Showing posts with label Kimiya da Fasaha. Show all posts
Showing posts with label Kimiya da Fasaha. Show all posts

Sunday, 2 June 2024

Karanta Ainihin Tarihin Bitcoin Da Amfanin Shi Da Matsalolin Shi Da Hukuncin Mu'amala Da Shi A Musulunci

Karanta Ainihin Tarihin Bitcoin Da Amfanin Shi Da Matsalolin Shi Da Hukuncin Mu'amala Da Shi A Musulunci

Bismillahir Rahmanir Rahim


Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa bakiɗaya.


Bayan haka, a yau Alhamis 15 Jumada Akhir, 1442 H.-28 Janairu, 2021 M., zan amsa tambayoyin da na samu ta fuskoki da yawa game da mu’amalar zamani ta Bitcoin da sauran mu’amala irinta. Daga cikin tambayoyin akwai waɗanda suka turo da cewa: “Malam ina tambaya ne game da halaccin cinikin online da ake na su bitcoins, cdmx, cdx da sauransu. Malam menene halaccin kuɗin a addini. Na gode. Allah ya saka da alheri”.  Zan dan faɗaɗa kaɗan a wajen bada amsar har na shigo da yadda tsarin yake domin waɗanda ba su waye da shi ba daga cikin ‘yan uwa da suke cikin lugunan birane da karkara su fahimci yadda Bitcoin yake. Ina fatan yin haka ya buɗe damar tattaunawa da gano wasu hukunce-hukuncen da suke cikin wannan sabuwar mu’amala mai cike da rintsi da sarƙaƙiya, wadda malamai har yanzu suna kaiwa, suna komowa wajen yanke hukuncin da ya dace da ita. A kan wannan aka rubuta wannan amsa.


TARIHIN BITCOIN DA AMFANIN SHI DA MATSALOLIN SHI DA HUKUNCIN MU’AMALA DA SHI A MUSULUNCI
Hoto: Cryptonomist


MarubuciAhmad Murtala Mansur


Mai son ya gane wannan bayanin da kyau, to aikin karatawa gaba ɗaya ya same shi. Insha’allah kuma za a fahimta. Da fatan Allah ya ba mu sa’a da dacewa.


1- A kowane lokaci yana da kyau a riƙa sanin tarihin abubuwa da tsarin da suke tafiya a kansa, musamman irin waɗannan sababbin mas’aloli na zamani waɗanda ake kiransu da sunan "النوازل", domin a fayyce yadda za a bada amsa a kansu.

 
i- Tun a shekarun 1990, mutane irinsu Nick Szabo suka fara zuwa da wani tunani na ƙulla cinikayya a kan intanet da sunan ‘Bit Gold’. Sai dai abin bai samu yaɗuwa ba sosai. Haka nan a 1998 Bernard von NotHaus ɗan Jihar Hawai a Amurka ya yi irin wancan tunani ya ƙiriƙiro ‘Liberty Dollars’. Amma ya firgita gwamnati don haka sai da aka ɗaureshi a kan wannan aika-aika tasa. A wannan shekarar dai, gwanaye a kan kwanfiyuta ba su daddara ba, sai da wani ɗan China mai suna Wei Dai ya ƙirƙiro ‘B-Money’. Bayan haka, a 2007, jami’an tsaro a Amurka suka rufe wata manhaja a kan intanet mai suna ‘E-Gold’. 


Wannan duk bayanai ne a taƙaice na irin yunƙurin da wasu suka yi don samar da tsarin hada-hadar kuɗaɗe a kan intanet ba tare da sa hannun gwamnati ba. Amma ba su sami cimma burinsu ba. Irin waɗannan kuɗaɗen na kan intanet kurum ake kira da sunan “Cryptocurrency”.


ii- Kalmar ‘Bitcoin’ kalmomi biyu ne na turanci a haɗe. ‘Bit’ tana nufin kaɗan ko gutsure. ‘Coin’ kuma tan nufin tsabar kuɗi masu kamanni da kwabo ko ƙwandala. An fara ƙirƙiro da tsarin Bitcoin da kuma yi masa rijista a kan yanar gizo-gizo a 2008. Babu takamaimai a kan wanda ya fara ƙirƙirar wannan tsari. An zaton mutum ɗaya ne ko kuma gungun wasu mutane da sunan Satoshi Nakamoto. Takardar da mai ko masu wannan suna ya/suka rubuta da taken “Bitcoin: A Peer-to-Peer Electronic Cash System”, kusan ita ce ta fito da wannan suna na Bitcoin a fili. Amma dai an san cewa yana daga cikin irin tsarin mu’amalar kuɗaɗe ta zamani a ƙarƙashin taken ‘Cryptocurrency’. An fara ɗora manhajar Bitcoin wadda kowa zai iya amfani da ita a watan January na 2009. A cikin wannan wata ne kuma aka fara hadahadar kuɗi ta wannan manhaja da kuɗi kaɗan. Amma 2010 hadahadar kuɗin ta fi bayyana sosai.

 
Zuwa January na 2021 akwai kusan kamfanoni 2,000 na crytocurrencies. Wanda aka fi sani a cikinsu shi ne ‘Bitcoin’. Ragowar kuma ana kiransu da ‘Altcoins’ ko ‘shitcoins’, waɗanda suka haɗa da ‘Ethereum’, ‘Litcoin’, Ripple, Stellar’, Chainlink, ‘Bitcoin Cash’, da sauransu.


Yawancinsu sun samo asali ne daga fasahar Bitcoin ɗin. A ɗan wannan lokacin, bincike yana nuna cewa Bitcoin su ne kan gaba da fiye da kaso biyu bisa uku na dukan mu’amalar juya ‘kuɗadɗn-gaibu’ (Digital Money) na cryptocurrency! Don haka duk hukuncin da aka faɗa a kan Bitcoin, ragowar ma ya hau kansu, sai dai in da ƙarin wani abin daban da ya daɗa cin karo da ƙa’idojin Shari’a!

 
iii-Abin mamaki dai har yanzu shi ne, tun a 2011 mai wancan suna Satoshi Nakamato, wanda ya yi kama da sunayen mutanen Japan, aka daina jin ɗuriyarsa. Kafin ya ɓuya ya turo da bayanin cewa shi fa ya janye jiki yanzu ya bar wannan harka. Ya yi bayani ta hanyar email cewa ya miƙa wannan harka a hannun amintattu mutane kamar su Gavin Andresen da Mike Hearn. Waɗannan mutane da ma wasu da aka yi zargin ko su suka ƙirƙiro manhajar duk sun musanta cewa suna da hannu a ƙirƙirota. Don haka har yanzu ba a gama gano waye wanda ya ƙirƙiro wannan tsari ba.

 
vi- Manufar ƙirƙiro da Bitcoin ita ce a bawa mutane dama su yi hulɗa da kuɗaɗe kai tsaye ba tare da wani banki ko kamfani ko wani mutum ya shiga tsakaninsu ba. Don haka tsarin Bitcoin ba ya kulawa da wata gwamnati ko wasu tsare-tsare. Mu'amala ce ta kuɗi tsagwaranta tsakanin mutane ba wani shinge kamar dai yadda suke kiranta da “Peer-to-peer”!

 
2- Abin la’akari shi ne an ɗora tsarin Bitcoin a kan abubuwa da yawa na ilimin kwamfiyuta da mu’amalolin yau-da-gobe. Amma akwai wasu abubuwa masu muhimmanci kamar haka:


i-An gina manhajar a kan amfani da ilimin lissafi da aka fi sani da “Algorithm”, tsarn lissafi ne da ake warware matsalolin lissafi masu wahala da shi. Ilimi ne mai muhimmancin da ɗaya daga cikin masana lissafi Musulmi da aka fi sani da Muhammad bn Musa Al-Khawarizmi (780-850 M.) ya ƙirƙiro shi. Gabadaya tsarin kwanfiyuta ma a kan wannan ilimi aka ƙirƙiro shi. Shi ma Bitcoin aka zuba shi a kan wannan ilimi.


ii- An ɗora manhajar Bitcoin a irin tsarin da manyan gidajen caca na duniya suke shirya injinan da ake gudanar da caca da su, wanda aka fi sani da “Lottery-Based System”.

 
iii- Waɗanda suka ƙirƙiro Bitcoin sun ƙaddara cewa zuwa shekara ta 2140 duk manhajar za ta tsaya cak ko kuma idan adadin ƙwandala da aka samo take miliyan ishiri da ɗaya. A halin yanzu ana da sama da miliyan goma sha bakwai.


3- Wanda yake son shiga hadahadar Bitcoin sai ya bi matakai daban-daban bisa yadda kamfanonin da suke taimakawa suka tsara. Domin dai a gane yadda abin yake ga hanya mai sauƙi kamar haka:


i- Dole sai mutum ya buɗe lalita “Digital Wallet” wadda take wuri ne mai kama da account na banki. Za a buɗe shi a ɗaya daga cikin manhajoji na musamman da suke kama da bankunan a kan internet.

Manhajar da take aiki sosai tare da Bitcoin ita ce “Blockchain”, wadda tana da sauƙin shiga da sarrafawa da buɗe wallet nan da nan.


AMFANIN BITCOIN
Hoto: Coin68

 
ii- A wannan wurin ne mutum zai shigar da email ɗinsa sannan kuma ya ba wa abin sunan da ya ga dama. Za a iya amfanin da ɓoyayyun sunaye “Anonymity”. Bayan haka kuma ya ƙirƙiri “password” da yake so daga kalma 1 har zuwa 78, amma sai ya cakuɗa tsakanin lambobi da harufa. Idan mutum ya manta su, yana da dama har sau goma ya gwada lambobi daban-daban ko zai dace ya samu daidai ya buɗe. Idan har ya cikasa na goman bai dace ba, manhajar za ta garƙame lalitar tasa har abada, kuɗin mutum sun tafi kenan. Manhajar ba ta riƙe waɗannan lambobi, don haka mutum yana da buƙatar ya shigar da su a kowane lokaci kafin ya sami hanyar shiga manhajar.


iii- Manhajar za ta turowa mutum da wani shafi mai muhimmanci da zai kawo wasu kalmomi masu suna “identifier”.


Waɗannan suna da matuƙar muhimmanci. Idan sun ɓata shi kenan komai ya ɓata. Don haka ne ma Manhjar Blockchain take jan kunnen mutum ya riƙe waɗannan lambobi da ta ba shi da kyau sosai. Ya rubutasu a wuri na sirri. Kada ma ya kuskura ya yi wasarere da su ko ya rubutasu a wani wuri a kan intanet. Don wasu ‘yan fashi na kan intanet za su iya bincikosu, su kwashe abin da mutum ya saya na Bitcoin.


iv- Daga nan mutum zai koma kan email ɗinsa, zai ga sun aiko masa da wata gajeruwar wasiƙa da ta ƙunshi abin da zai danna don ya tabbatar musu da shi ne yake da wannan email ɗin. A wannan gajeruwar wasiƙa dai za a ga wasu lambobi da suke kira da sunan “confirmation code”. Suna buƙatar mutum ya kwafesu ya ajiye a gefe kamar waɗanda suka gabata. Domin wanna shi ne ‘code’ ɗin da mutum zai riƙa rubutawa a lokacin da zai aika kuɗi ko in zai cire kuɗi daga lalitarsa.


v- Sai mutum ya koma kan Manhajar Blockchain, a inda zai sami tabbacin cewa Manhajar yanzu ta sami alaƙa da email ɗinsa. Daga nan sai ya danna “Login Now” don ya shiga shafin lalitarsa “My Wallet”.


Daga can ƙasa in an duba za a ga wasu lambobin “Code”, waɗanda su ma za a kwafesu a gefe a ɓoye kamar waɗancan na baya. Waɗannan lambobi na me wannan wallet ɗin ne shi kaɗai. Su zai riƙa rubutawa ga duk kamfani ko wani mutum da suke hulɗar Bitcoin tare don karɓar kuɗaɗe daga wurarensu. Daga nan shi kenan mutum ya shiga tsarin Bitcoin.

 
4- Ana mallakar ƙwandalar Bitcoin ta fuska biyu kawai:


i- Hanya ta ɗaya mutum ya sayi gwargwadon abin da yake so na kuɗaɗen Bitcoin ta hanyar miƙa kuɗaɗen da aka saba da su kamar Naira ko Riyal ko Dollar da wani ya sayar masa. –Wato “exchange” kenan. Domin ana iya gutsura ƙwandalar Bitcoin zuwa gutsure-gutsure yadda ake so, a kuma sayar da ita. Ita kuma ribar da mai sayarwa ya samu sai ya ajiyeta a cikin lalita. Haka dai har lokacin da za a so shi ma ya sayar!


ii- Hanya ta biyu kuma ita mutum ya shiga “zabari” wanda suke kira da sunan “Mining”. Mutum ɗaya ko gungun wasu mutane ko wasu kamfanonin suna iya shiga wannan aiki da zabarin ta hanyar sayan manyan kwamfiyutoci don su gudanar da aikin. Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa aikin yana ɗaukar lokaci da amfani da ƙarfin wutar lantarki da data masu yawan gaske kafin a ce an sami ƙwandala ɗaya tak. 


5- Wannan Manhaja ta Bitcoin tana da matsaloli masu yawa da suka haɗa da waɗannan:


i- Tun a 2011 wasu gungun masu fataucin miyagun ƙwayoyi da sunan “The Silk Road” suka sanar da cewa wannan manhaja ta Bitcoin za ta zamo hanyar da za su riƙa musayar kuɗaɗen kayan maye wajen saye da sayarwa. Domin za a iya amfani da manhajar ba tare da an gane mutane ko an san dalilin da za su yi musayar kuɗaɗen ba. 


A shekarun 2013 zuwa 2015, ma’aikatar leƙen asiri ta Amurka FBI sun bankaɗo lalitar Bitcoin masu yawa da suke da alaƙa da hadahadar miyagun ƙwayoyi..-(Characteristics of Bitcoin Users: An Analysis of Google Search Data na Matthew Wilson, University of Michigan, 2014).


ii- Tare da cewa Manhajar ba ta ba wa wani dama ya kutsa cikin lalitar wani haka kai tsaye, amma a shekarun 2018 zuwa yanzu, an sami yawan sace-sacen kuɗaɗen mutane da kutse a lalitarsu da kwashe musu kuɗaɗe.

 
iii- Mutum ba shi da tabbacin tsaro ga kuɗaɗensa sai dai idan abokan harkarsa waɗanda bai san su ba sun mutumta masa sun riƙe alƙawarinsu. Saɓanin bankuna da mutum yana da tabbas yadda za su kula da kuɗaɗensa. –(Engadget Primed: The Rise (and rise?) of Bitcoin na Daniel Cooper, 2013).


iv- Kimar Bitcoin ba ta tsayawa wuri ɗaya; tana mummunan tashi sannan katsahan/kwatsam ta sauka. A wasu shekarun sai ta yi tsada daga baya kuma sai nan da nan ta sauko ƙasa warwas. A farkon Janairu ɗin nan na 2021, ƙwandalar take Dala dubu arba’in da biyu ($ 42,000), sannan ta sauko ƙasa. A wannan sati na ƙarshen Janairu ta dawo Dala dubu talatin da biyu ($ 32,000).

 
v- wata matsalar kuma ita ce idan wani ya sayi kaya ta hanayar Bitcoin, amma sai ya ƙi tura kayan ga wanda ya saya, to ba wata hanya da za a dawo da kuɗin cikin sauƙi, domin ba wata masaniya a tsakaninsu, ba kuma wata kotu ko hukuma da za a ɗaukaka maganar da sunan kara.


vi- Idan an tura kuɗin Bitcoin ba za a iya shan kansu a dawo da su ba. Saɓanin banki wanda zai iya toshe kuɗin ya hana mutumin da aka aikawa amfani da su.


vii- Babu tabbas a yadda hadahadar crytocurrencies za ta kasance. Gold yana da tabbas, don ga shi a hannu za a ɗauka a taɓa, amma crytocurrencies, musamman Bitcoin daga cikinsu, ba su da wannan zarafi. Duk lokacin da tsarin manhajar ya ruguje a kan intanet, to kuɗaɗen mutane sun tafi kenan, kowa zai tsuguna ya yi jugum!


viii- Da yawa daga cikin kamfanonin da suke hulɗa da Bitcoin suna buɗe dama ga mutane don su shigo da kuɗaɗensu wajen wannan harka amma ba tare da sanin abokan haɗin gwiwar irin haɗarin da mu’amalar take da shi ba.

 
ix- Wani bincike ya nuna nuna cewa kusan kaso 20% cikin ɗari na kuɗaɗen da suke jibge a cikin babbar lalita ta Bitcoin, dukiyar mutane ce da suka kasa bude manhajar sakamakon manta lambobin buɗewar da suka yi!


6- A halin yanzu duk da waɗannan matsaloli amma akwai ƙasashen da suka huwace amfani da Bitcoin kamar su Jamus, Ingila, Sweden, South Korea, Kuwait, Oman, Jordon, da sauransu. Wasu manyan kamfanonin manhajar kwafiyoyutoci da kafofin sadarwa irinsu Microsoft da Google da Yahoo duk sun karɓi amfani da wannan ƙwandala ta Bitcoin. Haka nan wasu gidajen sayar da abinci da otel-otel duka sun yarda a biyasu ta hanyar amfani da ita. Takai ana sayan wasu tikitin na hawa jirgin sama da kuɗin Bitcoin. Sannan kuma an sami wasu jami’o’i kamar na Ƙasar Cyprus da suka yarda da a biyasu kuɗin makaranta da wannan kuɗi.


Duk da cewa ƙasar Jamus su ne suka fara yarda da tsarin mu’amalar Bitcoin, amma a zahiri ba wai a matsayin kuɗi ba. Sai dai kurum a matsayin ƙasar ta sami wata dama da za ta ɗora haraji ga manya da ƙananan kamfanonin da suke yin mu’amalar Bitcoin. Mutane kuma ɗaiɗaiku aka bar su ba tare da wani abu ba. Don haka sun yarda da shi ne don samun kuɗin shiga kurum.

 
A gefe guda kuma akwai ƙasashe masu yawa da suka hana amfani da Bitcoin kamar su Saudiyya, Dubai, Turkiyya, Misra, Morocco, Algeriya, Lebanon, Russia, da sauransu. Babbabn Bankin Ƙasar China ya hana hulɗa da Bitcoin tun 2013. Suka daɗa ɗaukar zafi wajen hana hulɗa da Bitcoin baki ɗaya a 2017 da 2018.-(Everything You Need to Know about Bitcoin: Its Mysterious Origins and the Many Alleged Identities of Its Creators na Zoe Bernard, 2018).


7- Wannan ya kawo mu ga yadda za a kalli mu’amala da Bitcon a Musulunce. Akwai abubuwa da yawa da za a duba daki-daki don a fitar da hukunci da ya dace da yadda ake gudanar da Bitcoin a hain yanzu. Abin da malamai suka tsaya suna ta ƙoƙarin tantancewa shi ne ɗabi’ar waɗannan ƙwandalar ta Bitcoin shin ‘kuɗi’ ce ko kuwa ‘kadara’ ce? An sami waɗanda suke kallo da fahimtar Bitcoin da ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi. A kan haka kuma suka fitar da hukuncinsu game da shi, wasu suka halatta, wasu suka haramta.-(The Shari’ah Factor in Cryptocurrencies and Tokens na Shari’ah Review Bureau a Ƙasar Bahrain; Shari’ah Analysis of Bitcoin, Cryptocurrency and Blockchain na Mufti Muhammad Abu-Bakar). Amma a gaskiya in an dube ta da kyau za a ga ba ta faɗa cikin ma’anar wani daga ɗayan abubuwan nan guda biyu ba. Haka nan yanayinta bai dace da yanayin kowane ɗaya daga cikinsu ba.


i- Duk da cewa masu harkar Bitcoin suna amfani kalmomin da suke nuna kuɗi ne kamar ‘coin’ ko ‘currency’ ko  "عُمْلَة" da sauransu, amma a haƙiƙa ba kuɗi ba ne. Domin bai cika wasu daga cikin ƙa’idojin da Musulunci yake la’akari da su a matsayin kuɗi ba. Waɗannan sun haɗa da:


a- Sai gwamnati mai ci ta amince da wannan abu a matsayin kuɗi wanda duk mutane za su rika mu’amala da shi.


Malaman Musulunci sun bayyana haka a fili. Imamu Ahmad bn Hanbal yana cewa, “Ba wanda zai buga kuɗi sai gidan buga kuɗi (na gwamnati) da izinin shugaban. Saboda mutane in an yi musu rangwame a kansa, sai su wuce gona da iri”. Sai Imamu Abu Ya’ala ya ce, “Imamu Ahmad ya hana a buga kuɗi ba tare da izinin shugaban ba. Saboda yin hakan wani ta’addanci ne gareshi”.—(Ahkamus Suldaniyyah na Abu Ya’ala: 181; Mukaddimatu Ibnu Khaldun: sh/226; Annukud Wal-Bunuk Fin Nizamil Islami na Dr. Auf Muammad Al-Kafrawi:sh/20-56) 


قال الإمام أحمد:"لا يصلح ضرب الدراهم إلا في دار الضرب بإذن السلطان، لأن الناس إن رخص لهم ركبوا العظائم". فعلق الإمام أبو يعلى الحنبلي قائلا:"منع من الضرب بغير إذن سلطان لما فيه من الافتيات عليه".

Imamu Nawawi shi ma ya yi bayanin cewa duk malaman Mazahabin Shafi’iyya ba su yarda da wani ko wasu gungun mutane su ware su buga kuɗi ko su ƙirƙiro wasu kuɗaɗe daban, wanda gwamnati ba ta yarda da shi ba. Ya ce, “Ana ƙin wanda ba shugaban ba ya buga kuɗi (kamar dinare da azurfa) ko da kuwa masu kyau ne sosai. Saboda buga kuɗaɗe aikin shugaba ne. Sannan kuma ba za a sami aminci ba, don za a iya samun algus da ɓarna a ciki”.(Al-Majmu’u na Nawawi:6/11; Raudatud Dalibina na Nawawi:2/258).


قال الإمام النوي-رحمه الله-:"يكره لغير الإمام ضرب الدراهم والدنانير، وإن كانت خالصة. لأنه من شأن الإمام. ولأنه لا يؤمن فيه الغش والفساد". 

Wannan yana nuna cewa kamar yadda ba a son fito-na-fito da gwamnati a sha’anin mulki da gudanarwa, to haka nan ba a son a Musulunce a keta alfarmar gwamnati wajen buga kuɗaɗe ba tare da wani izini ba. Domin tsayuwa da daidaituwar kuɗi wata alama ce ta tabbatuwar gwamnati.


Ibnu Khaldun ya yi bayanin cewa abubuwa guda biyu su ne ginshiƙan duk wata daula. Su ne ƙarfi soja da kuɗi. Idan za ta ruguje tana rugujewa ne ta hanyar rugujewar waɗannan abubuwa.-(Al-Mukaddimah na Ibnu Khldun: sh/294).

 
A nan Nigeriya, dokokin Ƙasa sun hana amfani da Bitcoin da hulɗa da shi. A 17 na Janairu na 2017 Babban Banki Ƙasa (CBN) ya haramta amfani da shi ta kowace fuska. Ma'anar wannan da a ce za a sami wani ya kai ƙarar wani da sunan ya riƙe masa kuɗi ta hanyar Bitcoin, ba za a saurari ƙarar ba. Saboda ba ta saɓawa dokokin ƙasa ba.
Sai dai yana da kyau a sani cewa, a zamani irin wannan ba wai yarda ko rashin yardar wata ƙasa kaɗai shi ne abin la’akari wajen halatta wani abu ko haramtashi ba. Saboda a yanzu ƙasashe sun yarda da tsarin banki mai ruwa, amma wannan bai sa an ce shi kenan yin hakan ya halatta ba. A lokacin da Daular Musulunci take da ƙarfi da iko, ana gudanar da abubuwa a kan Shari'ar Allah, a lokacin ana iya cewa ba laifi ana iya la'akari da wasu abubuwan saboda gwamnati ta yarda shi. Amma ko a da can har da kuma yanzu, ana duba yadda abu yake cikinsa-da-bayansa, sannan sai malamai su bada fatawa da za ta bayyana matsayinsa a Shari’a na halasci ko haramci. Wannan wani abin dubawa ne da kyau.


b- Bayan gwamnati ta yarda da duk abin da take ganin za iya tsayawa a matsayin kuɗi, za a ga duk mutane sun yarda da su a mu’amalolinsu na yau-da-gobe. Wannan shi ne abin da Imamu Malik yana cewa, “Da a ce mutane za su yarda da fatun dabbobi a tsakaninsu a buga su a matsayin kuɗaɗe, da ba zan so a sami jinkiri ba idan sun yi canja fata da dinare da azurfa".-(Al-Mudawwanah: 3/5. A dada duba ra’ayin Hanafiyya a Littafin Tanbihur Rukud Ala Ahkamiln Nukud na Ibnu Ibidn: sh/25).


قال الإمام مالك:"ولو أن الناس أجازوا بينهم الجلود حتى تكون لها سكة وعين، لكرهتها أن تباع بالذهب والورق نظرة".

Ma’anar maganarsa ita ce duk abin da mutane suka haɗu a kan cewa kuɗi ne, kuma suka gina rayuwarsu a kansa, ya zama kuɗi. Duk hukunce-hukuncen Shari’a na kuɗi za su shafe shi. Kuɗi suna da sifar zamowa tsanin da kowa-da-kowa zai yi amfani da shi wajen  saye-da-sayarwa. Ba a la’akari da kuɗaɗen da suka zamo masu gudanawa tsakanin wasu tsirarun mutane.-(Al-Warkun Nakadi na Sheikh Abdullah bn Mani’i sh/17). Bitcoin ba kuɗi ba ne da kowa-da-kowa yake da ikon amfani da su cikin sauƙi ba. Kudade ne in har an yarda ma cewa kuɗin ne da suke yawa a kan intanet kurum. Waɗanda suke hulɗar su kaɗai suka san da su, kunzumin mutane ba su da alaƙa da waɗannan kudaden na ɓoye!


c- Kuɗi abu ne na zahiri da yake zamowa ma’aunin kimar abubuwa a faɗin duniya, ta yadda abin da aka saya ya zamo daidai da kimar kuɗin da a ka sayeshi da su.-(Al-Mugni na Ibnu Kudama:5/419). Don haka ne ake da kuɗi kala biyu:


Na ɗaya: Abubuwan da su da kansu kuɗaɗe ne kamar gwal da azurfa. Har yanzu ana ɗaukar gwal cikin manyan abubuwan da ƙasashe suke ajiyewa a matsayin (Foreign Exchange Reserve).

 
Na biyu: Abubuwan da gwamnati ta yarda da su a matsayin kuɗaɗe kamar takardun kuɗi na Naira, Riyal, Dollar, Euro da sauransu. Tuntuni Malamai suka tabbatar da karɓar takardun kuɗi. Kafin wannan zamanin ma Imamu Malik ya faɗi maganar da aka kawo a sama. Har ila yau kuma Shehul Islam Ibnu Taimiyyah shi ma ya yi bayanin da za a ɗora takardun kuɗi a kansa. Ya ce, “Dinare da azurfa ba su da wata wani iyaka ta al’ada ko ta Shari’a.


Makomar lamarinsu ba ta wuce al’ada da abin da mutane suka yarda da shi a tsakaninsu. Saboda su kudi tun asali ba manufarsu kenan ba. Manufar ita ce su zamo ma’auni na abubuwan da ake mu’amala da su kurum. Dinare da Dirhami ba su da kansu ne manufa ba. A na ɗaukar su ne a matsayin tsani kurum don a yi mu’amala da su. Don haka ne ma suka zamo kuɗaɗe, saɓanin sauran dukiya, waɗanda asalin manufar samuwarsu ita ce a yi amfani da su”-(Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiyyah: 19/251).


قال شيخ الإسلام ابن تيمية-رحمه الله-:"وأما الدرهم والدينار فما يعرف له حد طبعي ولا شرعي. بل مرجعه إلى العادة والاصطلاح. وذلك لأنه في الأصل لا يتعلق المقصود به. بل الغرض أن يكون معيارا لما يتعاملون به. والدراهم والدنانير لا تقصد لنفسها، بل هي وسيلة إلى التعامل بها. ولهذا كانت أثمانا؛ بخلاف سائر الأموال. فإن المقصود الانتفاع بها نفسها. فلهذا كانت مقدرة بالأمور الطبعية أو الشرعية".

Manufar kawo wannan don a nuna cewa Bitcoin bai sami irin wannan darajar ta karɓuwa a matsayin kuɗi ba a ƙasashe da yawa ba. Abin da yake faruwa dangane da shi shi ne wani mutum ko wasu mutane ne kurum suka ƙiƙiire shi a kan intanet, sannan tsakanin duhun-dare da sanyin-safiya suka ɓace aka kasa ma gano ko waye har yanzu!

 
d- Sannan kuma ana biyan kuɗaɗe idan wani ya salwantar da su. Ita kuwa ƙwandalar Bitcoin, in ta salwanta, ba mai biya ko ya dawo da ita. Don haka ciniki da hulɗa da ita ya shiga haramci saboda garari da haɗarin da yake ciki.


e- Bitcoin ya fi kama da kuɗin-ganye (Alfulus): Ana ƙirƙirar kuɗin ganye ne saboda dalilai da yawa, musamman don a shirgar da su cikin mutane su bada mai kyau a ba su mara kyau. Ibnul Kayyim ya yi bayani mai gamsarwa a kan yanayin kuɗin-ganye. Idan aka yi la’akari da bayaninsa a kan Bitcoin za a ga kamannin ya bayyana sosai. Ya ce, “Kamar yadda ka gani dangane da rugujewar mu’amalar mutane da irin cutuwa da take samunsu idan suka fara amfani da kuɗin-ganye (Alfulus) a matsayin kadara don samun riba. Yin haka sai ya kawo cutuwa da za ta game ko’ina, zalunci ya yaɗu. Da an ɗauke su a matsayin kuɗi na-bai-ɗaya, baya ƙaruwa ko ya ragu, wanda zai zamo ma’aunin abubuwa, amma ba a auna shi da kadarori, da an yi haka da lamarin mutane ya gyaru...Saboda ba a burin samun kuɗi su a karan-kansu, sai dai ana buƙatar su ne don akai ga sayan kadara/haja. Idan kuɗaɗe su da kansu suka zamo kadara, ana hanƙoron a same su kamar kadara, sai lamarin mutane ya lalace. Wannan bayani ne na hankali da ya shafi zallan kudi, ba zai tsallaka zuwa wasu Abubuwan ba”.-(I’lamul Muwakki’in An Rabbil Alamin na Ibnul Kayyim:2/156-157).


قال الإمام ابن القيم-رحمه الله-:"كما رأيت من فساد معاملاتهم، والضرر اللاحق بهم، حين اتُّخذَت الفلوس سلعة تعد للربح، فعم الضرر، وحصل الظلم. ولو جعلت ثمنا واحدا لا يزداد ولا ينقص بل تُقوّم به الأشياء، ولا تقوم هي بغيرها لصلح أمر الناس...فالأثمان لا تقصد لأعيانها، بل يقصد التوصل بها إلى السلع. فإذا صارت في أنفسها سلعا تقصد لأعيانها، فسد أمر الناس. وهذا معنى معقول، يختص بالنقود لا يتعدى إلى سائر الموزونات".

Malamai irinsu Imamu Gazali suna faɗa cewa, “Idan kuɗin-ganye suka sami karɓuwa kamar kyawawan kuɗaɗe, to sai su zamo kamar kadara, a maganar malamai mafi inganci”- (Nuzhatun Nufusi Fi Bayani Hukumit Ta’amuli Bil Fulusi na Ibul Ha’imi Ahamd bn Muhammad, sh/47).



ii- Duk da cewa Bitcoin ya so ya yi kama da ‘kadara/haja’ (Legit commodity/goods) amma ba kadarar ba ce. Domin ita kadara/haja tana zamowa a hannu sannan ta biyawa wanda yake da ita wata buƙata ta musamman kamar ya sa a cikinsa ko ci ko ya sha ko ya shiga in gida ne ko ya hau kamar mota ko keke da doki da sauransu. Haka nan kadara tana samun kula ta wajen tabbatar da kyau da tsari daga hukumomi. Bitcoin kuwa ba ta da irin waɗannan siffofi. Saboda Bitcoin tana gujewa hukumomi. Sannan kuma iyakacinta kan intanet ba ƙari. Shi ya sa bai dace ba a ɗauke ta a matsayin kadara har kuma a gina hukunci na halaccin tsarin bakiɗaya a kan haka.


MATSALOLIN BITCOIN
Hoto: Newsbit

 
iii- Bitcoin ba shi da zubi da tsari irin na katinan da ake ajiye kuɗaɗe a cikinsu kamar su Visa Card, Master Card da sauransu. Saboda su waɗannan katina suna da wasu kamfanoni da suke kula da su. Amma tsarin Bitcoin ya tsani duk wata hulɗa da za a ginata a kan wani kamfani a tsakiya tsakanin mutane!


8- Bisa irin bayanai da aka kawo a ƙarƙashin lamba ta 5 na matsaloli guda tara, da bayanan da suka zo a ƙarƙashin lamba ta 7, duka waɗannan suna nuna cewa wannan harka ta Bitcoin tana ƙunshe da abubuwa da yawa da suka isa a ce ‘Haram’ ce bisa dokokin Shari’a.


Ga bayanin dailan haramcin a dunƙule:


i- Riba: Riba tana shiga hadahadar Bitcoin musamman ta fuskoki biyu:


Fuska ta ɗaya ana sayar da ƙwandalar bitcoin da bitcoin da fifiko da ƙarin wata a kan wata, wanda yake riba ne. Sannan a wasu lokutan ana samun jinkiri, ba a samun hannu-da-hannu ko da ‘bayarwa ta ma’ana’ ce a wajen canji da ake yi tare da sauran kuɗaɗe.

 
Fuska ta biyu kuma, kamfanonin da suke saye da sayar da Bitcoin a kasuwannin kuɗi, wato (brokers), suna karɓar kuɗin mutan kamar ₦5,000, sai su ranta masa wasu kuɗaɗen masu yawa kamar ₦50,000 a kan waɗancan. Daga nan sai su zuba su a sayen ‘share’. Idan kuɗi suka haɓaka, aka ci riba, sai su ba wa mutum iya kason da ya dace da kuɗinsa, su kuma su riƙe ragowar a matsayin (commission). Wannan shi ake kira da ‘Leverage’, wanda yake haramun ne ta fuskoki da yawa. Daga ciki dai Akwai bashi da riba da aka yi da sunan wanda ya sa kuɗi tun farko. Sannan kuma ya yarda da ya taimaka a ci riba. Wannan duka haram ne.

 
Idan kuma an faɗi, to duk kuɗin mutum (₦5,000) ɗin baki ɗaya sun salwanta, ya yi asararsu! Wannan ɓangaren ya shiga tsarin caca tsundim!


ii- An gina Manhajar Bitcoin a kan tsarin caca. Shi ma wannan zai iya zamowa ta fuskoki da yawa, musamman gida biyu.
Fusaka ta ɗaya ita ce wadda ta gabata a misalin da aka faɗa a lambar sama cewa idan mutum ya sa kudi misali (₦5,000), shi kuma ‘broker’ ya ƙara, sai a ka sami asara, to kuɗin mutum sun nutse baki ɗaya, ba zai sami komai ba.

 
Fuska ta biyu kuma kamfanomin da suke fafutukar samo ‘coin’ ɗin ta hanyar ‘mining’ suna kashe ɗimbin kuɗaɗe su tsunduma cikin zabari tare da sauran masu nema, a ƙarshe sai guda ɗaya ne zai iya samu a cikin minti goma. Sauran ba wanda zai sami wani abu. Kowane irin abu suka kashe na dukiya ya tafi a banza.
 

 
iii- Cin dukiyar mutane ba-gaira-ba-dalili: Kula da dukiyoyin mutane da kiyayesu daga salwanta yana daga cikin manufofin Shari’a. Akwai sauƙi sosai ta hanyar Bitcoin a sami damar cin dukiyar mutane ba tare da wata wahala ba. Saboda yadda farashin Bitcoin yake gwauran tashi a ɗan ƙanƙanin lokaci, yana huwacewa wasu su azurta da kuɗaɗen mutane ba gaira-ba-dalili. Sannan kuma ya sauka a ɗan lokaci, ta yadda wasu za su yi gagarumar asara. Wannan yana bada tsoro har ana tunanin cewa akwai wasu a ɓoye masu ci da gumin sauran mutane! Tsarin hawa da saukar Bitcoin ya wuce tsarin yadda aka san cinikayyar canji a kasuwar duniya ta yadda hawa da saukar ba wani mai yawa ba ne, amma ba ya ninninka ba. Misali Bitcoin ya taɓa ninkawa har sau ɗari uku a 2017 sannan kuma ya ruguzo! Wannan yana nuna Bitcoin ba kuɗi ba ne da za a dogara da shi. Wasu daga cikin masana tattalin arziki suna cewa, ‘hauhawar Bitcoin kamar tashin kumfa take’ (bubble), nan da nan za ta sauka a dawo ƙasa!


Imamu Ibnu Kayyim ya fayyace wasu ƙa’idoji da za a fahimci yadda tsarin kuɗi yake a Musulunci. Ya ce, “Dirhami da Dinare kuɗaɗe ne na kadarori da kayan sayarwa. Abin da ake nufi da kuɗi shi ne ya zamo ma’auni, wanda za a riƙa kimanta kimar sauran dukiya da shi. Don haka ne dole ya zamo mai iyaka, a san gwargwadon yadda zai kai ya kawo, ba ya tashi sama sosai, ko ya faɗi ƙasa warwas! Domin idan kuɗi yana tashi , yana sauka kamar wata kadara, ba zai zamo nan kuɗi da za a riƙa la’akari da shi wajen kimar kayan sayarwa ba. Sai duk su zamo kadara ne, tare da cewa buƙatar mutane zuwa ga tsuran kuɗi wanda za su riƙa la’akari da shi dangane da kayan sayarwa, wannan buƙata ce ta larura, da ta shafi kowa. Shi kuwa tabbatar da wannan sai da wani farashi da za a san kimar abubuwa da shi. Shi ma wannan sai da wani tsarin kuɗi da za a riƙa yi wa abubuwa kima ta kima da shi, wanda zai zarce a kan hali ɗaya, ba wai shi ya zamo ana yi masa kima da wani abin ba, saboda ya zamo kadara da zai tashi ya sauka. Yin haka kuwa zai ɓata tsarin mu’amalar mutane, saɓani ya shiga tsakaninsu, cutuwa ta tsananta a cikinsu” -(I’lamul Muwakki’in An Rabbil Alamin na Ibnul Kayyim:2/157).


قال الإمام ابن القيم-رحمه الله-"فإن الدراهم والدنانير أثمان المبيعات. والثمن هو المعيار الذي به يعرف تقويم الأموال، فيجب أن يكون محدودا مضبوطا لا يرتفع ولا ينخفض. إذ لو كان الثمن يرتفع وينخفض كالسلع لم يكن لنا ثمن نعتبر به المبيعات، بل الجميع سلع. وحاجة الناس إلى ثمن يعتبرون به المبيعات حاجة ضرورية عامة. وذلك لا يمكن إلا بسعر تعرف به القيمة. وذلك لا يكون إلا بثمن تُقوّم به الأشياء، ويستمر على حالة واحدة. ولا يُقوّم هو بغيره، إذ يصير سلعة يرتفع، وينخفض، فتفسد معاملات الناس، ويقع الخلف، ويشتد الضرر".

Wannan bayani ne mai matukar ƙarfi, tare da cewa Ibnul Kayyim ya yi shi ne bisa duba da la’akari da tsarin kuɗi tuntuni. Sai dai a zahiri bayani ne kamar yau aka yi shi da ya shafi irin gararin da Bitcoin yake son jefa mutane a ciki. Domin a halin yanzu mu’amalar da ake yi da Bitcoin ɗin tare da cewa ana yi masa kirarin cewa kuɗi ne, amma mu’amalar irin wadda Ibnul Kayyim ya faɗa tana so ta mayar da shi kamar kadara/haja ba kuɗi ba !!


iv- Garari: Akwai garari a ciki saboda idan an tura kuɗaɗe ba za a iya shan kansu ba a dawo da su ba, idan misalin an fasa cinikin. Sai dai in wancan ɓangaren wanda ba a san kowaye ba, ya tausaya ya dawo da su. Sannan wanda aka yi ciniki da shi zai iya cinyewa mutane kuɗaɗensu ba tare da an kai shi wurin hukuma ta hukunta shi ba. Don haka wanda yake wannan mu’amala ya shirya karɓar mummunar asara da abokan mu’amalar ba za su san mai yake ciki ba ma ballantana su yi tunanin tausaya masa ba!


v- Jahala: A cikin hulɗar Bitcoin akwai rashin sanin yadda wasu abubuwan suke gudana da yawa. Domin ba komai ne a fayyace ba. Hatta wanda mutum yake hulɗar da su, mutum bai gama fahimtar su waye ba, ta yaya suka tara kuɗaɗensu, shin yana taimakawa marasa gaskiya ko kuwa?


Da dai sauran irin waɗannan tambayoyi masu wahalar amsuwa. Muhimmi dai ana so a gina ciki ba jahiltar abin da cikin ya ƙunsa. Imamu Ibnul Arabi Al-maliki yana cewa, “Malaman wannan al’umma sun haɗu a kan cewa cinikayya ba ta ƙulluwa sai ga abin da aka sani, daga wanda aka sani, da abin da aka sani, ta kowace irin fuska wadda za a iya samun sanayyar”-(Al-Kabas Shurhul Muwadda na Ibnul Arabi Al-Maliki:2/786-803).


قال الإمام ابن العربي المالكي-رحمه الله-"وقد اتفقت الأمة على أنه لا يجوز إلا بيع معلوم من معلوم بمعلوم- بأي طرق العلم وقع".  

9- Kasancewar duk ma’anoni guda uku da suke ruguza ciniki wato, riba, garari da algush, sun haɗu a wannan mu’amala ta Bitcoin, ya wajaba ga wanda yake yin hada-hada da Bitcoin da ya dakata, ya daina. Ya sayar da abin da ya tara a lalitarsa sannan ya kwashe uwar kuɗinsa, ragowar kuma ya bada su sadaka ko ya sa su a wani aikin alheri da al’umma za ta amfana da su bakiɗaya. Wannan saboda Allah Maɗaukakin Sarki ya ce, “In kun tuba, to sai ku riƙe uwar kuɗinku, ba ku zalinci kowa ba, kuma ba a zalinceku ba”-(Bakara2:279)

 
"وَإِنْ تُبْتُمْ فَلَكُمْ رُءُوسُ أَمْوَالِكُمْ لَا تَظْلِمُونَ وَلَا تُظْلَمُونَ"-(البقرة:279) 

10- Mu’amalar Bitcoin tana da ɗan rikitarwa. Abubuwa da yawa ba su bayyana ba a cikinta sai daga baya. Wannan ya sa malamai sun yi ɗan saɓani wajen fitar mata da hukunci, musamman a shekara ta 2017, a lokacin da lamarin Bitcoin ya bunƙasa, mutane suka faɗaka da irin yadda za ta kawo musu kuɗi suna kwance, ba wata wahala.


Malamai a ɗaiɗaikunsu da kuma Majalisu sun zauna a lokuta daba-daban don su tabbatar da hukuncin wannan mu’amala.


Daga cikin waɗanda suka tattauna mas’alar, suka kuma tabbatar da cewa ta saɓawa Shari’ar Musulunci akwai Majalisar Malamai ta Ƙasar Turkiyya (Darul Ift’it Trukiyyah, 29/11/2017: https//goo/gl/KVqoyr), da Misra (Darul Ifta’il Misriyyah, 28/12/2017: https//goo/gl/WTMpdu); da Falasdinu (Majlisul Ifta’ Al-Filisdiniyya: https//goo/gl/TEMmlu).


Haka nan, akwai taron ƙarawa-juna-ilimi da aka yi a Doha ta ƙasar Qatar (4th Doha Islamic Finance Conference) a January, 2017 M. sun tattauna irin kuɗaɗen da ake hulɗa da su ta hanyar intanet kawai. Masu taron, waɗanda suka haɗa da Dr. Abdussattar Abu Ghudda-Allah ya yi asa rahama- da Dr. Aliyu Kardagi da sauran masana a fagen tsarin tattalin arziki na Musulunci, sun tabbatar da cewa irin waɗannan sababbin cinikayya suna da rikitarwa da haɗarin gaske, musamman da yake ba wani nassi da ya zo a kansu. Amma fitar da hukunci ga irin waɗannan mas’aloli ba zai gagari masana Fikihu ba a cikin malaman Musulunci.


Bayan haka manyan malamai sun daɗa zama a ƙarƙashin Majma’ul Fikihil Islami Addauli (International Islamic Fiqh Academy) a farkon shekara 1441 H./2019, a inda suka tattauna sosai a kan ɗabi’ar wannan mu’amala.

 
11- Akwai wasu abubuwa waɗanda idan Bitcoin da sauran hulɗoɗi masu kama da shi suka cika su za a iya la’akari da su a janye haramcin da yake kansu a yanzu kamar yadda Sheikh Aliyu Kardagi ya bada shawara. Waɗannan abubuwa sun haɗa da:


i- Gwamnati ta ɗauki Bitcoin a matsayin kuɗi. Don haka sai a samu wata ƙasa ta yarda da tsarin Bitcoin da makamantanta, ta yadda Babban Bankin ƙasar zai amince da hulɗa da ita. Sai a sawa manhajar ƙa’idoji. Yawancin ƙasashen da ake cewa a yanzu sun karɓi tsarin, sun karɓa ne a dunƙule, amma ba su sa dokokin da za su maida Manhajar ta zamo ƙarƙashin Babban Bankin waɗannan ƙasashe ba. Don haka kada wani ya ruɗu da zancen ai Akwai ƙasashen da suka yarda da tsarin.


ii- A ɗauki Bitcon a matsayin ‘kadara/haja’. Wannan kuma sai an sami kamfanonin da za su riƙa juya Bicoin ɗin a matsayin “share”, ta yadda kowace ‘share’ za ta zamo a na ganinta cikin jumlar tsarin waɗannan kamfanonin. A halin yanzu Bitcoin ba shi da wannan tsarin ta kowace fuska. 

 
iii- Ya zamo kamar tsarin su Visa Card, Credit Card, da sauransu. Ta yadda za a sami wasu kamfanoni da za su ɗauki gabaran gudanar da tsare-tsarensa da hadahadarsa da shige-da-fitarsa kamar yadda ake yiwa waɗancan katika.


Yin ɗaya daga cikin wannan zai ba wa Bitcoin wata sabuwar kima ta halacci a idon Musulmi.  

 
A ƙarshe, hadahadar Cryptocurrency a karan kanta ba za a iya cewa haram ba ce, ba laifi Musulmin duniya su fara tunanin yadda za su ci moriyar hakan ta hanyar da ta halatta wadda aka nuna a nan sama kaɗan. Saboda da alamu nan gaba kaɗan duk duniya za a raja’a a kan Digital Money. Amma dai a halin yanzu idan aka yi la’akari za a ga cewa wannan mu’amala ta Bitcoin ta faɗa ɓangarori da yawa na haramci a Shari’ah, ba wai wani ɓangare ɗaya ne kurum ba.

 

A ƙarshe muna yiwa Allah godiya, da  fatan ya sa mun dace.

Tuesday, 14 July 2020

Karanta Muhimman Abubuwa 13 Da Yakamata Ku Sani Game Da Kyankyaso

Karanta Muhimman Abubuwa 13 Da Yakamata Ku Sani Game Da Kyankyaso

Kyankyaso wanda akafi sanin sa da suna Cockroach yana da wasu abubuwan mamaki masu tarin yawan gaske kamar yadda bincike ya tabbatar.

ME KASANI GAME DA KYANKYASO...

Marubuci:- Kamaluddeen Kmc

1. Haƙiƙa kyankyaso yana cikin tsofin halittu wanda suka jima a duniya sosai, domin bincike ya gano cewa kyankyaso yajima a duniya tin zamanin dinosour (shekaru sama da dubu ɗaruruwa).

Wasu masana kimiya suna ganin kyankyaso a matsayin yajima a duniya sama da dinosours.

2. Aƙalla akwai nau'ikan kyankyaso (species) sama da 4,000 a duniya.

3. Kyankyaso yana iya kwana 30 (month) batare da yaci abinci ba.

4. Yana iya yin sati biyu batare da yasha ruwa ba.

5. Idan ka cire ma Kyankyaso kai (Head), to yana iya kwana bakwai batareda ya mutu ba.

6. Wasu daga cikin matan kyankyaso idan namijin kyankyaso yabisu (ya barbaresu) sau ɗaya to har su mutu sun riƙa yin koyi (Kwai) kenan batare da sun buƙaci namiji ba.

7. Ɗan adam bazai iyayin minti biyu batareda yayi numfashi ba, idan ɗan adam ya ɗauke numfashin sa na minti biyu batare da yayi numfashi ba to zai iya suma koma ya mutu baki ɗaya.

ME KASANI GAME DA KYANKYASO...

Amma shi Kyankyaso yana iya ɗauke numfashin sa na tsawon minti 40 batareda ya mutu ba.

8. Kyankyason da aka haifeshi a yau, a yau ɗin zai iyayin gudu sosai kamar babban kyankyaso.

9. Kyankyaso zai iyayin gudun kilo meter shida  (3 mile) acikin awa guda.

10. Wasu nau'ikan kyankyaso a amurka ansame su suna matuƙar son shan giya.

11. Wasu Kyankyason suna iya gama girman su daga haihuwar su zuwa girman su a cikin kwanaki 36.

12. Kyankyason da yafi kowanne kyankyaso girma a duniya ansameshi  yanada tsawon 6 inches (aƙalla rabin ruler irin na plastic ɗin nan kona katakon na wanda ake samu acikin math set).

13. Masana kimiya sunce, shi kyankyaso yana iya cin komai, shiyasa baya rasa abinci, yana cin ciyawa, ƙasa, da duk wani abinda ɗan adam ke ci.

Allah shine mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 12 June 2020

Karanta Manyan Abubuwa 6 Da Zasu Faru Bayan Dakile Yaduwar Cutar Sarkewar Numfashi Ta Covid-19 A Duniya

Karanta Manyan Abubuwa 6 Da Zasu Faru Bayan Dakile Yaduwar Cutar Sarkewar Numfashi Ta Covid-19 A Duniya

Na san muna ta jira a gama Covid19 kamar yadda aka gama Ebola ko Lassa FEVER mu koma sha'anin mu kamar yadda muka saba ko? Kwarai za a kammala Covid-19 ba da daɗewa ba, kwayar cutar za ta mace a hannun magungunan da ake ta samarwa.

DUNIYA BA ZATA KOMA YADDA TAKE BA!!!

Marubuciya:- Rahma Abdulmajid

Sai dai tasirinta na iya wanzuwa nan da shekaru ɗari masu zuwa in ba wani iko na MAI duka ba.

Me ya sa ba za a koma yadda ake ba kamar yadda aka yi zamanin Ebola? Tambayar kenan ko? Amsar ita ce Ebola ƙasashen Rabbana aatina ta kassara waɗanda ko a Africa ma basu da farcen Susa, yayinda Covid19 kuwa ƙasashe ashirin masu makullan Sarrafa duniya ta maƙure wa wuya. Daga Babbar giwa China ta soma rarrafe sannan ta balaga a babbar Giwa Amurka bayan da ta saki rassa a kasashen G8 da Rasha.

Amma Wane irin tasiri za ta iya bari bayan ta mutu wanda ko Ɗan Adam ne ya mutu bai taɓa iya bari ba ballantana wata ƙwayar cutar da bata kai ƙwayar Zarra ba? Wannan ma tambaya ce, bari na lissafa amsoshin kamar haka:

1. Zai yiwu an kawo ƙarshen zama a Ofis a manyan ƙasashen duniya, Kamfanin Facebook da Goggle tuni suka bai wa ma'aikatansu hutun zuwa ofis har zuwa shekara ta 2021, wannan alama ce ta cewa kamfanoni da manyan ma'aikatu akan hanyarsu ta zuwa hutu sun fahimci cewa za a iya aiki daga gida, kenan babu buƙatar tara manyan gine gine da biyan kuɗin wuta, kayan kyale-kyale da kwamfutoci da ɗumbin haraji da ofis ke ƙallafa musu tunda ma'aikata za su iya aiki daga gida. Su ma ma'aikatan za su sami karin kuɗin kashewa idan aka cire musu kuɗin mota na zuwa ofis daga nauyin da suke ɗauka.

2. Manyan Birane za su dena samin cinkoso, kai zama su dena yi wa ƙauyuka tinkaho. Eh mana! Dama ofisoshin da suke da su ne ke janyo mutane su narka kuɗi don kama wani ƙaramin ɗaki da zaman mota don kawai a je ofis. Kenan mutum da ya baro ƙauye ya zo birni saboda aiki zai iya komawa ƙauyensa batare da ya rasa aikinsa ba tunda zai yi a ƙaton gidan da kuɗin ɗakin birni zai iya samar masa. Wannan zai sanya ƙauyuka su fara samin ababen more rayuwa muddin ƴaƴansu da suka ɗanɗana birmi za su dawo su nemi haƙƙinsu na rayuwa da walwala. Kenan za rasa cinkoso a irin Biranen New Delhi, New York, Beijin, da Moscow kamar yadda za a iya rasawa a Abuja da Lagos ko Qahira da Iskandariya, ko Cape town da Johannesburg a nan Africa.

3. Makarantu na iya komawa yanar gizo. Tun da aka fara Covid19 makarantu da dama sun ƙarye bayan da aka rufe su iyaye ba za su biya kuɗin 3rd term ba. Sannan a dole sun ƙirƙiri ɗakunan karatu na yanar gizo don iya tsira da ɗalibansu ko ba ko sisi. Garin haka iyayen sun fahimci za su iya sanya ƴaƴansu a makarantu masu tsadar gaske a zahiri tunda yanar gizo zata rage farashin kuɗin makaranta, sannan su ma makarantun sun fahimci za su iya rage nauyin malamai da ɗakunan karatu tunda idan aji na ɗaukar yara 20 da malamai biyu to a yanar gizo aji na iya ɗaukar ɗalibai dubu 20 da malami daya!.

4. Hijira zata tsaya cak! Eh mana, muddin ina da ƙwaƙwalwa da zan iya aiki daga ɗakina me zai sanya sai na yi hijira daga Moriki zuwa Abuja, ko da ga Malawi zuwa Amurka? Saboda Dala? To ai za a biya ni da Dala a ko ina.

5. Kuɗin takarda zai ƙarasa mutuwa. Kwarai a zaman sama da sati biyar da ƙasashen duniya suka yi a kulle an sami ƙaruwar kasuwancin yanar gizo inda maimakon samar da cinkoso a manyan shaguna sai aka riƙa aikin Delivery inda zaka buƙaci abu shagon ya aiko maka. Ko a ƙasar nan da ba mu da jan wuya an yi cinikin kayan salla ta social media. Sannan ƙananan shaguna ma ko a nan Africa sun fi gane su rataye lambar Acc a gaban shago ka yi musu Transfer in ka sayi abu, saboda tsoron yaɗa cutar ta hanyar kuɗin takarda. Hakan ya ƙara sanyawa burbushin Takarda da ake ta rajin ɓatarwa nan da 2030 na iya tafiya kafin 2021.

6. Fiye da kashi 70 na gidajen karuwai na duniya na iya zama kufai. Kwarai ina nufin karuwanci zai yi mugun raguwa muddin mazaje suka dena hijirar neman aiki nesa da iyalansu wanda hakan ke sanya su zama kayan karau a hannun karuwai, sannan matan za su ƙara ƙaimi wajen sake mallakar zukatan mazansu da suka rasa a baya wanda hakan ya kashe musu gwiwa ta hanyar sallamawa. Su ma karuwan zasu nemi wasu sana'o'in muddin kuɗin shiga ya ragu.

Me ake buƙata ne don tarbar wannan sauyi hannu bibbiyu? Na san wasu za su ce 5G ake buƙata kamar yadda labarai ke cewa dama shi ake son ƙaddamarwa ko? Ni dai ban sani ba, amma na san tabbas babu abinda ake buƙata na karɓan wannan sauyi hannu bibbiyu sai Bisimillah da Karɓan ƙwaƙƙwaran WIFI.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng

Wednesday, 27 May 2020

Karanta Muhimman Abubuwa 21 Da Yakamata Ku Sani Game Da Kiyashi

Karanta Muhimman Abubuwa 21 Da Yakamata Ku Sani Game Da Kiyashi

A yau zamuyi dubi ne zuwa ga rayuwar kiyashi saboda suna ɗauke da wasu abubuwan al'ajabi acikin rayuwar su.

Kiyashi sukan bautar da junan su..

Marubuci:- Kamaluddeen Kmc

1. Kiyashi wani halitta ne kamar ɗan ƙaramin aljani saboda ƙarfin da yake dashi, domin yakan iya ɗaukan abinda yafishi (yaninka shi) nauyi sau 50.

2. Ana tsammanin nau'ikan kiyashi wato ƙabila-ƙabila sun kai aƙalla 12,000 a duniyan nan.

3. Da za'a tara yawan mutanen dake duniyan nan ahaɗa nauyin su waje guda, sannan atara kiyashin duniyan nan baki ɗaya ahaɗa nauyin su waje guda haƙiƙa da nauyin mutane da kiyashi yazo ɗaya.

4. Saboda ƙarfi irin na kiyashi, idan da yanada girma kaman akuya haƙiƙa da zai iya ɗaga mota sama chan chak.

5. Kiyashi sukan bautar da junan su, sukan kama wasu nau'ikan kiyashi wanda ba jinsin su ba su bautar dasu su zama bayi suna musu aiki, kiyashin da aka maidashi bawa ana kiransa da suna colony.

6. Yawancin bayi acikin kiyashi mata ne, kuma sune suke aikace-aikace da hidima wa sarauniya.

7. Kiyashin da suka fi girma ana samun su ne a jejin panama jungle, domin tsayin su  yakai 1.6 inches.

8. Aduk lokacin da namijin kiyashi ya barbari macen kiyashi, bazai jimaba zai mutu.

9. Kiyashi sune halittun da ake samun su ako ina a faɗin duniyan nan in banda yankin artic da kuma yankin antarctica.

10. Titanomymra wani nau'in kiyashi ne dasu ka taɓa rayuwa, saboda girman su sukan iya kaiwa 6 inches wato dai-dai da rabin rula na cikin mathset (sunfi kyankyaso girma), amma yanzu ba'a samun su anshafesu a duniya.

11. Black garden ant wani nau'ine daga cikin nau'ikan kiyashi da muke dasu, suna iya jimawa a duniya na tsawon shekara 15 batareda sun mutu ba. sun ma fi kare jimawa a duniya.

ME KASANI GAMEDA KIYASHI...

12. Kiyashi suna iya haɗa ƙwaƙwalwar su waje guda, idan suka haɗu dayawa sukan tsara aikin dasuke sonyi bisa hikima da basira.

13. Daga cikin nau'ikan kiyashi da muke dasu akwai wasu nau'ikan kiyashi masu iya kisa saboda hatsarin su, ana kiran su da suna bulldog ants, ana samun su a kasar australia ne.

14. Fire ants wasu nau'ikan kiyashi suma waɗanda suke rayuwa a ƙasar brazin , awani rafi mai girman gaske mai suna amazon rainforest, rafi ne kuma jeji ne.

Su waɗannan kiyashi suna iya taruwa su haɗa ƙafafun su waje guda su zama kamar wani kwale-kwale suyi tafiya akan ruwa domin zuwa kiwo.

15. Sarauniya acikin kiyashi itace mafi girma sosai, tanada ran ƙwalelen kai, sauran matsakaitan sune masu aikin, 'yan ƙananu sosai kuma basu wani aiki sosai, ita sarauniyar duk tafisu jimawa a duniya.

16. Bullet ant wani na'u'ine daga cikin nau'ikan kiyashi damuke dasu, wanda yafi kowani ƙwaro zafin cizo, idan ya chiji mutum yakanyi zafi da zugi sama da awa ashrin da huɗu (24-hours) batareda zafin yadena ba.

Masana kimiyar halittu sunce, chizon bullet ant dai-dai yake da mutum yasaka yatsansa ajikin wutan lantarki wanda ƙarfin wutan yakai 240 voltages , zafin schoking ɗin dai-dai yake da chizon bullet ant.

17. Mazan kiyashi sukan sato koyayen wasu nau'ikan kiyashin, idan suka fafe (ƙyanƙyashe) koyayen sai su maida yaran kiyashin bayi awajen su.

18. Yana daga cikin rawan da sarauniyar kiyashi take takawa wajen ganin ta ƙyanƙyashe koyayen kiyashi sama da 10,000 saboda a sami masu aiki sosai.

19. Kiyashi yanajin motsi ne ta hanyan vibration, amma baida kunne ajikin sa sai antenna.

20. Carpenter ant wani nau'ika ne daga cikin nau'ikan kiyashi waɗanda suke iya huda katako sugina gida acikin sa, sune suke zama sari masu lalata katako.

21. Kiyashi bayada hanci, dukkan jikin sa rami ne,  yakan shaƙi numfashi ne ta ramukan jikin sa.

ALLAH shine mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 10 January 2020

KARANTA ALAMOMIN KASUWANCIN BOGI A INTANET

KARANTA ALAMOMIN KASUWANCIN BOGI A INTANET

Kamar yadda na sha nanatawa, a intanet ana samun kuɗi sosai idan an yi da gaske. Wasu kuma suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna da wayon da suke yi su raba jama'a da abin hannunsu da sunan kasuwancin intanet. Masu irin wannan dabara suna da hanyoyi da yawa barkatai, har ma wani lokaci su ci da buguzum a ɗauka na gaskiya ne. 

Alamomin Kasuwancin Bogi a Intanet

Marubuci: Danladi Haruna

A yau na zakulo wasu daga hanyoyin da mutum zai yi wa kansa hukunci ya gane ko nau'in kasuwancin da aka bijiro masa na yi ne ko na bari.

Ga su kamar haka:

1. Abubuwan da ake sayarwa: Idan ka ga yawancin kayan da ake sayarwa ba wasu fitattu ba ne, watakila ma ba wadanda ake iya gani ba ne. Wasu na kiransu 'Packages' ko 'Bundles' ko 'Subscription'. Yawanci babu wani abu a ciki sai zunzurutun shiririta. Da za a ce ka nuna abin da aka sayar maka ko irin aikinsa ba za ka iya ba.

2. Kankanin Kudi  Babbar Riba: Daga yanayin ribar da aka yi alkawarin samu za ka fahimci akwai lauje cikin naɗi. Duk wani kasuwancin intanet da yayi alƙawarin samun ninki biyu ko fiye na abin da ka zuba cikin wata ɗaya, ka yi nesa - nesa da shi.

Yana da Kyau a Fara Tuntuɓar Masana Kafin a Fara Kasuwancin Intanet..

3. Shigo da wasu: Shi ne tsarin da ake kira 'Referral'. Watau za a ce idan ka kawo wani yayi rijista ta ƙarƙashinka za a baka wani abu na awalaja. Manyan kamfanoni fitattu kamar paypal da ebay da AliBaba da su Quickteller na nan Nijeriya duk suna yin haka, amma ba haka ta ci barkatai ba. Idan ka ga website na yin kasafin adadin kuɗin da za ka samu idan ka kawo mutane kaza zuwa kaza, lallai abin gudu ne.

4. Rijistar Kamfani: Kamar yadda muka san kamfanonin zahiri suna buƙatar a yi musu rijista da hukuma, haka ma kamfanonin intanet. Kowanne kamfani akwai irin rijistar da ta kamace shi. A Nijeriya dai, bayan rijista da CAC, wajibi ne kamfani mai hada hadar kuɗi ya yi rijista da SEC matukar yana da mutane 50 ko fiye da suka zuba kudinsu a cikinsa komai kankantar kudin.

5. Shugabanni da Jagororin kamfani: Idan ka ga kamfani ya ɓoye sunayen shugabanninsa an rumbun bayanai na Whois, to ka guje shi. Daga nan ne ake gane inda aka dosa har a iya tofa albarkacin baki. Kodayake, wasu na yin dabara su rubuta bayanan bogi a cikin rumbun. Don haka sai an kula kafin a saki jiki da su.

Bincike Kafin Shiga Fagen Kasuwancin Intanet..

6. Takardun Shaida: A Nijeriya, wajibi ne ga kamfani ya karbi wasu takardun bayanai daga masu son zuba hannun jari a cikinsa. Takardun shaidar sun haɗa da katin shaida, hoton mutum da BVN da katin ɗan ƙasa da kuma takardar biyan kuɗin ruwa ko wuta ko wata takardar shaida  da ke nuna adireshin mutum. Watau irin takardun da ake buɗe asusun banki da su. Duk kamfanin da ka ga ya kasance daga buhu sai tukunya, watau daga ka yi rijista da su ka zuba kuɗi sai kurum ka saurari 'alert', to abin gudu ne.

7. Ka'idojin Rubutu: Yawancin kamfanonin kasuwancin bogi ba su damu da rubutu cikin ingantattun hanyoyin ka'idojin rubutu ba. A kowane yare suke rubutun za ka ga kura-kurai barkatai tare da saka kalmomin da basu dace ba. Illar haka shi ne rasa martaba a farfajiyar duniyar google ta fuskar SEO. Wannan su ba damuwar su ba ne, saboda masu taya su tallan kamfanin suna iya isar da saƙon da ake bukata ta kafafen soshiyal midiya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa??

KARANTA HANYOYIN HARAJIN KASA DA NA JIHA

KARANTA DOKOKIN DA SUKA SHAFI HARKOKIN KUDI DA HARAJI

Ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, ko anan Nijeriya akwai kasuwancin intanet mai riba sosai wanda ba gara ba zago. Ni ma na zuba a wasu daga cikinsu.  Wadannan kamfanoni sun haɗa da I-Invest, Payday, Elixir, AlatNg da sauransu. Kowacce rana hukumar SEC tana bibiyar ayyukan waɗannan kamfanonin, ta yadda koda sun durƙushe mutum zai iya maida asarar da ya yi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





Friday, 20 December 2019

'YAN AREWA SUN KAFA TARIHI A YANKIN KUDU MASO KUDANCIN NIGERIA SUN GINA JAMI'AR KIMIYA DA FASAHA

'YAN AREWA SUN KAFA TARIHI A YANKIN KUDU MASO KUDANCIN NIGERIA SUN GINA JAMI'AR KIMIYA DA FASAHA

Wannan shine hoton ginin katafariyar cibiya na horarwa a kan fasahar sadarwa wanda hukumar NITDA ta gina a cikin jami'ar jihar Rivers dake birnin Fatakwal, kwanaki biyu da suka gabata Maigirma Ministan sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami yaje ya kaddamar da cibiyar a madadin gwamnatin Nigeria.

Yayin Bude Makarantar Kimiya da Fasaha


Marubuci: Datti Assalafy

Abin farin ciki garemu masoya Malam Dr Isah Ali Ibrahim Pantami, shine mutum na farko da ya fara gina wannan katafariyar cibiya a tsakiyar kudu maso kudancin Nigeria, sannan sai amintaccensa wato Malam Kashif Inuwa yazo ya karasa, wannan wani abu ne na tarihi.

An yiwa cibiyar lakabi a turance da "The Information Technology Innovation and Incubation Park Building" an kashe miliyoyin Naira kafin a gina cibiyar, mutanen yankin kudu maso kudancin Nigeria gaba dayansu sune zasu amfana da cibiyar.

Maigirma Ministan sadarwa Dr Isah Ali Pantami a gurin kaddamar da cibiyar yace; lokacin da nake shugabancin hukumar NITDA, shugabanta na yanzu Kashif  Inuwa yana matsayin mai bani shawara akan harkokin gudanarwan ma'aikatar, na kawo batun gina irin wannan cibiya a kusurwa shida na fadin tarayyar Nigeria ta yanda za'a samarwa matasa aiki, a farfado da tattalin arzikin kasa.

Yayin Bude Makarantar Kimiya da Fasaha

Maigirma Ministan yayi la'akari da gurin da yafi dacewa a fara gina wannan cibiya saboda yawan masana'antu da yankin ke dashi, wanda zai inganta tattalin arzikin Nigeria, sai ya fara a yankin kudu maso kudancin Nigeria ba tare da la'akari da ya fara a yankinsa ba, saboda kyakkyawar manufa da kishin Nigeria.

Ministan yaci gaba da cewa, na tabbata idan aka gudanar da wannan cibiya bisa gaskiya da rikon amana yadda ya dace, cibiyar zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Nigeria, shugaban Kasa Buhari yayi alkawarin yin adalci a kowani sassa na Nigeria, shiyasa hukumar NITDA zata tabbatar da wannan muradi na shugaban kasa wajen gina irin wannan cibiya a kusurwa shida na fadin tarayyar Nigeria.., inji Ministan

A nasa jawabin, shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwan zamani na Nigeria (NITDA) Malam Kashif Inuwa  a gurin kaddamar da cibiyar, yace an gina wannan cibiyar ne a cikin jami'ar Portharcourt don daliban ilmi, manyan masana'antu da kanana, 'yan kasuwa da sauransu akan manufa na inganta tattalin arzikin Nigeria .

Malam Kashif Inuwa yaci gaba da cewa, gwamnatin tarayyar Nigeria karkashin shugabancin Muhammad Buhari tun a shekarar 2016 ta kafa kwamitin kwararru a harkokin kasuwanci da aka yiwa lakabi da "Presidential Enabling Business Environment Council" tare da taimakon bankin duniya (World Bank) domin kwamitin ya cimma matsaya akan abubuwa guda uku, na farko; a farfado da tattalin arzikin kasa, na biyu: a gina hanyoyin inganta tattalin arzikin kasa, sannan a gina al'umma.

Gwamnati ta fahimci cewa kimiyyar fasahar sadarwan zamani zai iya kawo mafita ga matsalolin tattalin arzikin kasa, shiyasa ta bada muhimmanci a kai, a sakamakon haka, yanzu bangaren bunkasa fasahar sadarwa a Nigeria ya wuce man fetur da gas wajen inganta tattalin arzikin kasa.., a cewar Malam Kashif Inuwa shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwan zamani na Nigeria (NITDA).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Kalli Yadda Soyayya ta sa Wani Bawan Allah ya Sauya Sunan Shi Zuwa na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Kalli Yadda Wani Dan Sanda Ya Harbi Wani Matashi Dalibin Computer Science Har Lahira

SHIN TA YA YA KAKE JIN MAGANAR DA WANI KE FURTAWA?

Ina kira ga 'yan uwana na arewacin Nigeria mu dinga sanya wadanann bayin Allah cikin addu'ah na fatan samun nasaransu, manufarsu mai kyau ce, babu shakka akan sun rike amanar da shugaba Buhari ya damka musu da gaskiya.

Muna rokon Allah Ya daukaka darajarsu, Ya sa dukkan jama'ar  Nigeria su amfana da rayuwarsu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





Monday, 25 November 2019

SHIN TA YA YA KAKE JIN MAGANAR DA WANI KE FURTAWA?

SHIN TA YA YA KAKE JIN MAGANAR DA WANI KE FURTAWA?

Tun a shekaru Dari Uku kafin Haihuwar Annabi Isa (A.S) philosopher Aristotle ya fara tambayar kansa dalilin da yasa mutane ke jin maganar da yan'uwansu mutane keyi, ya bazama neman abun dake daukar maganar daga bakin wanda ya furta zuwa kunnuwan wanda ya saurara.

Philosopher Aristotle

Marubuci: Rabi'u Biyora

A zahiri sai a ɗauka kamar Hauka ne ya kamashi, wasu kuma sai su zata ko rashin aiki ne ke damunsa, wasu ma har suke zaton ya dorawa kansa aikin da ba zai taɓa yiyuwa ba, amma bayan dogon binciken ilmi tare da nazari sai ya fara gano cewa dukkan maganar da mutane keyi tana tafiya ne ta cikin Waves wanda ke daukar maganar daga baki zuwa kunnuwa.

Wannan tambayar da yayiwa kansa, ita ce ta temaka wajen samo amsoshin da har mutanen duniya suka fara amfana da hanyoyin sadarwa tun daga Radio zuwa Television da wayar tangarahu, gashi har zuwa yanzu da muma muke ci gaba da amfana da tambayar da Aristotle yayiwa kansa.

WHY AND HOW sune kashin bayan dukkan Ci gaban zamanin da aka samu a kimiyance.

MAKALOLI MASU ALAKA:




Har yanzu kofa a buɗe take nayin Tambayar Why ko How ba mamaki ka kasance wanda zaiyi solving din equation din Albert Einstein na Time Travelling ta yadda za'a iya tafiya a cikin lokaci.

Tambayi kanka, How.... ko Why....

Sometimes Impossible is Possible.....

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Tuesday, 15 October 2019

ALLAHU AKBAR: Karanta Yadda Za'a Tashi Al-Kiyama ta Hanyar Amfani da Hasken Rana tare da Ilimin dake Cikin Hasken Rana

ALLAHU AKBAR: Karanta Yadda Za'a Tashi Al-Kiyama ta Hanyar Amfani da Hasken Rana tare da Ilimin dake Cikin Hasken Rana

Abu Zarr, yace :

"Wata rana muna tafiya tare da manzon Allah (S.A.W) sai yace dani "Ya kai Abu Zarr ko kasan a ina rana take faduwa? sai nace "Allah da manzon sa su suka fi sani, ni kam ban sani ba, ya manzon Allah ka sanar dani, sai manzon Allah (S.A.W) "Tana zuwa ta fadi a 'karkashin Al-arshin Allah ne dake can saman sama ta Bakwai, sai tayi sujuda wa Allah, sai tace ya Allah na kammala aikin da kace nayi a yau".

Yayin Faduwar Rana


Marubuci: Abdulhadi Isah Ibrahim

Sai ta sake cewa ya Allah na fita ne? na koma ne? sai Allah yace mata "Eh" ki fita, Abu Zarri yace sai manzon Allah yace dani "akwai ranar da zata nemi fitowa ta gabas kamar yadda ta saba, sai Allah ya hana ta, sai yace ki fita ta wurin da Kika shigo (ta yamma) sai ta koma ta fita ta yamma".

Karanta Sahihul Bukhariy, Hadisi na 4,802.  za kaga Hadisin.

Daga wannan ranar kuma za'a fara shirye shiryen tashin al-ƙiyama, ba da dadewa sai ayi Busan ƙaho kowa ya fadi ya mutu.

Masu binciken kimiyya  da fasaha suka ce, idan rana zata fito a kullum, idan ka lura zaka ga tana fitowa a hankali ne, hasken ta baya bayyana kamar yadda ake kawo hasken wutar lantarki lokaci guda, hakan da rana take yi rahama ce ta Allah, domin da ace rana zata rinka fitowa kamar yadda ake kawo wutar NEPA da bayan shekaru 2 baza a samu mai gani da kwayan idon sa ba a duniya, saboda karfin hasken zai rinka cutar da idon mutane saboda yana zuwa musu a lokaci guda.

Bincike ya nuna cewa hasken  rana shine "Vitamin D" da  jikin dan Adam yake bukata, idan da ace za'a rinka kawo hasken rana  kamar yadda ake kawo wutar lantarki wannan Vitamin D din bazai samu ba, kuma ko ya samu bazai amfani jikin dan Adam ba, dan haka zaka ga yaran da jikin su bai samu Vitamin D na hasken rana ba zaka ga suna da matsalar tauyewar wasu gabobin jikin su, kamar kaga kafar yaro ya gwame, kamar ya juya bai-bai.

Hakan yafi faruwa a manyan biranen da babu hasken rana sosai, yawanci yaran su acikin gida suke basu fita, shiyasa zaka ga a kasashen da aka cigaba zaka ga kullum da safe suna kai yaran su Hasken rana su kamar shanya, zaka ga an jera su acikin rana, ko suna kuka ba'a daga su, saboda su samu wannan Vitamin D din wanda Allah ne kadai yake saukar dashi daga sama a kullum.

Haka Kuma da ace za'a rinka dauke hasken rana a lokaci guda kamar yadda ake dauke wutan lantarki da mutane da dama sai sun mutu a kullum saboda daukewar hasken ranar, saboda idan kana tafiya a mota cikin hasken rana sai kuma aka dauke hasken, za ka razana, zaka dimauce, daga nan ayi ta karo ana mutuwa.

MUKALOLI MASU ALAKA:

ME YA SA AKA HALACCI SAURO?

KARANTA CUTUTTUKA GUDA 30 DA LUWADI YAKE HAIFARWA GA MAI YINSA

AKWAI ABIN AL-AJABI GA RAYUWAR WANNAN DABBA MAI YAWAN GASKE WATO KADANGARE

Amma saboda Allah mai rahama ne, sai ya rinka kawo hasken a hankali, a hankali da safe a lokacin fitowar ta, har sai idon mutane ya saba, ya karbe ta a hankali, haka idan aka tashi dauke hasken a hankali ake daukewa, ana janye hasken ana turo duhu a hankali har idanun mutane su saba da duhun, ba tare da ya cutar dasu ba, Allahu Akbar, wannan aikin Allah kadai yake iya yi.

Nan gaba akwai karin sauran bayanan da suke da alaƙa da wannan.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode