Saturday 21 December 2019

KARANTA HANYOYIN HARAJIN KASA DA NA JIHA

Tura Wannan Zuwa Ga
A Nijeriya, an kasa hukumomin karɓar haraji zuwa uku, kananan hukumomi da jihohi da kuma gwamnatin tarayya. Kowacce hukuma da irin nau'in harajin da take karɓa.

Hanyoyin Harajin Kasa da na Jiha

Marubuci: Danladi Haruna

Gwamnatin tarayya ce kaɗai ke da alhakin karɓar haraji da ya haɗa da:

A. Haraji daga  kamfanoni (Company Income & Capital Gain Tax)

B. Harajin Ilmi (Education Tax)

C. Harajin Fasaha (Technology Tax)

D. Harajin sitamfi (Stamp duty)

E. Kudin Fito (Excise Duty)

F. Harajin VAT

G. Harajin Ribar Man Fetur

H. Harajin Ma'aikatan da ke Birnin Tarayya Abuja da na Jami'an tsaro da kuma ma'aikatan diflomasiyya.

I. Harajin WHT (Withholding Tax) na mazauna Abuja da sauran baƙi.

Da sauran abubuwan da suka shafi ƙasa da ƙasa.

Jihohi na da ikon karɓar haraji daga abubuwa kamar haka:

A. Haraji daga ma'aikatan da ke aiki a jihar (PAYE) da kuma dukkan 'yan kasuwar da ke sana'a a jihar.

B. Harajin WHT na ɗaiɗaikun jama'a mazauna jihar.

C. Harajin masu kwambala da ofisoshin caca da na gasa da sauransu.

D. Harajin ababen hawa, mota da babur.

E. Rijistar wajen sana'a (Business Registration).


F. Kuɗin gina ƙasa ga dukkan mutanen da ke zaune a jihar amma kada ya haura naira 100 a shekara.

G. Harajin ƙasa

I. Harajin kasuwannin da gwamnatin jihar ta gina.

J. Harajin masu ƙananan sana'o'i da ke yawatawa a faɗin jihar.

Su kuwa Kananan Hukumomi suna iya karɓar haraji daga waɗannan hanyoyi;

A. Harajin kantuna da shagunan masu sana'a.

B. Harajin gidajen haya

C. Harajin kuɗin rijistar haihuwa, aure da mutuwa.

D. Harajin mayankar dabbobi da ta kaji

E. Harajin lasisin sayar da kayan ruwan bagaja da sauran magunguna.

F. Harajin ƙasa a wuraren da ba na gwamnatin tarayya ko na jiha ba.

G. Harajin kasuwannin da ƙaramar hukumar ta sa hannu.

H. Harajin wurin ajiyar ababen hawa.

I. Harajin lasisin ajiyar dabbobi kamar kare da mage da biri da sauran dabbobin da ake kiwatawa a gida.

J. Harajin ababen hawa kamar keke, amalanke, kwale - kwale, wili baro da sauransu.

K. Kuɗin jangali.

L. Harajin kuɗin saka talabijin da rediyon mota da kuma na'urar satilayit.

M. Harajin yin fakin ba dai-dai ba.

N. Harajin gidajen wanka da bahaya.

O. Harajin kiwon kaji ga masu kiwo a gidajensu.

P. Harajin bunne gawa wadda ake yi ta hanyar al'ada (ba ta hanyar addini ba).

Q. Kuɗin iznin gina wajen bauta (Masallaci ko Coci ko makarantun addini).

R. Kuɗin iznin kafa allunan talla da fastoci da sauransu.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA DOKOKIN DA SUKA SHAFI HARKOKIN KUDI DA HARAJI

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa??

Hanya Mafi Sauki da Zaku yi Nasara Wajen Hana Banki Cazar Muku Kudi a duk Lokacin da Zaku Fitar da Kudi

Sau da dama akan samu ruɗani tsakanin hurumin jihohin da na ƙananan hukumomi. Wani lokacin har ga gwamnatin tarayya. Wani lokaci akan samu abu ɗaya ya zamana ana karɓar haraji akansa a dukkan matakan hukumomin nan. Don haka aka samar da dokar da ke fayyace hurumin kowa.

A rubutu na gaba da zan zo da wasu daga hanyoyin da ake lissafa kudin harajin da mutum ya kamata ya biya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user