Showing posts sorted by relevance for query Imam Aliyu Indabawa. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Imam Aliyu Indabawa. Sort by date Show all posts

Thursday, 28 March 2024

Abubuwa 28 Wadanda Ya kamata Ku San Su Game Da Ranar Alkiyama

Abubuwa 28 Wadanda Ya kamata Ku San Su Game Da Ranar Alkiyama

Allah ya ambaci sunayen ranar alƙiyama da sunaye mabambanta har guda ashirin da takwas. Za mu yi muku bayaninsu ɗaya bayan ɗaya da ma'anoninsu da kuma ayoyin da aka ambace su a cikin Alkur'ani.


JERIN SUNAYEN RANAR ALƘIYAMA A CIKIN QUR'ANI TARE DA MA'ANONINSU
Hoto: Awaz The Voice


Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa


1- Ranar alƙiyama. An ambaci wannan sunan a wurare saba'in a Alkur'ani. Kamar faɗinsa maɗaukakin sarki

"  وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ تَرَى الَّذِينَ كَذَبُوا عَلَى اللَّهِ وُجُوهُهُم
مُّسْوَدَّةٌ
Ma'anar ranar alƙiyama shi ne ranar tsayuwa. Kamar inda Allah ke cewa" 
يوم يقوم الناس لرب العالمين"


2. An ambace ta da Yaulmul Aakhir wato ranar ƙarshe kenan wacce ba wata rana bayanta. Kamar faɗinsa Allah cewa" إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالصَّابِئُونَ وَالنَّصَارَى مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ صَالِحًا فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ


3. An ambace ta 'Assaa'ah' kamar faɗinsa Allah cewa "
إِنَّ السَّاعَةَ آتِيَةٌ أَكَادُ أُخْفِيهَا لِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍ بِمَا تَسْعَىٰ

Al'imam Alqurtabiy ya bayyana ma'anar Assa'ah da cewa "
أنّ الساعة تدلّ في اللغة على جزءٍ من الزمن دون تحديدٍ، وسُمِّيت القيامة بالساعة؛ إمّا من باب قُرب وقوعها، وإمّا تنبيهاً على ما فيها من أمورٍ عظيمةٍ، وقِيل لأنّها قد تأتي فجأةً في أيّ وقتٍ"

A harshen larabci kalmar saa'a na nufin wani yanki daga lokaci wanda ba a ƙayyade ba. An ambaci Alƙiyama da Assa'ah ne ko don kusancin faruwarta, ko don gargaɗi a kan manyan al'amuran da ke cikinta. An kuma ce ta kan zo kowanne lokaci wanda ba a yi zato ba.


4. An ambace ta ranar tashi. Kamar faɗinsa maɗaukakin sarki cewa "
ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تُبْعَثُونَ


An ambace ta da haka ne saboda a cikinta ne ake raya matattu ake tashinsu daga kaburburansu.


5. An ambace ta ranar fitowa kamar faɗinsa ta'ala cewa"

يَوْمَ يَسْمَعُونَ الصَّيْحَةَ بِالْحَقِّ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْخُرُوجِ


An ambace ta da hakan ne domin a ranar ne mutane ke fitowa daga kaburburansu zuwa tsayuwa.


6. An ambace ta ranar rarrabewa kamar faɗinsa Allah cewa "
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ


An ambace ta da hakan ne domin a ranar ne Allah ke rarrabewa tsakain halittu.


7. An ambace ta ranar buɗi. Kamar faɗinsa Allah cewa "
قُلْ يَوْمَ الْفَتْحِ لا يَنفَعُ الَّذِينَ كَفَرُوا إِيمَانُهُمْ وَلا هُمْ يُنظَرُونَ"


8. An ambace ta da ranar addini.

Faɗinsa cewa" مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ

Malamai suka ce abin da ake nufi da addini shi ne sakamako. A ranar ne Allah zai yi wa bayinsa sakamako a kan ayyukansu.


9. An ambace ta ranar ƙara saboda tsananin ƙarfinta. Faɗinsa Allah cewa " فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ


10. An ambace ta da Attammah Alkubrah. Faɗinsa Allah cewa
فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَىٰ


Attammah a lugar larabci na nufin al'amarin da mutum ba zai iya da shi ba.


11. An ambace ta ranar hasara. Misali faɗinsa Allah cewa "
وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ الْحَسْرَةِ إِذْ قُضِيَ الْأَمْرُ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ وَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ


Hasara a lugar larabci na nufin nadama mai tsanani musamman ga 'yan wuta a kan ayyukansu.


12. An ambace ta Algaashiyah. Faɗinsa Allah "
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ

Akwai saɓanin malaman tafsiri a kan ma'anar wannan kalma. Kuma karatu ne mai zaman kansa ga shi ban son na tsawaita.


13. An ambace ta ranar dawwama.

Fadinsa Allah"
ادْخُلُوهَا بِسَلَامٍ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْخُلُودِ


Rana ce da 'yan aljanna ke dawwama a cikinta.


A taƙaice don kar na tsawaita ga ragowar sunayen da aka ambaci ranar alƙiyama da su a Alkur'ani.

14. يوم الحساب
15. الواقعة
16. يوم الآزفة
17.  يوم الجمع
18. الحاقة
19. القارعة.
20 يوم التلاق
21. يوم التناد
22. يوم التغابن
23. يوم الوعيد
24. اليوم العسير
25. اليوم المشهود
26. يوم عبوس قمطرير
27. النباء العظيم
28. الجاثية


Kowane suna yana buƙatar sharhi amma lokaci bai ba da haɗin kai ba.


Hikimar yawaitar sunayen alƙiyama shi ne kowanne suna yana bayyana wata siffa tsayayyiya. Hakan zai ƙara tabbatar da imani a zukata. Rayuka su zamanto shiryayyu saboda ranar alƙiyama.


Allah ka ba mu dacewa a gobe alƙiyama Amin.

Friday, 17 April 2020

Shin Ko Kasan Kana Yin Rayuwa Da Mutane Hudu Ne A Rayuwar Ka?

Shin Ko Kasan Kana Yin Rayuwa Da Mutane Hudu Ne A Rayuwar Ka?

A 'yan shekarun da nake dasu a duniya, nayi mu'amala da mutane iri-iri, na ɗauki darasi da dama.

Rayuwar Duniya Darasi Ce

Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa

Wani abu dana karanta game da ɗabi'un mutane ta fuskar mu'amala shine: mutane iri huɗu ne, gasu nan zan bayyana a falsafance.

1. Akwai mutumin da yake kirki amma bashi da mutunci.

2. Akwai wanda ke da mutunci bashi da kirki

3. Akwai wanda yake da kirki da mutunci duk biyun.

4. Akwai wanda bashi da kirki ba shi kuma da mutunci.

Bari nayi sharhin bayanin a taƙaice:

1. Mutumin da yake da kirki bashi da mutunci shine wanda a koda yaushe kuka haɗu zai dinga maka faran-faran yana janka jikinsa, amma babu kalar zagin da bazai maka ba a bayan idonka, shine idan mu'amala ta haɗaku zai yi maka cutar da baka taɓa tsammani ba, irin waɗannan mutane akwai ƙarya, yaudara, cin amana, butulci, hassada da rashin cika alƙawari a tattare dasu.

2. Mutumin da bashi da kirki amma yana da mutunci, shine sau tari ake ganin fuskarsu babu walwala, idan kun haɗu bai damu da yayi maka magana ba, amma fa bazai taɓa zaginka a bayan idonka ba, kuma idan mu'amala ta haɗaku dashi zai kyautata maka fiye da yadda kake tsammani, kayi ta mamaki ashe dama wane yana da mutunci? Irin haka yana faruwa a rayuwa.

3. Shi kuma wanda yake da kirki da mutunci akan same shi da faran-faran da mutane, bazai taɓa cutar dakai a bayan idonka ba, idan mu'amala ta haɗaku zai kyautata maka iyakar iyawarsa, sai dai ajizantaka.

4. Wanda bashi da kirki ba mutunci, shine wanda bai da faran-faran wa jama'a, mai raina mutane, wanda sam bai iya magana ba, mutakabbiri, mahassadi, macuci, ɗan son zuciya, wanda kowa yayi mu'amala dashi sai ya cutar dashi, akwai ire-irensu a rayuwar nan amma 'yan ƙalilan ne.

Yi ƙoƙari ka kyautatawa kowa daga kan fuska har cikin zuciya, domin babu wanda yasan inda rana zata faɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 23 December 2022

Falala 8 Ta Karanta Alkur'ani Mai Girma Ga Musulmai

Falala 8 Ta Karanta Alkur'ani Mai Girma Ga Musulmai

Karatun Alkur'ani ibada ce mai girma wacce ake samun lada mai tarin yawa tare da samun Aljanna, wanda da yawan mutane a yanzu sun shagala ga barin haka, akan sami wanda idan ba a cikin sallah ba ya kan shafe watanni bai ɗauki Qur'ani ya karanta ba, wanda hakan ba ƙaramar tawaya da asara ba ce.


Muhimmancin Karanta Alkur'ani Mai Girma Ga Musulmai
Hoto: Pexels


Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa


Alkur'ani rahama ne, ceto ne, kuma alkhairi ne ga mai karanta shi. Lokacin da Allah ke ambatar siffofin salihan bayinsa 'yan aljannah sai ya fara da makaranta Alkur'ani kamar faɗinsa cewa"


 إن الذين يتلون كتاب الله وأقاموا الصلاة وأنفقوا مما رزقناهم سرا وعلانية يرجون تجارة لن تبور 


"Waɗanda suke karatun Alkur'ani suke sallah a kan lokaci suke kuma ciyarwa a ɓoye da a bayyane suna ƙaunar kasuwanci mara yankewa".


Wasu daga malaman tafsiri suka ce kasuwanci mara ƙarewa da aka ambata shi ne rahama da lada.


An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar Allah ya ƙara musu yarda, Annabi (S.A.W) ya ce " Babu hassada sai a cikin abu biyu, mutumin da Allah ya ba shi Alkur'ani ya ke karanta shi dare da rana, da wanda Allah ya ba shi dukiya ya ke ciyarwa dare da rana".


لا حسد إلا في اثنتين‏‏ رجل آتاه الله القرآن، فهو يقوم به آناء الليل وآناء النهار، ورجل آتاه الله مالا، فهو ينفقه آناء الليل وآناء النهار


Daga faloli da darajojin karanta Alkur'ani:


1. Samun ɗaukaka a wajen Ubangiji duba da hadisin da Manzo (S.A.W) ke cewa " Allah yana da waɗanda ke matuƙar ƙauna a cikin mutane, aka tambaya su waye ya rasulallah? Ya ce su ne makaranta Alkur'ani.". Ibn Maja ya rawaito shi, Albani ya inganta shi.


قال رسول الله صلى الله عليه وسلم

إن لله أهلين من الناس قالوا: يا رسول الله ، من هم ؟ قال: هم أهل القرآن ، أهل الله وخاصته.

رواه ابن ماجة وصححه الألباني


Manzon Allah ya ce " Mafificin cikinku shi ne wanda ya karanci Alkur'ani ya ke karantar da shi.


 خيركم من تعلم القرآن وعلمه


2. Samun lada mai yawa tare da kyakkyawa ababen ninkawa.


Kamar hadisin da Muslim ya fitar da shi cewa Manzon Allah (S.A.W) Ya ce " Shin ɗayanku ba zai yi sammako zuwa masallaci ya fahimci ayoyin Alkur'ani guda biyu ko ya karanta su ya fi masa da a ba shi Taguwa guda biyu ba, aya guda uku ta fi Taguwa guda uku, aya guda huɗu ta fi Taguwa guda huɗu.


أفلا يغدو أحدكم إلى المسجد فيعلم أو يقرأ آيتين من كتاب الله خير له من ناقتين وثلاث خير له من ثلاث وأربع خير له من أربع ومن أعدادهن من الإبل


Manzo ya ce " Wanda duk ya karanta aya ɗari a wani dare ba za'a rubuta shi cikin gafalallu ba, ko za'a rubuta shi cikin masu ibada".


ومن قرأ في ليلة مائة آية لم يكتب من الغافلين أو كتب من القانتين


3. Samun ɗaukaka a duniya.


Kamar hadisin da ke cewa" Allah na ɗaukaka wasu mutane da Alkur'ani ya kuma ajiye wasu".


إن الله يرفع بهذا الكتاب أقواما ويضع به آخرين


4. Samun daraja maɗaukakiya a Aljannah.


Hadisi ya bayyana cewa" Ranar alƙiyama za a ce da ma'abocin Alkur'ani karanta ka yi sama, rera kamar yadda kake rerawa a duniya, mazauninka zai tiƙe a ayar da ka tsaya." .


‏يقال لصاحب القرآن‏:‏ اقرأ وارتقِ ورتل كما كنت ترتل في الدنيا، فإن منزلتك عند آخر آية تقرؤها‏


5. Samun ceto gobe kiyama.


Manzo (S.A.W) Ya ce "Ku karanta Alkur'ani don zai zo muku mai ceto gobe ƙiyama"


6. Saukar nutsuwa.


Hadisi daga Abu-huraira: Babu mutanen da za su taru suna karanta Alkur'ani sai nutsuwa ta sauka a gare su.


 وما اجتمع قوم في بيت من بيوت الله يتلون كتاب الله تعالى، ويتدارسونه بينهم، إلا نزلت عليهم السكينة، وغشيتهم الرحمة، وحفتهم الملائكة، وذكرهم الله فيمن عنده


7. Ninkuwar lada.


Annabi (S.A.W) Ya ce "Wanda ya karanta harafi guda daga Alkur'ani yana da lada, kowanne lada akwai ninkinsa goma.".


قال: من قرأ حرفا من كتاب الله فله حسنة، والحسنة بعشر أمثالها


8. Darajar kasancewa tare da Annabawa da manzanni.


Hadisi daga Nana Aisha (R.A), Manzo (S.A.W) Ya ce" Mahiru da Alkur'ani yana tare da Annabawa da manzanni, wanda ke karanta Alkur'ani yana sassarƙewa don wahala yana da lada biyu.".


الماهر بالقرآن مع السفرة الكرام البررة والذي يقرأ القرآن ويتتعتع فيه وهو عليه شاق فله أجران


Ma'anar Mahiru shi ne wanda ke karanta Alkur'ani ya ke kiyayewa da shi ya ke kuma aiki da shi.


Allah ya tabbatar da mu tare da Alkur'ani ya sa ya kasance ceto a garemu gobe ƙiyama Amin.

Wednesday, 2 October 2019

KARANTA BABBAN KALUBALEN DAKE GABAN SAMARI

KARANTA BABBAN KALUBALEN DAKE GABAN SAMARI

Daga cikin manyan kusa-kurai da Samari keyi a wannan lokaci shine barin zuciyarsu ta rinjaye su faɗawa soyayya da wacce basu gama sanin aihinin tarbiyyarta, addininta da nagartarta ba. Sai anyi aure ayi ta tashin-tashina zama yaƙi daɗi.


Rayuwar Samari a Wannan Zamanin


Marubuci: Imam Aliyu Indabawa

Soyayya gaskiya ce, kowa da irin kawazucin shi, amma kada ka yarda siffar mace ko iya kalamanta da wayewar ta su dulmiyaka cikin sonta, saɓanin tarbiyya da nagarta, domin kowanne namiji burinshi bai wuce samun mace tagari da zata kyautata mishi ta tarbiyyantar mishi da yara su zamo nagari ba.

Na jima ina ji ana faɗin wasu maganganu game da So cewa wai cuta ne kuma baya shawara, wannan magana ce mara makama balle tushe, a wajena wannan shaci faɗi ne kawai wanda bai taɓa faruwa dani ba kuma bazai faru ba. Kowa da irin kawazucin shi, wani karfin kawazucinshi yakan rinjaye jarumtarshi, amma ni kam jarumtata ta zarce karfin kawazucina, Wannan itace halittata kuma kaddarata.

Alaji Siffar mace, kwalliyarta, kwalisarta ko yauƙinta bai taɓa sawa naji ta burgeni, nayi mu'amala da mata iri-iri amma babu wacce tunaninta ya taɓa zuwa min akan shimfidar bacci na, tabbas ina son mace mai kyau da ado gami da aji, amma waɗan nan abubuwa sam basa tasiri cikin zuciyata, idan akwai abinda zai min tasiri bai wuce tarbiyya, addini da nagarta ba.

DUBA WADANNAN:

KARANTA ALAMOMI 10 DAZAKA FAHIMCI MACE TANA SON KA

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARII

KARANTA LAIFIN ME MALAM DR ISA ALI PANTAMI YAYI WA 'YAN KWANKWASIYYA SUKE KOKARIN HALLAKA SHI?

Hajiya kada mu'amala ta hadamu dake kodai ta zahiri ko chatting ki tunanin zaki min girman kai ko rainin hankali kamar yadda kikewa sauran maza, duk kyan siffarki, bokonki da kudin babanki, ko kallo baki isheni ba wallahi, bana jura rainin wayo kuma bazan jure ba, ni ba kowa bane kuma bani da komai, amma ni mutum ne da ban yarda da wulakanci ko rainin hankali daga wajen mata ba, wannan shine sanin martabar kai.

Allah ka zaɓa mana abokan zama na nagari Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Sunday, 10 May 2020

Karkai Aure Har Sai Ka Karanta Wannan Shawarar Mai Muhimmanci Ga Masu Niyyar Yin Aure Maza Da Mata

Karkai Aure Har Sai Ka Karanta Wannan Shawarar Mai Muhimmanci Ga Masu Niyyar Yin Aure Maza Da Mata

Alaji kada matsuwar gwaurantaka ta ingiza ka yin aure alhalin baka gama shiryawa ba, damuwar da zaka shiga a rayuwar aure sai ta zarce wacce kake ciki a sa'ilin da baka da aure, ci gaba da haƙuri har Allah ya kawo maka mafita ka tabbatar da zaka iya riƙe kanka, matarka da 'ya'yan da zaka samu.

SHAWARA CE...

Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa

Domin hakan na yawan faruwa ga matasa, sai daga baya a zo a shiga tsilla-tsilla, ni fa a ra'ayina babu yadda za'ai na taro aure idan har banfi ƙarfin dubu ɗari a kowanne wata ba, ba zan iya barin matata da shinkafa da wake da mai ba kullum, ni da ita yakamata mu sami canji a rayuwar gidan iyayenmu, amma fa wannan ra'ayina ne, alaji ko dubu arba'in kake samu indai ka haɗu da mai sonka da gaskiya wataƙila zata iya ɗaurewa.

Hajiya kada ki yarda takurawar iyaye ko gulmace-gulmacen mutane ya ingizaki auren wanda bashi da sana'a, ko wanda bashi da kyawawan ɗabi'u da addini, halin da zaki sami kanki bayan aurensa sai yafi tsanani fiye da rayuwar da kike a gaban iyayenki, komai girman da kikai a gaban iyayenki idan miji ya zo miki, kiyi bincike sannan ki aminta da batun aure, domin neman abokin rayuwa baya buƙatar gaggawa, sannu-sannu yake buƙata, bincike, nazari uwa uba addu'a.

Allah ya zaɓa mana abokan zama mafi alkhairi Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 11 June 2021

Dalilan Yin Soyayya Da 'Ya'yan Masu Kudi

Dalilan Yin Soyayya Da 'Ya'yan Masu Kudi

Duk da mummunar fahimta da ake yi wa 'ya'yan masu kuɗi 'yan mata, ta wata fuskar sun fi 'yan matan talakawa iya soyayya. 'Yar gidan Maikuɗi in dai tana son ka za ka sami zallar soyayya wacce ke tare da halacci gami da sadaukarwa.


Soyayya Da Ƴaƴan Masu Kuɗi


Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa


Har ga Allah kashi casa'in na matanmu na Arewa musamman irinmu 'ya'yan gidan talakawa da wahala ka ga sun so mutum saboda Allah sai sun ga akwai wata maslaha ta su, maslahar ita ce mutum maikuɗi, wanda hakan ke sabbaba musu nadama mai tsanani daga baya.


Yau ɗin nan mun tattauna da maza guda biyu waɗanda 'yan matansu suka ƙi aurensu sakamakon raina abin da suke samu. Yau waɗannan mata suna cikin matsaloli a ɗakunan mazajensu sakamakon son zuciyarsu, su kuma mazajen yanzu Allah ya rufa musu asiri su na rayuwa mai annashuwa da matansu.


Addini ma bai yarda ki auri wanda ba shi da sana'a ba. Amma dai a rage dogon buri ba wanda ya san inda rana za ta faɗi. Wani abun da ke burge ni da 'yan mata 'ya'yan masu kuɗi shi ne rashin girman kai da wulaƙanci saɓanin 'ya'yan talakawa irinmu. Akwai wacce muka yi ƙawance da ita a baya, wallahi 'yar gidan hamshakin maikuɗi ce babanta ma ba a ƙasar nan yake zaune ba, babban mutum ne a Canada  duk da a Arewacin Najeriya aka haife ta amma tana Burtaniyya tana karatu, na yi mamakin yadda ta neme ni da mu'amala kuma take matuƙar girmama ni a matsayina na wanda ke tsagin 'ya'yan talakawa. An ce 'yar maikuɗi idan tana son ka za ta yi ƙoƙari ta ga an cicciɓa ka kai ma ka tsaya da ƙafafunka, na san mutane da dama da aure ya mayar da su masu arziki.


Sai dai an ce kashi tamanin na auren jari akwai tarin ƙalubale a cikinsa, an ce mutum dole ya shirya rayuwa da wulaƙanci daga wajen matarsa. Mu kuma ba zamu juri wulaƙanci ba, wannan ya sa hatta 'ya'yan talakawan ma 'yan uwan mu muka ƙi mu'amala da su saboda ba a raba macen hausawa da wulaƙanci gami da girman kai mafi yawansu, gudun wulaƙanci ko gori ya saka na sha alwashin ba zan auri maikuɗi ko 'yar gidan masu kuɗi ba.


Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi. Su kuma matanmu na hausawa ya kamata su yi karatun ta-natsu su gyara ɗabi'arsu.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tuesday, 16 April 2019

KARANTA KAJI: DARASI GAME DA HARIN MASALLACIN KASAR NEW ZEALAND - Aliyu Imam Indabawa

KARANTA KAJI: DARASI GAME DA HARIN MASALLACIN KASAR NEW ZEALAND - Aliyu Imam Indabawa

A wannan maqaala zanyi tsokaci ne bisa darasin daya kamata a tsinkaya game da harin 'yan uwa musulmi a kasar New Zealand, musamman garemu musulmi da kuma wadanda ke adawa musulunci.






Marubuci: Aliyu Imam Indabawa

Duk Musulmin dake da kaifin Kwakwalwa gami da karfin tadabburi zai dauki darasin rayuwa game da irin karamcin da musulunci ya samu a kasar New Zealand bayan harin da aka qaddamar.

A wancan lokaci mun ga yadda aka dinga gudanar da kiran sallah a sassan duniya, da kuma yadda Shugabannin kasar New Zealand suka nuna damuwarsu da tausayawarsu ga musulmi matuka, inda Prime Minister wannan qasa ta lazamci saka Hijabi na dan wani lokaci don girmamawa ga musulmi, Haka nan wannan mata munji yadda ta janyo hadisin Manzon Tsira S.A.W. idon duniya, mun ga yadda aka dinga watsa khudubar juma'a a gidajen TV a sassan duniya. Haka nan mun kalli yadda Gwamnatin wannan kasa ta bayar da damar karanta Al'qurani mai girma a majalisarta tare da girmama 'yan uwanmu Shahidai.

Har ila yau dai, mun ga yadda dubbun nan 'yan kasar wadanda ba musulmi ba sukai fitar dango domin zaman makoki ga musulmi, wannan kadai ya ishi ya taba zuciyar me imani cewa mutuntaka ba addini bace, wata kololuwar kyautatawa ce a wannan rayuwa.

KALUBALE GAREMU MUSULMI.

Kada kishin Addininmu ya hanamu tausayawa wadanda aka zalunta koda ba musulmi bane, wannan shine tubalin da aka gina addininmu akai, idan muka duba tarihin Shugabanmu S.A.W cike yake da tausayi da jin kan raunana ciki har da yahudu da nasara, wanda hakan ya janyo dubunnan su zuwa Musulunci.

Yau a sami kisan kiristoci a wannan kasa da yawanmu murna zasu yi. Musulmin da zai jajanta laifin shi zamu gani, tabbas wannan ba hanya ce mikakkiya ba, domin addini dan siyasa ne, kuma dan nasiha ne.


DARASI GA MASU ADAWA DA MUSULMI


Masu adawa da addinin Allah su sani cewa ba'a kauda gaskiya da zalunci, Sa'banin hujja.

Mai abun fada ai baya fada.

Wannan ta'addanci da kuka kaddamar wa musulmi bai rage su da komai ba sai Daukaka, mun sami labarin yadda daruruwa ke shiga musulunci, yayin da dubbai suka fara bincike a kanshi.

Allah ya daukaka Musulunci Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Sunday, 29 September 2019

KARANTA LAIFIN ME MALAM DR ISA ALI PANTAMI YAYI WA 'YAN KWANKWASIYYA SUKE KOKARIN HALLAKA SHI?

KARANTA LAIFIN ME MALAM DR ISA ALI PANTAMI YAYI WA 'YAN KWANKWASIYYA SUKE KOKARIN HALLAKA SHI?

Na kalli wani Video wanda wasu daga ƴan kwankwasiya ke wa Sheikh Dr Isa Ali Fantami Ihun basayi, suna neman farmasa don su illata shi, wannan mummunan lamari mara dadi ya auku ne a filin tashin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Dr. Isa Ali Pantami

Marubuci: Aliyu Imam Indabawa

Tabbas wannan abun baƙin ciki da taƙaici ne garemu Kanawa da sauran mutanen kirki na Nigeria dama duniya baki daya.

Wannan ba komai bane sai Jahilci, Iskanci, rashin mutunci da dabbanci, Malam Fantami be wa wadan nan mutane laifin komai ba, idan ma yana da laifi be wuce kasancewarshi Malamin addinin musulunci wanda Allah yayi mishi ɗumbin baiwa gami da tarin ni'ima wanda babu dan siyasar dake da irinsu a kasar nan. Wanda ke kokarin kare addinin Allah da Sunnar Manzonshi S.A.W da ƙoƙarin ɗabbaka tauhidi da Suburbudar Jahilai masu izgilanci wa Allah da addininshi.

Alaji ita fa Siyasa ra'ayi ce, idan jin haushin Ni'imar da Allah yayi wa Malam yasa kake ƙokarin mishi ɓatanci me zai hanaka ƙokarin neman irin ilmin addininshi da bokonshi? Me zai hanaka neman fasaha da azanci  irin na Malam? Me zai hanaka lazimtar kyawawan ɗabi'u irin nashi irinsu takawa da tawadi'u?  Sai kazo kana Hauka da sunan siyasa, da wane yace maka dole sai kayi? Wannan ba komai bane sai hassada daga wajen mutane marasa daraja wanda basu sami tarbiyyar siyasa ba, waɗanda basu yarda da cewa Allah yana daukaka wanda yake so cikin bayinshi ya kaskantar da wanda yaso ba.

Ko kaɗan be kamata ace magagin Hassada da rashin mulki yasa kuyi rashin mutunci ga Malamai masu daraja irin Fantami ba, amma ba abin mamaki bane, Domin babu ta yadda barewa zatai gudu ɗanta yayi rarrafe, wannan muguwar ɗabi'a ba bakuwa bace a Jahar Kano, domin an sha ambatar malamai anawa Gemunsu izgilanci.

Wadannan yara masara daraja ba Malam suka wulakanta ba, Addinin musulunci suka wulakanta, duk wanda ya wulakanta musulunci Manzon Allah ya wulakanta, duk wanda ya wulakanta Manzon Allah S.A.W Allah ya wulakanta. Duk me wulakanta Allah da Manzonshi Tsinanne ne duniya da lahira.

Manzon Allah shine ya umarce mu cewa" Ku girmama Malamai domin su magada Annabawa ne." Yau an sami wasu marasa daraja suna wulakanta malaman nan da Annabi yayi mana wasici da girmamasu, ta yaya wannan al'umma zata ga abinda take so.

A karshe mu Kanawa mutane ne masu daraja da addini, mun barranta daga wannan Jahilci, bamu aikata ba, wasu bara-gurbin cikinmu ne suka aikata, bamu ji daɗi ba, bama goyon baya, muna Allah wadai da haka.

Ba Fantami ne ya kayar daku a zaben Jahar Kano ba Ganduje ne, ba kuma Malam ne yayi sanadin fara azumin irin na siyasa wa jagoranku ba son zuciyarshi ne, ba kuma Fantami ne ya baiwa kansa muƙamin dake rike dashi wanda kuke hassada ba Allah ne, to mene laifinsa da kuke ƙokarin hallaka shi? Laifin fantami be wuce raddi da yayi wa jagoranku ba na sukar hallitar Allah da yayi. Kuma malam yayi dai dai, domin ba'a kyale mutum indai ya taɓa Allah kowaye.

Masu magana sunyi gaskiya da suka ce" Kowanne tsuntsu kukan gidansu yake yi" kuma kowa yana bayar da kyautar abinda yake dashi ne, wannan mummunar ɗabi'a ta cin mutunci da zage-zage wa Malamai, Sarakuna da manyan gari sai ka wahala kafin samun wanda bai da ita cikin waɗannan yara marasa daraja, (ana samu) domin a haka madugunsu ya ɗorasa kuma koyi suke dashi.

Duk wanda ke bibiyar tarihin siyasa a jahar kano yasan wannan mummunar ɗabi'a ta jagoransu itace silar rasuwar Sarkin Kano na gaskiya Dr Ado Bayero rahimahullah akan mas'alar naɗin wazirci, wanda har yau mu kanawa bamu sami Sarki irinsa ba, kuma bamu daina baƙin cikin rashinsa ba.

In Iskanci kuke ji dashi me ya hanaku yiwa irinsu Dr Yabo Sokoto abinda kuke wa Malam Fantami? Malam yabo da yace "duk Nigeria ba'a taɓa Jahili irin Kwankwaso ba," saboda ɓatanci da akace yayi wa Shugaban halitta S.A.W kenan saboda Yabo ba kanwar lasa bane idan kuka ci mutuncinshi ba zai kyale ba sai yayi wa Jagoranku ninkin yadda kukai masa saɓanin Malam Fantami mai hakuri da kawaici.

Ko a Shekarar 2011 a lokacin data bayyana Kwankwaso ya sami nasarar lashe zaɓen Gwamnan Kano aka sami wasu ƴan iskan gari marasa mutunci maza da mata sukai tsirara suka ɗauki kwalaben giya suka je gidan Sheikh Umar Sani fagge suna mishi Shegantaka wai an kashe shari'a a Jahar Kano.

Tabbas babu abinda ke cikin Kwankwasiyya sai bala'i, musiba da rashin alkhairi, a shekaru shida baya nayi amma yanzu ba nayi, domin na gano Qungiya ce da babu addini,  tarbiyya da kyakkyawar manufa, sai Hassada, ƙyashi da baƙin ciki, babu abinda ake koyarwa sai rashin mutunci, Hegantaka , ta'addanci da aika-aika, yanzu idan kuka hallaka mana Sheikh Fantami a ina zamu sami madadinsa?

Ina tuna shekarar 2011 lokacin da nake Kwankwasiyya idan aka fito "rally" tun sha biyun rana jagorori basa tsayawa suyi sallah har zuwa dare  bayan an gama, sai dai wanda yake so yake yayi kayarsa, amma banda jagororin dake kan mumbari, cashewa kawai suke da waqar Kwankwaso dawo- dawo ko ruwa Baba ruwa, ƙatulan maƙatulan dasu ko kunya basaji, kuma da an fara magana ba wata maganar arziki da ake a wajen banda cin mutunci da habaici. Nagode Allah dana jima da fita daga wannan musiba. Domin duk wanda ke cikinta sai ta illata shi.

Wallahi babu wani cigaba a tafiyar  Kwankwasiyya sai tsantsar riya da propaganda, duk me bibiyar siyasar Kano da idon basira yasan haka, bani da ra'ayin cin mutuncin kowa a siyasa, shi yasa ko Jam'iyya bani da, amma ba zamu lamincewa iskancinku da hegantakarku akan Malamanmu ba, da sannu zamu saka ƙafar wando ɗaya daku a sannan ne zaku san abinda ake nufi da haƙikanin Saukale.

Na rasa meke damun al'umarmu ta arewa mafi yawancinmu ƙiyayya da adawa sun makantar damu, yau mene laifin Dr Isah Ali Fantami don ya karɓi mukamin minista? Siyasa halastacciyar abace, domin zamanin Annabawa da Sahabbai anyi ta.

Don haka kamata yayi ga duk wani mutumin kirki yayi farin ciki da hakan, domin samun Malam a matsayin ministan Sadarwa ba ƙaramin alkhairi bane ga gwamnatin Nigeria da Sauran jama'ar gari, kuma hakan alkhairi ne, martaba ne da gata ga addinin musulunci.

Masu cewa wai don a ramawa kura aniyarta aka baiwa Malam wannan mukami lallai sun cika mahassada, domin Malam baya Nigeria ma a shekarar 2015 da aka gudanar da zabe, yana Saudiyya, kuma malam bai zo gida Nigeria don ya gyara miyarsa ba, yazo ne domin ya hidimtawa ƙasarsa ta hanyar ilmi da baiwa da Allah ya bashi, domin abinda yake samu a can Saudiyya yafi wanda zai samu a nan nesa ba kusa ba.
 
Amma an sami wasu Jahilai munafukai suna sukar Malam wai a matsayinsa na malami be kamata ya shiga Siyasa ba, to ai siyasa bata haramta ba, asalima anfi son mutanen kirki irinsu Malam Fantami su shigeta. Ita kanta kalmar Siyasa an samota ne daga luggar Arabiya, ana cewa masdar dinta  سياسة fi'ili madhi shine ساس mudhari'i kuma shine يسيس fi'ili Amri kuma سس،
masana sukace ta'arifin siyasa shine

" ﻭﻫﻲ ﺍﻟﻘﻴﺎﻡ ﻋﻠﻰ شىء ﺑﻤﺎ ﻳﺼﻠﺤﻪ"

"shine tashi akan wani abu da abunda zai gyara shi."

Idan muka koma harshen turanci ana kiran siyasa da "Politics" "pä-lə-ˌtiks" Noun kenan, koda yake definition na politics nada matukar yawa a wannan harshe, amma bari na dauki guda daya kacal.

"Politics is Activities aimed at improving someone's status or increasing power within an organization"

"Siyasa wata harka ce da aka tsara akan Wasu ayyuka da niyyar tabbatar da matsayin wani, ko karin karfi cikin hadakarJama'a." (Fassara mai 'yanci)

Tsohon Shugaban kasar America na 34th Dwight D. Eisenhower ya bayyana siyasa kamar haka:

"Politics ought to be the part-time profession of every citizen who would protect the rights and privileges of free people and who would preserve what is good and fruitful in our national heritage."

"Ya kamata siyasa ta zama takaitaccen aiki ga kowanne ɗan ƙasa wanda zai kare haƙƙi da gatan mutane masu ƴanci, wanda kuma zai tanadi abinda yake mai kyau da shirya kyakkyawan sakamako a cikin ƙasarmu ta gado"

Dr. Isa Ali Pantami

Siyasa tanada matukar fadi a wannan harshe, akwai political philosophy wanda akafi sani da political theory, da Political science, haka nan idan muka duba litattafai irinsu "The shook doctrine" wanda Naomi Klein ya wallafa, da irinsu "The Rascal King" na Jack Beatty da irinsu "A foreign policy of freedom" cike suke da concepts na Siyasa.

Ashe kuwa siyasa bata nufin komai sai gyara, kishin al'umma da hidimta musu,  umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, jagoranci, gogewa kwarewa a zamantakewa, Iya mu'amala wayewa, Hakuri, rama Alkhairi ga Sharri, Jan ra'ayoyin mutane cikin hikima da dabara, shi yasa duk mutumin daya iya zama da mutane ake ce mishi dan siyasa, wannan yasa Dr Sani Rijiyan Lemo a cikin tafsirinsa ya ta6a cewa" duk duniya ba'a ta6a dan Siyasa kamar Annabi S.A.W ba," wanda maganar ta bawa mutane da dama mamaki, shin mene abun aibu don Dr Fantami yayi siyasa?

shi yasa Alfazazi me Littafin Ishiriniya cikin yabon da kewa Annabi yayi Amfani da Kalmar Siyasa yace"

و ساس بذاك الخلق لينا و شدة

ya Jagoranci mutane, ya sauqaqa a inda ya dace, ya kuma tsananta a inda ya dace.

bayan haka idan muka duba rayuwar Manzo S.A.W da Mulkin Khulafa'urrashidin zamu iske cike yake da  siyasa, idan mutum ya koma littafi irinsu السياسة الشرعية na Ibn Taimiyya ko kuma irinsu

(1)ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺴﻴﺎﺳﺔ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻓﻲ ﺇﺻﻼﺡ ﺍﻟﺮﺍﻋﻲ ﻭﺍﻟﺮﻋﻴﺔ

(2) ﻏﻴﺎﺙ ﺍﻷﻣﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻴﺎﺙ ﺍﻟﻈُّﻠَﻢ

(3)ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻧﻴﺔ ﻭﺍﻟﻮﻻﻳﺎﺕ ﺍﻟﺪﻳﻨﻴﺔ

Duk wanda ya duba wadan nan Litattafai zai gane cewa Addini yana tare da siyasa, idan babu siyasar to Addini bazai samu cigaban da ake so ba, masanin tarihi na ƙasar England George Edward ya siffanta siyasa a matsayin komai da ruwanka inda yake cewa":

 In our age there is no such thing as 'keeping out of politics.' All issues are political issues.

" A wannan Zamani namu babu wani abu da za'a fitar dashi daga Siyasa, dukkanin Lamura lamuran siyasa ne"

idan muka koma Alqur'ani akwai ayar dake cikin suratut tahrimi ayata 8 wacce Allah ke Umarnin Annabi kan yayi Jihadi ga kafurai da munafukai, ya kuma tsananta akan Jihadin,
ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺟﺎﻫﺪ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ ﻭﺍﻟﻤﻨﺎﻓﻘﻴﻦ ﻭﺍﻏﻠﻆ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﻣﺄﻭﺍﻫﻢ ﺟﻬﻨﻢ ﻭﺑﺌﺲ ﺍﻟﻤﺼﻴﺮ

Malaman tafsiri karkashin wannan ayar sukace Jihadin Addinin musulunci Guda biyar ne, ciki kuwa har da Jihadin Siyasa, wannan jihadin guda biyar sune الجهاد المالى Shine Jihadin fitar da kudi don Taimakawa Addini, da الجهاد التعلمى shine Jihadin Koyar da Ilmi, na Addini kona zamani, sai الجهاد باليد shine Jihadin Amfani da hannu wajen Umarni da Kyakkyawa da hani da mummuna,  الجهاد باللسان shine Jihadin Amfani da harshe wajen fadin gaskiya a inda ta dace, sai الجهاد السياسي shine Jihadin Siyasa, Shine ka shiga Siyasa don ka taimaki Addinin musulunci, kamar yadda malam yayi muke koyi dashi.

Yana daga dalilan daya saka yau  muke cizon yatsa a kasar nan nokewar da malamai da mutanen kirki suka ki shiga a dama dasu a harkokin Gomnati, wannan ya samo asali ne daga kallon da mutane kewa siyasa da 'yan siyasa, aka bar mutanen da basu damu da addini ba suke Jagorantarmu, yau wadan nan shugabanni suke daure gindi ana sabon Allah maimakon hanawa, yau su ke aikata  abubuwan da suka sa6a da addini a bayyanar jama'a, yau su ke Girmama Fasikai da mutanen Banza Maimakon Mutanen Kirki, su ke bari yahudawa ke shigowa da munanan manufofi su yada cikinmu, wannan be ishe mu abun kunya ba?

bazamu ta6a daina cizon yatsa a wannan kasa ba, muddin malamanmu da mutanen kirkin cikinmu basu yunkura sun shigo siyasa don tsaftace ta ba, garemu masu dangwale, Tsohon Shugaban kasar Amurka Abraham Lincoln dai na cewa" The ballot is stronger than the bullet. "kuri'a tafi bullet Karfi da amfani,"

Don haka nagarta itace tushen nasarar komai, ita kuma nagarta ba'a samunta sai da Addini, wannan yake nuna lallai babu mutumin daya cancanta ya shiga siyasa sai mai Addini, shi yasa Gogaggen dan siyasar nan na kasar faransa Alexis de Tocqueville ke cewa"

Liberty cannot be established without morality, nor morality without faith"

" 'Yanci bazai kafu ba batare da nagarta ba, haka nan kuma bazai kafu da nagarta kadai ba, batare da Imani ba"

Ashe bai ishe mu darasi ba yadda kiristoci ke shiga harkar siyasa dumu-dumu a ƙasar nan suna taimakon addininsu tare da cutar da namu addinin? Ko Me yasa saɓanin siyasa baya sa kiristoci sukar mataimakin Shugaban ƙasa Pastor Osinbajo kan shiga siyasa? Bayan ance akwai coci dubunnai a karkashinsa, dalili shine su sunfi girmama addininsu fiye da ra'ayinsu, saɓanin mu da muke fifita son zuciyarmu akan addininmu.

Alaji rainin hankali ne ma ka dubi matashi wayyaye mai ƙwaƙwalwa ɗan boko irin Malam gogagge ƙwararre, jajirtacce hafizin Alqur'ani masanin shari'ar Musulunci, mai hikima da zalaqar zance, mai ɗumbin baiwa kace wai kada ya shiga siyasa, idan su malam basu shiga siyasa sun kyautatawa al'umma da addini ba suwaye zasu shiga?
Mu masoya Malam munsan jihadin can da nayi bayani a sama shine silar shigar Malam siyasa kuma ko yanzu Malam ya bar siyasa kwalliya ta biya kudin sabulu domin ya farfaɗo da darajar malaman addini da musulunci. Kuma insha Allah indai muna raye Malam yayi ta samun cigaba da daukaka kenan a rayuwarshi. Insha Allah muna ji a jikinmu cewa wata rana Malam sai ya zama Shugaban Nigeria, kuma wannan dama alkawarin Allah ne wa mutanen kirki cikin Alqur'ani.

Allah yace"

ﻭﻋﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻣﻨﻜﻢ ﻭﻋﻤﻠﻮﺍ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﺎﺕ ﻟﻴﺴﺘﺨﻠﻔﻨﻬﻢ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻛﻤﺎ ﺍﺳﺘﺨﻠﻒ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻬﻢ"

"Allah yayi alƙawarin wa muminan daga cikinku wadanda sukai kyakkyawan aiki zai basu mulki a ban ƙasa kamar yadda ya bayar ga waɗanda suka gabace su.

A wani wajen kuma Allah yace"

ﻭﻟﻘﺪ ﻛﺘﺒﻨﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺰﺑﻮﺭ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﺃﻥ ﺍﻷﺭﺽ ﻳﺮﺛﻬﺎ ﻋﺒﺎﺩﻱ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﻮﻥ"

"Hakika mun rubuta cikin zabura (littafin Dauda A.S) bayan ambato mulkin kasa wa salihan bayi zamu bayar dashi"

Kalmar  الذكر Wato ambato da tazo cikin ayar nan. Malam Mujahid yace littafin Zabura ake nufi, yayin da Malam Ibn Abbas yace Alqur'ani ake nufi.

DUBA WADANNAN:

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa?

Kalli Yadda Aka Kashe Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto A Kan Idona-Inji Direban Sardauna

KARANTA KAMA DARACTAN FILM A KANO ZALUNCI KO ADALCI?

Wata ayar kuma Allah yace"

 ﺇﻥ ﺍﻷﺭﺽ ﻟﻠﻪ ﻳﻮﺭﺛﻬﺎ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻣﻦ ﻋﺒﺎﺩﻩ ﻭﺍﻟﻌﺎﻗﺒﺔ ﻟﻠﻤﺘﻘﻴﻦ

"Shi mulki na Allah ne yana bayar dashi ga wanda yaso cikin bayinshi, amma kyakkyawan karshe yana ga masu tsoron Allah"

Allah ka taimaki Malam Fantami ka kiyaye shi daga sharrin mahassada kai riko da hannayensa Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Wednesday, 28 August 2019

KARANTA KAMA DARACTAN FILM A KANO ZALUNCI KO ADALCI?

KARANTA KAMA DARACTAN FILM A KANO ZALUNCI KO ADALCI?

Na kalli videon waƙar da tasa Hukumar tace finafinai karkashin Jagorancin Malam Isma'il Afakallahu suka ƙwamushe wani daractan film me suna Sunusi Oscar zuwa gidan Yari, tabbas videon ya munana duba da rashin mutunci da iya hegen dake cikinsa.


Wakar da tayi sanadin kama Darakta Sunusi Oscar442


Marubuci: Aliyu Imam Indabawa

Mutane daban daban-daban sun tofa albarkacin bakinsu, sai dai bisa dukkan alamu da yawa suna tuya ba tare da albasa ba, duba da yadda suke dukan taiki su kyale jaki, a wannan gaɓa zan so nayi tsokaci wanda masu neman gaskiya zasu fahimta.

Duk wanda ya sanni a baya zai tabbatar da bana ga muciji da Jagoran Hukumar tace fina-finai na Kano Ismail Afakallahu, mun sha tataburza dashi a wannan saha, har ƙarar shi muka kai wajen hukumar muhyi magaji wato hukumar nan da ake kira "Public complaints and anti corruption" Hukumar ƙarbar ƙorafe ƙorafe da yaƙi da rashawa, ga wanda ya san wannan hukuma yasan tana da hurumin tsige Afakallahu daga mukaminsa, mun kai ƙorafin ne bisa sakaci dashi Afakallahun yake ga irin waɗan nan Videos na baɗala da iya shege, ban taɓa yabon Afakallahu na rana guda ba, na ƙwarzabe shi, na caccake shi na sossoke shi a baya, amma dole ya sami adalci a gareni a yau.

A taƙaice dai babu maganar zalinci cikin hukuncin da aka yanke wa Shakiyin darakta Sunusi Oscar domin dokar daya taka itace ta taka shi, da yawan mutane basu san irin ƙarfin da hukumar tace fina finai ke dashi ba, shi yasa suke ta tsetsegulo, ita wannan hukuma an kafa ta ne a Majalisar Jahar Kano shekarar 2001 ƙarkashin shugabancin Rabi'u Musa Kwankwaso, an bata damar kama duk wanda ya aikata ba dai-dai ba ta ɗaure shi ta kuma ci shi tara.

Darakta Sunusi Oscar442


Masu magana na cewa" A idaniya ake zawurya" Bari dai mu garzaya babban kundin wannan hukuma me suna " Censorship regulations" da kuma ƙaramin kundin me suna " Arrangement of the State Censorship Film Board Law 2001, wanda yake da Sassa 22. Mu shiga cikin sashe na 9 cikin Karamin Sashe na 2 na cikin baka me yace? 9

(2) The Board May, By Order, Ban,
Suspend or Prohibit The Production, Distributions, Sales or exhibitions of Any Film, Pornographic Books Or Publications In the State, Where in the opinion Of the Board it is offensive to public morality And decency.

Hukuma zata iya umarni ko ta hana, ko ta dakatar, ko ta haramtar da duk wani shiri wanda za'ayi a rarraba shi, ko a siyar dashi a kasuwa, ko wani film da za'a haska shi a sinema, ko mujallun batsa, ko bugaggun litattafai a garin, wanda hukumar ke ra'ayin cewa abun nan Laifi ne kuma zai cutar ga tarbiyya da nagartar mutane.

Za'a iya siffanta ƙarfin wannan Hukuma da ƙarfin Allah ya isa, don be tsaya iya nan ba, bari mu Garzaya Babban kundin mai suna "Censorship Regulations"  Mu shiga sashi na 98 karamin sashin C na cikin baka, ga Abinda yace"
(98)
(C) Advertises or makes Known by any Means whatsoever with a view assisting the circulation of, or traffic in, any such matters or things, that a person is engaged in any of the acts referred to in this section, or advertises or makes known how, or from whom, any such matters or things can procured either directly or indirectly; or
(D)publicly exhibits any indecent stage show or performance , play or any Show or performance tending to corrupt public morals, is guilty of an offence and is liable to imprisonment for 3 months or to a fine or to both such imprisonment and a fine.

(C) Tallace tallace ko samar da sanin wani abu, ta ko wace manufa ta koma yaya ne, tare da taimakawa wajen yaduwar abun, duk wadan nan abubuwan wanda mutum zai aikata suna komawa ne akan wannan sashi, ko tallace tallace ko samar da sanin abu kota yaya, ko daga wajen waye, duk waɗan nan abubuwa wanda mutum zai aikata kodai kai tsaye ko ba kai tsaye ba Ko
(D) Abinda za'a haska a cikin mutane, wanda ya sa6a da tarbiyya da nagarta, irinsu wasan da ake tara mutane ayi shi, (irinsu gidan rawa da kalankuwa da irinsu bikin party dasu D.J da sauransu,) ko abin da za'a kunna shi, ( irinsu fina finai da gidajen TV da gidajen Redio da sauransu) da duk wani abu da za'a nuna ko ayi shi, muddin abun zai janyo lalacewar Nagartar Mutane, to haka aikata laifi ne wanda zai janyo wa mutum daurin wata uku, ko a ci shi tara, ko duka biyun da daurin da kuma biyan tarar.

Akwai dokar da tace idan an so ma za'a iya yiwa mutum ɗaurin shekaru masu yawa domin ya zamanto darasi ga sauran, tsawaita wa ne banaso. Allah ya saka wa Dr Abubakar rabo Abdulkarim bisa ƙokarin ɗabbaka wannan doka.

Saboda haka Malam Afakallahu ya cancanci yabo da ƙarfafa gwiwa domin ya ɗore akan aikata doka, idan kuma ta tabbata tsuntsu biyu ya jefa da Hoge guda kamar yadda wasu ke faɗa wato anyi kamun ne don siyasa, sai muce yaji tsoron Allah ya sani Allah da Manzonsa S.A.W da addinin Islama sune suka fi cancanta a tsare haqqinsu ba Ubangidansa Ganduje ba.

Amma bamu san zuciyarshi ba, ba zamu mishi hukunci ba, ni bana Gandujiyya bana Kwankwasiyya, muna yaba mishi akan wannan hoɓɓasa, muna fata nan gaba zai mai da hankali ya ɗauki salon nan na ba sani ba sabo irin na Malam Abubakar rabo, ba ɗan Gandujiyya balle Kwankwasiyya kowa yayi a hukunta shi, har ila yau dai muna ƙara yabon shi bisa tsarin Malam Abubakar rabo da ya dawo dashi na tace waƙokin Yabo wanda Sha'irai ke furta kalaman da basu da kyau.

DUBA WADANNAN:

JARUMI SADIK SANI SADIK YAYI ABIN DA BABU WANI DAN FILM DA YA TABA YI A TARIHIN KANNYWOOD

Kalli Kayatattun Hotunan Jaruma Maryam Yahaya Na Wannan Makon

DAGA YAU DOLE NE SAI MASU TARBIYA NE ZASU YI FINA-FINAN HAUSA - SHEHU HASSAN KANO

Muna fata Malam Afakallahu zai tabbatar wa da Ubangidansa Sunan Khadimul Islam da ake mishi laƙabi ta hanyar tsaftace addini da tarbiyya daga sharrin ƴan iskan gari maɓarnata.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode