Saturday 7 December 2019

KARANTA DOKOKIN DA SUKA SHAFI HARKOKIN KUDI DA HARAJI

Tura Wannan Zuwa
Mutane suna tambaya ta dangane da abubuwan da sababbin dokokin kudi da majalisar kasa ta amince. Ni dai ban san komai ba akan tsarin dokoki amma ina da ilmin lissafin haraji daidai gwargwado.

Harkokin Kudi da Haraji

Marubuci: Danladi Haruna

Yau a Abuja na yi sa'ar gamuwa da wani masanin doka kuma kwararre akan harkar  haraji ya yi min warwarar yadda dokar take da kuma yadda za ta shafi hanyoyin tattara haraji.

Da wannan warwarar na gane ashe 'yan jarida ne ke zuzuta labarin shifcin gizo na cewar za a hana mutane aiki da akawun dinsu na banki idan ba su nuna katin shaidar haraji ba. Wannan abin iyakacin kamfanoni ya shafa, kuma sun jima da fara aiwatar da haka, sai dai yanzu ne aka maida shi doka.

Bayan haka dokar ma dai gata ta yi wa mutane da kamfanoni ta wasu wuraren. Domin kuwa yanzu sai cinikin mutum ya kai na sama da miliyan 100 za a caje shi harajin 30% ba kamar yadda ake yi yanzu ba inda komai kankantar ciniki, dole kamfani ya biya harajin 30% ma ribar da ya samu.

Kamfanonin Inshora ma sun samu tagomashi a karkashin wannan dokar, yanzu suna iya samun yafiya daga asarar da suka yi har illa masha Allahu maimakon yanzu da aka takaita musu zuwa shekara 4.

Haka kuma an yi rangwame sosai akan harajin da ake cirewa daga  ribar da kamfani ya raba. A da idan kamfani ya rabawa masu hannun jari kudin da ya wuce ribar da ya samu a shekara, to za a caje shi haraji na abin da ya raba din, yanzu kuwa an yafe haka. Har ila yau an soke cewar dole sai minista ya amince da kudin alawus na manyan daraktoci kafin kamfani ya nemi afuwar biyan haraji kan alawus din.

Haka kuma an saka ragi na 1% zuwa 2% ga wanda ya biya haraji akan kari.

Gwamnati za ta kara samun kudi inda dokar za ta ba ta ikon karɓar haraji daga kamfanonin da ba 'yan asalin kasa amma suna aiki sosai a kasar (Non - Resident Companies NRCs) musamman wadanda ke hada hadar tattalin arziki sosai a cikin kasar walau a zahiri ko a intanet. An ba wa ministan Kudi ikon ya zakulo irin wadannan kamfanoni domin su biya haraji.

Daidai kun mutane da suke biyan haraji kuwa, an yi gyara akan rangwamen da ake musu na dubu 10 akan 'ya'yansu. Kodayake ba a fito da bayanin dalla dalla ba, amma da alama za a fi maida hankali akan ragin da ake kira Consolidate Relief Allowance. Idan an yi haka, to jama'a da dama za su ji saukin biyan kudin haraji.

Inda dokar ke da aibu shi ne wajen karin kudin VAT zuwa 7.5%. Sai dai anan ma an cire wasu abubuwa da dama wadanda suka shafi talaka musamman kayan abinci da abubuwan sha.

Sannan an yi izni ga bankuna da su karbi lambar biyan haraji na kamfanoni mallakin mutum. Watau idan mutum yana da asusun kamfani, tilas sai ya bada lambar TIN dinsa kafin ya ci gaba da sarrafa akawun din kamfanin. Wannan tsarin kuwa tun da jimawa bankuna na aiwatar da shi bisa umarnin gwamnati.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa??

KARANTA BAYANI AKAN AIKIN MAMBILA HYDROPOWER PLANT DAKE JIHAR TARABA

KARANTA ABINDA YA KAMATA KU YI DA ZARAN ANYI GARKUWA DA 'YAN UWAN KU

Samun lambar TIN tana da amfani sosai wajen gudanar da wasu al'amura a kasar nan. Idan na samu zarafi zan zo da bayanin amfanin ta.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user