Showing posts sorted by relevance for query Ibrahim Garba Nayaya. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Ibrahim Garba Nayaya. Sort by date Show all posts

Thursday, 30 January 2020

Karanta Hadaddun Kalaman Soyayya Daga Saurayi Zuwa Budurwa

Karanta Hadaddun Kalaman Soyayya Daga Saurayi Zuwa Budurwa

DAGA ZUCIYA ZUWA GA ZUCIYA

Salam ya ke muradina,
Da safe na antayo ƙauna,
Na bayyana sirrikan raina,
Gare ki ina makwancina,
Zo amsa min cikin son rai.

Rayuwar Masoya

Marubuci: Ibrahim Garba Nayaya

Abar sona abar sona,
Abar ƙauna abar ƙauna,
Abar marari a rayina,
Yau ga ni da so cikar ƙauna,
Cikar buri cikar komai.

Gare ki masoyiya tawa,
Ki ji ni da zantukan baiwa,
Na ƙaunar nan da ba tsaiwa,
Cikin mararin cikar sowa,
Na bayyana baitukan so dai.

Idan na gane ki don ƙauna,
Na manta abin da ke raina,
Cikar buri ki zo guna,
Ki amshi buƙatuna,
Ki share min duhun komai.

Ranar wanka Bahaushe de,
Ya ce cibi waje buɗe,
Nufinsa a wangame buɗe,
Kowa ya gano ido buɗe,
A san shi a san kalar komai.

Kin san so ba a mai yarfe,
Ba a ƙyamar tuwon safe,
Zoben so ba a sa ƙarfe,
Burina na tattaro lefe,
Na kai ki garin da ba kome.

Kin san so ba a mai kulle,
Gararinsa yawa na 'yan talle,
Shuhurarsa a zuciya zille,
A ganta a fuska ba kyalle,
A san ya zarce duk komai.

Idan na taho a motata,
Cikin tafiya ta ƙasaita,
Idan na gane ki 'yar auta,
Kina tafiya ta ƙasaita,
Na manta batu na tukin dai.

Kalarki daban a mataye,
Sunanki daban na 'yar yaye,
Sautinki daban a Karaye,
A soyayya ana maye,
A sonki ko za na yo komai.

Naman da ake kira soye,
A cakuɗa kafi zabaye,
A sa naman a sa maye,
A sa gishiri a yo soye,
A so haka duk ake komai.

Maimaita aji fa sai dolo,
A so kam ba a son gwalo,
Ba a kome cikin salo,
Jifa kam sai da ɗan kwallo,
A so ba a barin komai.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA KALAMAN BADA HAKURI A SOYAYYA 

KARANTA KALAMAN SOYAYYA MASU DADIN GASKE DA RATSA JIKI

KARANTA TSANTSAR KALAMAN SOYAYYA 

Baitin ƙarshe na ce santsi,
Ya ɗebi mutum ya yo watsi,
Ya farfasa kai ya yo rotsi,
A soyayya a bar kutsi,
Aure a gare ki ne komai.

Ni Nayaya na ce ki dube ni,
Ki min kallon da ba raini,
Da zai mai she ni ɗan birni,
Na sa kaya na sa rawani,
Na so domin na zam komai.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Friday, 1 December 2017

HUKUNCIN SANYA TUFAFIN ARNA A
GARURUWANSU-Ibrahim na yaya

HUKUNCIN SANYA TUFAFIN ARNA A GARURUWANSU-Ibrahim na yaya

Lallai abu ne sananne saba wa Kafirai da
Mushrikai a abubuwa na rayuwa da suka kebanta
da su yana daga cikin manufofin Shari'ar
Muslunci.

Shi ya sa aka samu hadisai masu yawa
sun zo suna umurtanmu da saba wa Yahudu da
Nasara a siffofinsu na zahiri, na Tufafi da Al'adu
da sauran lamura na rayuwa, kuma suka hana
mu kamanceceniya da su da kwaikwayonsu.

Amma sai dai saba musun yana kasancewa ne a
lokacin karfi da izzan Musulmai. Amma duk inda
Musulmai suke da rauni to saba musun ba wajibi
ko mustahabbi ba ne, matukar zai haifar da
cutarwa.

Don haka duk lokacin da Musulmai suka kasance
a garuruwan kafirai da kasashensu, to babu
bukatar su saba musu, don tsoron cutarwa.

Kai,
kamantuwa da kafiran a siffofinsu na zahiri,
kamar tufafi da aski da wasu abubuwan na zahiri
zai iya zama Wajibi ko Mustahabbi gwargwadon
Maslaha ta Shari'a, kamar zuwa Kasar Kafiran
don Da'awa da kira zuwa ga Allah.
Shaikhul Islami ya ce: "Da a ce Musulmi yana
kasar abokan yaki, ko kasar kafirci ba abokan
yaki ba, to ba a umurce shi da saba wa Kafiran a
siffofi na zahiri ba, saboda abin da ke cikin haka
na samun cutarwa.

Kai, zai iya zama mustahabbi
ko wajibi a kan mutum wani lokacin ya yi tarayya
da kafiran a siffofinsu na zahiri (kamar Tufafi,
tara gashi ko aski), idan akwai maslaha ta Addini
a cikin hakan, na kiransu zuwa ga Addini, ko
leken asirinsu da kawo labari ga Musulmai, ko
kawar da wani cutarwa daga Musulmai da
makamancin haka na kyawawan Manufofi".

Saboda haka, matukar akwai maslaha ta Addini
to dacewa da kafirai a tufafinsu a cikin
garuruwansu wajibi ne ko mustahabbi.

In kuma
babu maslahar Addini hakan halal ne. Musamman
saboda yadda a yau ake zargin Musulmai Ahlus
Sunna da ta'addanci. Don haka Wajibi ne ga
wanda ya je kasashen Turai don yin da'awa ya
sanya tufafinsu".

Da wannan nake jan hankalin 'yan uwa Ahlus
Sunna, bai kamata muna kutsawa cikin abubuwan
da za su kara ta'assubanci da rabuwar kai a
tsakaninmu ba.

Sa'annan kuma yana da kyau mu
nisanci dukkan abin da zai zubar da haiba da
kwarjinin jagororin da'awar Sunna. Saboda yana
daga cikin manyan sabuba na
lalacewar al'umma idan ta wayi gari ba ta da
wasu jagorori a lamuranta da take ganin kimarsu
da kwarjininsu, a mayar da kowa bai wuce a ci
mutuncinsa da hakki ko ba hakki ba. Sai kuma in
wata matsala ta kunno kai mu fara lalubensu don
warware matsalar. Idan muka daraja jagororinmu
na da'awa da dukkan shugabanninmu sai mu
samu hadin kai da cigaban rayuwa.

Mu sani, kuskure ne mai girma abin da wasu
yan'uwa suke yi na hada hotunan malamai da
wasu cikin masu shirya fina-finai da da'awar
dukkaninsu daya ne! Har ma suke kiran wai a
daina magana a kan yan fim, tunda ga malamai
ma sun yi! Hakika wannan zalunci ne, domin
Allah ya bambanta su.

Kamar yadda na ga wani
dan'uwa mai kima; amma yana hada hotunan da
na wasu masu fina-finai a yayin da suke hade
mace da namiji, kuma har yake ganin ba su da
maraba
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com  hanya me sauki ko kuma daga kasan Website din akwai inda akasa

Name...
Email...
Message...

Sai Ku turo mana mun gode

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By   ©Dr. Aliyu
Muh'd Sani, Ibrahim Garba Ibn Nayaya

Wednesday, 29 November 2017

FINA-FINAN HAUSA; GYARA KO BARNA???

FINA-FINAN HAUSA; GYARA KO BARNA???

A wajajen shekarar 2013 zuwa 14, na yi wani
rubutu da ya janyo cece-kuce a da'irar fina-finan
Hausa, wanda karshe wasu ke kallon kiyayya ce
tsantsa ga masu sana'ar har ta sanya muke
bayyana wadannan maganganun. Bayan wannan,
na sha hakaito yadda wasu daidaikun mmalaman
jami'o'in Kasar nan suka fuskanci rashin kunya
daga wasu fitsararrun 'yan wasan, musamman
ganin yadda su malaman masana ne a game da
harshe da al'adun Hauwpsawa, wanda hakan ya
sa suke bayyana munanan hadarin fina-finan a
al'adance, kuma suka rinka kira a kan dole a zo a
yi gyara, amma karshe aka rinka yi musu rashin
kunya da fitsara ba tare da an duba matakinsu a
karatu ko matsayinsu a cikin al'umma ba.

A shekarar da ta gabata, na kai ziyarar ofishin
wani tsohon furodusa, marubuci, dan wasa kuma
darakta; bayan wata fira da aka yi da shi game
da yadda fina-finan Hausa na yanzu suka bar
tafarkin Hausawa da al'adunsu. Mun kara
tattauna makamanciyar abin da ya fada, sannan
ya nuna inda sababin kuskiuren ya faru.

Idan muka dawo kan batunmu, zai bayyana
karara a gabanmu yadda fina-finan Hausa a yau
suka mamaye gidaddajinmu da shagunanmu da
wayoyinmu.

Hakan sai ya sanya da dama cikin
mutane ke ganin wata hanya ce ta samun
sana'o'i halattacciya a bangarori daban-daban na
mutane.

Da zarar wani ya yi yunkuri taba harkar,
sai a fara cewa zai hana wasu sana'o'insu.

Kwarai fim sana'a ce! Amma wacce iri???

Idan muka kwatanta dabi'un gidajen aure a yau;
da kuma abin dake wakana a gidajen Hausawa,
sannan mu waiwaici baya kafin yawaitar fina-
finan Hausa, za mu iske babu hauragiya da
baranbarama a gidajen aure.

Domin a baya mafi
yawan auren da ake yi ana gina su ne kan
kyawawan al'adun Hausawa, ta yadda za a hori
mace da yin abaibai masu kyaiu koda mijinta ya
munana mata.

Sannan tana da yan fira, wato
yara mata wadanda ke zuwa domin debe mata
kewa, yayin da tatsuniya ta zame musu
makarantun daukar darusa da kaifafa tunani.

A
wancan lokacin, babu batsa da harkokin
sharholiya a cikin tatsuniya ko sauran dangogin
hanyoyin tarbiyyantar da al'umma, musamman
sauran al'amuran da suke kunshe cikin taskar
Adabin Bahaushe.

Mu dawo yanzu, za mu iske rayuwa ta sauya,
inda da yawa gidaddaji suka zama tamkar filayen
dambe da kokawa, ko guraren masha'a da rashin
tarbiyya, kamar tasha ko bariki. Za ku yarda da di
idan na ambata muku cewar mafi yawan
wadannan munanan halaye, sun samu ne
sakamakon tasirin wasu fina-finan Hausa a
tsakankanin al'umma.

Wannan sai ya haifar da
wani mummunan lamari na rashin tarbiyya a
gidan aure, mace za ta iya zagi ko marin mijinta,
kamar yadda za ta iya zabgawa uwar mijinta
mari, ko ta kuntuma mata ashariya.

Dukkan wani
fim da za a yi, lalle za ka iske yana cike da wasu
illoli koda kuwa masu fim din sun yi da'awar
wa'azantarwa suke yi.

Misali, a fim din Hausa ne
za a nunawa mace yadda za ta ci amanar
mijinta, ko yadda 'ya za ta ha'inci ubanta a yayin
da ya tura ta makaranta; sai ta tafi
karuwancinta, ko kuma yadda alhazan birni ke
lalata 'ya'yan mutane.

Haka zalika, mata sun koyi
rashin godiya ga mazajensu a fina-finai, kamar
yadda suka koyi butulci da hana a yi musu
kishiya ko kakarin hallaka kishiyar ko maigidan
gaba.

Magana ta gaskiya, a yau kam fina-finan Hausa
ba gyara tarbiyya suke ba, face rugurguza
tarbiyyar al'umma, wanda wajibi ne gwamnati ta
san wannan, kuma ta nemi gyara.

Duk wani
shedanci da za ka iske mace ta yi, idan ka
tsananta bincike, a fim ta gani.

Da wannan na
fahimci cewa fina-finan Hausa bai dace su shiga
sahun Adabin Hausa ba, sawa'un na zamani ne
ko waninsa, bal ma kamata ya yi su shiga sahun
adabin da su Auwal G Danbarno ke kira da
ADABIN BARIKI.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin√√√

Source By  ©Ibrahim Garba Ibn Nayaya