Friday 27 December 2019

KARANTA HANYOYIN MAGANCE MUMMUNAN FUSHI CIKIN SAUKI

Tura Wannan Zuwa Ga
Amirul-Muminin Ali Bn Abi-Daalib (RA) ya ce: Mummunan fushi da mutum ya kan yi saboda hakkinsa, ba don hakkin Allah ba, farkon sa hauka ne, sannan karshen sa nadama ne.

Hanyoyin Magance Matsalar Mummunan Fushi

Marubuci: Muhammad Abubakar

GA HANYOYIN KAMAR HAKA:

1. Ambaton Allah: kamar neman tsari daga SHAIDAN da kuma karatun Al-Qur'ani (Duba Qur'ani 18:2 da 7:200).

2. Gaggawan fita daga Halin Fishi: Idan ka na tsaye ka zauna, idan kana zaune ka kwanta.

(Duba Sunan-Abi Daud: 4782).

3. Kamewa daga Furuci: Annabi (S.A.W) yana cewa: Duk wanda yayi Imani da Allah da ranar ƙiyama, to ya faɗi alheri ko yayi shiru (Bukhari).

4. Allah yana yafewa mai yafewa wanin sa. (Qur'ani 24:22)

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA HANYOYI GUDA 10 DOMIN MAGANCE MATSALAR YAWAN FISHI

KARANTA HANYOYIN SAMUN RAYUWA MAI DADI CIKIN SAUKI

KARANTA ABU BIYU NE KAWAI ZAKA IYA YI IDAN KA HADU DA WANDA YAFI KARFIN KA

5. Allah yana ɗaukaka masu yafiya da afuwa: Annabi (S.A.W) yana cewa, Allah bai ƙarawa bawa dalilin AFUWA sai ɗaukaka (Muslim:2855).

Ya Allah ka karemu daga FUSHI da sharrin sa Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user