Saturday 22 February 2020

Shin ko Kasan Dalilin da Yasa Ma'aurata Suke Matukar Son Junan Su?

Tura Wannan Zuwa
Idan ka ga mata da miji suna son junansu, cikin farin ciki, da annashuwa, da kyakkyawar fahimtar juna, kada ka ce "Kai waɗannan sun ci sa'a!.

Sirrin Rayuwar Ma'aurata


A cikin rayuwar aure babu wani abu da ake kira da suna "sa'a".

Ba ka san irin yanda kowanne ɗaya daga cikinsu ya sauka daga ra'ayinsa domin rayuwa ta yi kyau ba.

Ba ka san yawan aibobin juna da suka kawar da ido ga barinsu, saboda rayuwar tare, da samun sulhu a tsakaninsu ba.

Ba ka san yawan kura-kuran da suka yayyafe wa junansu ba.

Kai ba ma za ka taɓa iya hararo matsalolin da suka samu a tsakaninsu, suka kuma haɗiye su saboda suna matuƙar son su kammala rayuwarsu tare da juna ba.

Ba ka kuma san tsawon lokacin da suka ɗauka a tsakaninsu domin samun fahimtar juna ba.

Ita soyayya ba ta taɓa zama "sa'a" ba.

Soyayya wata kyauta ce da baiwa da masoya suke yi wa junansu, imani ne daga zuci, abu ne da ɓangarori biyun suke raji, bajinta ne da tausayi, gami da haƙuri da juna.

Idan har babu waɗannan sifofi a cikin alaƙarka ta aure, to ka yi ƙoƙarin samar da su; saboda ka sami jin daɗi a karan kanka, ka kuma sanya abokin zamanka cikin jin daɗi.

MAKALOLI MASU ALAKA:
Ban san wanda ya faɗa ba, amma dai wannan haƙiƙa ce na tarjamo domin mu amfana.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user