Showing posts sorted by date for query Aliyu Nata. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query Aliyu Nata. Sort by relevance Show all posts

Friday, 27 December 2024

Matsalar Matan Hausawa A Soyayya

Matsalar Matan Hausawa A Soyayya

Akwai ƙananun abubuwa da suke sa namiji ya ji yana bala'in son mace wallahi, amma matan Hausawa ba su ankare da su ba kuma sam ba su ba su muhimmanci ba, su kawai burinsu a yi ta zuba kalaman soyayya kuma namiji ya yi ta musu hidima kamar sun siyo bawa a kasuwa.


Matsalar Matan Hausawa A Soyayya
Hoto: Zawaj

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Akwai abubuwa da yawa wanda za ki ja hankalin namiji wanda wallahi mai raba ku sai rabbul samawa wati ina magana akan 'yammata ne ba masu aure ba.


Yi masa 'yar kyauta kamar saya masa maɓalli hannun riga (Links), ɗan turare, 'yar hula mara tsada,  ɗan silifas ko na shiga wanka ne, na taɓa wata budurwa da take saya min irin waɗannan abubuwan duk da na san cewa hidimar da nake mata ta fi abin da take min wallahi duk abin da ta saya mini sai na ji na fi sonsa akan wanda na saya da kuɗina koda kuwa ya fi nata tsada.


Mun sani cewa mata mugayen marowata ne shi ya sa namiji yake tabbatarwa duk macen da ya ci kuɗinta koda kaɗan ne to ya tabbatar tana son sa da gaske ba wasa ba.


Amma matan Hausawa ba su cika wannan ba sai wadda wayewarta ta kai, su burinsu su yi ta karɓar naka kamar tsofaffun almajirai, ko kuma sun yi ƙoƙari su girka maka wata bushashshiyar dafaduka (Jallop) ko mai bai ishe ta ba da wani lemo ɗan haɗi, kuma wasunsu da wata manufa suke yi.


Idan kina da hali wani lokacin ki turawa saurayinki kati ko data shi ma fa mutum ne akwai lokacin da yake buƙatar su kuma wallahi ba shi da ko sisi haka zai ji son ki ya ƙara ƙaruwa a ransa.

Thursday, 5 December 2024

Kalli Kyawawan Hotunan Jaruma Rukky Alim

Kalli Kyawawan Hotunan Jaruma Rukky Alim

Ruƙayya Ahmad Aliyu wadda aka fi sani da Rukky Alim  ɗaya ce daga cikin sababbin jarumai mata masu tasowa a masana'antar Kannywood.


Rukky Alim
Hoto: Rukkky Alim/Instagram

Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.


Rukayya Ahmad Aliyu
Hoto: Rukkky Alim/Instagram

Rukky Alim ɗaya ce daga cikin jaruman da ke jan ragamar shiri mai dogon zango a halin yanzu mai suna Allura Cikin Ruwa.


Jaruma Rukky Alim
Hoto: Rukkky Alim/Instagram

Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan nata.


Rukky Alim
Hoto: Rukkky Alim/Instagram

Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:


Rukky Alim
Hoto: Rukkky Alim/Instagram

Jaruma Rukky Alim
Hoto: Rukkky Alim/Instagram

Jaruma Ruƙayya Ahmad Aliyu
Hoto: Rukkky Alim/Instagram

Rukky Alim
Hoto: Rukkky Alim/Instagram

Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe domin samun ainihin cikakken tarihin Rukky Alim nan ba da jimawa ba tare da zafafan hotunan ta na musamman.

Friday, 15 November 2024

Bambancin Soyayyar Mace Da Soyayyar Namiji

Bambancin Soyayyar Mace Da Soyayyar Namiji

Ya kai Ɗan Saurayi ka sani soyayyar da mace ke yi wa namiji ba irin ta namiji ke yi wa mace ba.


Bambancin Soyayyar Mace Da Soyayyar Namiji
Hoto: Set my wed/Pinterest 


Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ga abun dalla-dalla:


Mace


Mace tana son namiji ne don zai biya mata buƙatunta na yau da kullum, kamar ci da sha sutura, kiwon lafiya, da muhalli mai kyau har da bonus wato garaɓasa na kuɗi idan ta samu, wanda dukkanin wannan idan babu kuɗi so kawai ba zai gamsar ba.


Namiji


Namiji shi kuma yana son mace ne saboda halittar da Allah ya yi masa na buƙatuwa da ita a tsarin halittarsa, ita ma mace tana da wannan buƙatar, don haka ko ba kuɗi namiji zai iya zama da mace yayin da ita kuma mace idan babu kuɗin biyan waɗancan buƙatu nata zamanta da namiji ba zai yiwu ba.

Wednesday, 1 May 2024

Kalli Zafafan Kyawawan Hotunan Fatima Mai Zogale

Kalli Zafafan Kyawawan Hotunan Fatima Mai Zogale

Fatima Aliyu wadda aka fi sani da Fatima Mai Zogale, tana  ɗaya daga cikin waɗanda nasarar su take zama abar tattaunawa a gurare daban-daban a yau.


Fatima Aliyu
Hoto: Fatima Mai Zogale 


Fatima Mai Zogale, ita ce wadda fitaccen mawaƙin nan na Arewa wato Dauda Kahutu Rarara ya rera wa waƙa.


Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.


Fatima Mai Zogale ta kasance masoyiyar waƙoƙin Rarara ce ita tun kafin ma ta san shi.


Waɗannan ƙarin wasu ne daga cikin kyawawan hotunan nata;


Fatima Mai Zogale
Hoto: Fatima Mai Zogale 


Fatima Aliyu
Hoto: Fatima Mai Zogale 


Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe don samun tarihin Fatima Mai Zogale da zafafan hotunan ta na musamman.

Sunday, 16 August 2020

Sauke Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Ft Aliyu Nata - 'Yan Arewa Muso Juna

Sauke Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Ft Aliyu Nata - 'Yan Arewa Muso Juna

Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Nasiha.

'Yan Arewa Musu Juna

Wannan sabuwar waƙar haɗaka ce tsakanin fitaccen mawaƙi Hamisu Breaker da Aliyu Nata mai waƙar Aure Martaba.

'Yan Arewa Muso Juna waƙa ce da mawaƙan su rera domin tunatar da al'umma, musamman idan aka yi duba da yanayin da al'ummar mu suke ciki a zamanin yau, na kashe-kashe wanda ya addabi ciki da wajen arewacin ƙasar Nijeriya.

Wato tsayawa bayyana abinda wannan waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Wednesday, 12 June 2019

Kalli Kayatattun Hotunan Kwalliyar Sallah Na Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

Kalli Kayatattun Hotunan Kwalliyar Sallah Na Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

Kamar yadda shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin hotuna masu inganci waɗanda suka fi ɗaukar hankulan shafukan sada zumunta.


Aisha Tsamiya



MURYAR HAUSA24 Yau ma gamu tafe  hotunan Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya na Murnar Sallah.



Jarumar ta rubuta saƙon Barka da Sallah ga ɗimbin masoyan ta "Barkan Mu da Sallah, Allah ya karɓi Ibadun mu ya Kuma Maimaita mana Amin".


Saƙon Barka da Sallah



Hotunan sun dauki hankula sosai a shafukan sada Zumunta duba da yadda aka ɗauki hotunan wanda hakan ya taka rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar dama Duniya baki ɗaya.

Aisha Tsamiya


Wasu daga cikin mabiyan jaruma Aisha Tsamiya a shafin sada zumunta da musayan ra'ayi sunyi sharhi akan hotunan tauraruwar masana'antar shiya fina-finan Hausa (KANNYWOOD).


Sharhi


Ga wasu daga cikin Sharhin da masoyan nata suyi mata akan kwalliyar Sallah.

Sharhi


Masoyan Jaruma Aisha Tsamiya sun yaba da kyawun surar da Allah yayi mata.


Sharhi


MURYAR HAUSA24  Muna yi Mata fatan alkhairi.


KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN JARUMA AISHA ALIYU TSAMIYA


Kayatattun Hotunan Kwalliyar Sallah na Jaruma Hadiza Gabon




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode







Friday, 7 June 2019

Karanta Kaji: Kuskure 4 da akai a cikin Film din SALMA BANKWANA  tare da Sharhin Fim din

Karanta Kaji: Kuskure 4 da akai a cikin Film din SALMA BANKWANA tare da Sharhin Fim din

Suna: Salma Bankwana.
Daukar Nauyi: Nura M. Inuwa.
Kamfani: ABNUR Entertainment.
Shiryawa: Abdul Amart.
Bada Umarni: .Sadik N. Mafia.


Salma Bankwana




SHARHI: Musa Ishak Muhammad



Jarumai: Adam A. Zango, Fati Washa, A’isha Aliyu Tsamiya, Hadiza Muhammad, Baballe Hayatu, Balarabe Jaji, Asamau Sani, Alasan Kwalli, Malam Inuwa, Bankaura, da sauransu.


Fim din “Salma Bankwana” fim ne da aka gina shi a matsayin ci-gaban fim din “Salma.” Fim ne da yake dauke da labarin wani matashi mai suna Naseer (Adam A. Zango) mai tsananin soyayya ga kanwarsa kuma budurwarsa wato Salma (A’isha Aliyu Tsamiya). Sun kasance suna tsananin kaunar junansu, domin kuwa sun shaku sosai, sai dai kash! Salma ta rasa rayuwarta sakamakon hadarin mota da ya ritsa da ita a lokacin da ta tafi Sakkwato domin rabon katin bikinsu da Naseer.


Rasuwar Salma ta zowa Naseer da wani irin yanayi mawiyaci, wanda hakan ne silar susucewar komai nashi. Saboda a kullum ba shi da abun yi idan ba tunaninta da anbatonta ba. Ta kai har sunbatu ya ke a kanta. A bangare guda kuma akwai Minal wadda take tsananin kaunarsa wadda hakan ya tilasta mata yin komai irin na Salma domin ta samu shiga a gurun Naseer.


Wannan shi ne a takaice abunda ya faru a cikin fim din Salma wanda kuma shi ne tushe na wannan fim mai suna “Salma Bankwana.” A haka Naseer ya ci gaba da rayuwa cikin tsananin kewar Salma da kuma bayyana irin tsananin kaunar da yake mata duk da ce wa bata raye, domin har fada yake cewa shi fa a gurunsa Salma bata mutu ba domin tana rayuwa ne a cikin zuciyarsa.


Ita kuma Minal tana ta ci gaba da shirye-shiryen yadda zamanta sai kasance da Naseer domin kuwa an kusa aurensu. Tana ta shirin ya za ta yi ta saka shi ya manta da Salma sannan ya maye gurbinta a zuciyarsa da ita. Sai dai tun kafin auren nasu, Naseer ya sha fadawa Minal cewa dole sai ta yi hakurin zama da shi saboda shi bazai taba yi wa wata mace irin son da ya yi wa Salma ba.


A daya bangaren kuma, a can gidansu Naseer wato gidan da suka rayu da Salma a lokacin da take raye, akwai kanwar Salma mai suna Sakina wadda ita ma take cikin tsananin son Naseer sai dai ta kasa samun amincewarsa, saboda ya ce dabi’unta sam ba su yi kama da na Salma ba, saboda haka ba zai taba aurenta ba. Duba da irin mawiyacin hali da Sakina take ciki ne yasa mahaifinta wato Alhaji wanda shi ne ya rike Naseer a gidansa tun yana karami, ya kirawo Naseer a kan ya daure ya auri Sakina duba da cewa ita kadai ce ta rage musu a rayuwarsu tunda Allah ya karbi rayuwar Salma kuma basa so ita ma su rasa ta saboda ciwon sonsa. Sai dai a nan ma Naseer ya kara bayyanawa Alhaji cewa fa sai dai a yi hakuri saboda gaskiya shi bazai iya auren Sakina ba.


Bayan an yi auren Naseer da Minal, Minal ta fara karo da matsaloli tun a daren da aka kai ta gidan Naseer, domin ya ringa kiranta ne da sunan Salma wanda hakan ya yi matukar bakantawa Minal rai, sai dai ya bata hakuri da neman cewa ta yi masa uzuri. A Haka dai tayi ta rayuwa cikin kunci a gidan Naseer domin kuwa kullum haukarsa a kan Salma kara bayyana take.

Kullum kokarinta shi ne ya za a yi Naseer ya dan bata dama domin ta bayyana irin cikakkiyar soyayyar da take masa, amma sai dai hakan yaki samuwa. Haka Naseer ya bi ko’ina a cikin gidan nan ya cike shi da hotunan Salma, amma Minal duk tayi hakuri saboda burinta na ganin farin cikin mijnta.


Hakurin Minal ya je karshe, domin kuwa wata rana ta dauki hoton Salma ta yi jifa da shi a kasa wanda hakan ya saka ya farfashe, ai kuwa nan take Naseer ya hau dukanta. Yana cikin dukan nata ne sai ga mahaifiyarta Hajiya Balaraba (Asamau Sani) da kaninta Bashir (Abba Kabugawa) suka shigo, suna shigowa ne fa suka samu Minal tana ta kuka shi kuma Naseer ya biyo ta da gudu yana fadawa mahaifiyarta cewa wai Salma ta kirawo da gawa. A nan ne dai Hajiya Balaraba ta dauke Minal ta tafi da ita gida kuma ta ce mahifin Minal sai ya nemar mata hakkinta. Wanda sakamakon hakan ne aka saka ‘yan sanda suka shigo har gida suka kama Naseer aka je aka kulle shi.


A karshe bayan an fito da Naseer daga hannun ‘yan sanda, Shi ne Alhaji wato mahaifinsa na ruko ya dauke Naseer da abokinsa Kabeer (Baballe Hayatu) zuwa gurun Malam (Malam Inuwa) inda a nan ne aka yi wa Naseer wa’azi mai nawi da ayoyi da hadisai, wanda hakan ya zama silar yin nadamarsa a kan irin abubuwanda ya aikata. Sannan ya kirawo Minal ya bata hakuri, kuma ya yi mata alkawarin daina dabi’un da yake, wanda bayan ta amince ta dawo gidanta ne a ka nuno shi ya dakko duka hotunan Salma da suke gidan yana kona su. Sannan kuma ya koma gida ya yi wa Sakina alkawarin zai aureta yanzu.


Abubuwan Yabawa


1. Sunan Fim din ya dace da labarin.


2. Labarin mikakken labari ne wanda bai yanke ba tun daga farkon shi har karshensa.


3. Fim din ya samu aiki mai kyau kwarai da gaske.


4. Jaruman duka sun dace da labarin duba da irin rawar da kowanne ya taka a gurbinsa.

5. An samu kalamai na kwarewa a cikin fim din.


6. An nuna tasirin yin soyayyar gaskiya, domin tana yin tasiri sosai idan an gina ta a kan gaskiya.


7. An nuna tasirin samun mace ta gari domin dabi’un Salma kyawawa da kuma addinin da take da shi, su ne suka saka Naseer yake mata irin wannan so din.


Salma Bankwana




Kurakurai



1. Duk irin abinda Malam ya fadawa Naseer wanda har suka zama silar chanjawar sa,an fada masa irin su a baya amma mai yasa bai canja tun a lokutan ba har sai da aka zo gurun Malam sannan?


2. Lokacin da aka nuna Naseer yana tuna lokacin da yake fadawa Salma cewa yana so ya mallaka mata rabin dukiyarsa, ba a nuna wa mai kallo cewa za a shiga tunani ba kuma ba a nuna masa an dawo ba,


wanda hakan zai sa mai kallo ya yi zaton cewa ita ma wannan fitowar da aka nuna ana tunanin, ba wai tunanin bane.



3. Ya kamata a dan nuna rayuwar Minal da Naseer a gidansu bayan ya canja domin a nuna ta samu farin ciki ko yaya ne a gidanta.


4. Irin kalaman da Naseer yake amfani a kan kowa wajen bayyana irin son da ya ke yi wa Salma suna yin tsauri da yawa, duba da irin yadda yake magana da iyayensa da kuma sirikarsa akan Salma.


Karkarewa



Fim din “Salma Bankwana” fim ne da ya nuna irin yadda ake samun wasu sukan samu kansu a cikin matsananciyar soyayya da kuma irin halin da suke samun kansu a ciki.

An nuna tsantsar soyayya ta gaskiya a cikin fim din da kuma irin tasirin da take yi a cikin zuciyoyin maabotanta.

Sannan an nuna kwarewa sosai a cikin aikin fim din, domin kun an samu nasarori da yawa kuma ya kayatar da mai kallo.


Kuma ba a samu kurakurai da yawa a cikin fim din ba.




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






Source: Leadership Hausa

Friday, 25 January 2019

Karanta Kaji: Kuskure 3 da akai a cikin Film din MATAR MIJINA tare da Sharhin Fim din

Karanta Kaji: Kuskure 3 da akai a cikin Film din MATAR MIJINA tare da Sharhin Fim din

Suna: Matar Mijina
Tsara Labari: Nazir Alkanawi
Kamfani: S.H Ea: Abdul Amart
Umarni: Sadik N. Mafia


Matar Mijina


 Jarumai: Adam A. Zango. Aisha Aliyu Tsamiya, Fati Washa, Umar Gombe, Maryam Ceeter. Da sauran su.

 A farkon fim din an nuna Mutallab (Adam A. Zango) Yana bacci a cikin daki yayin da ‘ya’yan sa Yusra da Salim suka shiga suka tashe sa don yayi Karin kumallo. Bayan Mutallab ya tashi ya kimtsa ne ya fita wajen aikin sa, a sannan ne Suwaiba (Maryam Ceeter) tazo wajen Matar sa wadda ta kasance kawa ce a wajen Suwaiba. Suwaiba ta kasance tana nuna wa Jalila (Aisha Aliyu Tsamiya) aibun auren da tayi gami da ajiye karatun tan a jami’a ta zabi aure, yayin da Jalila take nuna mata hakan ba laifi bane saboda tana jin dadin irin soyayyar da mijin ta Mutallab yake nuna mata. Suwaiba tana kokarin zuga Jalila don kada ta cigaba das akin jiki da mijin ta Mutallab saboda gudun kada ya karo mata kishiya, amma Jalila tana nuna ko da hakan ta kasance ba laifi bane zata iya zama da kowacce mace wadda mijin ta zai aura. Wata rana Mutallab ya hadu da wata budurwa Samira (Fati Washa) wadda yaji ta birge shi kuma yana son auren ta, hakan ne yasa ya fara nuna wa Samira kudurin san a son auren sa kuma cikin dan lokaci kadan Samira ta amince da bukatar sa suka fara soyayya. Mutallab ya sanar da matar sa Jalila cewar yana soyayya da Samira sai hakan bai dameta bat a nuna masa goyon bayan ta akan auren da zai kara, har ya zamana cewa Mutallab yakan hada Jalila da Samira a waya su gaisa har ma suyi hira, sannan kuma yakan dauki ‘ya’yan sa Yusra da Salim ya kais u wajen Samira su gaisa. Tun Samira tana ja baya da Jalila hart a saki jiki da ita kuma ta fahimci cewa Jalila mace ce mai son zaman lafiya wadda kuma bata damu da soyayyar da ake yi da mijin taba. Wata rana Suwaiba kawar Jalila ta fito tare da kawayen ta daga cikin makaranta sai taga Mutallab ya budewa Samira motar sa yaja sun tafi, hakan ne ya kidima tat a garzayo ta sanar da kawarta Jalila abinda idanun ta suka gani, amma sai Jalila ta nuna rashin damuwar ta akan abin duk da Suwaiba ta nuna mata cewar yarinyar da ta gani tare da Mutallab bata da nutsuwa, amma yardar da Jalila tayi da mijin ta itace tasa ta gamsu da cewar ba zai ci amanar taba. Cikin dan lokaci kadan aka bikin Mutallab da Samira ya gabato, wanda hakan yasa Jalila ta soma gayyatar jama’a da sauran dangin ta har ma ta fidda kalar ankon da za su saka ranar biki. Hakan ne yasa wasu daga cikin ‘yan uwan ta suke kokarin zuga ta don kart a amince da hakan, yayin da wasu dangin nata kuma suka yi fushi da ita suke ganin kamar bata da hankali saboda tana murna don za’a yi mata kishiya. Ana ya gobe daurin aure sai Mutallab yayiwa Jalila sallama ya koma dakin hotel tare da abokan sa don su samu sakewa saboda baya son hayaniyar jama’a ‘yan biki. Kwatsam ana tsaka da shagalin biki sai ga Suwaiba kawar Jalila ta zo ta tabbatar mata da cewar Samira amaryar da za’a kawo mata tana dauke da cutar kanjamau, saboda abokin tan a makaranta wanda ake zargin tana mu’amula dashi an gane cewar yana dauke da wannan cutar. Jin hakan ne ya tashi hankalin Jalila ta kira mijin tat a nuna kada a daura wannan auren, amma sai Mutallab yayi zaton cewa kishi take da abin sai yaki saurarar ta. Sai dai kuma tun bayan auren Samira da Mutallab sai Jalila taja jikin ta gefe ta daina mu’amula da mijin ta, sannan kuma taki amincewa akan ya kusance ta saboda tana ganain cewa shima ya kamu da wannan cuta ta kanjamau. Hakan ne yasa ko ya kwana a kan gadon ta sai ta cire shimfidar gadon ta kona saboda kyankyamin sad a take yi. Ganin abinda ke faruwa ne yasa Mutallab ya soma nadamar karin auren da yayi saboda baya son abinda ke faruwa tsakanin sad a Jalila. Hakan ne yasa ya kira iyayen Jalila don su tuhume ta akan abubuwan da take yi masa, a sannan ne Jalila ta basu labarin abinda Suwaiba kawarta ta gaya mata, jin hakan ne kuma yasa Samira ta karyata cewar tana dauke da cutar kanjamau, wannan daalilin ne kuma yasa aka je asibiti akayi gwaji wanda ya tabbatar da cewa Samira da Mutallab bas u da wannan cuta ta kanjamau. Faruwar hakan c eta sa Jalila tayi nadama kuma ta roki gafarar mijin tad a ta Samira, wanda hakan yasa lokacin da Suwaiba ta sake zuwa gidan suka hadu gaba daya sukayi mata duka don kokarin kawo karshen munafurcin ta.

 Abubuwan Birgewa:

 Labarin ya tafi kai tsaye har ya adire bai karye ba.

Sunan fim din ya dace da labarin.

 Daraktan yayi kokari wajen tafiyar da labarin ta hanyar da ta dace, haka kuma yayi kokari wajen ganin cewa jaruman sun isar da sakon da ya dace, domin sun yi kokari wajen isar da sakon da ya dace. Hoto ya fita sosai, haka ma sauti ba laifi.

   Kurakurai:

 Bayan auren Mutallab (Adam A. Zango) da amaryar sa Samira (Fati Washa) me kallo ya gan su a wani falo na daban wanda bai yi kama da gidan sa da aka fara bayyanawa a fim din ba, sannan kuma yanayin da aka nuna kamar dama a gidan suke, shin canja gida suka yi? Idan kuma gidan bangare biyu ne to ya kamata tun a farko a bayyanawa me kallo, duk da dai yanayin yadda aka bayyana tsarin gidan a baya bai yi kama da cewar bangare biyu bane.

Lokacin da Jalila (Aisha Tsamiya) ta sami labarin cewa amaryar da mijin ta zai aura tana dauke da cutar kanjamau, me kallo yaga tana guje masa domin ko zama a inda yake bat a yi, wanda bayan ya kwanta akan shimfidar ta ma sai ta kona zanin gadon duk da shima zanin gadon bata taba shi da hannu ba har sai da ta sa leda ta rufe hannuwan nata, sannan ta dauka ta kona, shin Jalila ba ta san cewa ba a daaukar cutar kanjamau ta hanyar zaman takewa da masu cutar ba? Tun da an nuna cewar tana da ilimin addini da na zamani gami da fahimta, bai dace kuma a nuna cewar ta kona shimfidar da mijin ta ya kwanta ba don gudun kamuwa da cutar da take zargin sad a ita.

Lokacin da Jalila ta fara fadawa kawarta Suwaiba labarin cewa mijin ta zai kara aure, bayan tafiyar Suwaiba me kallo yaji muryar ta a waya sa’in da ta kira Jalila tana sanar da ita cewar yarinyar da mijin ta zai aura tana saka hotunan sa Instagram, haka zata zuba idanu bazata dau mataki ba, shin ya akayi Suwaiba ta gane cewar amaryar da za’a auro tana saka hotunan Mutallab a Instagram alhalin a sannan bat a san sunan tab a kuma bata ga ma hoton tab a balantana ayi zaton ko a sannan ta san ta? Ya dace a samar da dalili kafin faruwar hakan. 

Karkarewa:

Fim din ya fadakar domin an nuna illar daukar zugar kawaye tare da kuma illa ga budurwa mai sakin jiki da maza a waje wanda hakan yakan ja mata mugun zargi.

Haka kuma an nuna darasi ga wasu matan ta hanyar nuna musu ba laifi bane don mijin su zai kara aure. Wallahu a’alamu!



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Leadership Hausa


Wednesday, 9 January 2019

Karanta Kaji: Kuskure 3 da akai a cikin Film din RUDANI tare da Sharhin Fim din

Karanta Kaji: Kuskure 3 da akai a cikin Film din RUDANI tare da Sharhin Fim din

Suna: Rudani
Tsara Labari: Nasir S. Gwangwazo da Jamilu Ahmad Yakasai
Kamfani: Almubarak International Films Production Limited 
Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda Umarni: Ahmad A. Bifa 
Jarumai: Ali Nuhu, Jamilu Ahmad Yakasai, Ibrahim Mandawari, Aisha Aliyu Tsamiya, Rukayya Umar, Hajara Usman, Hadiza Muhammad da dai sauransu 



Sharhi: Hamza Gambo 

A farkon fim din an nuna Baba (Ibrahim Mandawari) ya shigo gidan sa iyalan sa sun tarbe shi suna yi masa murnar karin shekarar haihuwar sa. An nuna cewar yana zaune da matar sa (Hajara Usman) tare da ‘ya’yan sa Yaya Bashir (Ali Nuhu) da kanin sa Sadik (Jamilu Yakasai) wadanda suma suke tare da matayen su a cikin gidan. Duk da kasancewar shi Sadik suna samun rashin jituwa da matar sa Habiba (Aisha Aliyu Tsamiya) wadda tsananin kishin sa da take yi yasa har ta fara zargin sa akan yana bin matan banza, hakan yasa lokacin da zai tafi London taki amincewa da tafiyar sa saboda tana zargin cewa ba aiki zai tafi ba zai je ne kawai don ganawa da budurwar sa baturiya. Sun samu rashin jituwa a sanda mijin nata Sadik zai bar kasar duk da kasancewar yayi mata bayanin aikin da zai kaishi London din amma ta kasa fahimta. 

Bayan tafiyar Sadik London sai Habiba ta soma rashin lafiya, amma bayan zuwan ta asibiti sai aka tabbatar mata da cewar tana dauke da larurar cuta mai karya garkuwar jiki wato kanjamau. Jin hakan ne ya tashi hankalin Habiba ta kara tabbatar da zargin da take yiwa mijinta na cewar yana neman matan banza. Bayan ta dawo gida ta sanar da iyayen sa sai aka kira sa aka bukaci yaje asibiti acan London din don a auna jininsa don a gane ko yana dauke da cutar shima, amma sai Sadik yaki amincewa da hakan har a karshe mahaifin sa ya bukaci yabar aikin da yake ya dawo gida domin a sannan rigima ce ta afku iyayen Habiba suna neman mika maganar zuwa kotu don a bi wa ‘yar su hakkin ta. Hakan ne yasa Sadik ya dawo gida najeriya aka je wajen likita ya duba jinin sa, sai dai bisa mamaki da aka duba sai aka gane cewar babu cutar kanjamau din a jikin sa. Hakan ne ya sake haifar da hargitsi domin iyayen Habiba sun ki yarda da binciken da akayi saboda suna zargin cewa a jikin sa ne Habiba ta dauki cutar kanjamau. A karshe dai dangin Habiba suka kai Sadik asibitin da suke ganin za’a fada musu gaskiya, sai dai kuma acan din ma sakamakon iri daya ne bayanai sun tabbatar da cewar Sadik bashi da cutar kanjamau, hakan ne yasa zargin kowa ya koma kan Habiba, domin ta jima da guduwa gidan iyayen ta, acan din ne mahaifiyar ta (Hadiza Muhammad) ta rutsa ta da tambayar inda ta kwaso cutar kanjamau, sai dai kuma Habiba ta gaza bata amsa. Ana tsaka da haka ne Sadik yaje gidan su Habiba ya fada mata gaskiyar cewa baya mu’amula da matan banza kuma budurwar sa ta kasar waje sun jima da rabuwa domin saurayin ta yayi masa gargadin kada ya sake ganin su tare. Bayan Sadik ya gama bawa Habiba labari ne sai ya bukaci da tayi dai tunani don a gane inda ta samu larurar kanjamau, ya bata misalin cewar ba sai ta hanyar jima’i ake daukar cutar ba, akan iya samun ta ta hanyar yankan farce ko kitso ko wani dalili daban na haduwar jini. Jin hakan ne yasa Habiba ta bashi labarin cewa wata rana kawarta tazo gidan ta tun tana amarya ta bata shawara akan yin tsarin iyali don kada ta haihu da wuri, sai dai kuma bayan zuwan su asibitin sai likita ya tabbatar musu da cewar sirinji daya ne ya rage wanda za’a yi musu allura, sai dai ya fita ya siyo wani, amma sai duk su Habiba suka nuna sauri suke yayin da kawar ta ta bukaci cewar tunda su kawaye ne a yi musu da guda dayar kuma a fara yi mata sannan a yiwa Habiba, hakan kuwa akayi nan aka fara yi mata allurar sannan aka yiwa Habiba. Bayan Habiba ta gama ba shi labari sai Sadik yaje neman kawar Habiba a gidan ta amma sai ya samu labarin cewa ita da mijin ta sun rasu kuma ana zargin cutar kanjamau ce ta kashe su. 

Wannan dalilin ne yasa aka gane inda Habiba ta samu larurar cutar kanjamau, kuma Sadik yayi alkawarin zai kai ta London don nema mata magani kuma idan ta warke yayi alkawarin zai mayar da ita dakin sa.

 Abubuwan Birgewa

1- Labarin ya fadakar kuma ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba, sannan kuma an yi kokarin saka abubuwan da suka rike mai kallo har zuwa karshen labarin. 

2- An yi kokari sosai wajen samar da muhallin da su ka dace da labarin wato (locations)

 3- Daraktan ya yi kokari sosai wajen tafiyar da labarin ta hanyar da ta dace, haka yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman sun yi kokari musamman Habiba wato Aisha Tsamiya.

 4- Sauti ya fita radau, haka ma hoton fim din ya fita radau domin an yi kokari wajen nuna salon daukar hoton fim din.

 Kurakurai

1- An nuna cewar tun Habiba ta na amarya kawarta ta raka ta wajen yin allurar tsarin iyali (wato family planning) wanda dalilin hakan ne ya sa a ka samu matsalar da Habiba ta kamu da larurar cutar kanjamau, sai dai kuma duk da a na daukar cutar ta hanyar jima’ai kuma an nuna cewar Sadik ya na tare da matar tasa har na tsahon lokaci, amma shi bai kamu da wannan larurar ba, ya dace a nuna wa mai kallo dalilin da ya sa Sadik bai kamu da cutar ta kanjamau ba.

 2- Lokacin da Sadik ya bawa Habiba labarin budurwarsa wadda su ka yi soyayya a kasar waje, me kallo ya ga Sadik ya dauki budurwar tasa a can kasar London ya kai ta gidan wata dattijuwa wadda ya kira da Mom. Shin wace ce wannan dattijuwar wadda Sadik ya kai budurwarsa gidan ta a London? Tun da an nuna mahaifiyarsa a Najeriya (wato Hajara Usman). To, ya dace a yiwa me kallo bayanin matsayin dattijuwar nan a wajen sa ko da ta hanyar nuna cewar ‘yar uwar mahaifin sa ko mahaifiyar sa ce

 3- Shin ina mahaifin Habiba? Har fim din ya kare mai kallo bai gan shi ba kuma ko a baki ba a ambace shi ba, duk da kasancewar akwai matsaloli da yawa na fannin auren Habiba da suka taso wanda ya kamata ace an ga mahaifin ta a cikin maganar, amma ba a gan shi ba sai wani Barrister da aka nuna a matsayin kawun su. Idan ma mutuwa mahaifin ta yayi to ya dace ko a baki ne a fada. 

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa. An nuna illar bin shawarar kawaye, sannan kuma an yi kokari wajen isar da wani muhimmin sako wanda al’umma zasu amfana da shi, domin fim din ya koyar da wani darasi wanda jama’a zasu kiyaye rayuwar su da lafiyarsu. 

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


Source: LEADERSHIP A YAU



Wednesday, 31 October 2018

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai a cikin Film ɗin KAUYAWA 2018  tare da Sharhin Fim ɗin

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai a cikin Film ɗin KAUYAWA 2018 tare da Sharhin Fim ɗin

Suna: Kauyawa 2018
Tsara Labari: Maje Elhajj Hotoro
Kamfani: Mai Shadda Inbestment da Alrahuz Film Production
Shiryawa: Ali Worth Me
Umarni: Sadik N. Mafiya


Jarumai: Aminu Shariff Momo, Falalu A. Dorayi, Sulaiman Bosho, Rabi’u Rikadawa, Abubakar Dan Auta, Baballe Hayatu, Musa Mai Sana’a, Rabi’u Daushe, Jamila Umar Nagudu, Fatima Kokobi, Fati Abubakar Shu’uma, Iliyasu Abdulmumini Tantiri, Alasan Kwalle, Aliyu Rara, Tijjani Asase. Da sauran su.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna (Fatima Kokobi) ta fito tsakar gida sai ta tarar da akuyar ta a daure, kuma an saka kwado an kulle da makulli, kasan cewar ta kurma sai ta tambayi mahaifiyar ta (Binta Kofar Soro) don jin wanda ya daure mata akuya, amma itama mahaifiyar ta wadda itama kurmar ce, sai ta nuna bata san wanda ya daure akuyar ba, adaidai sannan ne mahaifin yarinyar wato Subullu (Abubakar Dan Auta) ya fito daga cikin bandaki gami da nuna mata ya san wanda ya daure akuyar, a sannan suka dunguma suka nufi wajen Haladu (Falalu A. Doray) wanda ya nuna shi ya daure akuyar saboda idan an saketa tana yawo a gari tana yiwa jama’a barna, anan dai Subullu ya nuna lallai sai an saki akuyar don farantawa ‘yar ta sa rai.
Daga nan ne kuma aka nuna Huwaila (Fati Shu’uma) t agama kwalliya a cikin gidan su za ta dauki tallan goro da sigari, a sannan yayan ta makaho ( Sulaiman Bosho) ya shigo suka soma hira shi da mahaifiyar sa Subulluwa (Jamila Nagudu) suka nuna kushen sana’ar da Huwaila take yi saboda karuwai ne ke tallan goro da sigari, hakan yasa Huwaila da yayan ta makaho (Sulaiman Bosho) suka fara sa’insa, ganin haka ne yasa yayan nata ya dauki kyautar kudi ya bata don su daina rigimar saboda sanin cewa akan kudi za ta iya yin komai. Wata rana (Aminu Shariff Momo) yayi sallama da matar sa ya fita wajen aiki, sai wani barawo (Musa Mai Sana’a) ya nufo gidan sa don yin sata, zuwan sa ne sai ya tarar da kwarto yaje kwartanci wajen matar gidan, barawon ya labe jin tattaunawar da kwarton suke yi da matar gidan sai ga mijin ta ya dawo gida ya hango sa a jikin Katanga, hakan ne yasa ya nufo sa don ya kama sa, saidai kafin ya iso wajen ne kurma ‘yar subullu ta biyo akuyar ta cikin gidan da gudu da nufin kama ta, jin guje-gujen akuyar da kurmar ne yasa kwarto (Rabi’u Daushe) suka fito daga cikin daki a guje shi da matar gidan, wanda hakan kuma sai ya firgita barawon suka fice daga gidan a sanda me gidan (Aminu Sharif) yabi bayan su da nufin ya kama su gaba daya. A wannan lokacin ne kuma me unguwa (Aliyu Rara) ya tsiro da dokar kara haraji a cikin kauyen, yayin da ‘yan fadar sa su (Tijjani Asase) suka goyi da bayan sa, sannan suka dauke sa a kafadar su kasan cewar sa guntu suka nufi cikin gari das hi da nufin sanar da dokar sat a karin haraji, a sannan ne Haladu (Falalu A. Dorayi) ya taho da gudu akan abin hawa ya buge me unguwa ya baje a kasa, ganin hakan ne yasa ‘yan fadar sa suka bi bayan Haladu da nufin kama sa, suna cikin gudu ne Haladu ya hadadu da kwarto da barawo (Musa Mai Sana’a) da (Rabi’u Daushe) wadanda (Aminu Shariff) ya biyo su saboda sun shiga gidan sa yin kwartanci, haduwar su ne yasa suka gudu gaba daya suka buya a cikin wata bukka har sai bayan wadanda suka biyo su sun tafi sannan suka fito suka sake guduwa, a sannan ne ‘yan fadar me unguwa suka kama Haladu suka nufi wajen me unguwa da su. Yayin da su kuma barawo da kwarton da (Aminu Sharif) ya biyo suka buge su Jatau (Rabi’u Rikadawa) wanda ya zauna suke caca da abokan sa.
Ganin an buge su ne suka tsorata duk suka arce a guje, duk suka nufi gidan kwarto (Rabi’u Daushe) shigar su cikin gidan ne har suka buge dan (Rabi’u Daushe) yaron ya karye, yayin da (Aminu Shariff) ya kama su, kuma iyalan kwarton bayan sun ji abinda mijin su ya aikata suka yi tur da halin sa. A bangaren Jatau (Rabi’u Rikadawa) sai ya shawarci matar sad a nufin su dauki da gidan su da suke zaune a ciki gami da gidan yayan ta Subullu (Abubakar dan Auta) da nufin a su saka gidajen a caca don su cinye ainahin gidan abokan sa wanda su ma za su saka gidajen a caca. Jin hakan sai ta amince kuma shima yayan ta Subullu ya amince da hakan suka dauki gidajen suka saka a cikin caca.

Abubuwan Birgewa:

1. Fim din ya nishadantar sosai gami da rike hankalin me kallo don son sanin abinda zai faru a gaba.

2. Daraktan yayi kokari wajen nuna kwarewa akan aikin sa, kuma yayi kokarin ganin jaruman sun yi abinda ya dace da labarin, kuma jaruman sun yi kokari wajen taka rawar da ta dace.

3. An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin.

4. Sauti ya fita radau, camera ma ba laifi.

Kurakurai:

1. Lokacin da Huwaila (Fati Shu’uma) ta taho dauki da farantin siyar da sigari, a sanda za ta hadu da ‘yar gidan jitandara sanda za ta bada mata yaji, Camera tayi rawa sosai a farkon bude scene din sanda Huwaila ke tafe da farantin talla a hannun ta.

2. Lokacin da kurma ta biyo akuyar ta cikin gidan Jatau dan caca, a sanda ta tunkude Subulluwa (Jamila Nagudu) har ta fadi kasa kurma kuma ta fita, daga nan aka dauke scene din aka cigaba da labari sai bayan tsahon lokaci aka sake dawowa scene din aka nuna Subullu a kasa inda aka jefar da ita tana kokarin tashi tsaye, tsahon lokacin da aka dauke scene din a farko yayi tsahon da bai kamata ace sai a sannan za’a sake nuno wajen ba, domin yin hakan tamkar dawo da mai kallo baya ne akan abin da yayi zaton cewa ya jima da wucewa.

3. Me kallo yaga an nuna wasu ‘yan sanda sun kama wani mai mashin wanda ba shi da takardun mashin, a sannan ne aka ga Haladu ya zo sanye da kayan sojoji yana yi musu shirme. Shin ‘yan sandan ba sa fahimtar mutum me ilimi ne? Tun da an nuna Haladu mutum ne mara ilimi wanda yake yiwa jami’an tsaron shirme, ya dace a nuna mamaki a fuskokin jami’an tsaron na ganin soja haka wanda bai san kalma ta turanci ko guda daya ba.

4. Bayan Haladu ya buge me unguwa (Aliyu Rara) har ‘yan fadar sa su (Tijjani Asase) suka bi sa suka kama sa. Shin bayan an kama sa din wane hukunci aka yi masa? Tun da an nuna yadda ‘yan fadar suka shiga lungu da sako don su kamo Haladu, to ya dace a nuna irin hukuncin da suka yi masa.

5. Me kallo ya ga Haladu ya dauki wasu kayan sojoji a jikin Katanga ya saka a jikin say a fita yin barazana. Shin kayan sojojin na wanene? Tun da ba’a nuna soja ko sau daya a cikin kauyen ba, to ya dace a samar da dalilin ta yadda aka samar da kayan.

6. An nuna Jatau (Rabi’u Rikadawa) tare da abokan sa su Jitandara dasu Subullu duk sun saka gidajen su a caca, sai dai kuma har fim din ya kare ba’a nuna karshen cacar don bayyana wanda ya ci gasar ba.

Karkarewa:

Fim din ya nishadantar kuma ya ja hankalin masu kallo, sai dai kuma babu wani muhimmin darasi wanda kai tsaye mai kallo zai karu dashi, domin an nuna abubuwa na rashin tarbiyya wadan da jama’a suke aikatawa, amma ba’a bayyana hanyoyin gyaran su ba, sannan kuma labarin bai dire har karshe ba, domin akwai abubuwan da ba a kammala tare da karkare su ba. Wallahu a’alamu!

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai a cikin Film ɗin WATA RUGA tare da Sharhin Fim ɗin

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Leadership A Yau

Monday, 24 September 2018

Karanta Kaji: Kuskure 5  da akai a cikin Film ɗin MATAR MAMMAN tare da Sharhin Fim ɗin

Karanta Kaji: Kuskure 5 da akai a cikin Film ɗin MATAR MAMMAN tare da Sharhin Fim ɗin

Suna: Matar Mamman
Tsara Labari: Nasir S. Gwangwazo
Kamfani: Asnanic Mobie Tone
Shiryawa: Usman Mu’azu
Umarni: Aminu Saira

Jarumai: Ali Nuhu, Hadiza Aliyu Gabon, Hafsat Idris, Asiya Barde, da sauran su.



Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din me kallo ya ga Uwale (Asiya Barde) ta na bacci wanda a cikin barcin ta tayi mafarkin wata gawa wadda jama’a suka dauke ta suka kai ta makabarta, bayan Uwale ta farka daga bacci a firgice sai mijinta Magaji (Isa A. Isa) yake tuhumar ta akan don me zata dinga mugun mafarki don kawai yace zai karo mata kishiya? Daga baya Magaji ya soma kokarin kwantar was da Uwale hankali a bisa dalilin sa na son kara aure amma bata saurare sa ba saboda mafarkin da tayi na gawar wata mace shi yafi tsaya mata a zuciya, hakan yasa ta tafi wajen malami ta fada masa mafarkin da tayi gami da son sanin fassarar mafarkin ta, amma sai malamin ya nuna mata cewar bazai fassara mata mafarkin ba har sai taje ta nemo bayani akan gawar matar da ta gani a mafarkin tunda ta nuna alamun cewar tasan wani makusancin gawar da ta gani. Haka kuwa Uwale ta tafi wajen Asiya (Hafsat Idris) don son sanin wacece matar da taga gawar ta a mafarki? A nan Asiya ta fara bawa Uwale labarin Mariya wadda itace Uwale ta gani a mafarkin ta, kuma Mariya (Hadiza Gabon)kawar Asiya ce wadda suka taso tare domin Asiya ce tayi mata siyan baki a lokacin auren Mariyar da mijinta Mamman (Ali Nuhu) bayan auren Mariya da Mamman sai Asiya ta cigaba da zuwa gidan Mariya a duk sanda take da lokacin hakan, kuma akwai mutunta juna a tsakanin Asiya da Mamman saboda akwai lokutan da idan tazo gidan Mariya yakan bukaci Asiya da cewar ta jira shi ya dawo daga aiki don ya sauke ta a gidan iyayen ta, akwai lokacin da Mamman ya dauko Asiya a motar sa don mayar da ita gida sai yake tambayar ta shin bata da masu son auren ta ne? Sai Asiya ta nuna masa cewar har a sannan bata samu wanda suka daidai ta ba shi yasa ma ta koma makaranta don cigaba da karatu, jin hakan ne ya bawa Mamman dama bayan ya koma gida sai ya fara turo mata sakonnin soyayya a shafin zumunta na ‘Whats’App’ bayan Asiya taga an turo mata sakonnin kulawa a wayar ta kuma da lambar da bata sani ba sai tayi mamaki gami da son sanin wanda ya turo mata sakon na kalaman soyayya, amma a cikin hirar sai Mamman ya nuna mata cewar zasu hadu da ita don ta gane wanda yake son ta, hakan kuwa akayi Asiya tana makarantar su sai taga Mamman yazo wajen ta a lokacin da tayi zaton ganin wanda yake turo mata kalaman soyayya, hakan yasa ta kasa yarda da cewar shine me turo mata sakonnin soyayya a waya sai ta fara zaton ko abokin Mamman din ne yake son ta, amma a nan take a wajen sai Mamman ya nuna mata cewar shi yake turo mata sako kuma yana son ta da aure, hakan ya bawa Asiya mamaki saboda ganin cewa ita kawar matar sa Mariya ce. Don haka sai Asiya ra roki Mamman akan ya canja shawara don bazai samu abinda yake nema a wajen ta ba. Da daddare kuwa Mamman ya shirya cikin kaya masu kyau ya fesa turare zai fita, amma da Mariya taga yayi wannan shirin sai ta tambaye sa inda zai je amma sai Mamman ya nuna wajen mahaifin sa zai je, jin hakan sai bai gamsar da Mariya ba sai ta fara zargin ko ya shirya yi mata kanwa ne saboda tun kafin ya aure ta yasha fada mata cewar bashi da ra’ayin zama da mace daya, amma sai Mamman ya nuna mata sam ba haka bane shi ziyara zai je. Bayan Mamman yaje wajen Asiya sai ta fito ta gargade sa akan kada ta sake ganin yazo gidan iyayen ta saboda bazata iya auren sa ba domin tana ganin yin hakan kamar zataci amanar kawar ta Mariya ne. Bayan Mamman ya koma gida sai ya cigaba da kiran wayar Asiya yana yi mata magiya akan ta so shi amma sai ta nuna sam bata amince ba. Cikin dare Mamman yana bacci sai Mariya taji shigowar sako a wayar sa, bayan ta duba ne sai ta fahimci cewa yana son ya auri kawarta Asiya, bayan ta fuskanci hakan ne sai ta soma bijiro masa da maganar tana so ya kara aure, amma sai Mamman ya nuna sam shi baya ra’ayin hakan. Asiya kuwa sai ta daina zuwa gidan Mariya sai bayan an dau tsawon wani lokaci sannan tazo, hakan ya kara saka Mariya zargi akan cewar tabbas akwai alakar dake tsakanin ita Asiya da Mamman, hakan yasa Mariya ta roki Mamman akan tana so ya auri Asiya, amma sai yayi fushi ya nuna cewar tana zargin sa da kawar ta ne, Asiya da Maryam suna cin abinci sai Mariya taji Asiya tana yabon halayen Mamman gami da nuna bai kamata ta dinga samun sa6ani dashi ba, hakan yasa Mariya ta yi amfani da wannan damar wajen bijirowa Asiya da batun tana so ta auri mijinta Mamman, amma sai Asiya taki amincewa da hakan har ma ta soma fushi da Mariya ta daina zuwa gidan, hakan yasa Mariya taje gidan iyayen Asiya ta cigaba da rokon ta akan ta auri mijinta Mamman, amma Asiya duk da hakan bata amince ba, sai dai kuma abin ya dame ta don ta rasa yadda zatayi, musamman da taga Mariya tana bibiyar ta a ko ina har a cikin makaranta don ta auri mijinta Mamman. Mariya ta yi nasarar shawo kan Mamman ya amince zai auri Asiya saboda dama can yana son ta kuma akwai lokacin da wani abokin sa ya taba bashi shawara akan tunda matar sa Mariya ta amince masa da ya karo auren wadda yake so ya dace ya amince, amma a sannan din ma dai Mamman yana nunawa abokin nasa cewar yasan kawaici ne matar sa take masa domin tana son duk abin da yake so koda kuwa ita bata son abin. Bayan Mamman ya amice da bukatar Mariya ta son ya auri kawarta amma sai ya nuna ai ba lallai Asiya ta amince da auren ba, nan ma dai Mariya ta nuna kada ya damu zata shawo kan matsalar. Haka kuwa aka yi, Mariya ta matsawa Asiya akan lallai tana so ta auri mijinta Mamman domin ko bai aure ta ba zai auro wata macen tunda yana da ra’ayin zama da mata biyu, hujjojin da Mariya ta dinga kawowa Asiya ne yasa har Asiya ta amince zata auri Mamman. Cikin dan lokaci kadan aka fara shirye shiryen aure har ma dangin Mamman suna mamakin halayyar Mariya saboda ganin da ita ake ta shagulgulan bikin auren mijinta da Asiya, a wannan lokacin ne kannen Mariya suka rutsa Asiya a makaranta suka ci mata mutunci har da marin ta saboda zata auri mijin yayar su Mariya. Wannan dalilin ne yasa mahaifiyar Asiya da kuma ita Asiyar suka janye maganar hada auren Mamman da Asiya, amma sai Mariya ta kai karar kannen nata wajen iyayen su wanda kuma su ma iyayen basu goyi bayan abinda yaran suka yi ba, har ma mahaifin su Mariya ya nuna bazai yafewa kannen Mariyar ba har sai sun je sun roki gafarar Asiya, haka kuwa aka yi sai da suka nemi yafiyar Asiya kuma Mariya ta sa baki har abin ya wuce kuma Asiya ta amince da zata auri Mamman. Bayan auren Asiya da Mamman Mariya ce ta karbi kudin siyan baki a wajen mijin su Mamman sannan ta yi musu nasiha gaba daya na zama lafiya. Bayan gama hakan ne ta shiga daki tana kuka saboda kishin mijinta da ya dame ta amma son abinda yake so ne da bin umarnin Allah hakan ya hana ta bayyana kishin ta a sarari. Ba’a jima da yin auren Asiya da Mamman ba sai abubuwa suka soma dagule masa, ya fara yin asara, kayan sa da aka turo daga wani garin ma’aikata suka rike, ba shi ya fara hawa kan sa. Nan fa dangin Mamman suka fara kananan maganganu akan ya auro mace me kashin tsiya ga komai nasa ya fara karewa, jin hakan bai sa Mamman ya gamsu da cewar matsalar daga wajen matar sa bane, haka itama Mariya ta kara nuna masa muhimmancin yarda da kaddara. Ana cikin wannan matsalar ne Asiya ta samu juna biyu wanda hakan yasa duk sukayi ta farin ciki, musamman Mariya tafi kowa farin ciki saboda tana ganin Asiya zata haifawa Mamman dan da ita bata haifa masa ba, Asiya tana mamakin saukin kai irin na Mariya gami da rashin nuna kishi akan juna biyun da ita Asiyar ta samu, ana cikin murnar ne aka gane cewa itama Mariya tana dauke da juna biyu, nan fa murnar su ta karu saboda suna ganin sun samu abinda kudi bazai basu ba, wato haihuwa. Bayan dan wani lokaci Mariya da Asiya su ka haifi ‘ya’ya mata wadanda duk aka saka musu sunan Mariya.

Lokacin da Asiya fa gama bawa Uwale labarin Matar Mamman wato Mariya, sai Uwale taji tana nadamar abinda take shirin yi na hana mijin ta kara aure, hakan yasa bayan ta koma gida ta roki gafarar mijinta gami da nuna cewar ta amince ya kara aure, amma sai mijinta ya nuna dama zai kara aure ne saboda munanan halayen ta, amma yanzu ya fuskanci tayi nadamar sa zata iya gyara halin ta don haka shima ya fasa kara wani auren.

Abubuwan Birgewa:

1- Marubucin yayi kokari matuka wajen gina labarin, domin labarin fim din ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba.

2- (Matar Mamman) Sunan fim din ya dace sosai da labarin.

3- Labarin ya fadakar domin yana dauke da mafita kan hujjoji masu karfi wadanda suke damun al’ummar mu, musamman ma ga mata.

3- Fim din ya rike me kallo wajen son ganin abinda zai faru a gaba, sannan kuma fim din ya ta6a zuciyar me kallo kuma mutum zai ga kamar rayuwar zahiri ta wadansu mutanen yake kallo.

4- Daraktan fim din yayi kokari wajen tafiyar da labarin, haka kuma me daukar Camera tayi kokari ta hanyar nuna salon daukar hoto me kyau. Daga hoto har sauti sun fita radau.

5- Kalaman jaruman wato (Dialogue) sun yi dadi gami da gamsar wa.

6- An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin. Wato (Location)

7- Jaruman sun yi kokari matuka wajen samar da yanayin da ya dace.

Kurakurai:

1- Shin wace alaka ce a tsakanin Asiya da Uwale? Me kallo yaga Uwale taje wajen Asiya an bata labarin Matar Mamman, amma ba’a nuna dangantakar dake tsakanin Asiya da Uwalen ba. Tunda ba’a nuna Uwale a cikin jerin kawayen Asiya ba, ya dace ayi bayanin alakar su ko da ta hanyar ‘yan uwan taka ne.

2- Shin wanene mahaifin Asiya ne? Har fim din ya kare me kallo bai ji ko a baki an ambaci mahaifin ta ba, musamman a sanda maganar auren ta da Mamman ta taso da kuma sanda aka ce an fasa auren, ya dace aji an ambaci ko wani Kawun ta ne, idan ma rasuwa mahaifin nata yayi, ya kamata ko a baki ne a fada.

3- Abin daukar sauti ya leko a lokacin da Mariya da Asiya ke cin abinci a falo, sa’in da Mariya ta fara bijirowa da Mamman batun ya auri Asiya a sanda yayi fushi ya fice daga gidan.

4- An samu discontinuity a lokacin da Mamman ya shirya a karon farko da daddare don soma zuwa hira wajen Asiya, an nuna bakar doguwar riga a jikin Mariya a sanda ta shigo daki take tambayar sa inda zai je, amma bayan ya dawo sai aka ganta sanye da koriyar doguwar rigar atamfa a falo, bayan kuma tabi Mamman cikin daki sai aka sake ganin ta da bakar doguwar rigar farko.

5- Lokacin da yayar Mamman wato Yaya Fati da kanwar ta suka zo gidan Mamman bayan sun dawo daga wajen kai kayan lefe, me kallo yaji sanda Yaya Fati take cewa, tana mamakin ganin yadda Mariya ta zage dantse wajen kai kayan lefe gidan su kishiyar ta. Amma a karshen hirar sai akaji kanwar Mamman tana tambayar cewa yaushe za’a kai kayan lefen? A cikin hirar gaba daya me kallo ya fahimci an kai kayan lefen saboda ko nuna su ma ba’a yi ba, don haka bai dace a karshen hirar a ji kanwar Mamman ta tambayi shin yaushe za’a kai kayan lefen ba.

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma yayi ma’ana sosai gami da gamsar da mai kallo, labarin yazo da kyakkyawan salon da zai iya yin tasiri wajen dakile mugun kishi ko mummunan zato daga wajen mata da sauran jama’a. Wallahu a’alamu!



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode

Source: Leadership A Yau