Sunday 24 November 2019

KARANTA YADDA AKE YIN SALLOLIN NAFILA TARE DA BAYANI AKAN ADADIN SU

Tura Wannan Zuwa Ga
SALLAR NAFILA:

Sallolin nafila sune sallolin da ba na wajibi ba.

Yayin Zaman Tahiya

Kuma suna da yawa daga cikin su akwai:-

RAKA'ATANIL FAJRI:

"قال صلى الله عليه وسلم: ركعتا الفجر خير من الدنيا وما فيها" رواه مسلم.

Ma'ana: "Manzon Allah (SAW) ya ce: Raka'atal fajri ita ce mafi alkhairi daga duniya da abin da ke cikinta". Muslim ne ya rawaito.

Raka'o'i biyu ne saukaka, ana yinta ne bayan bullowar alfijir kafin a tada sallar Asubahi, ana yinta ne raka'a biyu, a raka'ar farko ana karanta Fatiha da qulya'ayyuhal kafiruun, sannan a raka'a ta biyu ana karanta Fatiha da Qulhuwallahu ahad.

SALLAR WALAHA

Sallar Walaha ana yinta bayan bullowar rana, akalla raka'a biyu.

SALLAR WITIRI

Sallar witiri ana yinta bayan sallar isha'i mafi karancinta raka'a daya, yawanta raka'a (11), ayi biyu ayi sallama har ya rage daya a karshe a yi ta ayi sallama. Koda an yi fiya da sha dayan (11) babu laifi amma dai a karshe ayi witiri wato a rufe da raka'a daya (1) ayi sallama.

SUNNANUR RATIBATI:

قال صلى الله عليه وسلم "ما من عبد مسلم يصلي لله كل يوم ثنتي عشرة ركعة، تطوعًا غير فريضة إلا بنى الله له بيتًا في الجنة، أربع ركعات قبل الظهر، وركعتين بعد الظهر، وركعتين بعد المغرب، وركعتين بعد العشاء، وركعتين قبل الصبح" رواه مسلم.

Ma'ana: Manzon Allah (SAW) ya ce: Babu wani bawa Musulmi da zai rika salla dan (Zatin) Allah kullum raka'a goma sha biyu wacce ba ta cikin salloli Wajibai, fa ce sai Ubangiji (SWT) ya gina masa a gida a cikin aljanna, raka'o'i hudu kafin sallar Azahar, da raka'o'i biyu bayan sallar Azahar, da raka'o'i biyu bayan sallar Magriba, da raka'o'i biyu bayan sallar isha'i, da raka'o'i biyu kafin sallar Asubahi" Muslim ne ya rawaito.

SALLAR TARAWIHI (ASHAM)

Sallar Tarawihi (Asham) sallar nafila ce da ake yinta bayan sallar isha'i a cikin watan Ramadana ana yinta raka'a (11) ko kuma raka'a (23).

SALLAR IDI

Sallar idi sallah ce ta nafila da ake yinsu ranar Idi karama ko babba, kuma raka’o’i biyu ne, ake yinsu a wajen gari, sa’annan idan an idar Liman ya yi khuduba.

SALLAR KUSUFI

Sallar Kusufi salla ce da ake yinta raka’o’i biyu masu tsayi yayin zazzabin rana, ana farata ne da yayin da aka ankara da zazzabin har zuwa yayewar zazzabin rana.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ABUBUWAN DA SUKE BATA SALLAH

KARANTA MANYAN LADUBBA AKAN MUSULMI GUDA 10 A RANAR JUMA'A

KARANTA MANYAN FARILLAN SALLAH GUDA 14

SALLAR ROKON RUWA

Sallar rokon ruwa sallah ce da ake yinta yayin da aka fuskanci karancin ruwa (fari), ita ma raka’a biyu ce kuma ana yinta a wajen gari.

Da wasunsu da dama.

Allah yasa duk ibadun Mu karɓaɓɓune Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user