sonsa. Abin da ke jawo haka kuma shi ne, barin ƙofar zuciyarka a buɗe duk wanda ya zo ya shiga.


Dukkanin waɗannan abubuwan da muka kawo suna daga cikin abin da ke sanyawa ka ga masoya suna cewa su sun gaji da soyayya saboda rashin tabbas ɗin da ke cikin ta. A dalilin haka sai su ce sun haƙura da soyayyar ma gaba ɗayanta.


To abin lura anan shi ne, idan ka ce ka haƙura da soyayya ya za ka yi da halittar so da Allah maɗaukakin sarki ya yi a cikin jikin ka. Ya za ka yi da shauƙi da sha'awar da Allah ya saka maka a ran ka. Ya za ka yi da buri da muradin zuciya na son samun abin da zai kwantar maka da hankali. Taka ce fa ba ta yi kyau ba saboda rashin dacewar da ka yi a soyayya. Wasu suna can suna jin daɗin soyayyar su.


Da akwai mutane da dama waɗanda suke da buƙatar su samu soyayyar ka amma lokaci bai kawo maka su ba sai waɗanda ba su dace da kai ba suke ta kawo kansu.


Saboda haka yin murabus a soyayya ko daina ta ko haƙura da ita ba zai yi maka maganin cin amana ko yaudarar da aka yi maka ba, haka kuma ba zai cire maka haushin da ka ji na waɗanda suka ɓata maka lokaci ba, sannan kuma ba zai dawo maka da bara-bana-ba sai dai ma ka ci gaba da ɓata wa kanka lokaci har zamani ya shuɗe da kai.


Abin da za ka yi shi ne, ka nutsu ka yi soyayyar wayewa da fahimtar rayuwa ba soyayyar holewa da burgewa ba. Ka ba wa wanda ka yaba da nutsuwa da hankalin sa dama, ku yi soyayya sai dai idan aka samu akasi wanda zai iya kai wa ga an sake faɗa wa haɗarin da aka taɓa faɗawa a baya, sai a hakura har lokacin da Allah zai sa a dace.


Sannan kuma a daina saurin yanke hanzari a soyayya.


Haƙuri da juriya yana sa a fahimci hanyar da za ta ɓulle a soyayya.


Alhamdu lillah.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litinin, laraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

Monday, 10 October 2022

Kiyayya Ko Soyayya?

Kiyayya Ko Soyayya?

Bai kamata ƙiyayya ta shiga tsakanin ka da wanda bai karɓi soyayyar ka ba, saboda a soyayya babu tilas. Sannan kuma idan ya karɓi soyayyar ka ba da sonsa ba, to ya cuci kansa sannan kuma soyayyar ku ba za ta yi muku daɗi ba, haka kuma idan ya ƙi fada maka gaskiya akan buƙatar da ka zo masa da ita, za ka iya zarginsa da yaudara daga baya.


JAN HANKALI GA MASOYA
Hoto: Medium


MarubuciNura Nakowa


Bugu-da-ƙari, musammam ga masu iyali, akan samu lokacin da za ka iya tsintar kanka a cikin yanayin rashin samun sukuni ko nutsuwa a tsakaninka da iyalinka, to, wannan ba yana nufin ba kwa son juna ba ne, a'a, kawai dai ansamu akasi ne. Idan kuka yi haƙuri za ku fahimci juna.


Ka ga ashe kenan shi SO wanda ake nufi da SOYAYYA, ba da kowa ake yi ba sai wanda ta ku ta zo ɗaya da shi.


Saboda haka kada ka ce ko ta halin-ƙaƙa sai an so ka. Idan ka yi haka? To shi muke kira tilas ko kuma na ci a soyayya.


Allah yasa mu dace Amin.

Monday, 3 October 2022

Muhimman Abubuwa 14 Ga Dukkan Masoya

Muhimman Abubuwa 14 Ga Dukkan Masoya

Ashe dai kamar yadda manomi yake cin ribar abin da ya shuka haka masoya ma suke cin ribar soyayyar su.


RIBAR SOYAYYA
Hoto: Getty Image

MarubuciNura Nakowa


Duk wani manomi burinsa ya ci ribar abin da ya shuka. Ba za a ci ribar noma ba har sai an tabbatar da cewa gona ta yi kyau, wanda hakan ne zai sa a girbi kayan gona me kyawun gaske.


Haka abin yake ga masoya. Abin da suka shuka shi za su girba, kuma burin duk wani masoyi shi ne ya girbi alkhairi.


Mafi girman daraja a ribar soyayyar shi ne AURE. Duk ribar da masoya za su ci muddin ba su yi aure ba, to ba su samu mafificin darajar soyayya ba. Ana iya ribatar wasu abubuwan a soyayya tsakanin masoya kamar faranta ran juna da kyaututtuka da ɗebe kewa da makamantan su, amma dukkanin waɗannan ba kamar a yi aure ba.


Tazarar da ke tsakanin aure da soyayya zalla wacce ba ta kai ga an yi aure ba, tanada yawa sosai.


Ana iya shafe lokaci me tsawo dakuma nisan gaske ana soyewa da soyayya amma kwana ɗaya a gidan aure, ya shafe dukkanin shekarun da aka yi ba tare da aure ba.


Yadda ake ƙirga ribar so ko ribar soyayya;


1. Idan aka aminta da kai a soyayya, ka ci ribar so.


2. Idan ka sa ayi za ayi, idan kuma ka ce kada ayi ba za ayi ba, ka ci ribar so.


3. Ida ana yi maka biyayya sau da ƙafa, ka ci ribar so.


4. Idan ana maka fara'a da jan hankalin ka, ka ci ribar so.


5. Idan ana kwantar maka da hankali da ɗebe maka kewa, ka ci ribar so.


6. Idan ana gudun ɓacin ranka kuma ba a aikata abin da zai ɓata maka rai, ka ci ribar so.


7. Idan ana haba-haba dakai ana mararin ka, ka ci ribar so.


8. Idan ba a son a yi nesa da kai saboda ana jin daɗin zama dakai, ka ci ribar so.


9. Idan ana furta maka kalaman soyayya cikin tattausan lafazi me daɗi, ka ci ribar so.


10. Idan ka ji kullum ka ƙara jin son masoyin ka a ranka, ka ci ribar so.


11. Idan ana yi maka godiya da yabawa, ka ci ribar so.


12. Idan aka ce ba wani sai kai kuma ka tabbatar da hakan, ka ci ribar so.


13. Idan aka zaɓe ka a matsayin wanda za ayi rayuwa da shi, ka ci ribar so.


14. Idan aka aure ka, ka ci babbar ribar so, wanda shi ne burin kowanne masoyi.


Sunada yawa idan za a ƙirga su.


Duk wani abu wanda za ka iya bada shaidar sa na alkhairi game da masoyin ka, riba ce a soyayya.


Na san kai ma da kake karatun nan a yanzu, da akwai wasu abubuwan da kake samu daga masoyiyar ka ko kike samu daga masoyin ki masu burgewa waɗanda ban ambace su ba, to ka haɗasu da waɗanda na kawo, ka tattara su guri guda domin sanin adadin ribar da ka ci.


Alhamdu lillah.


Allah yasa mu yi soyayya don Allah don mu ci riba me tarin yawa Amin.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litinin, laraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa.

Wednesday, 28 September 2022

Hanyoyin Gina Ingantacciyar Soyayya Ga Masoya

Hanyoyin Gina Ingantacciyar Soyayya Ga Masoya

Duk wani manomi ba sai an gaya masa abin da ya kamata ba wajan kula da gonar sa. Ya san lokacin da gonar keda buƙatar ruwa, taki, ko feshin kwari. Duk Yana hakane don a samu yabanya mai kyau domin ya girbi alkhairin abin da ya shuka ba tare da hasara ko ɓacin rai ba.


SO GONA CE SAI DA GEWAYA
Hoto: The Conversation


Marubuci: Nura Nakowa


Ita zuciya tana buƙatar kulawa. Kamar su ɗaya da shuka dole sai da banruwa.


Saboda haka so gona ce sai ana kewayawa domin sanin halin da take ciki domin abin da rai ke so bibiyarsa yake yi domin sanin ingancin sa.


Rashin sanin hali ko yanayin da masoyi ke ciki tamkar rashin damuwa da shi ne. Ya zama tamkar tuwo ne babu miya, domin ɗaya ya damu da soyayyar amma kuma ɗayan bai damu ba. Shi yasa a soyayya ake son kulawa akai-akai domin jaddada ƙaunarka ga wanda kake so.


Zuwa gurin masoyi da kyakkyawar manufa domin a zanta yana ƙarawa masoyi martaba a zuciyar wanda yake so. Idan ba ka je ba da akwai wasu hanyoyi dayawa waɗanda za su maye gurbin rashin zuwanka wanda kuma suna daga cikin abin da muke magana akai cewa 'So Gona Ce Sai Da Gewaya'. Daga ciki da akwai yin aike ko tura saƙo, ko kuma idan ka samu ka zo ka yi bayani ko ka aikata abin da zai burge masoyin ka wanda zai sa ya manta da kewar ka da yayi na wasu lokutan. Yin hakan zai sa ka ci ribar soyayyar ka.


Da akwai abubuwa masu yawan gaske waɗanda su suke sawa so yayi ƙarko.


Kamar:-


- Bada lokaci da kulawa.


- Ihisani ko alkhairi.


- Kawar da zargi da ƙorafi.


- Rusunawa da rarrashi.


- Soyayya ba ta son gaggawa.


- Sai da lallaɓawa ake satar zuciya.


Akwai sirrika da yawa a cikin soyayya, kuma wanda ya san sirrin so shi yake ƙirga riba.


Wai shin, mene ne sirrin so kuma ya ake ƙirga ribar so..?


Mu hadu a rubuta na gaba.


Rubutu na zai dinga zuwa muku a tsakanin ranakun litinin, laraba da juma'a.


Muna maraba da saƙonnin ku dakuma tayamu sanar da wasu labarin wannan shafin.