Showing posts sorted by relevance for query Faridah Bintu Salis. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Faridah Bintu Salis. Sort by date Show all posts

Wednesday, 20 November 2019

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

Haƙiƙa Addinin Musulunci yazo mana da dukkan yadda zamu rayu cikin wannan duniyar cikin maslaha matukar muka bi dokokin ALLAH kuma muka bi umurnin Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta hanyar yin koyi da shi.

Hanyar Yin Mu'amala da Mutane

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Addinin Musulunci kamar yadda muka sani addini ne kammalalle, kuma addini ne wanda ya koyar damu dukkan yadda zamu rayu a wannan duniyar ta hanyar da zamu yi aiki acikinta sannan mu samu sakamako ranar gobe kiyama.

Hanyar Yin Mu'amala da Mutane

Al-Kur'ani da sunnah sun zo mana da bayanai daban-daban. Amma a takaicen takaitawa na takaita wannan dan rubutun ne domin tunatar da 'Yan-uwa game da HANYAR MU'AMALA DA MUTANE.

Wajibi ne mutum yasan hanyoyin da zai ringa mu'alantar 'Yan-uwa, domin ya kiyaye fadawa cikin hakkokin su kasancewar idan kayi wasa da hakkin mutane ta hanyar da bata dace ba toh hakika zaka yi dana sani, domin ALLAH (SWT) baya yafe Hakkin da ke tsakanin wani da wani face sai idan su suka yafi junan su.

Hanyar Yin Mu'amala da Mutane

Da wannan nake tunatar da 'Yan-uwa wasiyoyi guda tara (9) acikin suratul Hujurat dan kula dasu wajen mu'amala:

1. Bincike idan anzo maka da wani labari.

2. Sulhu a tsakanin mutane.

3. Yin adalci yayin yanke ko wani hukunci.

4. Kada ka ringa yiwa mutane izgilanci.

5. Kada ka aibata wani.

6. Kada ka ringa yiwa mutane Lakabi da sunayen banza.

7. Ka guji mummunan zato.

8. Kada ka ringa bibiyar wani kan dole sai ka gano aibinsa.

9. Kada ka ringa giban mutane (wato gulma).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Amfanin Sada Zumunta Guda 20

Karanta Muhimman Abubuwan da Yakamata Ku sani Kafin ku Fara yin Taimako

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Kowanne Miji ya Kula dasu Idan Zai Yi Magana da Matar Sa

Duk wanda ya kiyaye wadannan abubuwan a cikin mu'amalar sa da mutane, toh hakika zai rayu dasu cikin fahimtar juna da walwala.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Thursday, 20 February 2020

Kowanne Mutum Yana da Abokai Guda Uku a Rayuwarsa da Bayan Mutuwarsa

Kowanne Mutum Yana da Abokai Guda Uku a Rayuwarsa da Bayan Mutuwarsa

1. Abokin da yake tare da kai har numfashinka tun daga ranar da ALLAH ya nufi halittarka har zuwa mutuwarka: shine Arzikinka kuma zai amfaneka har bayan mutuwarka idan kayi amfani dashi ta kyakkyawar hanya musamman Sadaƙa mai gudana.

Ka Mu'amalanci Mutane da Kyakkyawar Manufa..

Marubuciya: Faridah Bintu Salis 

2. Abokin da yake tare da kai a yayin rayuwarka da lokacin da ka mutu da bayan mutuwarka: shine ilimin da ka gabatar a lokacin rayuwarka.

3. Abokin da yake tare da kai har zuwa ƙabarinka inda aka bizne ka da kuma bayan mutuwarka idan ya kasance nagartacce: shine Ɗan ka.

Hadith ya tabbata cewa Annabi (ﷺ) Yace: “Idan bawa ya mutu dukkan ayyukansa sun yanke sai dai abubuwa guda uku:

1. Sadaƙa mai gudana.

2. Da ilimin da ya amfanar.

3. Ko kuma ɗan da ya bari salihi wanda yake masa addu'a.” [Muslim ne ya ruwaito]

Wannan hadisi yana nuna mana Sadaƙa mai gudanarwa ita ce wanda ka taimakawa addininka dashi misalai: ka haƙa rijiya bayin ALLAH suna amfana da ruwan da ke fita daga gareta, ko kuma ka gina masallatai bayin ALLAH suna shiga suna gabatar da ibada, ko kuma ka gina wata makaranta ta addini, ko kuma ka taimakawa marayu, ko kuma kayi copy na wasu littafan addini kaɗan daga ciki ne waɗannan duk sadaƙa ce mai gudana.

Wannan hadisi yana nuna mana cewa idan ka tsaya ka karantar da al'umma wani ilimi da ALLAH ya hore maka shi, shima ka taimakawa addininka.

Wannan hadisin yana tabbatar da tsayawa ka bawa ɗanka Tarbiya Nagari wanda har zai samu ikon yi maka addu'a bayan baka raye wannan shima ka taimakawa kanka da kuma addininka domin idan ya zama nagari ana sa ran zai amfani al'ummah.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Irin Abokin da Yakamata Kayi Rayuwar Ka da Shi

Abokai Iri Uku Ne a Duk Fadin Duniya

Shin Ko Abokina Zai Iya Canza Min Halayena Bansani Ba?

Waɗannan abubuwa duk ka taimakawa addininka sannan kuma ka taimakawa kanka tunda har bayan ka bar duniya za'a ringa rubuta maka ladan, kuma ladan zai ringa riskar ka.

ALLAH Yasa mu dace Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Wednesday, 18 March 2020

Don Me Zan Zabi Yin Abota da Mutum?

Don Me Zan Zabi Yin Abota da Mutum?

Kayi Abota don ALLAH, saboda wannan soyayyar ce kaɗai za ta ci gaba da wanzuwa har a lahira.

Aboki Nagari Abun Alfaharin Mu

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Babban Malamin nan Imam Ibnul Qayyim (Rahimahullah) Yace: “Shi Aboki salihi yafi maka alkhairi fiye da ranka, domin ita rai tana umurni ne da aikata mummuna. Amma shi Aboki salihi baya umurni sai da aikata alkhairi.”

Sheikh Rabee Bin Haady Almadkhaly (Hafizahullah) Yace: "Ka nemi aboki Mumini, zai taimake ka akan bin ALLAH, kuma zai ƙarfafeka akan alkhairi, kuma zai kiyayeka daga sharri, Ba zaka samu daga gare shi ba sai Alkhayri." [Al-majmuu 68].

Aboki Nagari Abun Alfaharin Mu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Monday, 27 January 2020

SHIN KO KASAN ME NE NE ASALIN SO?

SHIN KO KASAN ME NE NE ASALIN SO?

Sau da dama mutane basu san me ake nufi da So domin ALLAH da ƙi domin ALLAH ba, su dai kawai sun sani a baki amma sam basu san shi a aika ce ba.

Kaso Mutum Don Allah Ka kuma ƙi Shi Domin Allah...

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

WANNE IRIN SO NE DOMIN ALLAH ?

SO DOMIN ALLAH: Shine kaso mutum domin yana son ALLAH kuma yana son Addinin Musulunci kuma yana tsaye wajen bin dokokin addinin tare da sauke haƙƙoƙin addini a Taƙaice mutum ne mai kwaikoyon Annabi (ﷺ) ta kowace fuska.

Wannan shine mutumin da ya cancanci a soshi saboda tsayuwa ga ALLAH da bin umurnin ALLAH.

Duk wata soyayya da zaka so mutum saboda wasu abubuwa kamar kaso shi saboda dukiyarsa, ko kuma saboda kyawunsa, ko kuma saboda yaɗuwar sunansa a Duniya ko don shi mutum ne mai yawan mutane kaima ka shiga sahun son shi saboda yawan jama'arsa ko wani abu mai kama da haka toh wannan duk shirme ne.

Sau da dama mutum sai yayi ta ikirarin wai yana son mutum amma kawai yana son shine don wasu abubuwa masu gushewa, baya tunanin shin wanda yake so ɗin nan yana son ALLAH, shi dai kawai ba ruwansa idan dai wanda yake so ya dace da abubuwan dake burge shi shikenan ba damuwarsa bace yaso ALLAH ko kada ya soshi. Idan ya mallaki abubuwan da yake so shine masoyin sa, idan kuma ya rasa Toh shine maƙiyinsa. Wannan shine halayyar mafi yawan mutane.

WANN IRIN ƙI NE DOMIN ALLAH ?

ƘI DOMIN ALLAH: Shine kaƙi mutum domin yana ƙin addinin ALLAH kuma baya sauke haƙƙoƙin Musulunci, irin wannan mutum shi yafi cancanta aƙi shi domin idan zaka so wanda yake ƙin ALLAH da addininka, zaka iya tauye addininka ta wani waje.

Duk da haka ba a hanaka yin mu'amala da wanda yake ƙin ALLAH da addininka ba kamar kyautata masa idan bai yaƙe ka ba, ko kasuwanci tsakaninka dashi da dai sauran mu'amala, amma dai kada ka ruɗi kanka cewa wai yana sonka don kawai kai kana son shi har ma hakan yakai ka ga sassutawa a inda shari'ah ta tsananta don shi.

Ka sani cewa duk wanda yaƙi Ubangijinka da addininka bazai taɓa sonka ba koda kuwa kai ka nuna masa soyayya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ALAMOMI 10 DAZAKA FAHIMCI MACE TANA SON KA

KARANTA LABARIN SOYAYYAR WANI MATASHI DA MUTUWA TA RISKE SHI YANA TSAKA DAYIN SOYAYYA

KARANTA ZAFAFAN SAKONNIN SOYAYYA GUDA 32 MASU RATSA ZUKATAN MASOYA

A lura cewa duk wani SO wanda badon ALLAH bane indai don wani abu mai gushewa ne na Duniya to ƙarya ce ba soyayya bace. Kuma duk wani ɗan adam wanda bazai ringa tunatar da kai da kusantar da kai zuwa ga ALLAH ba toh baya daga cikin masoyanka sai dai ka sanya shi cikin jerin maƙiyanka.

ALLAH Ya haɗamu da masoyan mu masu son mu don ALLAH, Ya nisantar damu da duk wanda ke son mu badon ALLAH ba Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Friday, 24 May 2024

Darajar Wanda Ya Je Sallar Juma'a Da Wuri

Darajar Wanda Ya Je Sallar Juma'a Da Wuri

Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Wanda ya zo a sa'ar Farko yana da ladar wanda ya yi Sadaka da RAƘUMI, a sa’a ta biyu kamar mai Sadaka da SANIYA, sa’a ta uku kamar sadakar RAGO, sa’a ta hudu kamar Sadaka da KAZA, sa’a ta biyar kamar mai Sadaka da ƘWAI ....” [Bukhari da Muslim].

DARAJAR WANDA YA JE SALLAR JUMA'A DA WURI
Ishraq fataftah


MarubuciyaFaridah Bintu Salis


KU YI SALATI GA MANZON TSIRA (ﷺ)

ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻛَﻤَﺎ ﺻَﻠَّﻴْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ، ﺇِﻧَّﻚَ ﺣَﻤِﻴﺪٌ ﻣَﺠِﻴﺪٌ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺑَﺎﺭِﻙْ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻛَﻤَﺎ ﺑَﺎﺭَﻛْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ، ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ، ﺇِﻧَّﻚَ ﺣَﻤِﻴﺪٌ ﻣَﺠِﻴﺪٌ .


ﷺ ﷺ ﷺ ﷺ ﷺ
ﷺ ﷺ ﷺ ﷺ ﷺ

Thursday, 24 September 2020

Karka Bari Har Sai An Fada Maka Wannan

Karka Bari Har Sai An Fada Maka Wannan

A lokacin da kake watsa ƙasa kake bunne wanda ya Mutu duk da soyayya da ƙauna dake tsakanin ku, bayan ya bar duniya. A lokacin zaka gane cewa lallai wannan duniyar ba ma tabbata ba ce.

BA SAI AN FAƊA MAKA WANNAN BA !!!

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Kuma zaka ƙara tabbatar da cewa waɗanda suka rage baza su taɓa dawwama ba zasu ƙare tamkar yadda suka kasance ada babu su.

Ya ALLAH ka jiƙan dukkan Mamatan mu musulmai tun daga zamanin Annabi Adam (A.S), Ya ALLAH ka kyautata ƙarshen mu ka sanya mu cikin bayin ka masu sa'ar tafiya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Wednesday, 10 April 2024

Shin Ya Dace Dukkan Mata Su Fita Sallar Idi?

Shin Ya Dace Dukkan Mata Su Fita Sallar Idi?

Sunnah ce mata su fita Sallar idi kamar yadda Hadith ya kwaɗaitar da kuma maganganun magabata da suka yi bayani akan halarcin fitar mata zuwa sallar idi.


Sallar Idi
Hoto: Britannica


Marubuciya: Faridah Bintu Salis


Ummu Aɗiyyah Nusaibah Bint Ka'ab Al-ansariyyah (RA) ta ce: Annabi (ﷺ) ya yi umurni a ranar idi mata su fita, da 'ƴan mata, da mai al'ada amma ita ta nisanci wajen sallar (tunda ba yi za ta yi ba).” [Bukhari: 981, Muslim: 890]


Abdullahi Ɗan Abbas (RA) Ya ce: “Manzon ALLAH (ﷺ) Ya kasance yana umurtar ƴaƴansa. da matansa, su fita a idi guda biyu (Babba da ƙaramar Sallah).” [Sahihul Jami'i: 3888]


Sayyidina Abubakar (RA) Ya ce: “Wajibi ce Sallar Idi ga duk wacce take da kwatankwacin malulluɓi da zai rufe ta, ta fita zuwa idoji guda biyu ƙarama da Babba.” [Ibn Abi Shaibah ya ruwaito shi a Musannaf 2/182 da sanadi ingantacce] 


Alhafiz Ibn Hajar (Rahimahullah) Ya ce: “Alƙali Iyad Bn Musa ya naƙalto wajabcin Sallar idi hatta ga mata daga Abubakar da Aliyu da Ibn Umar.” [Fat-hul Baary 2/545] 


Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy (Rahimahullah) Ya ce: “Toh a sani wannan shi ne gaskiya da babu ƙoƙonto a kai na wajabcin idi hatta ga mata, saboda yawan hadisan da aka ruwaito game da haka, Hadisin Ummu Aɗiyya da ya gabata ya isar mana, ba sharʼanci kawai ya ke nunawa ba, hatta wajabcin hakan yake nunawa ga su matan, saboda umarnin da Annabi (ﷺ) ya bayar, asali kama umurni wajabci ne.” [Salatul Idaini: 15] 


Sunnah ne mata su fita zuwa Sallar Idi, don haka mata ku yi ƙoƙari ku halarci Idi, sannan a kiyaye sanya turare ko bayyanar da wani abu na ado, ku lizimci hijabi na Sharia kuma ku zamto masu natsuwa da kamun kai, sannan a yayin tafiya ku kasance masu bin gefen hanya ba tsakiya ba, kuma ku kiyaye cakuɗuwa da maza, idan kuka kasance haka sai dai ace daku: MASHAA ALLAH.

Thursday, 13 August 2020

ABINDA ZAI RAGE MAKA A DUNIYA BAYAN MUTUWAR KA

ABINDA ZAI RAGE MAKA A DUNIYA BAYAN MUTUWAR KA

Masu Hikima sunce: Mutum kamar Fensir ne, Rayuwa zata ringa feƙe shi yana sake rubutu har yazo ya ƙare.

Abu Biyu A Rayuwar Duniya

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Idan ka mutu babu abunda zai rage sai abunda rayuwarka ta rubuta !!!

ALLAH Ya Sanya Ikhlasi da albarka da alkhairi a cikin dukkan abunda muke rubutawa a rayuwar mu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Monday, 9 March 2020

Matasa Kuyi Yaki da Sharrin Sha'awah

Matasa Kuyi Yaki da Sharrin Sha'awah

Lallai Sha'awah al'amari ne mai rikitarwa wanda yake yawo a tsakanin al'ummah musamman matasa, Sha'awah tana samun galaba ta hanyar taimakon shaiɗan da rundunarsa, amma ALLAH yana kiyaye wanda yaso daga faɗawa daga gare ta.


Sharrin Sha'awa..

MarubuciyaFaridah Bintu Salis

Al-imam Abu-bakr Abdullahi Bn Abiy Shaibah (Rahimahullah) Yace: “Al-amarin sha'awah lamari ne mai hatsari sharrinta mai girma ne, sau da yawa mai bautar ALLAH (SWT) ta maida shi fasiƙi, sau da yawa ta fitar da wasu mutane daga addini waɗanda suka kasance a zahiri ga wanda ya san su sune mafi nesa daga ɓata da karkacewa daga cikin mutane.”  [Musnaf Ibn Abiy Shaibah 4/46]

Sharrin Sha'awah bata bar mai bautar ALLAH ba face sai wanda ALLAH ya tsiratar, balle kuma wanda bai damu da bautar Ubangiji ba.

Wajibi ne ga dukkan  mutane musamman Matasa suyi ƙoƙarin jajircewa wajen yaƙi da Sha'awah wanda ako yaushe mutanen banza ke ƙoƙarin tallatawa al'ummah ita a kafafen sadarwa da tashoshin telebijin ta hanyar kawo fina-finan batsa da yaɗa maganganun batsa domin neman abokan kasancewa a wutar jahannama.

Yana da kyau al'ummah suyi ƙoƙarin kiyaye waɗannan abubuwan :

1. Yawan istighfari  dare da rana.

2. Sallah akan lokaci.

3. Abokai nagari

4. Yawan tilawar alkur'ani.

5. Tuna mutuwa a kowace rana musamman idan kina/kana kallon batsa  kada ya zama aikin ka/ki na ƙarshe a duniya.

6. Ka/Ki sani mai aikata laifi da gan-ganci baya samun yardar ALLAH har a karɓi adduo'in sa.

7. Kallon batsa na jawo zubewar mutunci da rashin kwarjini har kowa ya raina ka a tsane ka a cikin al'umma.

8. Kallon batsa laifin sa kamar zina ne, ai yafi muni ma idan sha'awa tana motsawa yayin kallon.

9. Yayin kallon batsa ana kallon tsiraicin wani ko aji maganar batsa duk haramun ne.

10. Kallon batsa yana jawo sauƙin ayi fasiƙanci da mace don kullum a matse take a aikata abunda take gani da ita.

11. Ana samun cutar tsiro a mahaifa in mace na taso da sha'awa bata samun biyan buƙata, har yakan kawo rashin haihuwa ko cutar daji a mahaifa.

12. Keɓewa a ɓuya ana kallon batsa na haifar da munafurcin zuciya.  Kuma mace ba zata samu miji ba sai mai hali irin na ta haka namiji ma bazai auri mace ba sai mai hali irin nasa.

ALLAH Ya tsare mana imanin mu ya kuma kiyaye mu da dukkan al'ummar musulmai Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tuesday, 25 February 2020

Kada Kayi Bakin Ciki Don Wasu Sun Juya Maka Baya

Kada Kayi Bakin Ciki Don Wasu Sun Juya Maka Baya

Sheikh Sha’araawy ya faɗi wata magana maigirma Yace: “Kada kayi baƙin ciki a lokacin da wasu mutane suka guje ka ko suka canja maka halayen su".

Kada Kayi Baƙin Ciki Don Wani ko Wata Sun Juya Maka Baya..

MarubuciyaFaridah Bintu Salis 

Wataƙila wata addu'a ce da kayi a wani dare kace "Ya ALLAH ka canja min wani sharrin da ka ƙaddaro mini".

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


Friday, 13 March 2020

Shin Ko Kasan Irin Halin da Azzalumai Suke Kasancewa?

Shin Ko Kasan Irin Halin da Azzalumai Suke Kasancewa?

MENE NE ZALUNCI?

Hali ne daga cikin munanan halayen da addini ya ƙyamata, duk wanda ya samu kansa da irin wannan hali haƙiƙa ya haɗu da halayyar da zai kasance dashi wajen ɗebe albarkar rayuwarsa kuma ya dasa masa ƙunci da baƙin ciki, ƙarshe kuma ALLAH yayi masa sakayya da sakamakon abunda ya aikata.

Zalunci Mugun Ciwo

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

KARKASUWAR ZALUNCI

Zalunci kuma ya kasu kashi uku kamar haka:

1. Zalunci tsakanin mutum da ALLAH wanda mafi girman shi shine shirka.

2. Zalunci tsakanin mutum da sauran Halittu sawa'un dabbobi ne ko mutane ta hanyar shiga haƙƙin wani da zalunci ko ta hanyar magana ko aiki.

3. Zalunci tsakanin mutum da kansa ta hanyar aikata wani laifi ko hana kansa wani alheri ta hanyar aikata zunubi.

AYOYI GAME DA ZALUNCI

Ayoyi da hadisai da dama sunyi hani akan wannan hali na zalunci kuma sun tsawatar akan azzalumai daga ciki:

ALLAH (SWT) Yana cewa: “Kuma kada kayi zaton ALLAH mai shagala ne daga abunda azzalumai suke aikatawa, abun sani kawai yana jinƙirta musu ne zuwa ga wani wuni, Wanda idanuwa suke fita turu-turu acikinsa.” [Suratul Ibrahim aya ta 42]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Haƙiƙa ALLAH Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi bazai kuɓuce masa ba.” [Bukhari da Muslim]

Kuma haƙiƙa ALLAH (SWT) Ya La'anci Azzalumai kamar yadda Yazo acikin AL-KUR'ANI MAI GIRMA: “Sai mai sanarwa ya yi yekuwa, cewa: La'anar ALLAH ta tabbata a kan Azzalumai.” [Suratul a'araf aya ta 44]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Kuji tsoron Zalunci domin shi zalunci duhu ne ranar alƙiyama.....” [Muslim Ya ruwaito shi]

Kuma acikin AL-KUR'ANI MAI GIRMA ALLAH (SWT) Yana cewa: “Waɗanda suka yi zalunci da sannu zasu sani wace makoma ce makomar su.” [Suratul Shu'araa aya ta 227]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Kaji tsoron addu'ar abun zalunta, domin ita bata da tsari tsakaninta da ALLAH.” [Bukhari da Muslim].

ABINDA ZAI BIYO BAYAN ZALUNCI

Lallai lokuta da yawa mutum yakan yi yadda yake so ta hanyar zalunci, ya zalunci wanda yaga dama. Sai dai addu'a ɗaya tak ta Wanda aka zalunta ta isa tasa ka rasa komai daka mallaka, domin addu'ar wanda aka zalunta karɓaɓɓiya ce anan (Duniya) ko a can (Lahira).

Wani mai waƙa yake cewa:

لا تظلمن إذا ما كنت مقتدرا , فاظلم آخره يأتيك بالندم

نامت عيونك والمظلوم منتبه , يدعو عليك وعين الله لم تنم.

Ma'ana: " Kada kayi zalinci in ka kasance kana da iko, domin zalunci ƙarshensa nadama zai kawoma.

Idon ka yayi bacci shi kuma wanda ka zalunta yana ankare , yana ma addu'a Idon ALLAH baiyi bacci ba."

KO ZAN IYA TAIMAKAWA AZZALUMI?

Addinin musulunci mai taushi da tausasawa sai mafificin Halitta masoyin mu Annabi Muhammad (ﷺ) Yace: “Ka taimakawa Wanda za'a zalunta koda shi Azzalumi ne. Sai akace masa ta yaya za'a taimaki Azzalumi ??? Sai Yace: "A hana shi yin zalunci wannan shine taimakonsa.” [Sahihu Jamee 2051]

Ya ALLAH kada ka sanya mu cikin Azzalumai, Azzaluman cikin mu Ya ALLAH ka shiryesu su daina, Ya ALLAH ka gafarta mana baki ɗaya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Wednesday, 11 December 2019

ME CE CE KUNYA KUMA TA YA YA AKE GANE MUTUM YANA DA KUNYA ??

ME CE CE KUNYA KUMA TA YA YA AKE GANE MUTUM YANA DA KUNYA ??

Kunya wata ɗabi'a ce daga cikin dabi'un musulunci wanda ake kwadaitar da musulmi na gari ya siffantu da ita.

Ma'anar Kunya...

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

MATSAYIN KUNYA A MUSULUNCI

Kunya a addinin musulunci ɗabi'a ce dake sanya mutum aikata kyawawan ayyuka ababan so ga ma'abocin ta, ta kuma hana shi aikata munanan ayyuka.

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “KUNYA wani rassa ko yanki ne daga cikin Imani.” [Sahihun Nasa'i 5020]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Kunya bata zuwa da komai sai alkhairi.” wani wajen kuma yace: “Kunya dukkanta alkhairi ce.” [Sahihaini]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Lallai ALLAH mai yawan Kunyane kuma mai son suturtawa ne, yana son suturtawa da kunya.”. [Abu-dawud da Nasa'i]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yana cewa: “Yana daga abunda mutane suka riska daga cikin kalaman Annabawan farko, idan baka jin kunya to ka aikata abunda kaga dama.” [Bukhari]

Manzon ALLAH  (ﷺ) Yace: “Lallai kowa ne addini yana da wani hali mai kyau, halin Musulunci shine kunya.” [Muwadda Malik da Sunan Ibn majah]

Ibn Sa'adiy (Rahimahullah) Yana cewa: "Da Kunya ake samun rayuwar imani, wato imani yana rayuwa ne idan akwai kunya acikinsa, da kunya ne bawa yake barin dukkan abunda zai janyo masa zubar da mutumci da matsayi, da kunya ne aka tabbatar da dukkan halaye masu kyau, domin kunya itace tushen dukkan hali mai kyau abun yabo, kuma ita ke korar da dukkan hali mummuna abun zargi.” [Attaudihu wal bayan: 95]

Ibn Uthaymeen (Rahimahullah) Yace: “Kunya wani sifface ko dabi'ace da take sanya mutum ya aikata dukkan abunda zai sanya masa yabo da daukaka da mutunci da matsayi, kuma take hanasa aikata abunda zai zubar masa da matsayi da kima da daraja.” [Sharh Riyadus-saliheen 4/42]

Abu-Tamaam Yace: “Wallahi babu wani alkhairi acikin rayuwa, har ma acikin duniyar baki daya idan kunya ya gushe! Idan har baka tsoron abunda zai je ya dawo, matukar baka da kunya, ka aikata duk abunda kaga dama.”

Ma'anar Kunya...

Wani Magabaci yake cewa: “Duk Wanda kunyarsa tayi Karanci, Toh takatsantsan dinsa zai yi kadan...”

Kunya na da matukar amfani da muhimman ci ga rayuwar dan adam mace ko namiji.

Haƙiƙa mata sune wadanda akafi siffantawa da ɗabi'ar kunya. Sai dai abun takaici ayanzu suna nema su saki wannan ɗabi'a ta kubuce musu a wannan rayuwa badan komai ba sai dan bin rudin duniya da mai halakarwa wato  shaidan.

Ayau mun wayi gari dayawa daga matayen cikinmu da mazajen mu basa jin kunyar Ubangijinsu wajen aikata saɓo kowanne iri ne amma abin takaici zaka samu yana tsoron mutane akan wani aibi nasa.

Hakika rashin kunya alamace ta raunin imani ga ma'abocinta.

Wani daga cikin magabata yana cewa: “imani tsirara yake tufafin sa shine tsoron ALLAH adonsa kuwa shine kunya”

Wani kuma yana cewa: “duk wanda ya mai da tufafin sawarsa ya zamo kunya to mutane baza su ga aibin sa ba.”

Wannan magana tana nusar damu cewa kunya da imani tafiyarsu daya.

IRE-IREN KUNYA: a taƙaice Kunya ta kasu kashi hudu:

1. JIN KUNYAR UBANGIJI: wannan nau'in kunyar shike hana bawa sabawa ubangijinsa. Aduk lokacin da bawa zai aikata mummunan aiki matukar akwai kunya atare dashi to lallai zaiyi gaggawar tuna cewa ALLAH yana ganinsa aduk inda yakasan ce kuma zai tambayeshi akan abunda ya aikata.

2. JIN KUNYAR MALA'IKU: ALLAH (SWT) Yana cewa: “lallai akan ku akwai matsara masu daraja marubuta suna sanin abunda kuke aikatawa.” Ansamu daga sahabbai wani na cewa lallai atare daku akwai wadanda basa rabuwa daku saboda haka kuji kunyar su ku girmama su.

3. JIN KUNYAR MUTANE: Huzaifa bin yaman (RA) yana cewa:  “Babu alkairi ga wanda baiji kunyar mutane ba. Ashe yan uwa kunya alkairi ce.”

MAKALOLI MASU ALAKA:

SHIN KO KASAN ZA KA IYA SABAWA ALLAH AMMA DA SHARUDA GUDA BIYAR?

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

CIKIN WADANNAN MUTANE WANNE IRIN ABOKI NE DA KAI ?

4. JIN KUNYAR KAI: aduk lokacin da mutum zai aikata mummunan aiki dazarar yatuna Ubangijinsa kuma yaji kunyar kansa to lallai zuciyar sa zata nutsu kuma ta tsoraci ALLAH ta hana shi aikata mummuna tayi masa umarni da kyakkyawan aiki.

ALLAH Yasa mu kasance cikin salihan bayi ma'abota jin kunya a duk inda addinin ALLAH yayi mana iyaka (Ameen).

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Saturday, 16 November 2019

Karanta Muhimman Abubuwan da Yakamata Ku sani Kafin ku Fara yin Taimako

Karanta Muhimman Abubuwan da Yakamata Ku sani Kafin ku Fara yin Taimako

TAIMAKO baiwace mai matukar tsada wanda ba kowa bane ALLAH yake bashi ikon taimakawa ba domin ba kowa ne yake da arzikin wadatar zuci ba.

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Sau da dama aduk sanda aka ambaci wannan kalma ta Taimako mafi yawan tunanin mutane yafi karkata zuwa ga neman wani abu musamman na daga arzikin dukiya wato kudi.

Sai dai abun ba haka yake ba hanyoyin Taimako suna da yawa, bawai kawai ka bawa mutum kudi shine ka taimaka masa ba. Kada kayi tunanin baka da hanyar taimakawa dan'uwanka musulmi saboda ka kasance daga cikin matalauta, ka sani cewa bada Dukiya (kudi) kawai ake taimako ba.

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Akwai hanyoyi da yawa daga ciki:

1. Kana iya taimakawa dan'uwanka ta hanyar karfi da lafiya da ALLAH ya wadata ka dashi.

2. Kana iya taimakawa dan'uwanka ta hanyar ilimin da ALLAH ya hore maka walau kai malami ne ko dalibi ne ko likita ne koma dai wani fanni ALLAH ya baka ikon fahimta zaka iya bada taimako dashi.

3. Kana iya taimakawa dan'uwanka ta hanyar addu'a musamman wacce kayita ba tare da ya sani ba. Ni a ganina ma wannan itace koluluwar gaba mafi girma domin idan ALLAH Ya amsa addu'ar da kayiwa dan'uwanka yafi masa daraja sama da bashi wannan duniyar da abunda ke cikinta.

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Akwai abubuwa da yawa wanda bawa zai iya taimakawa dan'uwansa dashi bawai sai da dukiya (kudi) kawai ba.

Acikin Al-Qur'ani Maigirma ALLAH (SWT) Yace: 

ﻭَﺗَﻌَﺎﻭَﻧُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺒِﺮِّ ﻭَﺍﻟﺘَّﻘْﻮَﻯ ﻭَﻻ ﺗَﻌَﺎﻭَﻧُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻹِﺛْﻢِ ﻭَﺍﻟْﻌُﺪْﻭَﺍﻥِ ﻭَﺍﺗَّﻘُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺷَﺪِﻳﺪُ ﺍﻟْﻌِﻘَﺎﺏ

“Kuma ku taimaki juna akan aikin kwarai da takawa, kuma kada ku taimaki juna akan zunubi da zalunci, kuma kubi ALLAH da takawa, lallai ne ALLAH mai tsananin ukuba ne.” [Ma'idah: 02].

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Wannan ayar ta kara fito mana da cewar bawai Dukiya (Kudi) dashi kawai ake taimako ba, balle daga an ambaci taimako ka zumbura baki saboda kana tunanin zaka bada taimakon kudi dukiyarka zata ragu. Akwai mutanen da suka daina Ziyartar masallatai da wuraren wa'azi wai don kawai ana ambaton neman taimako.

Shi fa taimakon nan ba ace dole sai ka bayar ba idan kana dashi ka bayar idan baka dashi kayi addu'a.

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Duk wanda ya samu wata dama daga cikinku da zai amfanar da dan'uwansa, to ya aikata.”

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Akwai Hadisai da dama da suka yi magana akan Falalar da mutum yake samu idan ya kasance yana Taimakon dan'uwansa daga ciki:

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Lallai ALLAH yana cikin taimakon bawa matukar bawa yana cikin taimakon dan'uwansa.” [Muslim].

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Mafi aikin alkhairi a wajan ALLAH, shine sanya dan'uwanka cikin farin ciki ko ka biya masa bashi ko ka ciyar da shi abinci.” [Sahihul-Jamee].
Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Ashe sanya dan'uwanka farin ciki shima taimako ne, hakanan akwai hadisin da ya tabbata cewa yiwa dan'uwanka murmushi ma sadaka ne.

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Duk wanda ya taimaki wanda yake cikin kunci, ko ya dauke masa wani nauyi da yake akansa, ALLAH zai sanya shi a inuwarsa, a ranar da babu inuwa sai Inuwarsa.” [Sahihul-Jamii].

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Dukkan wanda ya saukakawa wanda yake cikin kunci, shima ALLAH zai saukaka masa anan duniya da Lahira.” [Sahihul-Jamii].

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Ashe saukakawa dan'uwanka game da wani kunci da yake ciki shima taimako ne, Hakika akwai hadisai da dama da suka yi magana game da falalar da mutum yake samu ta hanyar taimakawa dan'uwansa musulmi.

Don haka mu sani ba wai ta hanyar Dukiya ce kadai ake taimakawa ba, akwai hanyoyi da yawa kuma muyi kokari wajen taimakawa junan mu ta hanyoyin da zai amfani junan mu bisa tafarkin ALLAH (SWT).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Amfanin Sada Zumunta Guda 20

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

KARANTA FA'IDODIN SADAKAH GUDA TALATIN DA UKU 33

Wadanda suke kokari wajen taimakon bayin ALLAH ta hanyar dukiyarsu da ilimin su da lokacin su da duk wata hanyar dama da ALLAH ya basu, ALLAH Ya saka musu da alkhairi (Ameen).

ALLAH Ya sanya mu cikin bayinsa masu taimakon Junansu, ALLAH ya bamu ikon kyautatawa da amfanarwa (Ameen).

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Tuesday, 4 August 2020

Karanta Muhimman Abubuwan Da Yakamata Ku Sani Kafin Ku Fara Yin Layya

Karanta Muhimman Abubuwan Da Yakamata Ku Sani Kafin Ku Fara Yin Layya

Lallai bayani dangane da Layya tana da faɗi sosai amma zamu taƙaita a taƙaice.

Bayani Akan Layya

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

LAYYA: ita ce dabbar da ake yankewa domin neman yardar ALLAH daga cikin nau'o'in Tumaki da Awaki da Shanu da Raƙuma waɗanda suka cika shekarun yin layya, kuma sun kuɓuta daga kowane aibi.

An sharɗanta yanke dabbar layya a ranar goma ga watan Zu-lhijjah da yini biyu masu bi mashi, bayan dawowa daga sallar idi, bayan kuma Liman ya yanke. [Fawakihud-dawaniy 1/440].

Sheikh Abubakar Jabir Al-Jaza'iriy ya faɗa acikin littafinsa mai suna [Minhajul Muslim] Yace: LAYYA wata dabba ce wadda ake yankewa ranar idi domin neman yardar ALLAH, ana yin ta ne don raya sunnar Annabi Ibrahim (A.S) domin ALLAH yayi wahayi zuwa gare shi da ya yanke ɗanshi Isma'eel (A.S), sannan kuma ya fanshe shi da Rago, ya yanke shi a madadinsa.

Kamar Yadda yazo acikin Alƙur'ani ALLAH (S.W.T) Yace:

ﻭَﻓَﺪَﻳْﻨَﺎﻩُ ﺑِﺬِﺑْﺢٍ ﻋَﻈِﻴﻢٍ

Ma'ana: "Kuma mun fanshe shi da abun yanka Maigirma." [Suratul Saffat aya ta 107].

Kuma an tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) akace masa: Mene ne matsayin wannan LAYYA??? Sai yace: Sunnar Babanku ce Ibrahim (A.S). [Minhajul Muslim].

LAYYA sunnah ce ta Manzon ALLAH ( ﷺ) kuma ya kwaɗaitar da yinta ga Al'ummarsa kuma ya tsoratar ga barin yinta ga wanda ya samu iko da dama.

Manzon ALLAH (ﷺ ) Yace: “Wanda yake da wadata, kuma bai yi Layya ba, to kada ya kusanci (Filin Sallar) Idin Mu.” [Sahihul Jamii 6490].

Wasu daga cikin maganganun Magabata dangane da LAYYA:

Layya sunnah ce ba wajibi bace. [Bn baaz da Bn uthaimeen].

Layya ta halatta mutum da iyalansa da duk wanda yasa (musulmi) a cikin layyar tare dashi [Bn uthaimeen Rahimahullah].

Iyalai guda layya guda ta wadatar dasu, koda mutum yana da 'ya'ya masu aiki kuma suna da aure ana basu albashi, da sharaɗin cewa abincinsu da abin shansu gudane; ma'ana wajen dahuwar abincin guda ɗaya ne, amma idan kowanne daga cikinsu yana da wajen dahuwarsa daban to layyarsa ta saɓa da layyar sauran. [Bn uthaimeen ].

Wanda zai yanka layyar shine Wanda yake ɗauke da nauyin gidan; Uba ko Miji ko Babban Ɗa ko Babban Yaya. [Bn uthaimeen Rahimahullah].

Mace layya bata lizimceta ba, tana shigane cikin ta namiji, Uba ko Miji ko Ɗa ko Ɗan Uwa, amma da zatayi nufin zatayi layya tana da damar yin haka, sai ta hanu daga cire gashinta da farcenta kamar namiji. [Bn uthaimeen Rahimahullah].

Ya halatta ga macce tayi layya [Bn uthaimeen Rahimahullah].

Yin layya ga mamaci tana da hali guda uku, ga maganar Bn uthaimeen:

HALI NA FARKO: Mamacin da yayi wasiya cewa amai layya to sai amai a zartar da wasiyarsa.

HALI NA BIYU: Rayayye yayi wa kansa layya sai yayi niyar shigar da mamacin aciki tare dashi wannan ya halatta.

HALI NA UKU: Mutum yayi Wa mamaci layya sai dai abinda yafi kar ayi saboda Manzon ALLAH baffansa ya mutu matar sama ta mutu amma baiyi musu layya ba.

Mutum yasamu yaci bashi dan yayi layya matuƙar yana saran samun ikon biyan bashin. [Bn baaz da Bn uthaimeen].

Bayani Akan Layya

Layya da shanuwa ko raƙumi ana iya yin haɗaka mutum bakwai amma tunkiya ba'a haɗaka acikinta. [Bn uthaimeen Rahimahullah].

Abunda yafi kada mutum yayi layya da Rago sama da ɗaya. [Bn uthaimeen Rahimahullah].

Mai aikin hajji baya layya sai dai zai iya barma iyalansa kuɗi don su sayi abin layya su yanka wa Kansu shi kuma yayanka hadaya a Makkah bazaiyi layya ba. [Bn uthaimeen Rahimahullah].

Ya halatta ga mai aikin hajjin da yayi nufin layya ya yankata a Makkah. [Bn baaz Rahimahullah].

Ba'a layya sai da dabbobin ni'ima raƙumi, shanuwa da tumakai, dole dabbar layya takai shekarun da aka iyakance ashari'a:

1. Raƙumi biyar
2. Shanuwa biyu
3. Tunkiya wata shida
4. Akuya shekara ɗaya

lokacin da shari'a ta iyakance ayi yanka shine bayan sallar idi har zuwa kiran sallar magrib akwana na uku ga sallah " [Bn uthaimeen].

Layya ba tayi har sai in dabbar ta kuɓuta daga aibi. [Bn uthaimeen Rahimahullah].

Wannan a taƙaice kenan daga maganganun da suka keɓanci Layya.

Manzon ALLAH (ﷺ ) Yace: “Lallai ALLAH Ya hukunta kyautatawa akan komai, idan zaku yi kisa ku kyautata kisarku, idan zaku yi Yanka Ku kyautata abun yankawarku, kuma ɗayanku ya wasa wuƙarsa ya hutar da abun yankawarsa.” [Muslim].

Addu'ar da ake yi idan za'a Yanka dabba:

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻨﻲ

"BISMILLAHI WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMA MINKA WA LAKA, ALLAHUMMA TAQABBAL MINNI".

Ma'ana: “Da sunan ALLAH, kuma ALLAH ne Mafi Girma, Ya ALLAH (wannan Dabba) daga gareka take kuma mallakar kace, Ya ALLAH ka karɓa daga gare ni.” [Muslim 3/1557, Baihaqiy 9/287].

ALLAH Ya bamu iko da dama Ya kuma amsa mana dukkan Ibadun mu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.