Saturday 9 November 2019

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Kowanne Miji ya Kula dasu Idan Zai Yi Magana da Matar Sa

Tura Wannan Zuwa
Masu iya magana dai na cewa ‘ Magana zarar bunu ce’, a don haka duk kalaman da mutum zai furta kan iya zama sanadiyar gyara ko wargaza zamantakewarsa da iyalinsa.

Nishadin Ma'aurata


 Ga jerin wasu abubuwa goma da ya kamata duk wani miji ya guji furtasu ga matarsa, saboda mata dan karamin abu kan iya sanya su cikin damuwa:

1. Ya rage naki Mafi yawan mata basu son jin wannan Kalmar. A wasu lokutan zai kasance kana hasashen yin wani abu sai matarka ta baka shawara ko dai kaza zamu yi ne, fadin ya rage naki na matukar bata wa mata rai.

2. Ban iya tuna lokacin da na fadi hakan Haba yallabai, ya zaka fadi magana kuma kace ka mance lokacin da ka fade ta.

Yana da kyau mu tuna mata na da kokarin rike abu a kwakwalwarsu, fadin wannan kalamin kan iya haddasa fitina tsakanin mata da miji.

 3. Ban sani ba Wasu lokutan ma tambaya kadan mata za tayi wa mijinta, kawai amsar da zai furta mata ita ce ‘ban sani ba’.

 A rika tauna magana kan a fade ta domin gyaran zaman takewa.

4. Ba komai Wasu mazan na da dabi’ar yin biris da matansu, da kuma matar ta tambaya ko lafiya sai ka ji sun ce ba komai.

5. Zanyi amma ba yanzu ba Ba yanzu ba, to sai yaushe? Ba yanzu ba kan iya daukar tsawon lokaci marasa adadi. Ina laifin ka sa lokaci kamar mako guda ko wata guda haka.

6. Meye kikeyi tun safe Wannan kalamin na bakanta ran mata, miji zai fita wurin aiki ya bar mace da dawainiyar yara sai kaji ya dawo abu kadan sai ya fara fadin meye kikeyi tun wayewar gari.

7. Bace min daga gani Idan rai ya baci hankali ke nemo shi, don kun samu rashin jituwa da matarka bai kamata ka furta mata wannan kalma ba wadda aka tsari da tsawa ake yenta.

8. Kin fiye yin…. ko baki taba yin abu kaza ba Korafi baida dadi musamman ga mace. Ai maimakon ka zauna kana kusheta mai zai hana kayi amfani da dubara cikin zance sai ka sako matsala daya ba tare da ka bata mata rai ba.

9. Ai duk laifinki ne Ko da kuwa laifin nata ne da gaske, kamata yayi ka samu wata hanyar lurar da ita domin ta gyara ko dan gaba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ILLOLIN ZAMA DA MATAR AURE GUDA DAYA

KARANTA YADDA RAYUWAR AURE TA LALACE A WANNAN ZAMANIN DA MUKE CIKI

KARANTA SHAWARA ZUWA GA MA'AURATA DA MASU NIYYAR YIN AURE

10. Kin fiye kiba Ka guji furta duk wata Kalmar da ka san za ta bata ran matarka.

Ko da kuwa tana da kibar ai ba abinda ya kamata ka rika hantarar ta bane a kai.

Allaj yasa Mu da Ce Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Source: Legit Hausa
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user