Showing posts sorted by date for query Abdul'aziz Hamza KKR. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query Abdul'aziz Hamza KKR. Sort by relevance Show all posts

Monday, 7 September 2026

Gajerun Sakonnin Barka Da Sabon Wata Ga Masoyiya

Gajerun Sakonnin Barka Da Sabon Wata Ga Masoyiya

Amintaccen abin alfarmar rubuta saƙona yana neman izinin zama dirshan wajen gabatar da rubutattun saƙonnin da ke cikin zuciyata. Kyakkyawar rana da lokacin da na samu sun wadaci zuciyata wajen wakitar gangar jikina domin isar da saƙon gaisuwar aminci a gare ki. Barka da sabon wata.


Gajerun Saƙonnin Barka Da Sabon Wata Ga Masoyiya
Hoto: Mix and match studio/Vecteezy

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Zan so a ce na zo inda kike domin na ba ki kulawa ta musamman, sai dai zan wakilta alƙalamin rubutuna domin ya iso da saƙona kafin na samu damar isowa zuwa ga babban birnin da kike sarauta. Barka da sabon wata


Abin da ke ƙaruwa a cikin raina bai yi ƙasa da ƙaruwar yawan tunanin abar sona ba,  komai salon yadda nake rayuwa, sai na dinga jiyo sautin ki, koda a cikin baccina nake jin daɗi. Barka da sabon wata


Murmushi kika iya cikin tsayuwar ƙwarewar girman daraja, kin saci zuciyata da kalamanki, zuciyata ba ta yi, babu ke. Barka da sabon wata


Ina son ki, cikin so wanda doguwar tafiyar hakan, ta sa nake miki ƙauna kullum, kalamanki su ne abokan hira ta. Barka da sabon wata


Ni fa a son ki ban yi niyyar wani hutu ba, komai girman huɗubar mahassada a kanmu, ba zai girgiza zuciyata daga ƙarƙashin inuwar son ki ba. Barka da sabon wata


Alƙalamin rubutun zuciyata yana farawa cikin farkon abin da faruwar hakan ke faruwa wajen isar da saƙon so zuwa ga gimbiyar mata. Barka da sabon wata

Sunday, 22 June 2025

Kalaman Gaisuwar Barka Da Asuba Ga Masoyiya

Kalaman Gaisuwar Barka Da Asuba Ga Masoyiya

Aminci a gare ki ya sarauniya mai kyakkyawar sura da cikakkiyar nutsuwar sautin zance wanda ke fita tamkar busa irin na sarewa. Matsayin girman daraja da biyayyar da zuciyata takewa ƙaunarki ta wuce adadin busawar iska cikin adadin tafiyar kwanakin numfashina.


Kalaman gaisuwar barka da asuba ga masoyiya
Hoto: Master file

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Ina miƙa saƙon so daga zuciyata zuwa ga zuciyar da nake neman haɗa zumunci wanda muke fatan kasantuwa har zuwa ƙarshen rayuwar numfashi.


Ya mai martaba sallama da kalaman gaisuwar aminci a gare ki tare da haɗaɗɗiyar daular murmushin fuska mai cike da nuni da isar da muhimmin saƙo zuwa gare ki.


Ki agaji zuciyata da kalaman son ki, ki yayyafawa ruhina ruwan sanyin murmushinki mai fitowa cikin tsakiyar laɓɓanki masu ɗaukar hankali.


Ina cikin tsakiyar son ki,  ke ce sabuwar duniyata ta musamman mai ɗauke da kayan alatu masu faranta ruhin jikina.


Haƙiƙa hasken annurin fuskarki bai gushe ba face ya yi awon gaba da dukkan wani kuzarin da ke jikina.


Ina miƙa saƙon gaisuwa mai ɗauke da fatan amincewar ruhin zuciyarki, fatana kawai ki ce min kin karɓa.

Monday, 12 May 2025

Sakonnin Soyayya Na Lokacin Faduwar Rana

Sakonnin Soyayya Na Lokacin Faduwar Rana

Murmushinki ya haskake ilahirin nahiyar dukkan jikina, ganinki yana bayyano da dukkan wani kuzari da shauƙina a kullum.


Sakonnin soyayya na lokacin faɗuwar rana
Hoto: Media bom

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Saƙon zuciya daga ɓangaren zuciya zuwa ga kyakkyawar sarauniya, kuma abun koyi ga dukkan sauran 'yammata.


Tsarin da na tsaro zuciyata shi ne na koya mata yadda za ta rayu da ke domin aminta da nagartarki da kuma ƙwarewarki wajen rarrashin abin da kike ƙauna.


Kin kasance wata alƙarya ta musamman wadda a cikinta ne nake wanzuwar kasancewa da shauƙi madawwami.


Tunanin zuciyata a kullum shi ne ki kusantu inda na kasance. Numfashina yana fita ne a cikin naki.


Son ki ya yi ado a cikin jikina, komai nake yi ina  kasantuwa ne a cikin yanayinki.


Kin zama ma'aunin da ke yawan  auna rayuwar jin daɗin da ke wanzuwa a tare da ni idan kina nan ni ma ina nan. 


Kin iya murmushin ɗaukar ruhin zuciya musamman lokacin da laɓɓan ki suka sha ado da kwalliyar jan baki.


Ni dai na san ina sonki. Kuma zuciyata ma tana sonki.


Ki taimake ni, ki agaji ruhina domin ki taya zuciyata sonki, da kuma taimaka mata wajen kulawa da ke.

Wednesday, 7 May 2025

Sakonnin Barka Da Maraice Masu Sa Budurwa Natsuwa

Sakonnin Barka Da Maraice Masu Sa Budurwa Natsuwa

A cikin almurin maraicen ranar da idona ya fara ganinki tun daga lokacin ban ƙara iya aikata komai ba tare da na sanyo tunaninki cikin raina ba.


Saƙonnin Barka Da Maraice Masu Sa Budurwa Natsuwa
Hoto: Peak PX

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Aikin da ke cikin zuciyata shi ne sonki. Raina ya kasantu cikin dausayin ni'imar begenki, sai tunaninki ya zamto wani ɓangare na jikina.


Na zauna tsaf domin nazarin samun dama cikin dama irin wadda na samu a lokacin da Allah ya fara haɗa mu tsakanin ni da ke.


Zuciyata tana son ki hakan ne yake ba wa idaniya damar isar da saƙonta a lokacin da na so na gan ki sai kuma ban samu damar ganin naki ba hawaye su ne matakin farko.


Barka da yamma dukkan wani tarin farin ciki ina murnar ganin ya riske ki domin ya yo silar bayyanuwar murmushin fuskarki.


Tasirin kallon fararen idanun ki sun yi nasarar ƙara dawwamar da zuciyata bisa kan alƙiblar son ki hakan shi ne ya haifar min da yawan tunaninki.


Ni dai da ke zan rayu, da son ki zuciyata ta soyu. Mun fi ta cikin sahu na marayu. Sannunki mai sufar 'yan gayu.


Jarumtakar girman haƙiƙar sonki ta yi sanadin kafa daular ɗaruruwan begenki dare da rana, da son ki nake rayuwa.


Ban son kallo ko kuma jin wani sautin zancen da ba ya tuna min da zuwanki cikin raina.

Thursday, 1 May 2025

Gajerun Sakonnin Soyayya Irin Na Sarakai

Gajerun Sakonnin Soyayya Irin Na Sarakai

Ranki shi daɗe hannuna a sama cikin aminci nake miki gaisuwar ban girma ga gimbiya sarautar mata, matsayinki ya kai a yaba miki.


Gajerun Sakonnin Soyayya Irin Na Sarakai
Hoto: Antonio Guillem/Dreams time

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR

Furucin furta sallama cikin karamci zuwa ga ma'abociyar kyawun suffa da kyawun diri. Ina motsawa ne da motsin da son ki yake matsar da ni cikin tsakiyar tekun ƙaunarki.


Kin hori zuciya da horon da ruhi yake hora ƙwaƙwalwata bisa irin yadda tunaninki yake yawan kawo ziyara cikin tsakiyar birnin masarautar zuciyata.


Gyara kintsi da kyau dole ne a cika miki fada yake sarauniyar da ke mulkin masarautar zuciyata. Taka a sannu yake jigon da ke jawo jerin farin cikin ruhina.


Ƙauna da son ki sun mamaye ruhina shiyasa zuciyoyinmu suke numfasawa a tare da junansu.


Sarauniya na zo gare ki da gaske zuciyata a makance, kalaman bakin ki su ne sinadarin ƙara ruruwar wutar son ki wadda ta mamaye zuciyata.


Akwai amana ni da ke babu ranar rabuwa, zahirin gaskiya ke ce wadda na zaɓa domin ki zamto ummin yarana.


Sannunki 'yar gaban goshin zuciyata. Na yi jinjina kuma na gaisheki. Burina ki zamto cikin farin ciki da tarin annashuwa, a daidai lokacin da kike karanta saƙonnina.

Sunday, 27 April 2025

Hirar Zamani Ta Budurwa Da Saurayi A Ganin Farko

Hirar Zamani Ta Budurwa Da Saurayi A Ganin Farko

Saurayi: Tun farko fara buɗewar ƙwayar hasken ganin idanuwana ban yi tozali da kyakkyawar fuskar da ta ɗimautar da zuciyata ba sai da na fara haɗuwa da ke.


Hirar Zamani Ta Budurwa Da Saurayi A Ganin Farko
Hoto: Kieferpix/Gatty Images



Budurwa: Wane ne?


Saurayi: Wani ɗan saurayi ne wanda ki kai ma sata.


Budurwa: Sata kuma? Satar me na yi maka? Kuma Wane ne kai?


Saurayi: Ni kaina ban san kaina ba sai da zuciyata ta fara ganinki, shiyasa na zo domin ki ba ni bayanan yadda nake.  


Budurwa: Bayanan yadda kake kuma? Ta ya za ka ce ba ka san kanka ba kuma kana so ka sani daga gare ni?


Saurayi: Yauwa tambayar da nake buƙata kenan daga gare ki, yanzu sai ki tsaya ki saurari batuna.


Ta ya zan iya gane kaina bayan ainihin suffar jikina ina kallonta akan tsakiyar fuskarki.


Ta ya zan iya gane kaina bayan kin tafi da dukka tunanin raina.


Ta ya zan iya gane kaina bayan gangar jikina kaɗai take yawo amma ainihin ruhina yana bin ki a duk inda kike.


Ta ya zan iya gane kaina bayan dukkan ƙofofin saduwar jini suna tare da ke.


Budurwa: Ɗan dakata da zanceka haka, na ji ka ce na yi maka sata shin wai me ne ne na satar maka ne da kake ta faman bi na a duk inda na yi?


Saurayi: Ehmmm kin saci abu mafi girman daraja da tsada a wajena.


Kin sace abu mafi saurin maida mutum rago duk tsananin jarumtar shi.


Budurwa: Kai Malam dakata haka nan ka zo ka cika ni da surutunka. Ni har yanzu na kasa gane abin da  na sace maka ka ga idan ba za ka yi bayani ba ni zan shige gida.


Saurayi: Wayyo Allah na ɗan dakata mana kar ki saka rauni da rashin kuzari a jikina ta hanyar hana ni kallon wannan fuskar taki.


Da ma ba komai ba ne kika sace mun sai zuciyata. Na yi zaton za ki fahimta tun farkon da na fara furta bayanaina a kanki to amma sai kika yi mun bazata dole sai da kika sa na fallasa sirrina gare ki.


Budurwa: Ta ya za ka ce na sace maka zuciya bayan ga ka kana magana da kanka kuma?


Hmm naku har kullum Abdul'aziz Hamza KKR.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

Monday, 21 April 2025

Sakonnin Soyayya Da Za Su Sa Mace Dogon Tunani

Sakonnin Soyayya Da Za Su Sa Mace Dogon Tunani

A kan son ki na shirya shiga dukkan wani nau'in yanayi. Zan zama jarumin da zan yaƙi dukkan wani wanda zai kawo miki wargi.


Saƙonnin Soyayya Da Za Su Sa Mace Dogon Tunani
Hoto: Stock adobe

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Wani sanyi nake ji a can cikin tsakiyar zuciyata, a daidai lokacin da nake jin sautin zancen ki yana shiga cikin ƙofofin jikina.


Ke ce salsalar farin cikina, da ke nake tafiya cikin duniyar nishadina. A duk sa'in da na tuna cewa ke ce zaɓin raina dukkan wata damuwa tana rabuwa da ni.


Kusantowar zuwan lokacin da nake son na zo gare ki yana ƙara min ƙaimi wajen ganin na kawo kaina domin na yi tozali da ke.


Babu lokacin zuwan lokaci cikin lokacin da zan iya ɗaukar dogon lokacin da ban yi tunanin ki ba.


Sarauniya mai cikakken iko kina da ɗumbin ladabi da tunani mai zurfi, haƙiƙa zuciyata ba za ta saurara a cikin aikin nuna ƙauna a gare ki ba.

Wednesday, 16 April 2025

Kyawawan Sakonnin Gaisuwar Barka Da Safiya Ga Masoyiya

Kyawawan Sakonnin Gaisuwar Barka Da Safiya Ga Masoyiya

Kasancewarki sarauniya mai cikakken iko, na san yanzu haka kina kwance ba ki tashi daga bacci ba, shiyasa na aiko saƙona domin ya zauna a bakin fadarki ya jira lokacin tashinki, sai ya yi gaisuwar aminci a gare ki.


Kyawawan Saƙonnin Gaisuwar Barka Da Safiya Ga Masoyiya
Hoto: Next luxury

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Sallamar aminci cikin amintar da ke amintar da ruhin zuciya, gaisuwa nake biyawa zuwa gare ki.


Ina cikin tsakiyar son ki, cikin wata sabuwar duniya ta musamman, mai ɗauke da kayan alatu masu faranta ruhin jikina.


Na koyi darasin ƙauna kasancewar na kwana cikin inuwar zuciyar da ta san yadda ake so da tarairayar zuciyar wanda take so.


Ke nake so kuma zuciyata take yayi. Ya zan yi na iya tsallakewa bayan kin mamaye dukkan jikina?


Kowanne matsayi kin cika shi wajen zama sarauniyar mata a cikin zuciyata, da ke zan yi rayuwata, kuma da ke zan rayu komai tsananin juyin yanayi muna nan tare da'iman.


Ina miƙa saƙon gaisuwa mai ɗauke da fatan amincewar ruhin zuciyarki. Fatana kawai ki ce min kin tashi cikin ƙoshin lafiya.

Saturday, 15 March 2025

Kalaman Soyayya Na Bayan An Bude Baki Masu Ratsa Jiki

Kalaman Soyayya Na Bayan An Bude Baki Masu Ratsa Jiki

Barka Da Shan Ruwa sarauniyata wadda na sadaukar ma da zuciyata. Shiga ki zauna kin zama sarauniya ta musamman a cikin ta, me kike da buƙata a kawo miki ki yi buɗe baki da shi?


Kalaman Soyayya Na Bayan An Buɗe Baki Masu Ratsa Jiki
Hoto: Nature vibes

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Da Sunan Allah Maɗaukakin Sarkin da ya tsara suffar halittarki cikin daidaituwar kyawun da ke burge dukkan idanuwan da su kai tozali da kyakkyawar fuskarki.


Yau Azumin mu 15 cif  shiyasa na dawo gare ki, ba zan gajiya ba tare da jinjina da gaisuwar aminci mai cike da tarin so da ƙauna zuwa gare ki.


Sannunki fa 'yar gaban goshin zuciyata na yi jinjina kuma na gaisheki. Burina ki zamto cikin farin ciki da tarin annashuwa, a daidai lokacin da kike buɗe baki hakan shi ne cikar burina.


Farin ciki abun so ne daga kowace irin nau'in zuciya  shiyasa tawa ta kasance cikin shauƙi da annuri kasancewar na samu farin cikin raina.


Na koyi darasin ƙauna kasantuwar na kwana cikin inuwar zuciyar da ta san yadda ake so da tarairayar zuciyar wanda take so.


Kuma da ke zan rayu komai tsananin juyin yanayi muna tare da'iman.


Kowane matsayi, kin cika shi wajen zama sarauniyar mata a cikin zuciyata, da ke zan yi rayuwata.

Thursday, 6 March 2025

Takaitattun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Masoya

Takaitattun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Masoya

Wash yau kam na ji azumi, tabbas ibadar Allah daɗi gareta, Allah dan isar ikon tsarkin mulkin ka Allah, ka karɓi ibadun mu. Barka da shan ruwa shalele.


Taƙaitattun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Masoya
Hoto: Envato

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Jijiyoyin da suke kawo jini a cikin jikina suna gaisuwar aminci a gare ki.


Kalaman da ke fitowa daga bakina sun kasance mallakinki ne ke kaɗai.


Kuma ba zan so ki ba wa kowa ba.


Na so ki ba zan so 'yar gidan kowa ba.


Ƙaunarki kaɗai ita ce na zaɓa har na yi mata babban masauki a cikin fadar zuciyata.


Da farkon farawar ranar da ta fito daga gabas zuwa yamma, tunaninki bai bar zuciyata ta samu sukuni ba.


Murna nake da ganin ki 'yar gata, zo ga wuri zauna, idanuwana su kalli kyawun da ke fita daga gare ki.


Ina son ki, na san ina ran ki kamar yadda ke ma kike raina.


Dan haka ina da ƙwarin gwiwa a kan son da kike a gare ni.


Ina  son ki wannan ita ce kalmar da nake amfani da ita wajen saita zuciyata a daidai lokacin da nake tunaninki.

Tuesday, 4 March 2025

Kyawawan Gajerun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Budurwa

Kyawawan Gajerun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Budurwa

Yau ce ranar azumin farko a cikinta ne nake fara ba ki saƙon farko wanda a farkon ranar haɗuwarmu zuciyata ta tanaje shi musamman domin ki. Manyan dalilan da suke ƙara saukar da ni'imar sanyin son ki a raina, sun samo alaƙa ne da irin suffatuwarki cikin sufar da ba zan iya misaltawa kowa ba.


Kyawawan Gajerun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Budurwa
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Farkon buƙatar zuciya ita ce ta fara sallama a gare ki cikin farkon rubutuna wanda nake farawa da saƙon da ke nuna girman matsayin muƙaminki a guna.


Buɗe min zuciyarki domin na shigar da saƙon zuciyata wanda yake ƙara danƙon zumuncin da ke a tsakanin junanmu.


Ke kamar ɗanyen farin zinare kike da zarar na kusanto inda kike sai na ji tamkar na zama wani sabon Basarake, a yayinda hasken haƙoranki yake ƙara ni'imtar da zuciyata cikin ni'imar son ki da ƙaunarki.


Sallama a gare ki yake mai martabar girman matsayin muƙamin shiga cikin ƙololuwar fadar zuciyata wanda babu abin da ta sani face son ki da ƙaunarki.


Matsayinki na daban ne a cikin raina. Na yi niyyar hidimtawa soyayyarki dan haka babu gudu kuma babu ja da baya.


Da'iman abadan da ke na yi alƙawarin ƙarasa dukkan rayuwata. Idan ina tare da ke ni ban gano ranar da akasin farin ciki zai riske ni ba.


Haɗuwata da ke shi ne shaidar da ke nuna cewa tabbas na yi bankwana da dukkan wata damuwata. Dan haka nake ƙara shigar da ke a cikin tunanin ruhina.


Aminci a gare ki tare da saƙon sallamar so da ƙauna yake abun tattalin so da ƙaunar da ta kewaye dukkan ruhina a koyaushe.

Saturday, 8 February 2025

Gajerun Kalaman Soyayya Masu Faranta Zuciyar Budurwa

Gajerun Kalaman Soyayya Masu Faranta Zuciyar Budurwa

Kin cancanci dukkan wani matakin so wanda zuciyoyin masoya suke ba wa abokan junansu a dalilin so da ƙauna. Son ki ya yi nisan zango a cikin raina, dukkan wani tanadin farin cikina ke zan mallakawa.


Gajerun Kalaman Soyayya Masu Faranta Zuciyar Budurwa
Hoto: Gumpanat/Istock photo

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Mafi shaharar lokutan da na fi shahara cikin shauƙi suna zuwa ne da shauƙi cikin lokacin da na samu saƙon son ki.


Mazauni da na zauna domin tattalin rayuwar soyayyarki ya zama na musamman cikin irin hikimomi da abubuwan da zuciyata ta tanada musamman domin ki.


Na yi matuƙar sa'a da kuma dacewa cikin ranakun da ke tuna min harafin sunanki.


Assalamu alaiki saƙon gaisuwar amincin so mai fitowa cikin rubutun ƙauna wanda suka taho musamman domin su yi gaisuwa a gare ki.


Kin shiga cikin tsakiyar ruhin zuciyata da tsayuwar neman kasancewa da ke nake kwana.


Kyakkyawar sarauniya murmushinki ya mallaki zuciyata da gangar jikina. Lallai ke sarauniya ce mai cikakken iko. Ina matuƙar son ki.


Ba ni da sauran wata matsala. Sannan na kan kasance cikin tsananin farin ciki a lokacin da na ji an ambaci sunanki.

Friday, 31 January 2025

Kalaman Soyayya Na Budurwa Ga Saurayi Masu Kwantar Da Hankali

Kalaman Soyayya Na Budurwa Ga Saurayi Masu Kwantar Da Hankali

Yau ma gani cikin fadarka ba na buƙatar komai sai kallon fuskarka don Allah ka amince na gano kyawunka. Godiya zan yi gare ka sarkin sarakuna mai farar zuciya ga ka da kyau kamar zinare dole ne na ce maka sarki.


Kalaman Soyayya Na Budurwa Ga Saurayi Masu Kwantar Da Hankali
Hoto: Marriage

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Ladubban so da ƙauna sun samu masauki cikin soyayyar da aka ginata bisa tsarin gaskiya da amana, hakan ne dalilin da ya sa shaƙuwarmu da kai take ƙara nisan zango har muke saurin shallake masoya suke ƙoƙarin koyi da irin rayuwar soyayyarmu.


Na fahimci abubuwa na musamman a tare da kai. Ka haɗu kuma ka halittu, ka san so kuma ka san haƙƙoƙin ƙauna.


Ingantacciyar sallama daga ƙarƙashin inuwar ruhin zuciyar da ke yawan begenka a kullum.


Zuwa gare ka mashahurin masoyina wanda ya yi nasara wajen sace zuciyata.


Saƙon so na zo na ba ka don haka ga zuciyata nan ɗauki ka faɗawa gidanku zan zo da sadaki.


Ko ka san Allah ya halicceka cikin halittun da suka halittu wajen ƙawatuwar wannan duniya tamu?


Saduwar zuciyoyinmu wuri guda shi ne haɗuwar ruhinmu idan muka zamto cikin wannan yanayin dole ne mu dinga tunanin junanmu.

Thursday, 23 January 2025

Gajerun Kalaman Soyayya Na Text Messages Masu Ratsa Sassan Zuciya

Gajerun Kalaman Soyayya Na Text Messages Masu Ratsa Sassan Zuciya

Fatana da roƙon zuciyata a kullum shi ne ki himmatu cikin shirin zama matar aurena. Akwai amana ni da ke, babu ranar rabuwa, zahirin gaskiya ke ce wadda na zaɓa domin ki zamto Ummin yarana.


Gajerun Kalaman Soyayya Na Text Messages Masu Ratsa Sassan Zuciya
Hoto: Racorn/Dreams time

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Ba zan kasa isar da saƙon zuciyata a gare ki ba domin hakan shi ne shaidar kin zama jagora a cikin ƙalbina.


Ƙauna da son ki sun mamaye ruhina shi ya sa zuciyoyinmu suke numfasawa a tare da junansu.


Son ki ne sanadi kuma jigon tsayuwata babu rana ko kuma dare wajen tsara baitocin bege a gare ki.


Yunƙurin jikina da kuma tsayuwar tsayawar saƙona shi ne fatan ganin shauƙi da murmushi ya bayyana a kan fuskar ki.


Ƙaunarki ta mamaye ƙirjina, a cikin jinina nake jin son ki yana min yawo shi ya sa ba na iya zirga-zirga sai na yi tunaninki.


Na zo gare ki da gaske, zuciyata a makance, kalaman bakin ki su ne sinadarin ƙara ruruwar wutar son ki wadda ta mamaye zuciyata yanzu haka.


Cikin ƙaramin lokaci na yi tafiya mai nisan zango a cikin son ki wanda fahimtar hakan zai zamo abun mamaki.

Tuesday, 21 January 2025

Sakonnin Bankwana Na Karshe Da Budurwa

Sakonnin Bankwana Na Karshe Da Budurwa

Me ya sa kika zaɓi son ganin kukana maimakon a ce ki so baccina wanda zan yi shi har cikin ƙalbina? Wayyo ni. Kaichona.


Sakonnin Bankwana Na Ƙarshe Da Budurwa
Hoto: Antonio Guillem/iStock photo

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR



Zancen aure muka ƙulla ni da ke domin zuciyata babu kalar ki. Ashe ke a ran ki akwai abin da yake faruwa.


Zuciyata kike son ki fasa, kin bar ni ina ta bacci kamar wata kasa, ina tunanin abin da ke a ƙasa, na soyayyar da muke wadda ba sa'insa.


Ashe dukkan kalamanki na yaudara ne? Da ma kin so ni domin ki ƙware ni ne? Me ya sa ki haka?


Ɗawainiya nake da ke a kowace rana, ina ta tunanin akwai wata rana wadda za ta zo a ce mun zauna muna murmushi muna yin murna.


Yau dai gare ki na zamo ɗan kallo, kin so ki maida ni kamar wata ƙwallo, maimakon farin wata sha kallo.


Kar ki sa zuciyata ta yi kuka bayan ta ɗauki so ta ba ki duka a kanki.


Son ki ne abun son ruhina, fushinki ne silar kukana. Ke nake so, kuma nake yawan ƙauna.


Yau ga shi ni da ke muna bankwana, na so a ce muna tare ba za mu rabe ba amma ƙaddara ba za ta bari ba.

Sunday, 19 January 2025

Kyawawan Kalaman Soyayya A Daren Farko Ga Ma'aurata Na Zamani

Kyawawan Kalaman Soyayya A Daren Farko Ga Ma'aurata Na Zamani

Ke kyakkyawa ce a cikin kyawawan 'yammatan zamanin nan, ke ce matakin farko, dukkan 'yammata kin zamo madubi a gare su.


Kyawawan Kalaman Soyayya A Daren Farko Ga Ma'aurata Na Zamani
Hoto: 18989612/Freepik

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Assalamu Alaiki saƙon sallamar so mabuɗin murfin ƙofar zuciyata zuwa gare ki, maƙurar soyayyar da zuciyata take ɓuɓɓugo da shauƙin begenki a fili, son ki ne sila kuma ma'aunin da ke auna mizanin rayuwar dukkan wani nishaɗin da ke ɓuɓɓugowa da shauƙin murmushin fuskata.


A karon farko cikin tarihin tsawon kwanakin rayuwar da na yi na samu kyauta ta musamman wadda Allah Ya zaɓe ta cikin kyawawan bayin shi Ya ba ni domin ta zamo abokiyar rayuwata ta har abada.


Ke ce nake nufi da kalamaina 'yar wajen Mama murmushinki nake buƙata domin ya zamto mabuɗin da zai buɗe mini ƙofar shigowa cikin nutsuwar samun zama a tare da ke.


Kafin na fara shiga cikin zangon rubuta miki saƙon da ke fitowa ta cikin numfashin zuciyata sallama a gare ki zan fara 'yar mutanen Larabawa.


Gwargwadon ruwan ƙoramu masu kwaranya cikin yanayin saukar ruwan sama suna ƙara bayyano da kwarjinin halittar kyawunki.


Babban burin ruhi da cikar ƙasaitar murmushin zuciyata shi ne ganin ki a kusa da ni kina mai fesa mini kyakkyawan murmushin ki.