Saturday 22 February 2020

Cikin Wadannan Zuciyoyi Wacce Irin Zuciya Ce da Kai?

Tura Wannan Zuwa
Daga cikin zukatan nan da Allah (S.W.T) ya kawo acikin ALQUR'ANI.

Wacce Irin Zuciya ce da Kai Cikin Waɗannan...

Marubuci: Hassan Goma

Sun kasu kamar haka:

1. AL-QALBUN SALIM: itace zuciyar da take yin ayyukanta don Allah kuma ko kaɗan babu burbushin kafirci acikin ta ko munafinci.

ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﻦْ ﺃَﺗَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺑِﻘَﻠْﺐٍ ﺳَﻠِﻴﻢٍ

2. AL-QALBUN MUNIYB: itace zuciyar da ako yaushe take mayar da al'amurranta ga Allah (S.W.T) kuma cike take da yawan tuba ga kuma ɗa'a ga Ubangiji.

ﻣَﻦْ ﺧَﺸِﻲَ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦ ﺑِﺎﻟْﻐَﻴْﺐِ ﻭَﺟَﺎﺀ ﺑِﻘَﻠْﺐٍ ﻣُّﻨِﻴﺐٍ

3. , AL-MUKHBIT: itace natsatstsiyar zuciya mai shiru-shiru.

ﻓﺘُﺨْﺒِﺖَ ﻟَﻪُ ﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢْ

4. QANBUN AL-WAJAL: itace zuciyar da take fargabar cewa anyah ankarɓi ayyukan alheri da nayi anya zan tsira daga azabar ubangiji (wanda hakanne yake ƙaramata
tsantseni).

ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﺆْﺗُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﺁﺗَﻮﺍ ﻭَّﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢْ ﻭَﺟِﻠَﺔٌ ﺃَﻧَّﻬُﻢْ ﺇِﻟَﻰ ﺭَﺑِّﻬِﻢْ ﺭَﺍﺟِﻌُﻮﻥَ

5. AL-QALBUN ATTAQIY: itace zuciyar da take girmama dokokin Ubangiji.

ﺫَﻟِﻚَ ﻭَﻣَﻦ ﻳُﻌَﻈِّﻢْ ﺷَﻌَﺎﺋِﺮَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﺈِﻧَّﻬَﺎ ﻣِﻦ ﺗَﻘْﻮَﻯ ﺍﻟْﻘُﻠُﻮﺏِ

6. AL-QALBUN AL-MAHADIY: itace zuciyar da ta sallama al'amuranta ga Allah kuma ako da yaushe take cikin yarda da duk wani hukunci na Allah (S.W.T)

ﻭَﻣَﻦ ﻳُﺆْﻣِﻦ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻳَﻬْﺪِ ﻗَﻠْﺒَﻪُ

7. AL-QANBUN AL-MU'DIMA INNA: itace zuciyar da take cike da tauhidi da Ambaton Allah (S.W.T)

ﻭﺗَﻄْﻤَﺌِﻦُّ ﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢ ﺑِﺬِﻛْﺮِ ﺍﻟﻠّﻪ

8. AL-QALBUN AL-HAYYU: itace zuciyar da takeyi aikin da iyakacin
abinda tasani daga alƙur'ani da hadisi.

ﺇِﻥَّ ﻓِﻲ ﺫَﻟِﻚَ ﻟَﺬِﻛْﺮَﻯ ﻟِﻤَﻦ ﻛَﺎﻥَ ﻟَﻪُ ﻗَﻠْﺐٌ

9. AL-QALBUN AL-MARIYD: itace zuciyar da take fama da rashin lafiya na kokwanto ko munafinci da fa'jirci ko kuma rashin lafiyar da yake cusa mata sha'awar haram.

ﻓَﻴَﻄْﻤَﻊَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻓِﻲ ﻗَﻠْﺒِﻪِ ﻣَﺮَﺽٌ

10. AL-QALBUN AL-A'AMAH: itace zuciyar da sai dai tai ta kalle kalle amma bata hango gaskiya kuma inma taga gaskiyar to bata wa'azantuwa da ita.

ﻭَﻟَﻜِﻦ ﺗَﻌْﻤَﻰ ﺍﻟْﻘُﻠُﻮﺏُ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﻓِﻲ ﺍﻟﺼُّﺪُﻭﺭِ

11. AL-QALBUN LIL LA'HIY: itace zuciyar da ta gafala daga alƙur'ani kuma tashagaltu da ruɗin Duniya da sha'awar duniya ba tare da lura da haƙiƙanin duniyar ba.

ﻻﻫِﻴَﺔً ﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢْ

12. AL-QALBUN ASIYM: itace zuciyar da take ɓoye shedar gaskiya.

ﻭَﻻَ ﺗَﻜْﺘُﻤُﻮﺍْ ﺍﻟﺸَّﻬَﺎﺩَﺓَ ﻭَﻣَﻦ ﻳَﻜْﺘُﻤْﻬَﺎ ﻓَﺈِﻧَّﻪُ ﺁﺛِﻢٌ ﻗَﻠْﺒُﻪُ

13. AL-QALBUN ALMUTA KABBIR: itace zuciyar da tayi girman kai ga tauhidi da biyayya ga Allah.

ﻗﻠْﺐِ ﻣُﺘَﻜَﺒِّﺮٍ ﺟَﺒَّﺎﺭٍ

14. AL-QALBUN GALIYZ: itace zuciyar da aka zare ma tausayi da jin ƙai.

ﻭَﻟَﻮْ ﻛُﻨﺖَ ﻓَﻈّﺎً ﻏَﻠِﻴﻆَ ﺍﻟْﻘَﻠْﺐِ ﻻَﻧﻔَﻀُّﻮﺍْ ﻣِﻦْ ﺣَﻮْﻟِﻚَ

15. AL-QALBUN AL-MAKHTUM: itace zuciyar da bata sauraren shiriya kuma batabin shiriya.

ﻭَﺧَﺘَﻢَ ﻋَﻠَﻰ ﺳَﻤْﻌِﻪِ ﻭَﻗَﻠْﺒِﻪِ

16. AL-QALBUN AL-QA'SIY: itace zuciyar da batabin Imani kuma bata tasirantuwa da duk wani abu da ake tasirantuwa da shi har imani ya ƙaru.

ﻭَﺟَﻌَﻠْﻨَﺎ ﻗُﻠُﻮﺑَﻬُﻢْ ﻗَﺎﺳِﻴَﺔً

17. AL-QALBUN AL GA'FIL: itace zuciyar da tayi sallama ga ambaton Allah kuma ta tafi akan abinda rai keso sannan ta riƙa biyayya ga wanin Allah (S.W.T)

ﻭَﻟَﺎ ﺗُﻄِﻊْ ﻣَﻦْ ﺃَﻏْﻔَﻠْﻨَﺎ ﻗَﻠْﺒَﻪُﻋَﻦ ﺫِﻛْﺮِﻧَﺎ
.
18. AL-QALBUN AL-AGLIF: itace zuciyar da aka lulluɓeta ta yadda saƙon Manzon ba zai shige taba.

ﻭَﻗَﺎﻟُﻮﺍْ ﻗُﻠُﻮﺑُﻨَﺎ ﻏُﻠْﻒٌ

19. AL-QALBUN AL-ZA'IG: itace zuciyar da take kaucema gaskiya.

ﻓﺄَﻣَّﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻓﻲ ﻗُﻠُﻮﺑِﻬِﻢْ ﺯَﻳْﻎٌ

MAKALOLI MASU ALAKA:

Cikin Wadannan Mutane Wanne Irin Aboki Ne da Kai?

Shin Ko Kasan Zabi Biyu Kake da Shi a Rayuwa?

Shin ko Kasan Abinda Yafaru da Kai a Farkon Rayuwar Ka Kuma Zai Sake Faruwa a Karshen Rayuwar Ka?

20. AL-QALBUN AL-MURIYB: itace zuciyar da take zaɓin abinda take kwankwanto akanshi.

ﻭَﺍﺭْﺗَﺎﺑَﺖْ ﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢْ

YA ALLAH (S.W.T) KASANYA ZUKATANMU SU ZAMA KUƁUTATTU DAGA SHIRKA KUMA MASU YIN AIKI DON KAI ALBARKAN ANNABI (S.A.W) AMIN.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user