Showing posts sorted by date for query Umar M. Sharif. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query Umar M. Sharif. Sort by relevance Show all posts

Tuesday, 22 October 2024

Kalli Hoton Umar M. Shareef Da Aisha Najamu

Kalli Hoton Umar M. Shareef Da Aisha Najamu

An ɗauki waɗannan kyawawan hotunan ne a yayin ɗaukar bidiyon waƙar Soyayya Karɓaɓɓa ta mawaƙi Umar M. Shareef.

Umar M Sharif
Hoto: Kinga team

Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.

Aisha Najamu
Hoto: Kinga team

Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:

Aisha Izzar So da Umar M. Shareef
Hoto: Kinga team

Umar M. Sharif da Aisha Najamu
Hoto: Kinga team

Fatan hotunan sun ƙayatar da ku. Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu domin samun ire-iren su.

Monday, 23 September 2024

Wakar Asiya A Rubuce Ta Umar M Sharif

Wakar Asiya A Rubuce Ta Umar M Sharif

'Yar budurwata!! 'Yar budurwata Asiya son ki yai nisa a zuciya.

Ko cikin birni aka bincika za a sha nema.

Ka'idojin so duka kin cika tunda kin girma.

Ko a tarihi aka waiwaya sunan ki na nan ma.

Ta daban ce ke Asiya zan kula ki kamar marainiya.

Waƙar Asiya A Rubuce
Hoto: Kinga team 2007

Da kin fito an gama.

Ganin ki ya sa ni kiɗima.

Soyayya an ce ruwan zuma.

Ki ba ni in sha a ƙorama.

Gani ki ban dama.

Don na yo girma.

Gani ki ban dama Asiya don na yo girma a zuciya.

A cikin birnin garin mu ke ce kike haske.

Kwalliya tsafta da natsuwa babu tamkar ke.

Da kin fito gayu ta ko'ina ke suke leƙe.

Ke ake rububi a zo a ga tun da kin zamto zinariya.

In ka ga na yi ado na caɓa kwalliya.

Na yi shi ne dan Asiya.

In ka ga walwala a fuskata da dariya, waye sila? Asiya.

Soyayya ce muke bil haƙƙi da gaskiya.

Tunda ga ƙoƙon zuciya.

Rana ta aure Allah ya kai mu in zama ni ne angon Asiya.

Ni wai yaushe mafarkina za ya zam gaske ne?

Wai ni yaushe tunanina za ya zam gaske ne?

Ba ni son wata 'ya mace sai ke.

Ban ganin kyawun mace sai ke.

Ba na ɓoyewa a ko'ina na shiga ni ne na Asiya.

'Yar budurwata!! 'Yar budurwata Asiya son ki yai nisa a zuciya.

Umar M Shareef ne ya rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi  ku.

Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce da ƙasidu a rubuce.

Wednesday, 27 March 2024

Kalli Sababbin Kyawawan Hotunan Umar M Sharif

Kalli Sababbin Kyawawan Hotunan Umar M Sharif

Umar M. Sharif, ya kasance ɗaya ne daga cikin manyan mawaƙan masana'antar Kannywood, wanda har yau ake ci gaba da damawa da su a fannoni daban-daban, domin kuwa ba kawai a harkar wakoki ya tsaya ba, ya kasance Jarumi. Sannan kuma mai shiryawa.

Mawaƙi Umar M Sharif
Hoto: Umar M Shareef

Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.

Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan sa.

Jarumi Umar M Sharif
Hoto: Umar M Shareef

Fatan hotunan nasa, sun burge masoyan sa.

Mawaƙi Umar M. Sharif
Hoto: Umar M Shareef

Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun sababbin kyawawan hotunan mawaƙan ku.

Monday, 30 November 2020

Sauke Sabuwar Wakar Rarara Ft Umar M Sharif - Bazoum Kai Zamu Bi

Sauke Sabuwar Wakar Rarara Ft Umar M Sharif - Bazoum Kai Zamu Bi

 Kamar yadda shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.

Bazoum Kai Zamu Bi

Gamayyar mawaƙan fina-finan Hausa ne suka  fito su rera wannan waƙar domin ƙara tunatar  da al'ummar ƙasar Nijar manufofin ɗan takarar jam'iyyar PNDS-Tarayya Muhammed Bazoum a zaɓen dake tafe na shekarar dubu biyu da ashirin da ɗaya (2021).

Taken waƙar "BAZOUM KAI ZAMU BI, A NIGER KAI ZAKA MAYE GURBI....".

Kaɗan daga cikin jerin sunayen mawaƙan da suka bayar da muryoyinsu domin isar da wannan saƙon ga dubban al'ummar Hausawa dake cikin ƙasar Nijar dama Duniya baki ɗaya:

Abdul D. One
Aminu Afandaj
Aminu Dumbulun
Hauwa Fullo Gombe
Jadda Garko
Kamilu Koko
Rarara
Umar M. Sharif

Da sauran su

Waƙar ta hau kan  tsari bisa tsarin mawaƙan waɗanda su baje kolin basira da hikimar su a cikin waƙar.

Wato tsayawa bayyana abinda wannan sabuwar waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Saturday, 26 September 2020

Sauke Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Ft Umar M Sharif - Arewa Mu Farka

Sauke Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Ft Umar M Sharif - Arewa Mu Farka

Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.

Arewa Mu Farka

Gamayyar mawaƙan fina-finan Hausa ne su fito su rera wannan waƙar domin ƙara tunatar da al'umma halin da ƙasar Nijeriya take ciki a halin yanzu, kana kuma a ƙara tunatar da al'ummar Nijeriya musamman yankin arewacin hanyoyin da za abi domin daƙile yaɗuwar fyaɗe da sauran ayyukan ta'addanci wanda su addabi yankunan ƙasar baki ɗaya musamman arewacin Najeriya.

Taken waƙar "INA ZAMU JE! INA ZAMU KWANA! MU TASHI MU FARKA 'YAN AREWA".

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Kaɗan daga cikin mawaƙan da suka bayar da muryoyinsu domin isar da wannan saƙon ga dubban al'ummar Hausawa dake cikin ƙasar Nijeriya dama Duniya baki ɗaya:

Ali Jita
Adam A. Zango
Adamu Nagudu
Ado Gwanja
El-Mu'az Birniwa
Fati Niger
Fresh Emir
Dan Musa Gombe
Hamisu Breaker
Hussaini Danko
Ibrahim Ibrahim
Nazifi Asnanic
Naziru M. Ahmad
Sadik Zazzabi
Umar M. Sharif

Waƙar ta hau kan  tsari bisa tsarin mawaƙan waɗanda su baje kolin basira da hikimar su a cikin waƙar.

Mawaƙan sun yi kira sosai ga shugabanni, kana sun taɓa fanni daban-daban wanda 'yan arewa suke ciki a gwamnatin ƙasar amma babu abinda muƙaman nasu suke tsinanawa al'ummar ƙasar musamman matasa waɗanda sune mafiya yawan al'ummar ƙasar Nijeriya.

Wato tsayawa bayyana abinda wannan sabuwar waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Thursday, 20 February 2020

Kalli Hadaddun Hotunan Umar M. Sharif

Kalli Hadaddun Hotunan Umar M. Sharif

Kamar yadda shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin hotuna masu inganci waɗanda suka fi ɗaukar hankulan shafukan sada zumunta.

Jarumi/Mawaƙi Umar M. Sharif

MURYAR HAUSA24 Yau ma gamu tafe da hotunan fitaccen jarumi/mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood) Umar M. Sharif.

Mawaƙi Umar M. Shareef

Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan sada Zumunta duba da yanayin da aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar  rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar dama Duniya baki ɗaya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Kalli Kyawawan Hotunan Umar M. Sharif Na Karshen Mako

Kalli Kayatattun Hotunan Umar M. Sharif Cikin Shigar Kauyawa

Kalli Kayatattun Hotunan Umar M. Sharif Mafi Daukar Hankulan Shafukan Sada Zumunta

Mawaƙi Umar M. Sharif

MURYAR HAUSA24 Muna yi Masa fatan alkhairi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Monday, 13 January 2020

Download Complete Best of Sareena Audio

Download Complete Best of Sareena Audio

Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙoƙin  Soyayya na Film ɗin Sareena.

Labarin Soyayyar Wasu Makafi guda Biyu..

Waƙoƙin Fim ɗin Sareena suna ɗaya daga cikin fina-finan da 'yan kallo suke muradi, musamman yadda aka shirya wakokin sun ɗauki hankula a shafukan sada zumunta musamman a shafukan Youtube da kuma Instagram.

Ganin hakan ne yasa Muryar Hausa24 muka ga ya dace mu kawowa 'yan Uwa da Abokan Arziki waɗannan ƙayatattun waƙoƙin musamman ma'abota kallon fina-finan Hausa (Kannywood) a Nigeria dama ƙasashen Duniya baki ɗaya.

Labarin Soyayyar Wasu Makafi guda Biyu..

Mawaƙan da suka baje kolin salon sarrafa murya a wakokin sune kamar haka:

1. Abdul D. One
2. Umar M. Sharif
3. Muhmmad Melery
4. Nura M. Inuwa
5. Murja Baba
6. Khairat Abdullahi

Jaruman da suka taka muhimmiyar rawa a wakokin  fim ɗin Sareena sune kamar haka:

Umar M. Shariff
Shamsu Dan Iya
Maryam Yahaya

Labarin Soyayyar Wasu Makafi guda Biyu..

Umar M. Shariff shine ya fito a matsayin Jarumin Fim ɗin, yayin da abokiyar aikin sa Jaruma Maryam Yahaya taja ragamar film ɗin.

Ga waƙoƙin Kamar Haka:

Abdul D. One Mai Hakuri

DOWNLOAD MUSIC HERE

Abdul D. One Abar Mu Ni da Ke

DOWNLOAD MUSIC HERE

Muhammad Melery Tallafa Mini

DOWNLOAD MUSIC HERE

Nura M. Inuwa Sarina

DOWNLOAD MUSIC HERE

Nura M. Inuwa Miyi Kwaikwayon Manzon Allah (S.A.W)

DOWNLOAD MUSIC HERE

Umar M. Sharif Neman Ki Nake

DOWNLOAD MUSIC HERE

Umar M. Sharif Bani da Kamar Ki

DOWNLOAD MUSIC HERE

Lallai film ɗin yazo da sabon salo kuma zai faɗakar da al'umma musamman matasa, kada ku sake a baka labari, yanzu haka film ɗin yana kasuwa ku nemi naku a shaguna mafi kusa da ku.

Yanzu Haka ya Fito Ƙasuwa..

MAKALOLI MASU ALAKA:

Download Complete Best of Karki Manta da Ni Audio

Download Complete Best of Mujadala 2018 Audio/Videos Songs

Kalli Zazzafar Sabuwar Wakar da ta Girgiza Kannywood dama Duniya baki daya

Bayanai masu alaƙa da fim ɗin:

Labari: Jarumi kuma Mawaƙi Umar M. Sharif

Tsarawa: Jamilu Nafseen

Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda

Umarni: Ali Nuhu

Labarin Soyayyar Wasu Makafi guda Biyu..

An gina labarin film ɗin ne dangane da soyayyar wasu makafi guda biyu, an nuna tasirin soyayyar gaskiya, wacce aka gina ta domin Allah (S.W.T) ba don abin Duniya ba.

Film ɗin ya samu kyakkyawan aiki, jarumai sunyi ƙoƙari matuƙa wajen isar da saƙon da ake son isarwa musamman jarumi Umar M. Sharif da jaruma Maryam Yahaya sai jarumi mai biye musu baya Shamsu Ɗan Iya, wanda tauraruwar sa take haskawa a masana'antar Kannywood.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Wednesday, 8 January 2020

Kalli Zafafan Hotunan Hamisu Breaker Na Wannan Shekarar Masu Kayatarwa

Kalli Zafafan Hotunan Hamisu Breaker Na Wannan Shekarar Masu Kayatarwa

Kamar yadda shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin hotuna masu inganci waɗanda suka fi ɗaukar hankulan shafukan sada zumunta.

Mawaƙi Hamisu Breaker

MURYAR HAUSA24 Yau ma gamu tafe da hotunan fitaccen mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood) Hamisu Breaker.

Mawaƙi Hamisu Breaker yayin ɗaukar Bidiyon Waƙar Sirrin Zuciya

Hotunan sun dauki hankula sosai a shafukan sada Zumunta duba da yadda aka ɗauki hotunan wanda hakan ya taka muhimmiyar  rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar dama Duniya baki ɗaya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Kalli Kayatattun Hotunan Umar M. Sharif Mafi Daukar Hankulan Shafukan Sada Zumunta

Kalli Kayatattun Sababbin Hotunan Nura M. Inuwa Na Wannan Shekarar

Kalli Sababbin Kayatattun Hotunan Ado Gwanja

WAƙoƙin mawaƙi Hamisu Breaker suna ɗaya daga cikin waƙoƙin da aka fi saurara a shekarar 2019.

Mawaƙi Hamisu Breaker yana yin Nazari dangane da Rayuwa

MURYAR HAUSA24 Muna yi Masa fatan alkhairi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Monday, 30 December 2019

Kalli Yadda Mawaki Ahmad M. Sadiq Yake Rera Waka a Studio..Latest Video

Kalli Yadda Mawaki Ahmad M. Sadiq Yake Rera Waka a Studio..Latest Video

A wannan lokacin mun kawo muku bidiyon yadda mawaki Ahmad M. Sadiq yake rera waka a studio.

Mawaƙi Ahmad M. Sadiq

Lallai Allah (S.W.T) shi yake bayar da baiwar Sa ga wanda yaso a kuma lokacin da yake So.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Ahmad M. Sadiq ya kasance  ɗaya ne  daga cikin fitattun mawaka a masana'antar shirya fina-finan Hausa (KANNYWOOD).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Kalli Yadda Mawaki Umar M. Sharif Yake Rera Waka a Studio..Latest Video

Kalli Yadda Dauda Kahutu Rarara yake Rera Waka a Studio...Latest Video

Kalli Yadda Mawaki Hamisu Breaker Yake Rera Waka a Studio..Latest Video

Kana Ahmad M. Sadiq ya kasance mawakin da al'umma suke son sauraron wakokin sa a ciki da wajen kasar nan.

Muryar Hausa24 Muna fatan za'ayi kallo lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Tuesday, 19 November 2019

Kalli Yadda Mawaki Hamisu Breaker Yake Rera Waka a Studio..Latest Video

Kalli Yadda Mawaki Hamisu Breaker Yake Rera Waka a Studio..Latest Video

A wannan lokacin mun kawo muku bidiyon yadda mawaki Hamisu Breaker yake rera waka a studio.

Hamisu Breaker

Lallai Allah (SWT) shi yake bayar da baiwar Sa ga wanda yaso a kuma lokacin da yake So.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye..

Hamisu Breaker ya kasance daya daga cikin fitattun mawaka a masana'antar shirya fina-finan Hausa (KANNYWOOD).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Hamisu Breaker - Dajin So

Kalli Yadda Mawaki Umar M. Sharif Yake Rera Waka a Studio..Latest Video

HAMISU BREAKER - TAKA RAWA LATEST SONG

Kana Hamisu Breaker ya kasance mawakin da al'umma suke son sauraron wakokin sa a ciki da wajen kasar nan.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Wednesday, 6 November 2019

Music: Hafiz Abdallah Ft Murjanatu Bukhari Adam - Ita Kadai Hujja Ce

Music: Hafiz Abdallah Ft Murjanatu Bukhari Adam - Ita Kadai Hujja Ce

Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Begen Annabi Muhammad (SAW) Yau ma gamu tafe da waƙar yabo ta Muhammadur Rasulillah (SAW).

Hafiz Abdallah Ft Murjanatu Bukhari Adam

Kasidar da Fitacciyar Sha'ira
Murjanatu Bukhari Adam (Murjanatu Hafiz Abdullah) ta rera cikin sabon salo mai kayatarwa da daukar hankulan masoya Annabi Muhammadu (SAW) .

Kasidar mai taken "ITA KADAI HUJJA CE ".

MURYAR HAUSA24 kasidar tana ɗauke da saƙonni masu muhimmanci da yakamata al'umma su sani musamman ma'abota sauraron kasidun sa.

Abin dai ba'a cewa komai sai wanda ya saurara zai sani, ta rera kasidar ne cikin wani irin salo mai ban sha'awa.

Kardai mu cika ku da surutu ku sauke wannan kasidar yanzu domin sauraro.

Ku sauke kasidar yanzu domin sauraro.

DOWNLOAD MUSIC HERE

Nan bada dadewa ba Muryar Hausa24
zamu kawo muku Takaitaccen Tarihin
Murjanatu Hafiz Abdullah .

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Kasidar Umar Abdul'aziz Fadar Bege Ft Ramlat "Sarki Jiran Halittu"

Zazzafar Sabuwar Kasidar Umar M. Sharif "YA RASULILLAH (SAW) MANZO NA FIYAYYAN HALITTA"

DOWNLOAD SABUWAR KASIDAR MUSA GARBA GASHUWA "ANNABI SHA YABO"

Ku ci gaba da kasancewa da mu domin samun sababbin wakokin Murjanatu Bukhari Adam MP3 (Sababbin Kasidun Murjantu Hafiz Abdullah) .

Muryar Hausa24 Muna fatan za'ayi sauraro lafiya cikin Nishadi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Saturday, 2 November 2019

Kalli Kyawawan Hotunan Umar M. Sharif Na Karshen Mako

Kalli Kyawawan Hotunan Umar M. Sharif Na Karshen Mako

Kamar yadda shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin hotuna masu inganci waɗanda suka fi ɗaukar hankulan shafukan sada zumunta.

Umar M. Sharif

MURYAR HAUSA24 Yau ma gamu tafe da hotunan fitaccen jarumi/mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood) Umar M. Sharif .

Umar M. Sharif

Hotunan sun dauki hankula sosai a shafukan sada Zumunta duba da yadda aka ɗauki hotunan wanda hakan ya taka muhimmiyar  rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar dama Duniya baki ɗaya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

HOTUNA DA CIKAKKEN TARIHIN UMAR M. SHARIFF

Kalli Kayatattun Hotunan Umar M. Sharif Mafi Daukar Hankulan Shafukan Sada Zumunta

Kalli Sababbin Kayatattun Hotunan Umar M. Shariff a Kasa Mai Tsarki

Umar M. Sharif

MURYAR HAUSA24 Muna yi Masa fatan alkhairi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Sunday, 27 October 2019

Karanta Kurakurai 4 da akai a cikin Film din HAFEEZ tare da Sharhin Fim din

Karanta Kurakurai 4 da akai a cikin Film din HAFEEZ tare da Sharhin Fim din

Suna: Hafiz

Tsara Labari: Fauziyya D. Sulaiman

Kamfani: Maishadda Global Production Limited

Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda

Umarni: Ali Nuhu

Jarumai: Umar M. Sharif, Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, Hassana Muhammad, Maryam Yahya, Amal Umar, Bilkisu Shema, Aisha Humaira, Abba El-Mustafa, Asma’u Sani, Jamila Umar Nagudu, Aisha Yola. Da sauran su.

Sharhin Fim din Hafeez

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Salma (Aisha Humaira) suna hira da kanwarta Saudat (Amal Umar) a sannan ne kuma mahaifiyar su (Asma’u Sani) ta shigo dakin ta kira Salma da nufin taje wajen bakon saurayin ta Hafiz wanda yazo gidan, jin hakan ne yasa Saudat ta soma yabawa da Hafiz amma sai Salma tayi saurin dakatar da ita ta hanyar gargadin ta akan kada ta shiga sabgar sabon saurayin ta.

Sai dai kuma cikin rashin sa’a, bayan Salma ta fita zuwa wajen Hafiz tun a haduwar farko yaji bata birge shi ba saboda sabanin fahimta da suka samu wanda ya janyo sanadin day a mari Salma din kafin ya bar gidan.

Amma kuma duk da wulakancin da yayiwa Salma mahaifiyar ta bata ji haushin abin ba sai ma laifin Salma din da take gani saboda ta bata mata shiri domin ta kasha kudi masu yawa a wajen malamai don a jawo mata hankalin Hafiz zuwa kan ‘yar ta saboda kasancewar shi dan masu kudi, a dalilin haka ne ma yasa bayan kanwar Salma ta samu mahaifiyar tasu da rokon a shawo mata kan Hafiz ko ita zai saurare ta, mahaifiyar ta su bata bata lokaci ba wajen daukar Saudat din suka nufi gidan iyayen Hafiz.

Amma duk da kasancewar mahaifiyar Hafiz wato Azeema (Jamila Nagudu) ta kasance aminiya ga Mahaifiyar su Salma (Asma’u Sani) Hakan bai sa Azeema tayi kokarin tilastawa Hafiz akan yayi soyayya da Saudat ba, domin shi dan gata ne sosai a wajen iyayen nasa wadanda ba sa son ganin abinda zai bata masa rai. Shima kuma Hafiz ko bayan day a shigo gidan ya hadu da Saudat sai ya fice daga gidan saboda ganin yadda take kallon shi, amma duk da haka sai da Saudat tabi bayan shi zuwa waje inda ta nuna masa cewar tana kaunar shi, nan Hafiz ya watsar da ita ba tare daya karbi soyayyar ta ba.

Shi dai Hafiz ya taso mutum me tsananin farin jini a wajen ‘yammata, duk budurwar da ta gan shi sai taji ya birge ta kuma ta fara soyayya dashi, akwai ba don komai ba sai don kyau da iya kwalliyar sa gami da kudin da mahaifin shi ya mallaka wanda yake takama dasu. Babban abin takaicin kuma shine, Hafiz sam bai taba ganin yarinyar da ta birge shi ba akaf cikin ‘yammatan da suke zub da ajin su wajen nuna masa cewar suna son shi, gaba daya wulakanci yake yi musu bay a basu fuskar da zasu rayu tare, yayin da a kullum iyayen shi ba su da burin da ya wuce su ga yayi aure ya zauna da iyalin sa.

Hakan ne kuma yasa iyayen shi suka bashi goyon baya wajen zuwa ya ga ‘yar abokin mahaifin sa ko zasu daidaita har ya aure ta, amma cikin rashin sa’a Hafiz sai yaga itama yarinyar bat a birge shi ba, hakan yasa yayi mata kyautar kaya yayi tafiyar sa, wanda ganin haka sai ya yiwa mahaifin yarinyar ciwo (Abba Al-Mustafa) saboda yana matukar son Hafiz ya auri ‘yar shi ko don hakan ya zamo sanadin wani cikar burin sa, dalilin hakan ne yasa yaje ya sanar da mahaifin Hafiz wato (Yakubu Muhammad) cewar Hafiz ya amince da auren ‘yar sa, amma ko da mahaifin Hafiz ya tuntube sa sai ya nuna sam ba haka bane.

Ana tsaka da haka ne Hafiz ya hadu da Safna (Hassana Muhammad) wadda ta kasance ‘yar talakawa, tun daga sanda ta taimakawa da Hafiz ruwa ya zuba a motar shi sai yaji ta birge shi har ya kamu da son ta, sai dai kuma tun daga lokaci na farko day a fara zuwa hira wajen ta yaci karo da mahaifin ta Malam Sada (Ali Nuhu) sai hankalin Hafiz ya tashi, domin ya taba cin zarafin Malam Sada ya ture shi da mota har yaji masa rauni kuma ya soma kokarin dukan Malam Sada din.

Ko da Hafiz ya fahimci cewar Malam Sada ne mahaifin Safna sai hankalin shi ya tashi amma son da yake mata ne yasa ya kasa hakuri da ita yayi yunkurin turo iyayen sa, sai dai kuma Malam Sada yaki yarda da auren Hafiz da Safna saboda wulakancin da Hafiz din yayi masa. Ganin yadda Hafiz ya rikice akan son Safna ne hakan yasa iyayen sa suke takaici saboda ba ‘yar masu kudi ya nema ba, amma son da suke yiwa Hafiz ne yasa suka yi ta kokarin ganin cewar an daidaita da mahaifin Safna, ana cikin haka kuma sai aka tashi mahaifin Safna wato Malam Sada daga gidan da yake haya, hakan ne yasa ya hada kan iyalan sa gaba daya ya koma kauye, duk da kafin tafiyar shi, mahaifin Hafiz yayi masa tayin muhalli amma Malam Sada yaki amincewa domin shi mutum ne me zafin zuciya da gudun abin hannun wasu.

Ko da Hafiz ya samu labarin cewa Safna sun koma kauye sai ya gujewa iyayen sa ya tafi kauyen su Safna don neman soyayyar ta. Bayan zuwan Hafiz kauyen ne da yadda yake yin wahala sai abin ya soma bawa Malam Sada tausayi wato mahaifin Safna har daga karshe ya amince da nadamar Hafiz sannan ya bawa Hafiz din dammar turo magabatan sa don ya aura mishi Safna.

Abubuwan Birgewa:

1. Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa sannan an nuna tsantsar soyayya muhimmancin da jajircewa kan abinda mutum yake so.

2. Daraktan fim din yayi kokari wajen tafiyar da labarin bisa tsari ba tare da ya karye ba, haka kuma yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman sun yi kokari sosai.

3. Sauti ya fita radau, hoto ma ba laifi

4. An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin.

5. Wakokin fim din sun yi dadi kuma sun nishadantar.

Kurakurai:

1. Lokacin da Malam Sada (Ali Nuhu) yaje neman rancen kudi a wajen wani me kanti, da kuma lokacin daya dawo gida sa’in da akayi masa rauni a kafar sa, muryoyin jaruman basu hau da bakin su ba a wuraren.

2. An nuna cewar iyayen Hafiz masu kudi ne kuma suna nuna masa gata da tsantsar kulawa, amma kuma lokacin da Hafiz ya gujewa iyayen na sa ya tafi kauye wajen masoyiyar sa, me kallo bai ga sun yi yunkurin neman shi ba. Ya dace a nuna cewar sun watsa cigiyar sa ko da ta kafafen sadarwa ne.

3. Me kallo yaga Hafiz ya taso cikin gata da sangarta daga wajen iyayen sa, wanda hakan ya ba shi damar da ya ke cin mutuncin duk wanda ya so, musamman na sama da shi, amma sai ga shi kuma lokacin da Hafiz ya gane kuskuren da yayi wajen cin zarafin Malam Sada mahaifin budurwar sa, wanda har Hafiz din ya bar gaban iyayen sa don neman soyayya da kuma yafiyar mahaifin budurwar tasa, duk da ganin faruwar hakan amma ba a nuna cewar iyayen Hafiz sun yi nadama ba a bias tafarkin da suka dora dan nasu na rashin tarbiyya, ya dace a nuna cewar sun yi nadama ko don ganin illar da rashin tarbiyya ta ja wa Hafiz wanda abin ya zamo sanadin da Hafiz ya nisance su.

4. Shin wace irin sana’a mahaifin Hafiz yake yi ne? An nuna cewar Hafiz ya taso cikin gata da tunkaho da dukiyar mahaifinsa, sai dai kuma har fim din ya kare ba a nuna irin sana’ar da mahaifin nashi ya ke yi ba wadda ta sa ya mallaki dukiya me tarin yawan da a ke fada.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Kurakurai 4 da akai a cikin Film din NAMIJIN KISHI tare da Sharhin Fim din

Karanta Kuskure 5 da akai a cikin Film ɗin MATAR MAMMAN tare da Sharhin Fim ɗin

Karanta Kuskure 7 da akai acikin Film din KANWAR DUBARUDU tare da Sharhin Fim din

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma labarin ya yi nasara wajen rike mai kallo, sannan kuma an nuna tsantsar soyayya gami da muhimmin darasi a kan wasu matasan masu ji da giyar kudi, wanda hakan ke sa wa su wulakanta makaskanta, yayin da daga karshe su ke yin nadama a kan hakan. Wallahu a’alamu!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: LEADERSHIP A YAU