Sunday 23 February 2020

Kada Ka Yiwa Mutum Irin Wannan Tambayar Domin Tana Tafasa Zuciya

Tura Wannan Zuwa Ga
Kada ka ga wanda yakamata yayi aure, ko ta kamata ta yi aure kace musu wane ko wance ke har yanzu ba ki yi aure ba? Musamman mace.

Wasu Lokutan ana wuce gona da Iri..

Marubuci: Ibrahim Muhammad Abu Muh'd

Babu mai yin aure sai lokacin da Allah ya rubuta masa yayi, kai ma ba wayonka ko iyawarka ba ne.

Kar ka tambayi wanda yayi aure bai haihu ba, kace masa kai har yanzu shiru? Anya ma kanada lafiya kuwa? Da sauran tambayoyi Irin waɗannan.

Babu wanda ƙarfi ko dabararsa ke bashi haihuwa. Idan Allah yayi za su haihu.

Kar kayiwa mahaifa gorin mai yasa ba su aurar da ƴarsu ba?

Sau da yawa waɗanda sukazo daga baya sun fi waɗanda suka shiga tun farko samun niitsuwa da abinda ake buƙata.

Ba ka san halinda ya hana mutum ba, babu mai zama babu aure haka kawai babu dalili ko babu haihuwa domin dukkansu abin so da ƙauna ne.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Magance Matsalar Mummunan Fushi Cikin Sauki

Karanta Nasihohi Guda 10 Ga 'Yan Uwana Matasa

Shin Dan Alllah Malam Mene Ne Hukuncin Yin Saki Uku a Cikin Fushi?

Tsakani da Allah waɗannan tambayoyi ne da ake yinsu bisa raha da wasa amma suna matuƙar tafasa zuciyar wanda aka yiwa, ko da yayi dariya.

Kar ka fusata Ɗan Uwanka Musulmi.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user