Showing posts sorted by relevance for query Sheikh Aliyu Sa'id Gamawa. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Sheikh Aliyu Sa'id Gamawa. Sort by date Show all posts

Saturday, 4 January 2020

Shin ko Me ne ne Yasa Maza Suke Neman 'Yan Uwan su Maza domin yin Luwadi?

Shin ko Me ne ne Yasa Maza Suke Neman 'Yan Uwan su Maza domin yin Luwadi?

'Yan uwa mun shiga wani zamani mai juyawa yana canzawa daga nasara zuwa hasara, wassu kuwa daga bata zuwa shiriya, ko daga zaƙi zuwa daci.

Babban Bala'i Babbar Masifa Neman Maza (Luwaɗi)

Marubuci: Sheikh Aliyu Sa'id Gamawa

Dan adam ba dabba bane, ƙazanta ba tsabta bace, aikin zunubi baya taɓa zama lada ko shiriya har sai an tuba an koma ga Allah an nemi tsira da rahmar Allah.

Tabbas komi da kowa ikon gudanar da rayuwar sa na hannun Allah koda waye shi.

Naji damuwa da tausayin jin yadda kazamiyar dabi'ar dabbanci ta Luwadi da Madigo ya yawaita tsakanin al'ummar mu ta yau musamman matasa da wassu masu dukiya.

Mafi yawan su har kungiya ko ƙawance sukeyi da lalata juna, ana bin jinsi ba tsoron gamuwa da Allah. Ana bayyana komi a fili ba tsoro ko kunya.

To mu sani duk ma suyi don tsafi, da masu yi don bin umarnin bokaye, da masu biyan buƙatar sha'awar su ta wannan kazamiyar hanya to basu da makoma a duniya da lahira sai halaka da cutar da kansu da gadar da wulakanci ga rayuwar su da zuriyar su.

Mu tuna tarihi a baya Allah ya aiko da hani akan waɗannan mummunar hanya, kuma an kifar da masuyin wannan aiki da halakar dasu. Sannan hanya ce ta kaskantattu da yaɗa cuta a junan su.

Ga mugun aikin yana da wuyan bari, kuma yana busar da zuciya. Kuma ana samun gafala da yin nesa ga kwaɗayin rahamar Allah ga mai wannan aiki. Munafurci da yaudarar juna na yawaita tsakanin masu wannan aiki da ƙyamar juna a rayuwar su.

Tabbas ba alheri cikin wannan aiki sai nadama da nisa daga rahmar Allah. Kuma anan duniya a fara ganin kyama da kaskanci cikin dukkan al'amurran rayuwa.

Mu tuba ga Allah, muyi kwaɗayin rahamar sa, mu ji tsoron Allah yayi fushi damu, mu godewa ni'imar rayuwa da Allah yayi mana.

Mai wannan aiki ya ji tsoron kada ya zamo masa ajali, ko aikin sa na ƙarshe yayin komawar sa ga Allah yana cikin mummunan aiki irin wannan aiki.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA MANYAN SIFFOFIN 'YAN LUWADI DA RAYUWAR SU CIKIN SIRRI KASHI NA FARKO (1)

KARANTA CUTUTTUKA GUDA 30 DA LUWADI YAKE HAIFARWA GA MAI YINSA

Karanta Babban Sako Zuwa ga 'Yan Luwadi da Wadanda Suke yin Sha'awar Harkar Luwadi - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Zai yiwu ruɗin abokai ne ya jefa ka wannan aiki, ko son duniya na kwaɗayin dukiya, ko neman shugabanci, ko bin umarnin masihirta bokaye, to duk ba zai zamo alheri gareka a duniya da lahira ba.

MU GUJI KAZAMIYAR RAYUWA DA ƊABI'A MAI HALAKARWA TUN A NAN DUNIYA DA LAHIRA.

ALLAH YA TSARE MANA ZURI'AR MU DAMU KANMU DAGA WANNAN ƊABI'A (LUWAƊI DA MAƊIGO) AMIN SUMMA AMIN.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





Tuesday, 10 December 2019

CIKIN WADANNAN MUTANE WANNE IRIN ABOKI NE DA KAI ?

CIKIN WADANNAN MUTANE WANNE IRIN ABOKI NE DA KAI ?

Dan adam a rayuwar sa yakan yi abokai da masoya iri-iri, haka kuma zai iya samun Makiya nau'i  daban-daban.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai...

Marubuci: Sheikh Aliyu Sa'id Gamawa

1. Akwai wanda zai yi da'awar Shi Masoyinka ne, amma ba zai tashi Matsowa jikinka ko kuma nuna maka soyayya ba, sai lokacin da yaga wata nasara ko ni'ima ta samu gareka.

Amma da zaran ka samu matsala a rayuwa ba zaka sake ganin sa a kusa da kai ba.

2. Akwai wanda yana nan tare da kai ko yaushe, amma duk abinda kasa a gaba sai ya tayaka kuyi. Ba ya yi maka musu, ko gyara a cikin lamarinka ko da ya ganka akan kuskure haka zai tayaka kuyi.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai..

To wannan masoyi ne amma yana da rauni, kayi hattara dashi don zai jefa ka in da ba zaka iya fita ba a duniya da lahira.

3. Akwai wanda yana tare da kai ko yaushe amma idan yaga abin alkhairi tare dakai sai ya binne labarin. Idan kuma yaga mummunan abu tare dakai sai ya watsa ma duniya. Ta wajensa ake samun Miyagun labarai game dakai.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai..

Wannan Makiri ne, Mahassadi ne. Ka nisanceshi.

4. Akwai masoyin da ko yaushe yana tare da kai a zuciyarsa haka a fili. Duk lokacin da ya ganka akan alkhairi sai yaji dadi har ya taimakeka kuyi. Idan kuma ya ganka akan kuskure Sai ya gyara maka Koda ranka bayaso. Wannan shine masoyi na gaskiya.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai..

Ka riƙeshi da kyau domin Irinsa suna da wahalar samu.

'Yan uwa mu sani a ranar alƙiyamah abokai zasu zamo suna gudun gamuwa da junan su saboda tsoron hisabi kan haƙƙin jikan su.

Haƙiƙa akwai abokai masu alaƙa don kwaɗayi da son abin duniya masu halakarwa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Shin Zan Iya Zama Sanadin Shiriyar Abokina?

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

KARANTA ABU BIYU NE KAWAI ZAKA IYA YI IDAN KA HADU DA WANDA YAFI KARFIN KA

Kuma akwai abokai na kwarai masu alaƙa don Allah.

Kuma sune masu samun shiga inuwar al'arshin Allah, waɗanda suka gina kauna da abotarsu bisa gaskiya da riƙon amanar juna sune zasu rabauta.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai..

Kuma su zama Sanadiyyar Samun rahama ga junansu.

Allah ka bamu dacewa duniya da lahira ka haɗamu da abokai na kwarai, amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Sunday, 15 November 2020

Neman Yardar  Mutane

Neman Yardar Mutane

Kada ka damu kanka sai ka yardar da kowa da kowa, Annabawa ma ba su iya cimma haka ba.


NEMAN YARDAR MUTANE

MarubuciSheikh Aliyu Sa'id Gamawa


Wanda yake ƙaunarka zai kalli abin da ka yi ya ga ya yi kyau, wanda ba haka ba kuwa zai ga mai kyau daga gare ka ya ga ya kai ƙarshen muni.


Idan abu mara kyau ya same ka sai mai son ka ya ce: Jarrabawa ce. Wanda ba ya son ka kuwa sai ya ce: Allah ne Ya kama shi.


Don haka mu fahimta.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Monday, 24 February 2020

Ka Kasance Mai Tunawa da Wannan a Tsawon Rayuwar Ka

Ka Kasance Mai Tunawa da Wannan a Tsawon Rayuwar Ka

Idan kana tuna lokacin da kake jariri, wato lokacin da baka iya komai sai dai ayi maka, dole ka ƙara godewa Allah, Allah Shine mai iko.

Rayuwa Tana Faruwa Wucewa Take..

MarubuciSheikh Aliyu Sa'id Gamawa

Idan ka dubi yadda kake a yanzu, wato ka girma har kana iya yiwa kan ka abubuwa da yawa, Tilas kace Alhamdulillahi.

Idan Allah yayi maka tsawon rai, zaka iso zangon da wata rana zaka  tsufa, ka koma komai sai dai ayi maka. Daga nan sai tuba da natsuwa da cewa Allah yasa muyi kyakkyawan ƙarshe.

Kada ka manta da tunanin barin duniya, ranar da za'a rabu da iyalai da dukiya da kome-da kome! Kai tabbas mutuwa wa'azi ce.

Ana son kana tuna cewa wata rana zaka zama gawa, yadda dangi da masoya zasu ɗauke ka su fitar da kai  daga cikin gidan ka! Allah sarki duniya, haƙiƙa rayuwar nan bata da tabbas.

Ɗan uwa wallahi Ni da kai wata rana za'a saka mu a cikin wani rami, a ƙarƙashin ƙasa a ɗora itace a rufe da ƙasa, ba komi ciki sai matsi da duhu gashi ciki babu shimfiɗa! Ba abinda zai baka sauƙi a kabari sai ayyukan da kayi na bin Allah a Duniya. Kai ɗan adam ba komai bane.

Tabbas ba makawa wata rana za a tashe mu daga kabari, a koramu filin hisabi anan ne zamu amsa tambayoyi kan yadda muka gudanar da rayuwar mu. Kai 'yan uwa akwai aiki a gaban mu.

A lahira za a tsayar da kowa domin yayi bayanin abun da ya aikata a duniya! 'Yan uwa mu faɗaka muna yiwa kanmu hisabi kafin ranar hisabin mu.

Bayan hisabi sai shiga wuta ko Aljannah.

Allah ka bamu dacewa da shiga Aljannah kayi mana tsari daga Wuta.

Haƙiƙa ba mai tabbaci na shiga cikin Aljannah! Sai nace mu nace da roƙon Allah yayi mana Rahama.

Dan Allah, mu na tunawa da cewa mutum mai rauni ne.

Allah ya zama gatan mu, Allah Kasa mu dace duniya da lahira Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.



Tuesday, 6 October 2020

Shin Ko Kasan Irin Matsayin Da Kake Da Shi A Cikin Al'umma?

Shin Ko Kasan Irin Matsayin Da Kake Da Shi A Cikin Al'umma?

Ana so a rayuwa ka yi ƙoƙari ka zama ƙofa wadda Alkhairi yake shigo ma mutane daga cikinta. Idan ka kasa yin hakan to, ka zama taga ana samun haske daga wurinka. Idan bai yiwu ba, sai ka zama bango wanda ake jingina gare shi.

YAYA KAKE A CIKIN AL'UMMA...

MarubuciSheikh Aliyu Sa'id Gamawa

Kada ka yarda ka zama kamar shanyayyen hannu a cikin al'ummah wato mai rauni maras amfani sai ɓata kama da nuna tawaya.

Kuma kada ka zamo mai buɗe ƙofar sharri ko jawo fitina da yaɗa ɓarna ga al'umma. Haka nan kada ka zamo laruri kuma nauyi da matsala ga mutane.

Mafi Alkhairi daga cikin mutane shine wanda mutane suke amfana da shi. kuma ka zamo kamar zaure ɗakin fakewa, ko bango abin jingina, ko damina uwar albarka.

Allah ya rufa mana asiri ya tsare mana imanin mu da mutumcin mu yasa mu gama lafiya, Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.