Thursday 21 November 2019

Ku Yi Koyi Da Abinda Annabi Muhammad (S.A.W) Ya Koyar Cewar - Jarumin Fina-finan Amurka Van Damme

Tura Wannan Zuwa
Jarumi Dan kasar Amurka Jean Claud Van Damme ya shawarci mutane su yi koyi da abinda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar.


Jarumi Van Damme

Marubuci: Bangis Yakawada

Musulunci addini ne na gaskiya, Allah ya saukar mana da Al-Qur’ani a matsayin shiriya don mu bi shi.

Allah ya turo mana Annabi Muhammad a matsayin dan aike ne, Madubin dubawa ne garemu kuma an umarcemu da mu bi sunnarshi, Ba Musulmai kadai ke bin koyarwar Annabin rahamar ba.

Kwanan nan aka tambayi dan wasan fina-finan kasar Amurkan nan na masana'antar Hollywood, Jean-Claude Van Damme ( Commando) a kan yadda ake cin abinci kamar yadda kiwon lafiya ya tanadar, sai ya bada amsa da: “Annabi Muhammad ne ke da amsar, don ya koyar da yadda za a ci abinci tare da abubuwan da yakamata matasa su ci masu kara lafiya.”

Ya kara yin bayani akan yanayin jinin mutum da sauran abubuwan da suka shafi kiwon lafiya.

Ya ce: “Cin abinci mai kyau, barci mai kyau. Zaka iya cin abinci da nama ko a sati sau daya ne, Idan nace nama, ba ina nufin nama mai yawa bane. Ganyayyaki da sauran abincin larabawa masu gina jiki.”

“Ka duba lokacin Annabi Muhammad, Musulmai na cin gurasa ne da kuma kayan lambu. Annabi Muhammad ya san abinda ya dace da kowanne zamani kuma mai gina jiki. Don haka ni bana son kuna tambayata, ku bincika daga koyarwar shi."

MAKALOLI MASU ALAKA:

Musulman Amurka Sun Yi Nasara Akan Gwamnatin Kasar Amurka

DARASI GAME DA HARIN MASALLACIN KASAR NEW ZEALAND 

KALLI YADDA 'YAN NIGERIA SUKAI ABIN KUNYAR DA BA A TABA YI BA A TARIHIN DUNIYA

"A cikin koyarwar shi akwai tarin hikima da dabarun da zasu dace da zamani," in ji Van Damme.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user